Sashe 76
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda suka sauka ta ɓangaren da ɗakin yake,sai gaba ɗaya tunanin da hankalin ta suka koma wajen,sai yanzu abin yake dawowa kanta wanda tun ranar da abin nan ya faru sai yau ta kuma jin shauƙin shiga ɗakin, wani irin ƙwarin gwiwa takeji a tare da ita, tabbas sai ta shiga ɗakin nan sai kuma tagano menene aciki,kuma sai ta gano mallakin waye,haka nan take jin kamar buɗe ɗakin nan shine wata buɗaɗdiyar hanyar sada ta da duk wani abu da take burin nema ko tace suke burin nema,ido ta zaro ganin mutumin da ya fito daga ɓangaren kamar almaraa haka take ganin al amarin wanda ya matuƙar hautsina tunaninta....
Karku damu komai ya kusa zuwa ƙarshe ku dai kuci gaba da bina sannu dan War ware muku turka turkar,
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 45 ```
Kafin ta fita daga mamakin ganin Dady Habib da tayi sai kuma ga Dady Mansur shima ya ɓullo ta can inda yafi kusanci da ɗakin,wai meke shirin faruwa ne,me yasa suke san burkita mata tunani?to acikin su waye?ko duka su biyun ne?me hakan yake nufi ne? runtse idanun ta tayi yayin da har shenta ya shiga nanata innalillahi tare da allahumma ajirni filmusi bati wakalifni khairan minha,a dai dai lokacin da Abdallah ya gama sallamar Yahya ya juyo dan su tafi, tsayawa yayi yana kallon ta cike da mamaki, yayin da ita kuma har lokacin idanun ta suna rufe tana maimaita duk addu'ar da takama, cikin nutsuwa ya juya yana kallon ɓangaren shima dan yasan komeye baya rasa nasaba da wajen,shi dai baiga komai ba dan haka kawai sai yaja hannunta suka fara tafiya,wanda sai alokacin ne ta buɗe idanun ta da suka kaɗa suka koma wata kala saboda tsabar damuwa,binsa kawai take batare da tasan inda take taka ƙafafunta ba,ita dai kawai tagan su cikin falon inno,basu samu inno a falon ba dan haka kawai sai ya wuce part ɗin sa kai tsaye,
Suna shiga ɗakin sa ya riƙota jikin sa,wanda hakan ne ya kuma haifar da wani irin rauni azuciyar ta, a hankali ta kuma cusa kanta a cikin ƙirjin sa tana giga fuskarta a kai wanda ya riga ya gane wannan alamar tace"da take nuna masa yanayin damuwar da take ciki,hannun sa yasa a bayanta ya shiga fatin ɗin ta cikin salon rarrashi,A hankali ta shiga sakin wata ajiyar zuciya a jajjere tare da samun nutsuwa da salama,sai da ya tabbatar da nutsuwar ta kana ya saketa tare da nuna mata hanyar bayi,cikin body language ɗin sa yayi mata nuni da ta shiga tayi wanka,duk da halin da zuciyar ta take ciki sai da ta ɗan tura baki tana ƙunƙunin rashin maganar sa,bai kula ta ba ya fita daga ɗakin.
ɗakinta ya shiga tare da ɗauko mata kayan bacci, da wasu abubuwan da yasan zata iya buƙata, ya fito yana ƙoƙarin shiga falon sa sai ga inno ta fito daga sashen Alhaji Baba,tace"a'a Abdallah ashe kun dawo?cikin girmama matar yace"mun dawo inno amma bamu jima ba,tace"to madalla ina fatan dai anyi nasarar abinda A kaje nema?yace"Alhamdulillah inno insha Allah an samu nasara tunda dai gashi nan yayi mata tofi da ya bata magunguna,ya kuma bamu lokacin komawa!'inno tace"to masha Allah Ubangiji ya sa a dace!'ya amsa da Amin kana ya shige ita kuma inno ta shige ɗakinta,
Tunda ya koma ɓangaren sa,ya kasa samun nutsuwa,ita kanta Nafisar ta bata san shigowar sa ba,babu abinda yake damun zuciyar sa sai batun iyalan sa,yana son Laila da abinda ta haifa masa bai son so ba sai akan Laila Bai san ɗaɗin ɗa ba sai akan abinda ta haifa masa,wai waye yayi masa wannan mummunan cutarwa? tabbas duk ranar da yayi ido biyu da wanda yayi sanadin rabuwar sa da sanyin idaniyar sa,baya jin idan yakama shi zai iya barin sa da numfashi, babban abinda yake bashi mamaki ya akayi aka san ya auri Laila da inda take zaune kai harma da gidan Sulaiman ɗin da aka bisu,San nan wan nan mutumin daya kirashi waye shi?me yake nufi da wannan tambayar da yayi masa?san nan ya akayi yasan iyalan sa sun ɓata?anya kuwa ya kamata ya bar wannan magana? tabbas yanzu ba lokacin zama bane a wajen sa yanajin lokaci ne yayi da zai fita dan neman nasarar sa,yana ji ajikin sa ya kusa haɗuwa da farin cikin sa,ya dade bai samu nutsuwar da ya samu a wannan karon ba kuma a cikin wannan lokacin da ya gabata,fuskar Bintu da Abdallah ne suka gilma ta idanun sa murmushi ne ya suɓuce masa,yana jin ƙaunar yaran tamkar jinin jikin sa, yanajin mizanin ƙaunar su na ninkuwa duk sakan a zuciyar sa.
