Sashe 116
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can ESTATE kuwa Taufiƙa ce take ta zuba haukanta, a sashen inno wai murnar zata auri wanda takeso zata cika burinta, Sayyid yana zaune yana kallonta bai ce mata komai ba,dan shi tunda yaji al'amuran da suka faru acikin gidan nasu ya saduda ga kuma ji nasabarsa da BINTU da Abdallah wanda shine ya kara kashe masa jiki,kuma yanzu ne ya tabbatar da cewa soyayyar da yayiwa Bintu ta jini ce, dan haƙikanin gaskiya bai taɓa jin ƙiyayyar Bintu da Abdallah ba komai ya faru ne sanadin huɗu bar sheɗan,dan haka yanzu ma kallon mahaukaciya yakewa Taufiƙa dan ya tabbatar da cewa Abdallah ba zai taɓa auren ta ba,zurata kawai su Alhaji Baba sukayi,to inno ma dai kusan kallon da takewa Taufiƙan ke nan dan ita dariya ma lamarin ya koma bata,ita kuwa Taufiƙa tsakaninta da Allah take sabon shiri, dan yanzu ta sake tana komai cikin walwala da farinciki,hatta su Farida sun haƙura tuni sun karɓi Bintu a matsayin ƴar uwar su kuma ƙanwarsu, dan idan ka gansu a tare bazaka yi tunanin sune mutanen nan da suka cusgunawa rayuwar Bintu ba,duk kan al'amuran da suka kafaru cikin ESTATE din ya zame musu izina,kowa ya dawo hankalinsa.
Aunty Nafisa kuwa tana cikin wata iriyar rayuwa ta ganin ishara, dan tunda mahaifinta yaki karbarta,sai garin su ta koma can lafiya,wanda kuma ba wani arziƙi ne dasu ba kowa ta kansa yake,kuma lokacin da take dashi babu irin wulaƙancin da batayiwa danginta ba,shi yasa yanzu babu mai tausaya mata,idan ka dubeta baza ka ganeta farar ɗaya ba,abinda ta shuka shi take girbewa,ga dai kudin mahaifinta amma hakan bai sa taki ganin hukuncin Allah da sakamakon cutarwa ba,ita kanta tasan sakayyar Allah ce ke bin rayuwarta.
A ɓangaren tawagar Dady Habib ma,dai zamu iya cewa gayyar ta watse dan dukkan su sai da su Abdallah suka tarwatsasu,suka ƙona gurin da suke shuka tsiyar shirkar tasu,daga haka dai kowa ya fece wasu an kama su wasu kuma tun daga nan suka sami taɓin hankali,
Dady Habib ma kusan zan iya cewa ya zare,dan yanzu bashi da aiki sai surutai da fadin abinda ya aikata,kukan mutane kuwa har yanzu ya kasa rabuwa dashi wala a farke ko a bacci,(to wan Nan dai kadan ne daga ikon Ubangiji ita sakayya dama ba lallai sai anje can ba,tun a duniya Allah ya kan nuna sakamakon masu mugun hali dan ya zama izina garemu amma duk da haka sai mai rabo ne yake gane hakan Allah Ubangiji ya shiryemu kuma ya ganar damu tun da sauran numfashin mu Amin Ya Allah)
