← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 120

Sashe 105

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A wannan rana da yawa daga cikin alhalin Alhaji Baba baccin su ragaggene daga na cikin gidan har na wajen irin su Baba nura kenan dasu Alhaji Hashir waɗan da kowa yasan da wannan taron dan duk da cewa suna garƙame amma saƙon ya tarar dasu,dan Abdallah bai bari Alhaji Baba yasan cewa ƴan uwan sa da ƴaƴan sa basa cikin gidan ba shi yayi uwa yayi makarbiya yace"zai sanar dasu,dan haka gaba ɗayansu hankalin su atashe yake, dukkanin su suna cikin halin nadama domin babu wanda ya tsammaci zuwan wannan rana agaresu, Alhaji Hashir kuka yake da idanun sa yana kaicon rayuwarsa da tsufan sa da gemun sa amma yabi ruɗin zuciya da kiɗan shaiɗan,yana matuƙar tsoro da jin kunyar haɗa ido da ɗan uwan sa,ji yake yi inama Allah zai ɗauki rayuwar sa kafin wannan rana ta jin kunya da mozanta ta waye,

Shi kuwa Dady Habib, bai san komai da yake faruwa ba, Abdallah bai bi takan sa ba,dan yasan shu'uman cin sa zai iya neman hanyar kufcewa daga garesu,tunda har yanzu baiga alamun nadama atare da shi ba,shi yasa ya rabu dashi sai agoben zaisa arufe masa idanu a shiga dashi har cikin falon Alhaji Baba,

Misalin ƙarfe takwas na safe Abdallah ya fito cikin shirin sa tsaf,sai zabga ƙamshi yake kamar wanda yayi ɓarin turare ajikin sa,Bintu dake ta sharar baccinta hankali kwance sai buɗe idanu tayi taga yana shirin fita,ai kuwa wata irin wuntsilowa tayi daga kan gadon tare da fara murza idanun ta,dan ba sai yayi mata bayani ba tasan cewa fita zaiyi ya barta,bai san ta farka ba sai takunta da yaji abayansa,tsayawa yayi tare da juyowa,kallanta ya shiga yi tun daga sama har ƙasa sanye take cikin wata ƴar figigiyar riga iya gwiwa gashinta kuwa duk yabi ya baje a kaɗarta,kana ganinta kaga wadda ta tashi daga bacci,da gira yayi mata nuni da jikinta,sai tashiga bin jikin nata da kallo amma dai ita bata ga komai ba,dan haka ta ɗago ta kalleshi da alamar tambaya,ɗan lanƙwashe kansa yayi a kafaɗarsa kana cikin taushin muryarsa yace"ba bina zakiyi ba?da sauri ta ɗaga mashi kai,yace"A hakan zaki bini me yasa yanzu bakya son zama a gida?tura ɗan bakinta tayi tare da cewa aiya nikam tsoro nakeji!'matsowa yayi gab da ita kana yace"Dady zanje na ɗauko kafin ki shirya ko kin manta da taron da muke dashi anjima?girgiza kai tayi tare da cewa to amma ka tsaya nayi wanka sai mu fita tare Ni sai na zauna wajen inno kafin ka dawo!'jan hannun ta yayi har zuwa cikin toilet ɗin kana ya shiga zare mata rigar jikin ta,duk da ƙoƙarin hanashi da tayi amma hakan ya gagara a wannan rana kuma a wannan lokaci sai da Abdallah yagane mata sirrin jikin ta, dan kuwa wanka yayi mata mai sunan wanka,tare da nan naɗota a tawul ya fito da ita,kana ya shirya ta kamar wata ƴar baby, ko da yake shi baby ce awajen sa, Bintu dai ta kasa haɗa ido da Abdallah har sa ilin da ya kaita ɗakin inno shi kuma ya juya ya bar gidan,dan zuwa ɗauko Dady Abubakar.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 58 ```

A FALON ALHAJI BABA.

Damisalin ƙarfe goma daidai falon Alhaji Baba ya ɗauki haramar al'ummar da suke zaune a ƙarƙashin sa,ciki kuwa har da Dady Habib wanda yayi tsumu-tsumu,dan shi sam bai taɓa tsammanin zai fuskanci wannan rana ba,tunda asirin sa ya tonu bai taɓa jin wani abu mai kama da jin kunya da nadama ba sai yanzu, wannan dalilin ne yasa ya kasa haɗa ido da kowa dake zaune cikin falon,a ta ɓangaren su Alhaji Hashir da Alhaji Nasir ma kusan hakane a gurin su,da sauran ƴan tawagar su ma baki ɗaya,Bintu dake kallon su ɗaya ɗaya,duk ta fahimci abinda ke zukatansu,abinda ya so bata dariya kenan wai kunyar duniya sukeji,bata lahiraba,kunyar Alhaji Baba sukeji ba ta ubangijin su ba,kaico da irin wannan rayuwar,da babu tsoran Allah acikin ta,kallonta ta maida kan Anty Nafisa wanda tana kallonta ta fuskanci tana farin ciki acan cikin ƙasan zuciyar ta,yayin da kuma azahirinta fuskar ke ɗauke da alhinin abinda take tsumayin ji cikin kunnuwanta, rashin ganin Umar shi ya kuma tabbatar mata da abinda take fata ne yake son tabbata,falon yayi tsit baka jin ƙarar komai sai ta na'urar sanyaya ɗaki da kuma fankokin dake kaɗawa,sai fitar numfashin waɗan da suke da nutsuwar yin sa.

