← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 120

Sashe 109

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Safwan ne yayi sallama ya shigo tare da Abigirl wadda tayi firi firi da ita kana ganin ta kasan cewa alhaki na biye da ita,tsakiyar falon Alhaji Baba ya zaunar da ita,kana ya juya ya koma inda ya a fito,kowa sai hankalin sa ya dawo kan Abigirl ita kuma hankalinta yana kan Dady Habib da ya zuba mata ido kamar wanda yake son aikamata da wani saƙo na gargaɗi,kawar da kanta tayi ta maida kan Abdallah da ya farayi mata magana cikin nutsuwar sa ta ko da yaushe,yace"kamar yadda na gaya miki ranar ne bana so kiyi min gaddama ko kuskure acikin abinda nake son sani daga gareki,nasan kin san abinda zai iya biyowa baya akan rashin bani haɗin kai da zakiyi,dan haka inaso ki faɗi komai da komai da kika sani akan yadda kika sameni, da yadda kika raine Ni da kuma manufarki akaina!'daga haka yayi shuru tare da maida kallon sa can ɓangaren da Bintu take,yayin da kuma ɗaukacin mutanen dake falon suka maida hankalinsu kan Abigirl, wadda ta zubawa Dady Habib ido,shi kuma yana maida mata da kallon gargaɗi, harma ya manta abin da yagama faɗa yanzu cikin fita hayyaci,kawar da kanta tayi daga gareshi tare da share hawayen da suke ta rige rigen sauka kan fuskarta,Dady jafar ne yace"ke muke sauraro!'duban shi tayi cikin saddaƙarwa tace"zan faɗa,zan faɗi duk wani abu da nasani,amma dan Allah karkuyi min komai,kubarni na koma garin mu bazan kuma waiwayar garin nan ba, ko da me maƙwaftaka dashine!'Dady jafar yace"idan har kika faɗi gaskiya kuma waɗan da kika aikatawa laifi suka yafe miki,to babu abun da za ayi miki,dan haka muna sauraranki!'

SHEKARA TALATIN da suka gabata,

Sunana Abigirl Adebayo ina zaune acikin garin Abuja nida mijina pastor David,tun da mukayi aure bamu taɓa haihuwa ba,tun bamu damu ba har muka fara nuna damuwar mu afili, mutane suka fara fuskantar halin da muke ciki,wala agida ko choch kullum addu'oin mu shine Allah ya bamu haihuwa,sai dai abin yaci tura shuru kamar ba roƙo muke ba,har ta kai da cewa na fara bin manyan bokaye da matsafa,amma duk abin da nakeyi mijina David bai sani ba,dan Ni nafishi damuwa da rashin haihuwar mu,mahaifiya ta ita ta kuma ƙara iza mun wutar san haihuwa saboda huɗu bar da tayi min wanda a da sam ba tunanina kenan ba,tayi min nuni da yadda David yake da arziki,ta nuna mini cewa idan ban haihuba,bazan taɓa samun abinda nakeso daga David ba,tace"min ai yanzu dan ban aihu bane yasa baya sakimin kuɗaɗe masu yawa,amma duk randa na samu baby to zanyi arziƙi ta sanadin baby,huɗubar ta tayi tasiri gareni,hakan ne yasa na kuma tashi tsaye gurin neman aihuwa ba dare ba rana,a kuma cikin lokacin ne komai ya faru,a ranar da bazan manta da ita ba,naje gurin bokana yake sanar dani Lallai sai na samo ƙaramin yaro na raine shi tsawon shekara talatin sa an nan zan samu abinda nakeso wannan shine laƙanin da bokana ya bani,kuma shine dalilin da yasa na taho ina tunanin hanyar da zanbi dan samun yaro karami.

