← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 120

Sashe 93

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda aka dauko ta bata san inda kan ta yake ba,sai yanzu da ta farfaɗo daga suman da tayi,tun bayan shigowarta cikin ƙungurmin dajin,wanda komai akan idonta ya faru,ko rufe fuskar da ake yi wa wanda akasato basuyi mata ba,hakan ne ma ya bata damar gane cewa daji mai tsananin haɗari suka shigo,razar da tayi ne yasa ta suma,shine bata far faɗo ba sai yanzu wajen misalin ƙarfe tara na safiya, bin ɗan tsukakken dakin tayi da kallo kana ta tsaida idanun ta akan basamuden dake tsaye akanta da sunan gadi,kawar da fuskarta tayi,yayin da idanun ta suka ciko da ƙwalla,ko ya Yah Abdallah zaiyi da wannan sarƙaƙiya da aka saka shi dan komai da yafaru akunnen ta ya faru sai dai ba akan idanun ta ba tunda har yanzu batayi ido hudu da Oga kwatakwata ba,wanda ita kuma fatan ta kenan ganin wanene wannan baƙin azzzlumin,ko da daga haka ƙarshen numfashin ta yazo,yanzun ma bata karaya ba saboda tasan halin gwarzon mijin ta tasan bazai batta agurin nan ba,kuma bazai bari su kashe ta ba,indai har ba Allah ne yayi zata mutu ba,kuma tasan bazai kawo masa Dady Abubakar ba,kuma ko anan ba zata fasa ƙoƙarin ta na ganin bayan azzalumai ba,insha Allah alƙadarin su ya karye karshen zaluncin su yazo..

Ya dade da samun guri ya fake,tun daga zuwan ta har shigar ta ɗan tsukakken lungun da bai wuce kamu goma ba, duk akan idon sa,nutsuwa ya sake yi wajen miƙa hankalin sa kanta,sai da ya tabbatar ta shiga ciki kana shi kuma ya bi bayan ta cikin nutsuwa da sanɗa irin ta ɓarayi,Dije ta samu zaune akan ɗan kututturen dutsen dake girke a wajen tana saƙa da warwara,da sauri ta tashi tare da cewa ranki ya daɗe kin ƙara so?duk da bata ga fuskar matar ba ta tabbatar da cewa murmushi tayi,cikin ƙasai tacciyar Muryar ta ta isa da taƙama tace"Dije tawa Dije aikin ki na kyau yadda ya kamata,maza tashi ina saurarenki ki sanar dani inda Abubakar yake da wannan mutumin ko waye!'cikin yin ƙasa da kai Dije tace"ai ranki ya daɗe Abubakar yana hannun Mansur kuma man sur shine wannan mutumin dakike ta son sani tsawon shekaru amma hakan ya GAGARA,,daɓas taga ta zauna akan ƙasar gurin jikin ta yana wani irin kyarma kamar ana kaɗa mazari,shuru ne ya gifta ta ta wajen kamar babu wani halitta agurin,yayin da Abdallah ya kuma gyara tsayuwar sa yana mai kafe fuskar matar da ido zuciyar shi na dokin ganin fuskar ta ta ainahi.

