← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 120

Sashe 83

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin da ya shigo falon inno babu kowa hakan ne yasa Bintu bata san da dawowar sa ba,amma kuma ga mamakin ta sai taji kamar zuciyar ta na gaya mata cewa Abdallah na kusa da ita,abin ya bata mamakin jin yanayin da ta saba ji aduk lokacin da yake gab da ita ya mamayeta,cikin yammacin nan tana tunanin mai zai dawo da Abdallah gida?sauri tayi ta zura doguwar hijiabi akan ƙaramin siket ɗin da ta saka bayan fitowarta wa daga wanka,fitowa tayi ta nufi part ɗin sa,kai tsaye duk da cewa bata tunanin shi ɗin ne ya dawo,babu kowa a falon dan haka ta wuce bedroom ɗin sa kai tsaye,tana shiga ta ganshi kwance ƙasan carpet babu abinda ya cire hatta takalmin sa yan ajikin ƙafafun sa,da cikin sanyin jiki da wata irin fargaba ta ƙaraso inda yake ta tsuguna,kana tace"baka da lafiya?shuru bai bata amsa ba ga idanun sa alumshe,Yahh Abdallah ta faɗa cikin wata irin murya mai matukar taushi da kwanciya,wanda hakan ya fito da wani irin amo mai tada tsikar jiki, Abdallah bai san ya akayi ya buɗe idanun sa ba,saboda yadda Muryar tayi matuƙar tasiri a zuciyar sa da gangar jikin sa,ganin sa zaune ya zuba mata idon sa masu sakata jin bacci yasa ta ɗan tura baki tana cewa yo hakan nan sai atayarwa da mutum hankali,ta faɗa cikin ɗan murguɗa bakin,tana farfari da fararen idanun ta,bata gama faɗar abinda ke ranta ba ta baƙumci bakin Oga Abdallah cikin nata wanda hakan ne ya hana ta ƙara sa faɗar abinda ke ranta,

Zaro manyan idanun ta tayi tana mamakin wannan irin ta adi na ogan nata,ture shi ta fara ƙoƙarin yi amma sai taji ya tattarota jikinsa tare da yaye hijabin dake jikinta,zaro idanun ta kuma yi wanda shi Abdallah ma bai san tanayi ba,harshen sa yana sarƙafe da nata yana faman tsotse shi kamar wata sweet,hannu tasa tana dan ture shi dan kar ya yaye mata hijabin bayan shine kadai sitturar data suturce jikinta dashi bayaga dan guntun siket ɗin da tasaka,bata dawo daga tunanin yadda zata yi ba taji Abdallah yayi nasarar zare hijabin,runtse idanunta tayi lokacin da taji hannun sa nayawo bisa sassan jikinta,har yanzu kuma bakin sa yana maƙale da nata,ɗan cire bakin sa yayi anata yana goga fuskar sa a ƙirjinta,cikin kasalar da yake saukar mata tace"wai maye haka Ni ka rabu dani bana so nifa ba ƴar,,,,maganar ta katse mata lokacin da taji sanyin bakinsa bisa nn ta bata san sanda ta saki wani ɗan ƙaramin sauti ba oshhhhh,wai maye haka Ni karabu dani wayyo fafina ka taimaka zai cire min ƙirjina,dan ɗago fuskar sa yayi cikin ɗage mata gira yace"Bint kibar ni na rama mana,ke idan kina cikin damuwa ba ƙirjina kike shigewa kina goga fuskar ki ba,to Ni dan me yasa bazaki barni na rage damuwata da raɗaɗin dake cikin zuciyata ba?ki barni mana kinji Bint ya fada cikin wata irin muryar da yasa gaba ɗaya tsigogin jikin Bintu miƙewa,maida kansa yayi cikin wuyanta yana shaƙar dadda ɗan ƙamshin ta..
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 48 ```

Take nan Bintu taji duk jikinta ya mutu,ɗan zunɓura bakin ta kumayi cikin yanayin da take ciki tace" Ni yaushe nayi maka haka?kuma Ni ai ba haka nake maka ba!'cikin mutuwar jiki da wata irin kasala yace"ramuwar gayya Bint ita nakeyi idan kuma kika ƙara ambatar abinda nake miki da iskanci sai na cire bakin gaba ɗaya kowa sai ya huta!'ya faɗa cikin ɗan kama laɓɓan ta da haƙorin shi ya ciza a hankali,amma dake Bintu tana kan sharafin ta na taɓara,sai kawai tasa masa kuka wai ya cijeta,shine ka cijeni bayan Ni ban taɓa cizan kaba!'ya wani lumshe idanun sa tare da miƙa mata lip ɗin sa cikin wata irin kasalalliyar murya yace"Bint ram,,,,kafin ya ƙarasa maganar da zai faɗa tuni Bintu tayi caraf da lip ɗin sa a cikin bakinta daga ramuwa saiga Bintu ta koma tsotsewa bawan Allah harshe kamar ta samu alewa ko da ike ita a wajen ta daɗin bakin Abdallah yafi daɗin alewa, Abdallah har cikin jinin jikin sa da ƙwaƙwalwar kansa yake jin tsotsar da Bintu kewa bakin sa,kiran sallar da aka ƙwala cikin masallacin ESTATE shine ya dawo da su cikin hankalin su,zame jikin ta tayi daga nashi,shi kuma Abdallah so yake yaga idanun maras kunyar da take cewa ana iskanci, cikin wani irin farin ciki da ya cika zuciyar sa ya leƙa fuskar ta da take ƙasa,yace"Bint wan nan fa abinda kikayi min iskan,,,,da sauri ta rufe masa baki da hannun ta idanun ta cike taf da ƙwalla ji take kamar ta zane kanta saboda ta kaici,tace"dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba!'ta faɗa tana son fashewa da kuka,ɗaga ta yayi suka tashi tsaye,kana yace"gaskiya bazan haƙura ba,daga rama cizo sai kawai ki cinye min baki!' ya faɗa cikin rangwaɗar da kai kamar wanda akaci zali,cire ta yayi daga jikin shi tare da cewa bari idan nayi sallah zan zo sai ki faɗa min abinda ke bakin ki,amma kiyi sallah anan kar kije ko ina kinji ko!'gyaɗa kanta tayi tana ci gaba da ƙunshe kanta da tafin hannun ta,wucewa yayi ya shige bayi jim kaɗan ya fito cikin sauri saboda jin ana ƙoƙarin tada sallah,yana fita itama ta shige ta ɗauro alwalar ta tada sallar a nan cikin ɗakin,