Ina cikin wannan tunanin sai kawai na tsinkayi kukan yaro tamkar al mara,kasancewar daji ne sai na fara tunanin ko dai aljanu ne suke san zautani Saboda sun san laƙanin da boka ya bani,sharewa nayi na cigaba da tafiya,amma sai naji kukan yaron yaƙi tsagaitawa kamar dai anayi masa wani abu ne,dan haka sai kawai nabi kukan da sawayena,banji tsoro ba saboda na saba shiga irin dajikan nan saboda neman biyan buƙata ta,daga ɗan nesa na tsaya dalilin hangen wani mutumi da nayi da jajayen kaya na riga da wando da kuma yaro a hannun sa yana shirin yanka shi,abin ya bani mamaki har kuma lokacin ban daina tunanin ko jinnu bane,amma dake sam bani da tsoro sai kawai na tunkari gurin da niyar idan ma jinnu ne ai Ni ina da buƙatar su cikin rayuwata,ina zuwa nasa hannu na tare hannun mutumin dake shirin yanka ƙaramin yaron da bai wuce shekara uku ba,ɗagowa yayi a fusace,ganina sai kawai ya kasa magana ya tsaya yana kallona da mamakin abinda ya kawoni cikin wannan dajin,zaiyi magana ke nan na tari numfashin sa da cewa,kaiko mutum ne ko aljan? sai naga ya tuntsure da dariya tare da cewa ke kiji min da shegiyar mata,ai Ni zan tambayeki bake ZAKI TAMBAYENI ba,ko da yake ai idan aljana ce ke to tabbas zanji ajikina domin duk da cewa Ni ba aljan bane,amma ina gane su,saboda tsananin tarayyata dasu!'nace,to meyasa zaka kashe yaron nan?kai tsaye ya bani amsa da cewa saboda zai zama masifa arayuwata zaman shi tare da mu acikin ESTATE zai iya rusa duk wani burina!'sai nace masa'mai zai hana ka bani shi domin cika wani buri nawa!'girgiza kai yayi tare da cewa Ni kashe shi nake son yi,lallai sai ya mutu!'da na ga alamun dai ba zai bani shi haka nan ba kawai sai na bashi labarina da abinda yasa nake son ya bani shi ɗin,amma da na fahimci cikin gaggawa yake son mutuwar yaron, sai kawai na juya maganar mai makon nace shekara talatin da boka ya bani, sai nace shekara biyu,na kuma bashi tabbacin da nayi shekara biyu da shi zan kasheshi,a nan dai mukayi yarjejeniya,bai kuma ɓoyemin daga inda yaron yake ba har sunan kakansa sai daya sanar dani amma duk a matsayin gargadi ne,dan ya tabbatar min da cewa duk ranar da nayi kuskure cikin alƙawarin mu sai ya kasheni har lahira,da wannan batun muka rabu,da sauri na juya na koma gurin boka na na nuna masa yaron da na samu,yana ganin Abdallah sai kuwa ya zabura tare da cewa zaki iya rainin sa amma duk ranar da na bari ya karbi Musulunci shikenan duk abinda nayi ya tashi a banza, kuma shima sihirin da zaiyi min na tsawon shekara talatin ɗin duk sai ya karye,dan haka sai na kula da tarbiyyar sa da kuma waɗan da zai dinga mu'amala dasu, wannan shine sanadin zuwan ka hannu na,kuma koda na dawo gida sai nacewa David gidan marayu naje na karɓoka,dake shima san yaran ya rufe mashi ido sai kawai ya karɓe shi ba tare da bin cike ko tsaurarawa ba.

Ɗan shuru tayi kana ta cigaba da cewa,tunda nazo da yaron a cikin kwana biyu nafara fuskantar ƙalubale daga gareshi, saboda wani irin shegen taurin kai da kake dashi da baƙar zuciya,Ni kuma ganin nawa zan haifa sai kawai na shiga gallazawa rayuwarka,idan ina dukan ka kuwa tamkar na samu jikin wani ƙaton saurayin,kusan kullum sai munyi faɗa da David akan ka,da yaga naƙi dainawa ne sai yayi min barazana da zai ɗauke ka ya maida ka can gidan marayu,Ni kuma da naji haka nasan kuma ba da wasa yake ba,sai na dai nayi maka agaban sa,amma bawai dan na daina ba,a kwana a tashi da irin wannan wahalar da nake baka na gina tsanata acikin zuciyarka,a lokacin Ni duk ban damuba saboda burina kawai nake hange,mun saka ka amakaran mai tsada kayi karatunka na primary,a Turkish,Wanda anan ne kuma na fara fuskantar ɗabi unka suna kuma sauyawa kana abu kamar na Musulunci,sai hakan kuma yaɗaga min hankali na fara tasaka gaba muna tafiya choch,wanda kai kuma anan ne kake nunamin asalin taurin kai,da baƙar zuciya,Ni kuma sai abin ya haɗe min ga tsanar ka ga kuma fargabar halin da kake nunamin,hakan ne yasa na tashi tsaye haiƙam da cusgunawa rayuwarka,duk saboda kana ƙin zuwa choch,sai na saka ka aɗaki na rufe yini guda baza kaci komai ba ko da ruwa kuwa sau ɗaya nake baka, shima dan kar ka mutune,daga nan na kaika makarantar horas wa ta kiristoci,a nan ma kasha azaba iri da kala,amma duk da haka baka sauko daga kan dokin naƙin da ka hauba,Ni kuwa alokacin tuni na manta da wani wanda ya bani kai da sharaɗin sa,burina kawai naga lokaci ya cika nima na samu ɗan kaina,da naga abun ya ci tura sai kawai muka yanke shawarar kaika waje dan kayi karatu wataƙil idan kana cikin waɗan da ba Musulmi ba ka haƙura da addinin Kirista,haka kuwa akayi sai dai ban sani ba ashe tuni yaɓe nakeyi akan suminti dan alokacin ma tuni Abdallah ya riga da ya musulunta tun yana primary,sai lokacin da ya tashi dawowa Sai kawai ya dawo min da wannan guzurin da yasa na kusa zaucewa,daga baya kuma da naga yadda ya maida Ni mara amfani da kuma wani tsoransa da nakeji na tsananin kwarjini da hasken Muslunci yasa nazo ina nadama da abinda na aikata masa wanda nadanamar bata da wani amfani alokacin,daga baya na fara tunanin yi masa aure amma hakan baiyuwuba,shine daga baya David ya kawo shawarar sa ta cewa zai kaishi gidan horaswa,wanda Ni kuma bansani ba ashe cikin ahlinsa ya kawoshi,daga nan ta ɗora da labarin yadda akayi ta fara ƙoƙarin kashe shi da wayar da sukayi da mutumin da ya bata Abdallah,har kawo yanzu bata ɓoye komai ba,sai dai kuma har lokacin bata faɗi kowayeba,wanda su kuma da yawa mutanen dake cikin falon abinda suke ɗaukin ji kenan,
Chapter 109 · 0% Book details