Yana zuwa yasa su Hajjo suka fito da komai nasu ba tare da ya amsa musu tambayoyin da suke ta jera masa ba,sai da suka shiga mota kana yace"da Anty Asma'u ƴan biyu suna Yola ko? tace e suna can basu dawo ba!'daga haka bai kuma cewa komai ba yaja motar suka fara tafiya,tunda ya fara tafiya ya kula da motar dake binsa,kuma zuciyar shi ta aiyana mashi cewa mutanen Nafisa ne suke binsa,A hankali ya dinga rage gudun motar har ya tsaya agefan hanya,yana kallo suma sukayi fakin abayan motar tasa,Hajjo da ta kula da abinda ke faruwa tace"Umaru mai makon mu guje musu sai kuma kanemi guri ka tsaya!'yace"Hajjo da akwai abinda nake son aiwatarwa!'ƙwanƙwasa glace ɗin window sa da akayi shi ya maido da hankalin sa wajen,zuge glace ɗin yayi,yana kallon yaron da ya tsare shi da jajayen idanun sa da suka sha sukayi tatil,yaron ji yayi kawai ya kasa aiwatar da abinda yayi niya akan Abba Umar,wani irin kwarjini yayi masa,wanda har bai san sanda Abba Umar ɗin ya fito daga cikin motar ba,sai ji yayi yana cewa ɗan samari nasan abinda ya kawo ku gurina ko nace yasa kuke bina!'dafa kafaɗar sa yayi suka fara tafiya, ɗan nesa da su Hajjo suka tsaya,daga nan sukayi magana da Abba Umar wanda sam basu bari naji abinda suka ce ba,na dai ga kawai sunyi hannu da Abba Umar, da sauri, Abba Umar ya koma motar sa yaja ba tare da yayiwa su Hajjo bayanin komai ba..

Sai da taja mintuna a haka kana ta tashi ta kaɗe jikin ta,idanun ta sunyi jajur saboda yanayin firgicin da tashiga,kallon Dije tayi tare da cewa, Dije na gode da ƙoƙarin ki gareni kuma yanzu zan cika miki alƙawarin da nayi miki,daga nan ba zamu wuce ko ina ba sai inda na ajiye miki yaran ki,kuma suna nan babu abinda ya same su kamar yadda na alƙawarta miki!'Dije tace"naji wannan ranki ya daɗe saura ɗayan alƙawarin!'Hajiya tace"ina sane da wannan ma amma shi ina so kiyi min alfarmar bari muje inda yaranki suke sai na buɗe miki fuskata acan!'Dije ta jinjina kanta alamar gamsuwa,sai dai kuma Abdallah fa ya zatayi dashi?wata zuciyar tace"da ita, kema kin san kowaye Abdallah ba zai rabu da ku daga nan ba dole zai biku ko dan sanin manufar ki ta bin matar bayan ba haka kukayi ba,hakan yasa ta sauke guntuwar ajiyar zuciya,tare da bin bayan matar da ta ƙauta taga fuskar ta,

Sai dai kuma abinda Dije bata sani ba shine komai akan kunnuwan Abdallah suka faɗe shi, dan kuwa Allah ya bawa Abdallah ji tamkar maciji,dan haka yana jin haka yayi saurin fita daga inda ya ɓoye,motar sa ya koma yayi shirin bin bayan su Dije ba tare da ya bari matar ta gano shi ba.

Sai da suka ɗan yi nisa kasan cewar a Nafef suke shi yasa basuyi masa nisa ba,haka kuma ya dinga binsu cikin nutsuwa ba tare da ya bari sun kula da hakan ba,tafiya sukayi doguwa sosai,kana suka shiga wata hanya kamar hanyar da zata iya kai ka zuwa wani ɗan ƙaramin ƙauye,wajen shuru babu kowa sai gidan ƙwalli ɗaya a gefan gonakin mutane,tsayawa sukayi ta sallami mai adaidai ta sahun su kuma suka shige cikin ma daidaicin gidan, Abdallah baiyi gangan cin binsu ba sai da yaga mai Nafef ɗin ya fito kana,ya bisu bayan yayi fakin ɗin motar sa acan baya,shiga yayi gidan cikin sanɗa da kiyaye wan da zai iya ganin sa.

Duk ma aikatan da suke mata gadi acikin gidan bin ta sukayi suna girmamata tare da bata bayanai akan cigaban da akasamu na aikin da yake wakana A cikin gidan,hakan ne ya bawa Abdallah damar shiga gidan ba tare da sun ganshi ba,sai dai kuma ɗakin da suka nufa ne ya ɓace masa kamar wasu walƙiya haka suka ɓace masa,ko magan ganun su baya ji,ɗan jim yayi cike da tunanin abinda ya kamata yayi,fara tafiya yayi cikin sanɗa yana bin bango,wani ɗaki ya hango yana facin ɗinshi,ƙara sawa yayi bakin ƙofar ya ɗan kara kunnen sa ko da zaiji sautin maganar su,sai dai maimakon haka sai sautin kuka da yaji da kuma addu'oin da akeyi, Allah ina rokon ka ka kawo ƙarshen matar nan, ka kawo me kuɓutar damu daga wajen nan dan girman annabin da alƙur ani!'ji yayi kawai ya murɗa mariƙin ƙofar ga mamakin sa kuwa sai yaji ta buɗu,ba tare da tsoro ko shakka ba ya saka kansa dan ya tabbatar ba dakin su Dije suka shigo ba.

