← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 120

Sashe 85

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar an min tsine shi haka ya farka, cikin matuƙar tashin hankali da kiɗima ya lalubo wayar sa, wajen kira ya shiga ya lalubo nombar dayake son kira,yadda ya saurara yake jiran aɗauki wayar haka yake sauraren bugun zuciyar sa,har wayar tayi ta katse ba'a ɗauka ba,kira yasake yi nan ma dai abu ɗaya ne No respond,zirga zirga ya shiga yi cikin ɗakin yana cigaba da kiran wayar,can bayan wasu ƴan mintuna sai aka ɗaga wayar,ba tare da ya saurara yaji mai magana ba ya hau surfa ruwan ashar da masifa,dan wulaƙan ci kunaji ina kiranku amma kunyi biris dani,shin kun ɗauko Abigirl ɗin kun kasheta? yallaɓai ba masu wayar bane ga yanzu aka tsinci wayar abakin ramin hanyar da ta tsaga ta shigo Abuja da Kano,ansami masu motar da motar sun faɗa ramin nan sunƙune gaba ɗayansu babu wanda ya tsira!'cikin rawar baki yace"motar ɗaya ce ko biyu?me maganar yace"a'a mota ɗaya ce"kashe wayar yayi tare da wulla ta gefe,ya shiga yarfa hannuwa,shike nan yanzu Abigirl tayi nasarar kubuta daga gareni yanzu wannan shegen yaron sai ya samu nasarar ganin bayana?tabbas na kaɗe idan har ya samu kan Abigirl yanzu me ya kamata nayi ke nan?ya tambayi kansa,cikin sauri yace"ya kamata naga shugaba domin yasamomin mafita,na rasa yadda zanyi da Abigirl ita ba musulma ba amma sai taurin rai ko me yasa na kasa kashe ta ta hanyar tsafi?ya kuma tambayar kansa kamar wani zararre,wani abu naga yayi tare da faɗin wasu ƙalasimai irin na waɗan da suka riga suka bata suka bar turbar gaskiya,cikin ƙanƙanin lokaci saiga shugaba azukyi ya bayyana agaban sa,durƙusawa yayi cikin magiya da tashin hankali yace"shugaba ka taimakamin duk wata dabara ta fara ƙwace min shegun mutanen nan sun tsira daga tarkon da na ɗana musu,yanzu kuma na rasa fafita, ka taimakamin na sace Abigirl daga hannun yaron nan!'shugaba Ezukyi yace"nanu ka sauka daga kan hanya ne shiyasa al'amuran suke ta zuwan maka a haka,amma bari na gwada na gani!'wani siddabaru yayi saiga su Safwan acikin mota suna gab da shigowa cikin gari,hannun sa ya miƙa dan ɗauko Abigirl daga cikin motar amma kafin ƙigtawar ido ya dawo da hannun da wani irin sauri yana yarfa shi ga dukkanin alamu wani abu ne ya samu hannun,cikin zafin da yakeji ajikin hannun yace"nanu a kwai matsala fa dan kuwa bazan iya taɓa Abigirl ba,kana ganin yadda suke ta addu'a ga kuma karatu da suka saka gaskiya bazan iya ba,sai dai mu canja wata hanyar!'nanu yace"to tunda hakane shugaba mu rufe mata baki mana,kaga idan sunje babu bakin da zata iya faɗar ko mai a kai na!'shugaba Ezukyi yace bari mu gwada wannan,saida yayi siddabarun sa na tsawon minti ɗaya kana ya dubi nanu da ya zuba masa ido yace"munyi nasarar wan nan, amma dai kasan duk sihirin da kayi yana zaune ne karkashin ikon wannan ɗakin dan haka ka daɗa kiyayewa!'ɓat ya ɓace ba tare da Allah ya bashi ikon gano matsalar da nanu yake ciki ba, ta shiga ɗakin nan da su Abdallah su kayi,sai alokacin hankalin nanu ya kwanta yasan kafin su Abdallah su ankara zai kashe Abigirl shi ke nan bakin sa ALAIKUM,

