Sashe 38
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washe gari Bintu garau ta ta tashi (yarinya taji hannun likitoci,)ko da ta farka banɗaki ta shiga tayi wanka tare da brosh,tana fitowa kuma taci karo da haɗaɗɗiyar doguwar riga A kan gado,dan haka ta shirya A nutse kana ta ɗauki rigar ta saka,masha Allah tubarakalla maƙi gani ya kau da ido tabbas Bintu kyakykyawar yarinya ce ta ajin farko Allah Ubangiji ya hore mata ƙira mai kyau da jan hankali duk sutturar da tasaka sai kaji kamar ka saceta,turarukan da ta gani ta ɗauka ta feshe jikinta dasu kana ta nufi bakin ƙofar da nufin fita,tana ɗora hannun ta kan mariƙin ƙofar, taji ana ƙonƙosawa A hankali,dan haka kawai sai ta ƙara sa buɗewa,wani irin wal hasken fatar sa ya haske mata idanuwa,babu shiri ta shiga rage girman idanuwanta A kan sa,yayi matuƙar kyau cikin shigarsa ta ƙananan kaya fuskar sa sai fitar da wani haske take da kwarjinin sa, ganin ta shirya kawai sai ya juya batare da yace mata komai ba,da sauri ta bi bayansa dan tasan tafiya gida zasuyi maganar ce dai ba zai iya ba saboda tana masa wahala.
A can asibiti kuwa Sayyid ya samu farfaɗowa, Dady Mansur kuwa ba tare da wani jinkiri ba yashi ga watsawa ɗan nasa tambayoyi A kan wanda yaso kashe masa shi,gyara zama Sayyid yayi ya shiga sheƙa musu karya abinda ya faru da ban abin da ya faɗa musu da ban, Dady Mansur ya miƙe A matuƙar fusace yace" kai tashi mu tafi gida ai banga ta zama ba,ashe da ɗan ta adda muke rayuwa bamu sani ba!'batare da ya jira sallama ba ya tasa ƙeyarsu sai estate.
Kamar tare suke lokaci ɗaya sukayi pakin suka fito gaba ɗayansu,Bintu tana arba da Sayyid kuwa ta zunduma wani uban ihu tare da komawa bayan Abdallah ta ruƙunƙumeshi,so sai fa Bintu ta firgita da ganin Sayyid dan A haƙiƙanin gaskiya ya dasa mata mugun tsoron sa,wani mugun kallo Abdallah ya shiga aika musu gaba ɗayansu kamar yadda Dady Mansur yake auna masa nasa mugun kallon tamkar idanun sa zasu waɗo, A hankali ya juyo da ita gaban sa tare da saka yatsansa guda ya ɗauke mata hawayen da suke ta gudu kan kyakykyawar fuskarta,cikin nutsuwa yace" mata, ke ki nutsu babu abinda zai sameki ina tare da ke!' daga haka ya janyo hannun ta suka wuce su Dady Mansur sake da baki,ɗaga murya yayi yace" Ni ba sa anka bane wannan maganar bazan ƙyale ta ba tunda ba jaki kasamu ba anjima kuzo falon Alhaji Baba kai da kilakin taka!'ko juyowa Abdallah baiyi ba balle yasa ran cewa yaji abinda yace masa,fuuu ya ja hannun Sayyid mama ta mara masa baya.
Tunda suka shiga falon babu abinda Taufiƙa ke yi sai kallon hannayen su da suke saƙale dana juna,ji take tamkar ta kashe Bintu kowa ma ya huta, lokaci yayi da ya kamata tayi wani abu akan Soyayyar Abdallah,inno kuwa kasa ɓoye murnar ta tayi, sai da ta rugumo Bintu jikinta tana mai tsananin nuna farin cikin ta,kan ta kai ga cewa wani abu wayar Abdallah tayi ƙara ɗagawa yayi cikin nutsuwa,ɗan jim yayi kana yace" to yanzu zamuzo insha Allah!'kallon inno yayi yace" Alhaji Baba ne yake kiran mu gaba ɗaya!'tace"har dani kenan!'Taufiƙa yaga tana ƙoƙarin miƙewa, batare da ya dubeta ba yace" ban daku"daga haka yay tafiyarsa,inno ta ja hannun Bintu suka nufi part ɗin Alhaji Baba,yayin da su Taufiƙa suka bisu da wani mugun kallo tamkar zasu gaɗo da ƙwayar idanuwan su,Taufiƙa tayi wata ƙwafa mai cike da fassarori.
