← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 120

Sashe 102

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune take ta haɗa kanta da gwiwa kana kallon ta zaka san cewa cikkakiyar kafura ce,jin motsin da tayi ne yasata ɗagowa da sauri,wata irin zabura tayi ganin Abdallah wanda bata taɓa tsammanin gani a daidai wan nan lokaci ba, cikin rawar harshe ta kira sunan da tafi ƙware wa da faɗarsa, Fatash!'wani irin mummunan kallo ya shiga watsa mata,yayin da Bintu ma ta kuma bude idanun ta jin sunan da aka kira Abdallahn ta dashi, cikin tsanar sunan da wadda ta ƙirƙiri sunan yace"ba tun yauba kuma batun yanzu ba nake miki jan kunne akan kirana da sunan kafirai,yanzu kina cikin tarkona ne,dan haka idan na kuma jin wannan baƙin sunan a bakin ki sai na zubda hakoranki gaba ɗaya!'shuru tayi tana kallon sa babu abinda ya sauya daga halayyar dayake nuna mata tun asali,zama yayi ya turawa Bintu kujera itama dan ta zauna, amma sai ta kasa zama ita kawai so take tasan wani abu akan matar nan da kuma sunan da ta ambacesa dashi,gane hakan da yayi ne yasa yayi mata banza,ba tare da yakuma duban inda take ba,ya juya kan Abigirl wadda tayi tsumu- tsumu da ita,tabbas ta daɗe tana fargabar wannan rana da Abdallah zai zo ya tutsiyeta dan sanin abinda take ta ɓoyewa tsawan shekaru,kallon da yake mata yasa ta kuma rikicewa duk ta rasa wata nutsuwa, zuciyar ta cike take da tsoron Abdallah da irin hukun cin da zai yi mata,dan ta san tunda ya rutsata dole sai ta faɗa masa asalin labarin ko taki ko taso, Abigirl yadda ya kira sunan ma kansa abin firgici ne,dan hatta da Bintu dake tsaye idanun ta kan Abigirl ɗin sai da ta juyo ta dubeshi,fuskar nan babu alamun wasa ko wani annurin dake nuna zaiyi sassauci A al'amarin sa da Abigirl ɗin, cikin ƙara kiɗimata da sautin muryarsa yace"waye yabaki Ni kuma a wane dalilin sannan da wace manufa aka bakini?zatayi magana ya dakatar da ita,da hannun sa tare da cewa ba yanzu nake buƙatar amsarki ko musuntawarki ba,ina miki tambayar ne dan ki shirya amsata agaban dimbin jama'a da kuma wadda ko wanda yasaki aita aikin da zai zamo miki danasi wanda Hausawa suke kira da ƙeya,ina mai tabbatar miki da cewa duk ranar da nazo dan karɓar amsar tambayoyina ki kayi min gardama to wallahi sai kin gane kurenki sai kin gwammaci baki zo duniyar ba,dan haka ki shirya zuwa cikin ESTATE dan fallasa sirrin da kike ta sirrintawa tsawon waɗan nan shekarun!'daga haka ya mike tare da hanƙada kujerar da ya tashi akai zuwa fuskar Abigirl,wanda badan tayi saurin kaucewa ba da tuni ya cire mata wani abun daga sassan fuskarta.

