← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 120

Sashe 24

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana biyu da yin maganar Bintu da Hajiya ladidi,da misalin ƙarfe goma na safiyar asabar,Aunty Nafisa ta shigo falon Inno,lokacin da tashigo Inno tana cikin ɗakinta yayin da Bintu take kiching tana wanke kwanonin da oga Abdallah ya karya,kai tsaye ta nufi ɗakin inno tayi sallama daga bakin ƙofar,inno ta amsa tare da bata umarnin shigowa,Aunty Nafisa ta gaida Inno cikin girmamawa, kana ta ɗora da cewa inno runtsawa zakiyine? Inno tace"a'a kin san Ni banfiye zaman cikin ɗaka ba nafi son zama a falo saboda gurin baya rabo da baƙi,Gara ina kusa!' Anty Nafisa ta miƙe tana cewa to bari najiraki A falon!' Inno tace"babu laifi yanzu ina fitowa!' to A fito Lafiya!'Anty Nafisa ta faɗa tana fita daga falon.

A falon ta sami Bintu tana ƙara kakkaɓe kujeru,zama tayi A kan kujerar da Bintun take kaɗewa, kana cikin ƙasa da murya tace" kizama cikin shirin fita,kuma kiyi dabarar sanar da dije tun wuri saboda itama ta shirya fitar tare da tsayar da gurin haɗuwa!' tana rufe bakinta wani sassanyan ƙamshi me tsananin daɗi ya game duka hancinansu,ita Bintu tana shaƙar ƙamshin tasan cewa oga Abdallah ne ya kusanto falon dan haka cikin sauri ta matsa daga kusa da Aunty Nafisa ta cigaba da abinda takeyi tamkar ma batasan da wata halitta A gurin ba, A dai-dai lokacin ya ƙara so falon cikin takunsa na isassun maza masu matuƙar aji kwarjini,kafin kace wannan tuni kwarjinin sa da ilhamarsa wanda rabbi ya bashi suka mamaye falon,wani irin kallo Anty Nafisa take binsa dashi har yasamu guri ya zauna ya hakimce tamkar basarake.

Tap ɗin sa ya buɗe yashiga aikin dake gabansa batare da ko kallon ɓangaren da Aunty Nafisa take yayi ba,cikin kwarewar sa ya shiga sarrafa ta hankalin sa kwance,Anty Nafisa kuwa ina wuta tasaka Abdallah A ciki, iya ƙarshen ƙulewa ya ƙular da ita, Anty Nafisa tanasan A girmamata macece mai san ƙasaita dan haka jin zuciyar ta take tamkar zata kama da wuta saboda baƙin cikin wulaƙancin da Abdallah yayi mata,cikin ƙufula da jin tsanar sa A ranta ta ɗauke kanta tana duban inno dake shigowa falon bakinta ɗauke da sallama, tana cewa lallai kuce na haɗa manyan ƴan hira A falona amma ba Aje ansanar dani ba dan nayi saurin fitowa!"Abdallah da ya san dashi take ya ɗago kansa yana ɗan dubanta kana yace" my inno kin tashi lafiya!' inno tayi dariyar jin daɗin sakewar da Abdallah ya farayi da ita duk da dai bawai ya canja bane amma yanzu yana ƙoƙarin ganin yayi mata magana, tunda gashi har fitowa falonta yakeyi ya zauna,duk da ba wani magana yakeyi ba amma hakan na mata daɗi sosai,tace" lafiya ƙalau na tashi Abdallah,ina fatan dai babu wata damuwa tare da da kai? jinjina mata kai yayi kawai ya maida hankalinsa kan tap dinsa.