Zuba masa ido Sarah tayi cikin tausayin mijin nata,kana ta ɗan numfasa tace"dan Allah yaya Habibu ka tashi daga kan sallayar nan kazo mu kwanta haka tun ɗazu fa kake abu ɗaya ai rai ma yana buƙatar hutu ga cofee ɗin na kawo maka,kazo ka ɗan sha ko zaka samu nutsuwa!'wani irin kallo yayi mata, kana yace"Sarah me kike faɗa hakane dama ana gajiya da ibada?to idan ma ana gajiya Ni dai bazan gaji da roƙon Allah da kai masa kukana ba,kuma kike batun nutsuwa ai tunda na ɗora goshina aƙasan gurin nan na miƙa lamurana gurin Allah to nutsuwa ta gama samuwa a gareni,dan haka kar ki kuma hana Ni yin ibadata,tunda ke bazaki yi ba!'ya faɗa cikin nuna ɓacin ransa da abinda tayi ɗin,cikin kwantar da murya tace"kayi haƙuri ba manufata ke nan ba ya za ai na hana ka ganawa da ubangiji amma kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba!'ɗan murmushi yayi tare da cewa yauwa ko kefa kawai ki tayani da addu'a Allah ya kawo mana ƙarshen matsalolin mu!'tace" insha Allah yaya Habib!'daga nan suka koma suka kwanta kowa da abinda yake saƙawa azuciyar sa.

Wani irin rawa jikin Bintu ya shiga yi cikin kiɗima da tashin hankali tace"Oga Yahh Abdallah kana ganin abinda nake gani? innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un!'shine abinda Abdallah ya shiga furtawa cikin nasa tashin hankalin,ɗakine wanda aka tara kayan tsafi dana siddabaru kala kala ko mai kagani da ɗigon ja ajikin sa,sassan jikin mutane kuwa yafi hamsin wasu an tsaface su a haka wasu kuma sun mutu sai gangar jikin ce ke aiki, idanuwan Bintu ne suka shiga ƙoƙarin rufewa saboda tsabar tashin hankali,da sauri Abdallah ya tarota yana goge mata fuska tare da cewa Bint ki tashi karki suma da akwai matsala zaman mu bazai yiwu agurin nan ba ki faɗa abinda ya kamata muyi yanzu,kamar wanda ya watsa mata ruwa haka tayi saurin buɗe idanunta saboda tunawa da tayi da wata ƙofa acikin ɗakin wadda aka bata tabbacin sai ta buɗe ta,saidai duk iya hangen ta bata ga wata ƙofa ba,cikin tashin hankali tace"Yah Abdallah mu duba a kwai wata ƙofa da matar tace"mu duba kuma Ni bangan ta ba anan!'cikin sauri yaja hannunta tare da cewa muduba sosai!'tace"sakeni na duba wani ɓangaren kaima kaduba wani wajen!'bint mu duba tare kawai bazan yadda ki keɓe ke kaɗai acikin wannan lokacin ba!'da sauri suka shiga tutture ƙwalangwal ɗin da suka yiwa ɗakin ƙawanya tare da cire duk wani abu da suka ci karo dashi ajikin bangon ɗakin,ɓanna sukeyi fa bata wasa ba,gaba ɗaya sun har gitsa ɗakin baka jin sautin komai saina karar zubewar abubuwa da fashewar su,kafin wani ɗan lokaci ɗakin ya turnuƙe da wani irin hayaƙi me shiga tsakiyar kai harda wani yaji me ƙarni da saka amai,cikin fitar da numfashi da ƙyar Abdallah yace"Bint zo mu fita kar dakin ya ƙone damu ko ki samu matsala da wannan hayaƙin!'itama numfashin take fitar wa daƙyar tare dacewa bazan bar ɗakin nan ba sai na ɗauko abinda aka ɓoye a ciki!'me akaɓoye aciki bayan kina ganin abubuwan da suke ciki!'Ya Abdallah bazaka gane ba kawai karabu dani sai na ɗauko shi koda bazan same shi a raye ba!'waye ne haka?bata bashi amsa ba saboda ganin wani waje daga can kusurwar ɗakin anyi shedar zanen ƙofa amma babu ƙofar,gurin ta tunkara gadan gadan tare da saka hannunta a tunanin ta bangone saboda babu wata alama da zata nuna maka ba bango ne gaba ɗaya ba,ashe ƙoface akayi mata kalar fentin san nan kuma ashafe take babu tudu, kamar yadda bangon yake haka take sak sai wannan shatin da Bintu ta gani, cikin sauri suka kalli juna da Abdallah,kana kuma atare sukayi Bismillah suka tura ƙofar saiga ƙofa ta buɗe.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 49 ```