Binsa Bintu tayi ganin ya fita, zuciyar ta cike da tunanin ko ita wannan wacece kuma,tana da tarin tambayoyin da take son yi masa amma yaƙi bata damar hakan,ko meye dalilin sa na hana ta tambayar sa kuma oho?bayan ita duk abinda ya tambayeta tana amsa mashi dai dai da abinda yake son sani,ji tayi wani haushinsa ya kamata tare da kewar fafinta,ko wane hali suke ciki, yace" ta kwantar da hankalin ta zai kawo mata ummin ta da fafi amma har yanzu shuru ko maganar ma bayayi,sai ma can wasu al'amura da yakeyi wanda bata gane musu ba,wani kuka taji yana taho mata wanda hakan yasa ta saka hannun ta ta toshe bakinta,juyowa yayi tare da zuba mata ido sai dai baice komai ba,cikin kallon nata ya fahimci damuwarta da kuma dalilin kukanta,ji yayi jikin shi ya mutu tare da wani irin tausayinta ya kan rasa meke damun shi akan Bint indai lamari akanta ne bashi da wani sukuni ko pawer, hakan yasa ya jawota jikin sa suka ci-gaba da takawa har zuwa bakin motar su,da sauri Yahya ya buɗe musu suka shiga,shi kuma ya zaga ya shiga mazaunin drever,sai da suka fara tafiya kana ya ɗago fuskarta dake kwance kan kafaɗar sa,zaro oily eyes ɗinsa yayi cikin san kawar mata da damuwarta,yace"me yafaru da idanunki haka wannan ai sai ki bani tsoro!'sai ya ɗan rufe idan sa alamun wai baya son gani tana bashi tsoro,sanin tsokanarta yake da kuma yadda yayi da fuskarshi sai hakan ya bata dariya,ga kuma tsananin mamakin yadda yake mata wanda tasan da wannan duk ba halinsa bane,amma yanzu wai duk dan yasata farinciki yake yin abinda bai saba dashi ba,ganin hakoranta sai ya samu kansa da samun nutsuwa har shima ya saki wani ɗan ƙawattacen murmushi da ya ƙawata kyawunshi da kwarjinin shi,wanda har bata san da ta zubawa fuskar tashi idanu ba,ɗan gemunshi dake matuƙar burgeta ta mai da hankali wajen kalla,ji tayi yace"kinaso ne?da sauri ta maida kanta ta ɓoye a ƙirjinshi saboda kunyar da taji ta rufeta, cikin taushin murya yace"Bint kiyi haƙuri Ina sane da abinda nakeyi na kusa cika miki burinki,ki ɗauka tamkar kina tare da Ummi da fafi ne,kinji ko bana son ganin damuwa akan fuskarki!'ya faɗa yana jan lafiyayyan kumatun ta,A hankali tace"to ya Abdallah ka kaini naga Dady mana dan Allah!'zan kaiki shike nan?

Ɗan ƙif-ƙif tayi da idanun ta kana cikin sanyin murya tace"wacece wannan matar da take kiranka da wani suna?kawar da kanshi yayi sam baya san abinda zai dan gantashi da wannan kafurar matar,yace"matar da ta riƙeni ce!'wata irin zabura tayi tana kallon sa cike da mamaki,ganin yaƙi kallonta sai ta ɗan langaɓar da kanta bisa kafadunshi tare da cewa,ayya to meyasa zaka kawota nan?ko itama tasan wani abu game da barinka gida?sai da tayi wannan tambayar ya juyo da fuskarsa inda take,yace"inye kaga yarinya tayi gadon basira,tayi tambaya ta bawa kanta amsa kuma!'dariya tayi wanda saida fararan haƙoran ta suka baiyana,haka nan takejin wani irin nishadi da farinciki duk lokacin da ta kasance da oganta Abdallah, bare yanzu da yake ririta farincikin ta yake gudun damuwar ta yake neman duk wani abun da zai cire kunci a zuciyarta ga shi kuma ta gama fahimtar halayyar sa tsaf sai ɗan abinda ba arasaba,yace"Bint zakisan abinda ya faru dani da kuma irin rayuwar da nayi tare da wannan kafurar matar,amma sai agaban dukkan ahlinmu, acikin falon Alhaji Baba,tare da Dady da Ummi da fafy,da kowa da kowa da yake buƙatar sanin rayuwar da mukayi Abaya!'jinjina masa kai tayi cike da gamsuwa da bayanin sa,daga nan kai tsaye gidan malam suka nufa.

