← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 120

Sashe 59

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ɗan bin ɗakin tayi da kallo tana wani irin murmushi me cike da jin daɗi,tasan zata samu abin da takeso saboda mijin ta bai iya ɓoyo ba, dan haka tana da yaƙinin cewa bazata sha wahalar haɗa muhimman kadarorin sa ba,wani tunani ne ya faɗo mata wanda yasa ta ɗan cizan yatsa, ko wane abune Bintu zata gaya mata ta fasa? tabbas a kwai ayar tambaya akan wannan lamarin akwai abinda Hajiyarta ta gargaɗi Bintu da kar ta gaya mata shi,to meye wannan dahar Hajiyar ta zata iya munafuntar ta akan sa wane abu take son ƙullawa batare da sanin ta ba?wata zuciyar tace da ita kin manta halin ladidine? komai fa A kace ta aikata indai akan kuɗi ne tabbas zata iya ai katashi,to amma meye na ɓoye mata?wani ɓangare na zuciyarta ya kuma cewa da ita a'a Nafisa karkiyi saurin yanke hukunci ki bari ki lallaɓa Bintun ta sanar dake abinda yake da akwai, daga baya saiki yanke hukunci,da wannan tunanin ta tashi dan fara binciken abinda ya kasan ce shine burinta da buƙatar ta,

Wai shin ina Abigirl ta lula ne? Tunda ta tafi garinsu can inugu bata ƙara waiwayar Abuja ba balle kuma tunanin mijin ta, ita dai kawai tunda tana ganin ta tsira da rayuwar ta to shike nan,sai dai abinda bata sani ba shine,tuni Dady jafar ya sanar da Abdallah yana zargin Abigirl amma bai sanar dashi ainahin abin da ya saurara daga gareta ba, dan yasan Abdallah idan ya sani ba lallai ne ya barsu subi aikin A sannu ba,cikin zafin zuciya zaibi lamarin na Abigirl tunda dama yana ciki da ita Abigirl ɗin,kuma hakan da zaiyi, shi zai ƙara bawa makiyan su damar da zasu iya cutar dasu ba tare da sun ankaraba,dan haka ya ɓoyewa Abdallah komai,shi kuma Abdallah batare da ɓata lokaci ba yasa akabi masa bayan Abigirl tare da ɗauko masa duk wani bayanan ta, da duk wani motsinta.

Shi Dady jafar so yake sai Abigirl ta sakan kan ce kawai sai su sa aɗauko ta, dan ta amsa tarin tambayoyin da shima yake matuƙar buƙatar jin su daga gareta,lallai ya zaƙu yaji yadda akai tasamu Fatash wanda A yanzu ya koma Abdallah?kuma waye suke waya da shi?meye burinta akan Abdallah? me yasa kuma take ƙoƙarin kashe shi a halin yanzu? tunda tace kasheshi shine marufar asirinta,kuma gashi duk da haka sai da abin da take gudu ya faru,wanda shine dalilin da yasa tayi masa ƙaryar mutuwa ta gudu garin su?ɗan ƙara gyara kashingiɗar sa yayi tare da cewa, afili tabbas komai ya kusa ƙare muku duk wani munafiki an kusa yin walƙiya dan muga fuskokin ku,asirin ku duk ya kusa tonuwa,ɗan zakin da suka hana shaƙar numfashi tare da iyayen sa to shi zai ruguza tasirin su da duk wani makircin su,insha Allah lokaci ya kusa,shi kan sa ya ƙagu yaga ɓaƙaƙen fuskokin su,badan farin ciki ba sai dan san ganin ƙarshen su, insha Allah ƙudurar Allah ta kusa baiyana.

Akan idon Taufiƙa Bintu ta fito daga sashen Abdallah, jikin ta sanye da rigar baccin da yabata ta saka a daren jiya,Bintu da ta fito a saɗaɗe dan kar inno ta ganta, sai tayi turus ganin Taufiƙa zaune akan kujera tana watso mata wani irin kallon tsana mai cike da ɓakin ciki mara misali,A hankali Bintu ta ɗauke kanta tare da cigaba da ta kawa dan isa ga ɗakin ta,tsayuwar da Taufiƙa tayi agaban ta shi yasata ɗan ja da baya tare da zubawa Taufiƙa ido kamar yadda itama Taufiƙan take bin duk ilahirin jikin Bintu da kallo na tsan tsan tuhuma da san gano wani abu, Bintu gefe taja da niyar canja hanya da sauri Taufiƙa ta wani sa hannu ta finciko ta ta dawo baya,tana wani irin huci na tsan tsan baƙin ciki da hassada, Bintu tsayawa tayi tana kallon ta cike da jiran ko takwana dan ta ɗau alwashin ta daina ragawa kowa dake cikin gidan, dan da hakane kawai zata samu ƴancin yin abinda ya kawota batare da tunanin wasu shirgin ƙwarƙwata ba.