Inno tana gama shirya kayan karin da za a kaiwa su Abdallah ta kira Yahya a waya,jim kadan ya shigo bayan ta amsa gaisuwar sa,tace"yauwa Yahya ga abincin ogan naka nan na kammala sai a miƙa masa!'ta ɗan dubi Taufiƙa da taci uban ado kamar me shirin zuwa gidan fati,tace"Taufiƙa ko zakuje ki kaiwa angon naki abincin kari?cikin rawar jiki ta mike tunda dama tsoran gwaliyar innon ne ya hanata tace"zataje,tace"me zai hana inno? ya dauko mu tafi!'duban Yahya inno tayi tace"kuje tare tunda kaine kasan gidan!'amsawa yayi cikin girmamawa kana ya kwashi kulolin da zai iya dauka,itama Taufiƙan ta dauki wasu bayan ta dauko yalolon mayafinta,da kallo inno ta bita, tana ganin fitar su tayi dariya, tare da cewa idan da rabon kin dawo da kukan jinine ai shike nan,dan nasan hawayen ruwa sunyi wa idanuwanki kaɗan idan kikayi tozali da zinaren masoyan da tauraron su ke haskawa,wataƙil hakan yasa kiyi haƙuri ki saduda ki karbi mijin da yazo a ƙaddararki!'Siddiƙa dake fitowa daga daki,itama cikin dariya tace"gaskiya dai inno kin iya shirya wasa nasan da biyu kika turata gidan ya Abdallah!'inno tace"yo idan ba ta kaici take shaƙa ba banga zata haƙura da Abdallah ba,idan ma ba wauta da hauka irin na Taufiƙa ba ya za ayi kizo kiyiwa yarinya kamar Bintu sharri kice ta amince ki auri mijinta,yo mu haukane ya sake mu da zamu bari hakan ta faru,ai duk da cewa hakan ba haramun bane,amma ai ana barin halas dan kunya,kuma Taufiƙa zata iya cutar da Bintu dan haka wannan abun ma tamkar kwado haka yake!'Siddiƙa tace"to amma inno me yasa kuka amsa mata kun yadda da aurenta da ya ABDALLAH,?inno tace"Siddiqa idan ba haka mukayi mata ba bazata bari ayi auren nan cikin kwanciyar hankali ba,amma kinga hakan da akayi mata ai mun samu saukin fitinarta,in yaso idan an daura auren da Sayyid ta ya galgala naman jikinsa faƙat, Siddiqa tayi dariya tana cewa ai inno Ni tuni na dawo daga rakiyar Taufiƙa dan naga abun nata nema yake yashiga tsakanin zumuncin mu da ƴan uwana,wanda Ni kuma a halin yanzu bana fatan haka, so nake mu haɗa kanmu mu zama tsintsiya madauri ɗaya!'cikin farin ciki da jin daɗi inno ta rungumo Siddiqa tana shi mata albarka tare da yiwa taufiƙa fatan shiriya da gane gaskiya.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 63 ```
Zumudi da rawar jiki ya hanata tayi tunanin abin da zata je ta iya tararwa,gaba ɗaya idanunta sun rufe, danunta da zuciyarta shi kawai take hangowa,bata hango mata cewa Abdallah baya sonta bai kuma taɓa sonta ba,san nan bazai taɓa sonta ba,
A daidai lokacin ne kuma Bintu take ta faman zubawa Abdallah shagwaɓa da sangarta,tun da suka tashi a bacci sukayi wanka suka shirya tsaf tamkar wasu taurari,sai kuma ta dasa masa rigimar wai ita ciwo takeji ajikin ta,hakanne yasa shi fitowa da ita ƙasa suka baje a faffaɗan kushin ɗin da yayiwa falon ƙawanya,matsa mata jikin ta yakeyi a hankali cike da taka tsan tsan ɗin samuwar ciwo ko jin zafi ajikinta,sam taɓarar Bintu da san jikinta baya damunshi,saima alfahari da yake yi da hakan.
