Sashe 18
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Baba ne zaune shida Abdallah yana yi masa bayanin fadima da ainihin labarinta da inno ta gaya masa,da kuma irin hukuncin da ya yanke akan zaman nata, shi dai Abdallah ya amsa masa ne kawai batare da ɗaukar zancen da wani muhimmanci ba, sai dai jin cewar daga cikin estate din aka kawota dan yi masa aikin abinci, yasa yaji wani Abu can ƙasar zuciyarsa me kama da rashin yarda,duk da baisan wacece ainahin Anty nafisan ba, cikin salon maganarsa ta muskilanci da ɗaukar hankali yace" Baba Alhaji shikenan tunda ka gamsu da ita bani da matsala sai dai inaso ka haɗa ita yarinyar da dady dan ya gaya mata tsarina!'Alhaji Baba yayi murmushi irin nasu na manya, kana yace"a'a Abdallah basai na tambaye shi ba nasan abinda kake da damuwa dashi, ba dai hayaniya bane bakaso ita ma yarinyar bata da hayaniya dan abinda na fara dubawa kenan na tabbatar zaka amince da zamanta dan haka baka da damuwa da wannan, hatta da list ɗin Abincin da kake ci da lokacin da kake cinsu, da haɗin copy duk an sanar da ita fatana na gaba kawai Allah ya sa Abincin yayi maka!'jinjina kansa yayi kana ya miƙe cikin takunsa na ƙasaita da nutsuwa ya fita daga falon.
Hajiya zulaiha ce tayi sallama falon inno,inno ta amsa sallamar tana cewa Ammin rahima kece haka da yamma!' Ammi ta amsa tana ɗan sakin murmushi tace" wallahi inno daga side ɗin Hajiya Babba nake kwana biyu jikin nan ya hanani zuwa dubaku!'inno tace haba Ammin Rahima ai mune zamu zo mu dubaki dan yanzu mun fiki jin karfi ke da ba wani cikakken lafiya gareki ba da kinyi zamanki!'ammin tace"inno ai da sauki jikin daga nan ma wajen Hajjo zanyi, naje na duba Alhaji Baba shima!' inno tarike haba tare da cewa to sannunki da kokari, ya kuma karfin jikin?Ammi ta amsa da cewa da sauƙi, inno yanaji gidan naki shiru ina sabon jikan naki?inno tace"wai Abdallah kike magana wannan baya nan yana can Asibitin sa ko da yana nan ma bazaki gane ba dan basan hayaniya yakeba, su kuma yaran duk sun daina zama saboda shi!'Ammi tayi dariya tace ai kam yayi mana maganin ƙiriniya yanzu shiru kikeji kunnan mu ya huta!'
Zahra..zahra,inno tashiga ƙwala mata kira, yayin da take sanar da Ammi cewa bari na kira zahra ku gaisa yarinyar da Nafisa ta samo min dan debe kewa, sai dai kuma marainiya ce..shigowar Bintu ne ya katse mata zancen, sallama Bintu tayi cikin sassan yar muryarta me tsananin daɗin sauraro,A lokaci ɗaya kuma tana tsugunawa A gaban inno tare da rissinawa ta gaida Ammi,Ammi ta zubawa Bintu ido, kana cikin sanyin murya itama ta amsa gaisuwar, ta dubi inno tace masha Allah inno yarinyar ko kyakkyawa, ko itace'Rahima ta dameni da zancen ta?inno ta washe haƙora cikin jin daɗi tace" itace ai naga jininsu ya haɗu da Rahima tana sonta! Ammi tace"kinsan Rahima da son Abu mai kyau!'ta kare maganar da mikewa tsaye,tace" inno ni bari na wuce zan shiga wajen Hajjah!'to madalla Allah ya ƙara sauƙi!'ahankali Bintu tace"ki gaida gida Allah ya ƙaro sauƙi!'cikin ƙure bintun da kallo ta amsa ta da Amin na gode!'tare da barin falon gaba daya,
Tafe take zuciyarta cike da da tarin tunaninnika, bata ga komai A game da yarinyar ba,haka nan kallon da tayi mata ta gano babu komai cikin idanunta sai tsananin kunya da gaskiya,tanajin wani ɓangare na zuciyar ta nasan amincewa da Bintu, to amma kuma me yasa takejin wani irin tsoro A kan yariyar? tanaji kamar da wata maƙarƙashiya A kan zuwan yarinyar duk da bata da wani zargi A kan Nafisa sai dai can ƙarƙashin zuciyarta tanajin wani Abu daban, amma dai komeye zan sakawa yarinyar ido,dan kaf gidan nan ba abin yadda bane dole ne na gano komeye Ake shiryawa.