Kamar yadda ya saba saida ya gabatar da sallar isha'i kana ya nufo part É—in su,a kan hanyar sa ta shiga ne daniyal ya kira shi a waya nan yake sanar masa cewa ya gano gidan da su Hajjo suke kuma bai dawo ba sai da yaga Abba Umar shima ya taho, Abdallah yace"yauwa daniyal idan Allah ya kaimu gobe zaka rakani muje san nan ina so kadinga kular min da Abba Umar bana so wani abu ya same shi!'daniyal yace"don worry oga i can take care!'daga haka suka katse kiran,

Duk da bata da tabbacin zaici abinci amma hakan bai hana ta jera masa kayan abincin sa,duk da dai ba wani me nauyi bane dan tuwon semo tayi masa da haɗaɗɗiyar miyar kuɓewa wadda taji ragargajejjen naman kaza sai zabga ƙamshi take, Bintu dai aranta take rayawar ta gaji da waɗan nan girkunan dole ne idan ta samu nutsuwa taje koyan girkin ƴan gayu koda na kwanaki ne,wai dan ma shi Abdallah baya gajiya da cin nau'ikan abincin mu na gargajiya,a nutse ta kammala ko mai amma fa ta ƙagu ya dawo sabo da bata son Shirin ta ya ɓaci, a cikin wannan rana take son aikata ƙudurin ta,sallamar sa ce ta katse mata tunanin ta,tana ganin sa kuwa abinda ya faru awa biyu da suka wuce ya shiga dawo mata,cikin takaici da kunya ta sunkuyar da kanta,ƙarasowa yayi dinnin ɗin yaja kujera ya zauna,bai tanka mata ba,ya fara ƙoƙarin savin ɗin kansa,tana kallo ya saka tuwon sa ya fara ci, amma bata ce masa ba kuma ta kasa motsawa daga inda take tsaye,ɗan satar kallonta yayi yasan abinda ya hanata sakewa,amma yanzu zaiyi maganinta,kasan cewar ba wani tazara bace a tsakanin su ba,hakan yasa bai sha wahalar kamo hannun ta ba, Bintu jinta tayi kawai asaman cinyar sa,zabura tayi zata tashi,ya riƙeta cikin haɗa fuska yace"malama saurara ba abinda zanyi miki cizona kawai zan rama!'zaro manyan idanunta tayi bakinta na rawa tace"to ai ban cijeka ba!' amma aikin cinye min baki!'ya faɗa yana mai tsare ta da manyan idanun sa masu maiƙo tamkar an ɗiga musu man gyaɗa,ɓoye fuskar ta tayi a ƙirjinsa tana jin tamkar ƙasa ta buɗe ta shige ciki,ci gaba yayi da cin abincin sa,sai da ya gama kana yace"kinci abinci?girgiza masa kai tayi,tashi yayi da ita ajikin sa kana ya maida ita inda ya tashi ya zaunar yace"maza kici yanzun nan ki sameni a ɗaki muyi magana!'yasan idan ya zauna bazata iya sakewa ba shiyasa yayi mata haka,cikin sauri tace"bazan iya cin komai ba idan har banyi abinda zuciyata ke Umar tata ba a yau!'zuba mata ido yayi na sakanni kana yace"nace kici abinci ko!'ganin yadda ya tsatstsare ta da mahukuntan idanun sa yasa ta shiga tura tuwon da ya saka mata batare da tana gane ɗanɗanon sa abakinta ba,bai matsaba sai da yaga cewa tabbas ta ƙoshi kana ya janyo hannun ta suka koma ɗakinsa, brosh yaje yayi kana ita ma yasa ta tashiga tayi,yana sane da yadda yaga duk ta ruɗe bata yin komai cikin nutsuwa sai duban lokaci take yi,zama yayi abakin gadon yace"itama ta zauna,a ɗarare ta zauna,kafin yace komai ta miƙa masa wayarta tare da danno masa recording ɗin Muryar Nafisa wadda ta fito tar- tar tana bawa Bintu labarin tsiyar da ta shuka,bai tanka ba kuma bai motsa ba sai idanun sa da suke kan wayar Bintu tamkar wanda yake ganin Nafisa azahiri.
Chapter 83 · 0% Book details