Ɗan bude idanunta da suke lumshe tayi,tana kallon kyakykyawar fuskar shi,ɗage mata gira yayi,sai tayi saurin rufe idanun tana sakin wani sassanyan murmushi,can cikin kunnen ta ta fara jiyo sassanyan Muryar shi yana rera mata waƙa(a tsakanin mu Ni dake babu sabawa baƙon zuciyar ki Nine gani nan zaune, kyakykyawa kece kike rikitani na kasa ganewa, ashe kece kike kiɗima Ni ina ta dubawa, nai ƙoƙarin na gyara ganina amma na kasawa, guguwar son aciki na cake zuciyata saitawa)kallon da bata taɓa masa ba shi yanzu take masa,ji tayi kawai bakinta ya kama rera wata waƙa da take matukar so, tana yawan ji Rahima najin waƙar Sarina,(Bintu ta kace in dai da alƙawarii rabamu zai wuya indai a soyayya ne)gaba ɗaya suka saka dariya,kwanciya yayi a kusa da ita yana cewa my jewel yaushe kika iya rangaɗa waƙa haka?shimfiɗe kanta tayi a ƙirjinshi tana cewa kai yaushe ka iya?kai tsaye ya bata amsa da cewa,tun sanda na gano na faɗa komar ki!'murmushi tayi tare da da cewa Ya Abdallah ka goyani idan ba haka ba ciwon jikina ba zai warke ba!'saukowa yayi ya juya mata baya tare da cewa da zani kikeso ko haka?kafin ta bashi amsa sun ji knoc ɗin kofa,kasancewar inno ta shaida masa za akawo musu kayan kari sai hakan bai bashi mamaki ba dan yasan Yahya ne,yana tashi tabi shi,buɗe ƙofar yayi kafin yace komai sai ga murmushin Taufiƙa na haske mashi fuska,zakuyi mamakin yadda lokaci ƙanƙani fuskar Abdallah ta haɗe yawa hadarin da ya haɗo gangami,gaisuwar da Yahya yake masa ce ta ɗauke masa hankali har ta shige cikin falon tana wata tafiyar kwarkwasa, karɓar kulolin hannun Yahya yayi ya rufe ƙofar tare da nufar dinnin, anan ya samu amarya Taufiƙa yayin da Bintu ke ta faman bunshi kamar jela dan ko duban inda Taufiƙan take ba tayi ba,cikin sanyaya murya ta gaida shi,amma tamkar ba da shi take ba,saima hankalin shi da ya maida kan Bintu yana kallon rigimammiyar fuskarta da take a kwaɓe ƙiris ya rage ta fashe masa da kukan da baya buƙatar shi a ko da yaushe,zama yayi saman kujerar tare da janyo ta ya zaunar da ita saman cinyar shi, cikin san lallashin ta yace"me kuma ya faru my princess jewel?ɗan tura ƙaramin bakinta tayi tana kuma hararar gefan da Taufiƙan take a tsaye kamar zata haɗiyi zuciya da wulaƙancin da Abdallah yayi mata,gane abinda take nufi ne yasa shi miƙewa da ita a jikinsa yana cewa cikin miskilar muryarshi da ba yayi agaban Bintu,my wife,goyon kike buƙata ko abinci?girgiza kanta tayi tana murza idanunta irin yadda shagwaɓaɓɓun yara sukeyi,tace"Ni bancin abincin yanzu ka fara goyona!'da sauri ya durƙusa a saitin ta yayi mata alamar ta hau saman bayansa, cikin farin ciki da wata rigimammiyar dariya ta haye gadon bayanshi tare da zagaya duka hannayen ta ta cikinshi, Taufiƙa dai bata san sanda hawayen baƙin ciki sukafara saraftu akan fuskarta ba,sai kuma take taji sha'awa Ina ma itace akewa wannan soyayya,to ta yaya za ayi miki haka bayan ke kikeso bake ake so ba,zuciyarta tacigaba da bata shawara da cewa Taufiƙa kiyiwa kanki faɗa tabbas kika bari Abdallah ya aureki to hoto zaki zama a gurinsa hoton ma mara amfani,kije ki auri Sayyid tunda shine yake sonki,ki canja rayuwarki,tunda gashi kina kallon duk abinda Inno ta zaiyano akan zai faru da rayuwar Bintu shi kike gani yana faruwa tamkar wadda a kasanar da ita,bayan kuma ba haka bane kawai dai tayi mata fata ne na kasancewar zuciyar zinaren da Bintu take da ita, Taufiƙa kiyi haƙuri ki karɓi zabin da ya zamo naki tun kafin a haifeki,