Baƙaramin farinciki sukayi ba ganin yadda aka samu ci gaba a lafiyar Dady Abubakar,sosai yake samun kulawa a gurin malam da sauran ɗaliban sa,duk da dai yana kwance har yanzu bai buɗe ido ba, amma tsaf yake tamkar idanun sa biyu,Bintu ce ta matso kusa dashi tare ɗora hannun ta kan hannun sa ta riƙe a hankali ta shiga karanto addu'oin samun sauƙi gareshi,tanayi tana tofa masa asaman kansa da idanun sa, Abdallah kuma magana suke da malam dan haka sai hankalinsa ya rabu biyu,kamar almara Bintu taga hannun da tarike yana motsawa,nutsuwa tayi tare da zubawa hannun ido dan tana son gasgata abunda idanunta suka gani,ganin bai kuma motsawa ba sai ta dawo da kallon ta kan kyakkyawar fuskarsa wadda asalinta da kwarjinin ta suka bayyana,zubawa fatar idonsa ido tayi saboda ganin kamar tana motsawa,tabbas kuwa ba gizo idanunta kemata ba,kafin tayi wani abu kuwa sai ga idon Dady Abubakar akanta ya buɗe su fes yana kallon ta,wata irin zabura tayi tare da sakin kuka da kabbara duk alokaci ɗaya,wanda hakan yasa malam da Abdallah suka zaburo zuwa inda take, Abdallah jikin sa na rawa yake tambayar ta lafiya?kafin ta bashi amsa ya hango amsar da idanunsa,ɗurƙushewa yayi gaban gadon da Dady yake kai kusa da Bintu,yayin da malam yake ta kabbara tare da hailala, Bintu kuwa cikin wani irin yanayi na tsantsan farinciki take cewa Alhamdulillah masha Allah,Dady kana gani? kayi magana ga Ya Abdallah ga kuma Ni Bintu ɗiyarka ɗiyar ɗan uwanka Abbana Umar!cak taga ya tsaida ƙwayar idanun sa akanta,yana mata wani irin kallo, Abdallah kuwa kwantar da kanshi yayi jikin Dady yana fidda wani sassanyan murmushi wanda yake fitowa tun daga asalin zuciyarsa,A hankali Dady ya shiga jan hannunsa cikin nutsuwa da rashin ƙwarin jiki ya ɗora bisa kan Abdallah yana shafawa wanda hakan ya kuma jefa BINTU cikin wani irin shauƙi jin farin ciki take har ƙoƙon ranta,sai kuma taji wasu hawaye masu ɗumi suna gangarowa kan fuskarta,sha awar Dady da Abdallah taji ta mamaye ta,ina ma itama zata ganta jikin Abbanta yana shafa kanta cikin so da ƙauna,tunanin tane ya katse lokacin da taji Muryar Dady duk da ba fita take sosai ba amma zaka fahimci abinda yake cewa,yace"tashi ka bawa ɗiyata gurin ta ba kanka naso na fara taɓawa ba kanta ne saboda itace bata taɓa jin ɗumina ba bata taɓa zama tare dani ba,ba ta taɓa yin wasa dani ba,kai kuwa ka hau jikina kafin azzalumai su rabamu,kayi wasa dani kafin mu rabu kuma kaci abinci dani,dan haka matsawa ɗiyata ta fara samun nata gatan tun yanzu kafin Allah Ubangiji ya bani ikon miƙewa gaba ɗaya na nuna mata gatan da babu wata diya da ta taɓa samun shi a cikin duniyar mu!'wani irin kuka ne ya ƙwacewa Bintu mai haɗe da wani irin shauƙi da jin ta yau tacika ƴa, ƴar gata,waɗawa jikin sa tayi shi kuma yasa hannu a gadon bayanta yana bubbugawa cike da san rarrashinta,ko Ni tunda nake ban taɓa ganin dariyar Abdallah da hawaye ba sai yau,jarumtar shi ta ƙare ba zai iya jurewa ba,farinciki tare da tausayin su baki ɗaya da kuma kalaman Dady suka saka shi hawaye,malam ma sai da ya share hawayen tausayin waɗan nan bayin Allah,shi tun da yake arayuwar sa bai taɓa cin karo da abin mamaki da tausayi ba kamar labarin bayin Allah nan, Allah ka ƙaremu daga makircin shaidan kayi mana tsari da faɗawa halaka,a hankali Bintu ta ɗago kanta kana tace"Dady na ina son ka,dama haka kasancewa da uba yake? dama haka waɗan da suke tare da iyayensu sukeji? murmushi kawai Dady yakeyi kana yace" fiyema da haka suke ji kema zakiji fiye da haka tukun na dai Allah ya bamu aran lokaci!'amin suka amsa, Abdallah cikin marairaice fuska yace"tunda abun wariyace,nima yanzu zanje na nunawa Abbana ɗan sa da ya daɗe yana bege sai kowa ya riƙe nashi!'dariya sukayi baki daya cikin tsananin farin cikin da ya mamayesu a wannan rana mai ɗinbin tarihi.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*
Chapter 102 · 0% Book details