Yau ne ya kama, kamun Amare wanda yayi daidai da kwanan Bintu biyu A estate, Æ´an matan Amare sai shirye-shirye suke, wasun su da yawa suna sashen inno,yayin da Bintu sai shiga da fita take, itace wancan itace wannan ko Abincin daren Abdallah sun hanata ta É—aura, gashi yau A time table É—in sa sakwara zata yi masa da miyar egusi,
karma hauwa'u da amna suji labari, sun takurawa Bintu, kuma bakomai ne yake ɗawainiya dasu ba face kishi da hassada, duk da suma ba munana bane amma suna jin suna raina kansu A duk lokacin da bintu ta kasance A waje, shiyasa suka ɗauki karan tsana suka ɗora mata, hakan baƙamin faranta wa Anty nafisa rai yake ba,duk da har yanzu basu kuma haɗuwa ba tunda ta kawota.
Saida duk ta sallamesu kana ta fara aikinta shima saida Inno ta fito ta tsawatar musu,cikin sauri take sarrafa duk abinda.yazo hannunta,duk da cewa basu taba haɗuwa ba har yau, amma tana ƙoƙarin kiyaye duk wasu ƙa'idojinsa da Aka lissafo mata,kai wannan mutum da shegen fi'ili yake komai bayaso,A haka ta gama aikinta lokacin babu kowa duk sun tafi wajen da Ake kamu shima A cikin estate ɗin yake,sai da ta gama jera masa komai kana cikin sauri ta nufi ƙofa dan fita, sam bataso su haɗu da wannan murɗaɗɗen mutumin, gashi yau har ta shiga lokacin dawowarsa shiyasa take sauri ta fice kar ya tarar da ita.
Tana buɗe kofar tayi wani irin gware da wani irin faffaɗan ƙirji, duk da ita bata gama tan-tance da abinda tayi karon ba, runtse manyan idanunsa yayi dan haƙiƙa yaji zafi har cikin ƙahon zuciyarsa,
Buɗe Manyan idanunsa yayi, A daidai lokacin ita kuma Bintu ta gama murza goshinta, ta ɗago dan ganin mugun da yai mata wannan aika-aikar, zaro manyan fararen idanun ta tayi tare da dagewa iya ƙarfinta ta kurma wani uban ihu, tare da komawa cikin falon da gudu tana neman gurin ɓuya,kira take wayyo inno yau nayi gamo, wa innahu sulaimanu, fafina yau nayi gamo, kuka takeyi sosai tamkar zata fitar da numfashinta,
Mamaki haushi ta kaici duk sune suka cushe zuciyar Abdallah,yana nan tsaye ya kasa ko da motsawa, balle sanin abinda zaiyi, ga ƙararta da duk ta cika masa kunne har ya rasa me ya kamata yayi, kaji yarinya da rashin hankali, amma shi bai ce mata Aljana ba sai shi zata cewa Aljani,tsuka yayi kana yaja ƙafafuwan sa ya ƙarasa shiga cikin falon,ɗago idanunta tayi da suka fito waje kamar na preter, cak ya tsaya yana kallonta dan shi dai ba ma'abocin kallo bane amma sosai yaga kamar su da preter har zaro idon da yanayin tsoronsu amma azahirance bintu tafi preter kyau,hannu yasa ya finciko ta ransa A matuƙar ɓace, ya daɗe bai ji ɓacin rai makaman cin na yau ba,idanunta, ta kuma zarowa kamar zasu faɗo ƙasa saboda firgita da tsoro,ji tayi kawai yaja ta har bakin ƙofa ya turata waje,ya maida ƙofar da matuƙar ƙarfi ya rufe,