Anty Nafisa tayi wani ɗan gajeren tsaki yadda baza aji taba,to amma batasan kunnen Abdallah da shegen ji bane,dan tsaf yaji tsakin da tayi tamkar A kunnensa ta raɗa masa,amma baza ka gane hakan ba saboda yadda hankalin sa kaf yake kan tap ɗinsa,juyawa tayi suka cigaba da hira da inno,saida ta samu kamar mintuna goma da fara hirar tasu,kana cikin girmamawa tace" inno wallahi tun jiya nake san faɗa miki amma ban samu shigowa ba sai yau,inno ta ɗan muskuta tare da cewa to lafiya daiko? Anty Nafisa tace"a'a ba wani abin damuwa bane,dama Hajiyata ce takeso ki ɗan ara mata Zahra zata tayata aikin abinci saboda zatayi baƙi daga can garinmu, to shine tace"bazata iya gaya miki ba dan kar kiga kamar tanaso ta nuna miki isa ne A kan Zahra shiyasa!" Inno ta shiga tafa hannuwa gami da sakin salati kana tace"kai amma dai Hajiya ladidi sai A barta, yanzu dama tsakanina da ita akwai irin wannan? gaskiya amma banji daɗi ba,kiyi kiranta kiji yaushe takeso Bintun taje? da sauri Aunty Nafisa ta shiga kiran Hajiya ladidi A wayarta.

A can ɓangaren Bintu kuwa tana fita daga falon ɗakinta ta koma,sintiri ta shigayi tana neman hanyar haɗuwa da dije, sai dai kuma batasan ko ta yaya hakan zata faru ba, hasalima batasan A wanne ɓangare Dijen take aiki ba,san nan koda ta sanima ai baza ta iya zuwa kai tsaye ba, dan matsawa tayi jikin window ta ɗaga labulen window ɗin ta shiga rarraba manyan idanuwan ta A cikin harabar gurin,hannunta taji kamar yana taɓa wani abu,janye hannun tazoyi tare da kai idon ta kan abun,zaro idanunta tayi cike da wannan yanayin nata na tsoro dake matuƙar ƙarawa fuskarta wani irin sihirtaccen kyau,A hankali tasa hannu ta zaro cukurkuɗedɗiyar paper dake soke jikin window ɗin, sauri tayi ta mayar da cotain ɗin ta rufe,cikin hanzari ta buɗe paper,wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke yayin da tayi arba da saƙon Dije wanda take sanar da ita lallal ta samu hanyar fita A yau saboda itama ta samu hanya, dan Hajiya Rabi ta aiketa cikin kasuwa,A yayin da ta kuma ɗora mata da adireshin gurin da zata sameta tare da yimata gargaɗi da ta lura dan za a iya samun me bin bayanta dan haka sai ta kiyaye kar kuma ta bari drever ya kawota, kiran inno ne ya shiga kunnuwanta, cikin wani shegen gudu ta faɗa toilet tayi floshin ɗin paper kana ta fita tana cewa inno gani nan!'

Dai dai Lokacin da ta ƙarasa falon, ita kuma Hauwa'u shigowar ta kenan tana gaida Inno da Anty Nafisa,cikin sanyin jiki ta dubi ɓan garen da Abdallah ke zaune har yanzu yana aikinsa tamkar bai san da mutane A falon ba, tace" Yaah Abdallah barka da safiya! A kan tausasan laɓɓan shi ya amsa da lafiya!' wanda ba daban idanunta na kallon bakin nasa ba da baza ta gane ya amsa ba ma,zama tayi kawai tana mai ci gaba da kallon sa tamkar zata cinye shi, A yayin da da Bintu ta ƙarasa gaban inno tace"inno gani!'inno tace"yauwa Batula maza ki shiga kiching ki haɗawa yayanku Abincinsa,tunda yana gida sai kije ki shirya Hajiya ladidi nasan ganinki!'ɗan ƙasa tayi da kanta kana tace"to inno!' har zata miƙe Hauwa'u tayi saurin cewa inno tunda aika zatayi Ni bari naje kiching ɗin na haɗa masa lunch ɗin!'kafin inno tayi magana sun tsin kayo kamilalliyar muryar shi yana cewa ba buƙatar hakan,tare da jefawa Bintu wani mugun kallo wanda bata san lokacin da ta ganta ƙofar kiching ɗin ba, ta dafe ƙirjinta tana maida numfashi tare da cewa kai wannan mutum kwai masifaffe, bada ban Musulunci ba alƙur an sai na bari su Anty Nafisa su hambuɗe ka kowa ma ya huta da bakin halinka!'sai kuma ta ɗan taɓe ɗan ƙaramin bakinta ta kuma cewa ke ma dai Anty Hauwa'u n nan kamar wata mara zuciya kullum mutum yana gwasaleki amma kina daɗa shige mai!'can kuma ta tuna da mutanen ta wani ƙawataccen murmushi ta saki,tanajin farinciki A ranta ta yadda akayi tayiwa mugayen nan da baibayi,yanzu tayi matuƙar gamsuwa da yardar da Hajiya ladidi tayi da ita.