AlÆ™alaminâœðŸ½
Fatimah y Adam
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 27 ```
Bayan ALHAJI BALARABE sai matansa da kuma yaransa maza wanda abin ya shafa Dady Mansur sai Dady Habib sai kuma Abba Hassan da bai jima da dawowa daga itali ba, shi kuwa dama Abba Aliyu ba A ƙasar yake ba yana can gana tare da iyalansa,sai dai yana yawan zuwa,sai kuma uban gayya Oga Abdallah da Bintu da Sayyid sai Dady jafar, dukkanin su sun nutsu suna sauraran Alhaji Baba da yafara magana cikin kamilalliyar muryarsa mai cike da hikimar zance,yace" Abdallah muna sauraren ka ka gaya mana abin da Sayyid yayi har kayi masa hukunci!'Dady Mansur da ya kasa jurewa ya ɗan zaburo yace" haba Baba,hukunci ko zalunci? wani kallo Alhaji Baba ya watsa masa wanda babu shiri ya kama bakinsa sai dai sam ransa bai gamsu da wannan salon tambayar ba,
ÆŠan sunkuyar da kansa Abdallah yayi kana cikin taushin Muryar sa mai daÉ—in sauraro yace" Alhaji Baba bani ya kamata na fara magana ba wadda abin ya faru akan ta ita zata faÉ—a mana yadda ko mai ya kasance!'Dady Habib yace"hakane maganarka to ke muna saurarnki!' ya juya maganarsa ga Bintu,
cikin sanyin murya da kuma tsoron kallon da Sayyid yake ta aika mata ta buɗe baki tare da basu labarin abinda ya faru har zuwa lokacin da Abdallah yazo ya taimaketa daga hannun Sayyid,runtse idanu Alhaji Baba yayi,kana cikin rawar murya irin ta wanda yake cikin tsananin ɓaci rai yace" A cikin zuriya ta akasamu mazinaci? kaicona rayuwa baki da tabbas yanzu Sayyid kaine kake ƙoƙarin farma yarinya ƙarama marainiyar Allah?shiru yayi gami da sunkuyar da kansa ƙasa wanda shi ƙadai yasan irin takaicin da ke ƙunshe cikin zuciyarsa,Dady Mansur ya miƙe tsaye cikin yanayinsa na hargagi da rashin yin ko mai cikin nutsuwa yace" wallahi baku isah ba,kunyi kaɗan kuyiwa yarona ƙazafi, Sayyid ba mazinaci bane sai dai idan kune mazinata!'wata gigitacciyar tsawa Hajjah tayi masa tare da cewa kai me yasa baka da nutsuwa ne iye Mansur? me yasa kullum girma kake amma hankalinka yana da ɗa komawa na yara?bazaka dinga girmama mahaifinka ba yana magana kanayi duk cikin ƙannen ka gasu nan kaji wani yayi magana yayin da mahaifinsu yake magana? to akul ina yi maka gargaɗi akan wannan banzar ɗabi ar taka idan baka gyara ba zanyi mummunan saɓa maka!' ta dire maganar tana mai watsa masa kallon baƙin ciki,komawa yayi ya zauna dan duk abinsa yana shakkar mahaifiyar tasu tana da san mutane da jansu ajiki amma sam bata yadda da raini ba ko kaɗan bata ɗaukar sa,
Tsit falon yayi suna jiran jin ta bakin Alhaji Baba,can dai ya ɗago kansa fuskarsa babu wasa ya dubi inda Sayyid yake a zaune fuska duk A kunbure,yace" Sayyid abinda yarinyar nan ta faɗa hakane?cikin in ina ya fara ƙoƙarin kare kansa,amma hakan bata samu ba saboda mugun kallon da Oga Abdallah ya watsa masa mai cike da gargaɗi,ai Sayyid bai san sanda ya saki baki ya gaskata zan cen Bintu ba, Dady Habib ne ya zuba masa ido cike da mamakin sa, Abba Hassan ma kawar da fuskar sa yayi dan baya son cewa komai saboda halin yayan nasu,inno ce tace"gaskiya Sayyid baka kyauta ba na rasa Abin da Bintu tayi muku kuke neman hana ta zaman lafiya ba, gaskiya banji daɗin wannan abuba!' Hajjah kuwa ƙwafa tayi tare da cewa aini Abdallah baka burgeni ba da har kayi masa dukan da ya tashi A kwana ɗaya, aikamata yayi ace har yanzu bai san inda kansa yake ba!'Hajiya Babba kuwa Bintu take ta kallo yayinda can cikin zuciyarta take wasu irin saƙe saƙe,me yasa ake bin yarinyar nan da sharri ka kala kala ne? anya kuwa babu wani abu aƙasa amma dai zata ci gaba da yiwa Bintu addu'ar kariya, Dady jafar ne ya danyi gyaran murya kana yace"Alhaji Baba kayi haƙuri yaran ne na yanzu sai dai addu'a kawai, babu tsumi ba daabara duk abinda Ubangiji ya rubuto to tabbas babu makawa sai ya faru,yanzu kawai jan kunne za ayiwa shi Sayyid babu shi babu Bintu!'da sauri Sayyid ya matsa gaban Alhaji Baba cikin nuna na damar sa yace" dan Allah kayi haƙuri wallahi ba halina bane sharrin shaidan ne kuma insha Allah hakan baza ta kuma faruwa ba,amma dan Allah ina rokon ku wata alfarma!'duk zuba masa ido sukayi kana Alhaji Baba yace" wace alfarma kake so muyi maka? ƙara matsawa kusa da Alhaji Baba yayi kana ya riƙe hannayen sa duka biyun cikin ƙanƙar da kai yace"alfarmar ita ce ina so a bani auren Bintu!'
Shiru falon ya kuma ɗauka baka jin sautin komai sai na bugun zuciyoyi,shi kuwa Sayyid cigaba yayi da cewa dan Allah Alhaji Baba ka auramin ita wallahi santa nakeyi da gaske,zan riƙe maka ita amana ka taimaka ka bani auren ta!'yadda yake maganar babu yadda zakayi ka fahimci ainahin zuciyarsa,dan haka ko Ni ban san me Sayyid yake ciki ba a halin yanzu shin da gaske yake san Bintu yake ko kuma wani salon ne ya fito dashi na daban? wannan dai dole sai mun bibiyi Malam Sayyid tukun zamu sani.