Tsuru tayi A bakin ƙofar zuciyarta cike da fargaba,yanzu hankalin ta ya riga ya dawo jikinta,sai yanzu ta fahimci waye, A fili tace kai waini wace irin matsoraciyace? mutum da falonsa amma na kirashi da Aljani?cikin irin muryarta da ta saba yiwa fafi tace me yasa nake hakane? gashi najawo zai karya min hannu,to koma kurma ne ? kai inno dama tace sai ya kwana biyu baiyi magana ba, to kuma bakinshi baya yin komai? hannunta ta kalla taga har yayi ja ga shi sai raɗaɗi yake mata,kallon ƙofar tayi tana zabga mata harara tare da murguɗa ɗan ƙaramin bakinta, tace kuma ban yafe ba mugu!'ta arta A guje kamar wadda zai kama.
Yana shiga bathroom ya sakarwa kansa shaya,yanayi yana sakin tsaki, kai wannan yarinya A kwai bagidajiya kawai tazo ta ƙaran ciwon kai,
sai da yagama shirinsa tsaf, kana ya fito falon, wajen cin abincin ya nufa kai tsaye dan shi Abdallah yana cin binci sam baya wasa da cikinsa, shiyasa ma yasa a samo masa mai girkin, gashi kuma bai iya bin gidajen abinci ba saboda tsantsani, zama yayi ya zuba sakwarar yaci sosai dan sosai ɗanɗanon abincin yayi masa ɗari bisa ɗari, har ya shiga mamakin wannan ƴar yarinyar ce ta iya sarrafa abinci haka ga nau'in lemuka masu inganci da'A cikin kwana biyun suka kama zuciyar sa, A hankali ya miƙe ya koma cikin falon tare da zama cikin kushin, hannu ya miƙa ya ɗauki ɗaya daga cikin wayoyinsa, wadda take ta buruntun neman agaji, cikin hakimtacciyar muryar shi yayi sallama bayan ya dannata A amsa kuwa, muryar Dady ce ta ratso ta cikin wayar, bayan ya amsa sallamar tare da gaisuwar da Abdallah yayi masa,yace" Abdallah ina fata ko mai lafiya, batare da ya jira amsarsa ba ya cigaba da cewa anya kuwa Abdallah kanayin wani ƙoƙari kuwa dan najika shiru babu wani motsi,ina tsoron kar mutanen nan su sham mace mu,dan na lura A kwai mutanen da suke bin diddigina, amma bansan ko suwaye ba ban san kuma daga ina suke ba amma ga dukkanin alamu mutane ne mabanbanta shiyasa nakeso naji kai ta wajenka babu wani Abu?
Cikin nutsuwa Abdallah yace" dady ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai sameni da ikon Allah, kuma ina yin komai ne cikin lura, dady bamu ne zamu fara kai farmaki ba dole yanzu nasan bazasu zauna ba, da farmakin su zamu fara gano su kar ka damu babu wanda baza musawa ido ba insha Allah ko mai zai tafi dai dai!'hamdala dady yayi ya kuma tabbatar Abdallah yana yin komai da hangen nesa.
Anyi biki angama cikin kwanciyar hankali, an kuma kai Amare gidajensu, an bawa ragowar ƴan matan inno fili suna zuba sha anin su, yayin da masu shiri suka fara shiri masu makirci suka fara shirin ƙulla makircinsu,