Sai misalin ƙarfe ɗaya kana duk suka bar falon saboda gabatar da sallar zuhur,lokacin kuma tuni Bintu har ta kammala aikinta ta kai masa falonsa,inno kuma ta jera mata A kan dining,ɗakinta ta shiga tayi wanka ta shirya cikin wata baƙar Abaya wadda tayi matuƙar amsar dirin jikinta,Bintu tana da matuƙar diri mai tafiya da hankalin jama'a tun yanzu ma ballantana kuma nan gaba idan ta ƙara girma za ayi kallon halittar ƙudurar Allah.

Ɗakin inno ta nufa kai tsaye bayan tayi sallama, ta shiga inno tana zaune bisa sallaya tana lazimi,durƙusawa tayi Agabanta tace"inno na kammala shirin,inno tace"to ki duba driver duk wanda kika samu cikin su musa ko nafi'u kice ya kaiki, cikin yin ƙasa da kai Bintu tace"inno da zan tafi Ni ɗaya da naso saboda ina son ganin hanya kuma wallahi mota amai take sani!'inno ta riƙe baki tare da cewa ikon Allah to zaki gane gidan ne? kuma dai kinga kafin ki fita daga ESTATE ɗin nan zaki sha wahala,amma bari nace su fita dake get ɗin ƙarshe inyaso sai ki wuce! jakarta ta janyo ta fito da kuɗi kimanin dubu biyar ta miƙa wa Bintu tace"gashi sai kiyi kuɗin napep!' Bintu tace" Inno kuɗin yayi yawa ki rage,inno tace" a'a banason musu kije ko zaki ga abin da kike buƙata A hanya! godiya Bintu tayi tare da miƙewa ta fita daga ɗakin ita kuma inno tayiwa ɗaya daga cikin dirobobin waya tasanar da shi cewar ga Bintu nan ya fita da ita ƙarshen get ɗin estate.....

Drivern yana A jiyeta sai da ta tabbatar ya koma, kana ta shiga ta kawa A hankali har ta fito bakin hanya,wani mai napep ne ya ja ya tsaya A gaban ta tare da cewa hajjaju ina zuwa ne? miƙa masa paper hannun ta tayi wadda ta kofe adireshin da Dide ta rubuta mata, yana dubawa kuwa yace" Hajiya kuɗin ki naira ɗari huɗu! Bintu ta hau napep ɗin tare da cewa Allah ya kaimu lafiya...

Yana ajiye ta miƙa masa dubu ɗaya tace ya je kawai ta bar masa canjin, Allah dai ya biya Hajjaju godiya nake! jan napep ɗin yayi aguje, ita kuma ta fara gan garawa ɗan gidan da aka fara gina shi ba A gama ba, sai dai yana ta can baya ƙofar shiga wurin ita kuma ta bayan ginin aka sauketa,tana shiga kuwa ta ga Dije sai sintiri take, alamu ya nuna ta daɗe tana jiranta, tana ganinta kuwa ta zabura tare da kamo hannunta tana cewa kin tabbatar da babu wanda ya ganki ko ya biyo bayan ki? cikin tabbaci Bintu tace"na tabbatar babu wanda ya ganni dan kafin na shigo ma sai da na da ɗa dubawa sosai! ajiyar zuciya Dije ta sauke kana tace"na yadda dake saboda nasan kina da hankali da wayo!

Sai da ya tabbatar da tashiga gurin kana ya ɗauki wayar sa ya daddanna san nan ya karata A kunnensa,jim kaɗan ya fara magana da cewa sir na kawota kuma na maida Napep ɗin yanzu haka ina ɓoye cikin gurin da suke! bansan me akace masa ta ɗaya ɓangaren ba naji dai yace"zan kunna sir ba ka da damuwa da wannan kuma bazan je ko ina ba har sai na tabbatar ta tafi......
Chapter 24 · 0% Book details