Kamar an tsunkule shi haka ya tashi afirgice,zoban sa da yake ta faman wuta ya kalla abin baƙaramin ɗaure masa kai yayi ba,saboda tunda yake da zoban baitaba nuna masa wan nan alamar ba,da sauri ya tashi tsaye Saboda tunawar da yayi duk sanda zoben yayi wuta shike nuna masa cewar da akwai matsala,siddabarun sa yayi dan ya ɓullacikin ɗakin ba tare da yayi tafiya ba kamar yadda ya saba a duk sanda yaso,sai dai ga mamakin sa abin yaƙi yiwuwa hakan ne ya kuma tabbatar masa cewa da akwai babbar matsala,cikin sauri ya fita daga ɗakin nasa ya wuce falon sa ya fita duk cikin tashin hankali da fargaba,duk takun da zaiyi bugun zuciyar sa ƙaruwa yake.

Ihu Bintu ta saka tare da kanƙame Abdallah cikin wata irin kiɗima da rawar jiki,riƙeta yayi ajikin sa tare da zubawa daskarerren mutumin ido, lulluɓe yake cikin wani abu kamar yana, babu abinda ke motsi ajikin sa sai ƙirjin sa dake nuna alamun bugun zuciya,ƙirjin Abdallah shima babu abin da yakeyi sai bugu dan har yanzu bai fuskan ci waye a cikin wannan dabai bayin ba amma dai tabbas ganin mutumin ya tsunkar mai da zuciya,Bintu ce tayi saurin dawowa cikin hankalinta lokacin da kunnuwan ta suka fara jiyo mata alamun taku ta can wajen dakin saboda tagar da ke kusa da ita wadda take agarƙame, jijjiga Abdallah ta shiga yi cikin tashin hankali tace"wayyo Yahh Abdallah lokaci yayi yana nan tahowa mu ɗauke shi mu gudu!'yace"Bint sai dai mu mu nemi gurin tsira tunda kinga bashi kadai bane,kuma idan mun ɗauke shi bamu san inda zamu kaishi ba!'cikin tashin hankali da kukan da ya kufce mata tace"Yah Abdallah saboda shi nazo saboda na fita dashi nazo idan ban fita dashi daga gurin nan ba to babu amfanin da zuwa dakin nan yayi mana!'shi dai har yanzu Abdallah bai fahimci abinda Bint take nufi ba,amma dai zaiyi ƙoƙarin yin abinda take so,kallon ƙofar tayi cikin wani irin tashin hankali da ketowar wata zazzafar zufa tace"musan abin yi Yahh Abdallah da akwai matsala idan mutumin nan ya gan mu fa!'

Tun daga bakin ƙofar yasan cewa yau akwai babban tashin hankali,cikin matsanancin tsoron da ya fara fin ƙarfin zuciyar shi da gangar jikin sa ya faɗa cikin ɗakin, wayyo Ni kam Fatima saida na gwammace banzo wan nan tsurkun ba,tashin hankalin da nagani ya wuce abin misali,samu nayi na kuma raɓewa ajikin ƙofar ɗakin da su Bintu suke ciki kamar wata ƙadangaruwa,zuciyata kuwa tafi tasu bugawa dan Ni dai banga fitowar su daga ɗakin ba,wata irin gigitacciyar ƙara ce ta dawo dani hankalina,meye haka?waye yayi min wannan ɓannar?wani irin ƙara yake wadda take nuni da mugun tashin hankalin da yake ciki,hargitsa gurin yake yana wani irin juyi aɗakin,waye yake son ganin karshena?baku isa ba ko su waye kunyi kaɗan ku sabauta min burina na shekaru sama da talatin dole sai na cika burina,ɗakin ya nufa gadan gadan dan san tabbatar da ko ajiyar sa tana nan.
Chapter 85 · 0% Book details