Gyaran muryar da Alhaji Baba yayi yana tafe ne da bugawar zuciyar wasu da kuma samun nutsuwar wasu,A hankali ya fara gabatar da addu'a cikin tsananin nutsuwar sa da kamalarsa,bayan shafa addu'oin ne ya kuma gyara zaman sa tare da maida hankalinsa kan Abdallah kana yace"to Alhamdulillah Abdallah na cika maka alƙawarin ka kamar yadda nayi maka gashi nan na tara maka duk al'ummar dake cikin ESTATE ɗin nan,dan haka yanzu zaka iya fara gabatar da dalilin da yasa kasa aka tarasu!'rufe bakin Alhaji Baba dai dai yake da ƙara ƙarfin bugun zuciyoyi,sai kuma nutsatstsiyar Muryar Abdallah ta ƙara sa ruguza ɗan ragowar ƙarfin halinsu,yace"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangijin halittu,sai kuma ya ɗan yi shuru yana tunanin ta inda zai fara,idanunsa ne suka sauka akan Dady Habib dan haka ya cigaba da cewa'Alhaji Baba ina fata zakayi min afuwa game da abubuwa masu yawa da suka faru ba tare da saninka ba,san nan ina fata ka zama jarumi mai ƙarfin hali da yadda da duk wata ƙaddara da ta zo maka mai kyau ko akasin haka!'wani ɗan murmushi Alhaji Baba yayi kana yace"Abdallah baka da damuwa dani akan haka ai duk Musulmin ƙwarai dole ya kasance mai yadda da ƙaddara dan haka ka faɗi duk abinda yake tafe da kai insha Allahu zan kasance mai haƙurin ɗauka!'ya faɗa yana maida kallon sa kan matansa dan ya tabbatar da cewa suma haka take agaresu, Hajjah ce ta saki murmushin ƙarfin hali duk da bata da tabbacin zaman ya shafe ta ko bai shafeta ba,amma ya zama dole ta cigaba da yin pritendin dan tsira da ragowar mutuncinta,Anty Nafisa kuwa ji tayi zaman ya fara gundurar ta tunda yanzu ta fara hasaso wani abu daban,tunaninta ya fara bata cewa lallai wannan taron bai dangance ta ba kuma bai shafeta ba,tunda taga alamun duk mutanen cikin falon basu da wata masaniya akan abinda za a tattauna a wannan taron gaggawar, muryar Abdallah ce ta dawo da ita cikin hayyacinta inda ya cigaba da cewa,a kwai abubuwan mamaki wanda zan fara gabatar maka dasu yanzu,amma sai dai kuma banga Abba Umar ba ko bai ƙarasoba?wata mummunan faɗuwar gaba ce ta samu Anty Nafisa sai dai tayi saurin shiryawa abinda zata faɗa game da mutuwar Umar ɗin idan har saƙon bai tarar dasu ba,sai dai kuma Muryar da taji daga bakin ƙofar falon ALHAJI BABA ita taso zautar da tunaninta,Abba Umar ne yake shigowa cikin ɗan gaggawa tare da cewa afuwan ku gafarceni na makara ne saboda wani dalili mai ƙarfi!'mutanen da suka biyo bayan shi su kaja hankulan mutanen dake cikin falon har da Bintu wadda tayi saurin miƙewa cike da farin ciki ta rungume Hajjo da Anty Asma'u,take kuma kallo ya koma sama hatta da shi kansa Abba Umar ɗin da mamakin inda Bintu tasan su Hajja yake kallonsu, Abdallah kuwa wani irin murmushi ne ke fitowa daga bakinsa zuwa saman leɓansa,Alhaji Baba ne yace"Batula kin san sune?da sauri tace"Baba wannan kakata ce,da yayar ummina!'wata irin zabura Anty Nafisa tayi tare da cewa ƙarya kike wannan abun ba zai taɓa tabbata ba,bazaki taɓa zama ƴar Umar ba,kamar yadda ban taɓa haifa masa ɗa ba!'Abba Umar kamar wani dolo haka ya tsaya yana bin Bintu da su hajjo da Nafisa da kallo,gaba ɗaya ya rasa tunanin da zaiyi komai nashi ya tsaya,
Chapter 105 · 0% Book details