Yana cikin wannan halin ne Nafisa ta ƙara so inda yake,zama tayi gefan sa,cikin nuna tsananin damuwar ta akan sa, tace"yallaɓai baka jin daɗi ne?girgiza mata kai yayi,ta kuma cewa to meke damunka naga dai kamar lafiya kafita,amma gashi ga dukkanin alamu ka dawo da matsananciyar damuwa?nan ma dai girgiza mata kai yayi,ƙara matsawa kusa dashi tayi tare da ɗan roƙo hannunsa tace"haba Umar yanzu kana da wanda yafini kusan ci da kai wanda zaka iya kai masa damuwarka bayan ni?dan Allah ka gayamin abinda ke damun ka yau ɗaya dai, ko ina da abinda zan iya taimaka maka dashi!'kallon da ya watsa mata ne ya ɗan so ya razana ta,amma duk da haka batayi ƙasa agwiwa ba ta kuma langaɓar da kai tare da cewa,pls Umar telk to me,ko baka yadda dani bane?wani rikitaccen kallo da ta kasa gane masa ya kuma watsa mata kana ya ɗauke kanshi daga kanta,shurune ya ɗan gifta,kowa da abinda yake saƙawa A cikin zuciyar sa,Umar ya san Halin Nafisa nesa ba kusa ba,ko ita bata san kanta yadda yasan ta ba,ya daɗe yana mugun tunani akanta game da al'amarin sa,idan yace baya zargin ta ma tabbas yayi wa kansa ƙarya,sai dai har yanzu bai kamata da wani laifi makacin wannan ba, bare ya tabbatar,to amma yanzu wayar wan can mutumin ta zaburar dashi daga baccin da ya kwanta yi,dole sai ya binciki Nafisa domin bai yadda da ita ba,ita kuma tunanin ta kawai bai wuce ta yadda za ayi ya sanar da ita ko mai akan lamarin sa ba,cikin san yi masa dabara tace"wai ni kuwa Umar baka tunanin lokaci yayi da yakamata mu nemi yarinya ko yaro a gidan marayu ba tun da har yanzu babu wani labari akan samun haihuwata!'kallon ta yayi cikin wani irin yanayi yace"me ya kawo wannan maganar kuma?anzo wajen dama so take ya magantu,tace"to ai ina ganin damuwar taka duk bata rasa nasaba da rashin haihuwar mu kuma kaga nima,ina buƙatar ganin ƙwaina a duniya kafin na mutu!'ta faɗa cike da alamun tausayawa kanta,irin tana cikin damuwar nan sosai,miƙewa yayi tare da watsa mata kallon tuhuma,ganin yana ƙoƙarin barinta agurin yasa tayi saurin cewa'cikin muryar dake son fashewa da kuka,yanzu Umar kana so kace baka yarda dani ba ke nan, da ba zaka iya gaya min damuwar ka ba?ban yarda dake ba Nafisa!'itace kalmar da ta daki dodon kunnen ta,kafin ta dawo daga ruɗewar da tatafi, ya kuma yanko mata wata da cewa,Nafisa tabbas ban yarda dake ba, saboda ina zarginki da aikata mun wani mummunan laifi,kuma wallahi duk wanda na samu da saka hannun sa kan aikata min wannan ɓarna to kuwa zan iya saka wuƙa na yanka maƙogaron shi ko wanene kuwa,shi yasa nake miki fatan kar ki kasan ce cikin waɗan da suka aikatamin wannan babban laifi,ko nace kar ki kasance kece kika aikata min wannan mummunan laifi,dan haka ki rabu dani,bazaki samu damar jin ko mai daga bakina ba yanzu har sai ranar da asiri ya tonu gaskiya ta bayyana!'daga haka bai ƙara cewa ko mai ba ya fice ya barta A zaune cikin tafiyar sumar wucin gadi,gaba ɗaya ƙwaƙwalwar ta tsaya ta daina aiki duniyar kanta ta tsaya mata,bata ganin ko mai bata jin komai, ayanzu dai acikin wannan yanayin.
Lokacin da ya shiga ɗakin bata fito daga toilet ɗin ba,dan haka wayar sa ya ɗauka,ƙira ya tafi,bayan wucewar wasu ƴan sakanni,aka daga kiran nasa,daga can ɓangaren akace Yes ogah,a hankali yake magana cike da nutsuwa,yace"daniyal,aikin ka yazo,me wannan hotan dana turo maka ya dawo kamar yadda na gaya maka, a kwai inda muke so yayi mana jagora to kasan dai aikin namu na sirri ne,ina so duk inda ya shiga ya fita Kabi min shi har sai ka gano mun wannan gida danayi maka bayani a kan sa,dan haka ka inaso ka zama cikin shiri,ka kuma saka ido akan shiga da fitar sa, dan kar yaje batare da ka sani ba!'daga can ɓangaren daniyal ya amsa masa cikin ladabi,kana suka yi sallama.