Da sauri ta ɗago kanta da yake sunkuye tana ta malalar hawaye,kallon kallo suka shiga yi tsakanin ta Abdallah,wan da shi kuma Abdallah tuni ya shiga wani irin shock mai ƙona jinin jiki,kallon fuskar matar sa Bintu yake yi acikin fuskar dake gaban sa, sai dai kawai wahala da girma su ban banta Bint da wannan matar dake gaban shi,da sauri Laila ta miƙe tana cewa zuwa kayi ka fitar damu ko? Allah ne ya turoka,maza mu tafi mu dauko yaya, dama naji ajikina yau addu'a ta zata karɓu yau Allah zai fitar damu daga cikin wannan uƙubar!'ta faɗa tana kama hannun Abdallah da ya rasa abin cewa saboda tsabar mamaki da al'ajabi,idan tunanin shi ya bashi dai dai kenan wannan itace Laila mahaifiyar bint ɗin shi,tunanin sa ne ya katse lokacin da yaji muryar ta kuma dukan dodon kunnen sa tana cewa mai ka tsaya yine ko ba mu kazo taimako ba?za fa ta iya zuwa ta same mu idan bamuyi gaggawar barin gidan nan ba!'hakan da ta faɗa ne ya zaburar da Abdallah yaja hannun ta da sauri yana cewa ina fafy yake?duk da tayi mamakin ambatar yayanta da fafi da yayi amma hakan baisa ta tsaya yi masa tambayoyi ba,cikin san ɗa suka fita daga ɗakin,A hankali suka murɗa mariƙin dakin dake kusa da na Laila,cikin ikon Allah shima suka samu A buɗe yake,da sauri suka kamo fafi da ko magana baya iya yi saboda tsananin cuta da jigata ko kansa bai san inda yake ba,sunkutar sa Abdallah yayi tare da kama hannun Laila,cikin ƙudurar Allah da nasarar dake bin rayuwar su,suka fita daga gidan ba tare da ko tsuntsu ya gansu ba..

Da gudu Dije ta ƙarasa ta rungume yaran ta da sukayi zuru zuru saboda tsabar kewa da zaman guri ɗaya, duk da dai an kwana biyu ba ayi musu wata azaba ba,sun daɗe suna kuka ita da yaran ta,yayin da su kuma su Hajiya suka tsaya suna kallon su duk da bawai tausayi ne ya sa su kallon na su ba,abin mamaki babu wanda yayi musu magana ko tsawa wanda dalilin hakane yasa suka kwashi kusan minti ashirin A haka,daga bayane Hajiyar ta kalli yaranta tare da cewa ku ba mu guri zamuyi magana,kuma ku tabbatar kun kula da ragowar Ajiyar dake gidan!'fita sukayi tare da jawo musu kofar,dan taku tayi biyu zuwa uku kana ta tsaya tare da cewa Dije ko kin san cewa mahaifiyar Bintu na cikin gidan nan?maganar ce ta zowa Dije a wani irin bazata bata gama fita daga wani shock din ba ta shiga wani, sakamakon saka hannun ta da tayi akan fuskar ta tana yaye liƙabin fuskar ta,miƙewa Dije tayi tana nuna ta da yatsa cikin tsananin firgici da kiɗima da mamaki da tashin hankali,bakinta na rawa tace"in...........

Kar ku manta ganin COMMENT ɗinku shike bani ƙarfin gwiwa...

FATIMAH Y ADAM✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 53 ```
Chapter 93 · 0% Book details