"Ke mahaukaya ƴar talakawa matsiyaciya,macijiya mai saran ƴaƴan masu gida da mugun dafin da yafi na kowace macijiya zafi da raɗaɗi,kinzo kin kanai naye wa mutane gida sai kace ramin macijin ubanta da na uwarta masu saran ɓoye,su noƙe su nuna tamkar basu taɓa saran ko wane ɗan adam ba,to ina mai tabbatar miki da cewa muddin baki fita hanyar ahlina ba saina kassara rayuwar ki yadda nan gaba bazaki iya moruwa ko ga makaho ba balle mai ido da cikakken lafiya,zan tabbatar miki da abinda nake faɗa in dai har baki san inda dare yayi miki ba!'wani mugun kallo Bintu take bin Taufiƙa dashi har ta kammala zantukan ta cikin wani irin huci da sauke numfashi,tsaki Bintu tayi tare da cewa,me kike da suna Taura ko Tofi? to inaso ki sani duk abinda kuke yi ba wai dan kun gagari Bintu bane yasa ta kasa yin komai ba, a'a sai dan ina da manyan kune ku kun yi min ƙanƙanta A sarah sai dai na sari na sama daku domin yaƙi na dasu nakeyi bawai daku ƙananan marasa kunya da abinyi ba,tabbas Ni macijiya ce amma inaso ki ɗan da ɗan lokaci dan in tabbatar miki da hakan, Taufiƙa Ni macijiya ce wadda idan tayi sara sai dai mutum ya mutu ko ya na ƙasa amma ba dai a warke ba,idan kina buƙatar sarana to ina so kibi ayari domin abin layin markaɗe ne bai zo kan ƙaramin kai irinki ba,idan na gama da manyan kawuna zan tsaya na saurare ki,kuma kisha kurumin ki ki daina haƙilo shi wanda kikeyi dan shi wallahi ko fuskarki ba zai tan-tance ta cikin ahlin ALHAJI BALARABE ba balle yayi miki duba irin na zumunci balle kuma duban soyayya, Oga Abdallah yafi ƙarfin ki dan ba dan irinku Aka halicce shiba Allah ya halicci bawansa Abdallah don mata masu kyakykyawar zuciya da tsoron Allah da kuma taimakon bayin Allah, zuciyar Oga Abdallah ta zinare ce ke kuma ta gawayi,to gaya min tayaya wannan haɗin gambizar zai yuwu,dan haka ki sawa zuciyarki shidin ba abokin rayuwar ki bane dan insha Allah Allah ba zai yi masa wannan jarabtar ta Auren ki ba ko iri-irin ki ba,ina so ki cigaba da saka ido akan wannan wasan Ni kuma insha Allah zanyi miki addu'ar tsawan kwana domin kiga ƙarshen wasan wanda zai zama gaskiya Abdubint for ever,ya kika gani?Taufiƙa ki kiyayi ranar na dama ranar da nasani ranar da sirrin ɓoye zai fito ranar da fuskoki da yawa zasu baiyana suna masu kaico da rayuwar da suka shuka,ki kuma kiyayi ranar da ƘUDURAR ALLAH zata baiyana,dan haka ina mai baki shawara da ki tuba tun kafin ranar dan karki kasance,cikin masu danasani wadda zata zamar miki ƙeya,kuma zaki kasan ce cikin mutanen da saran da nayi musu shi kaɗai ya isheki ba sai na kai ga asarar zubar da dafina ba!'har zata wuce sai kuma ta ɗan juyo dai-dai saitin kunnen Taufiƙa wadda ta tafasa kamar wuta saboda zafi da mamakin kalaman Bintu wanda suka matuƙar sakata cikin ruɗani da shakku mai tsanani akan Bintun,tace"abinda na manta ban gaya miki ba shine dafina baya cin wanda ya tsaya ga Allah ya kuma kiyaye dokokinsa,dafina ya tsaya ne akan mugaye ɓaragurbi masu ɗoyin baki da ƙwaƙwalwa,daga haka tayi shigewar ta ɗakinta tare da banko mata ƙofar da ƙarfi saboda ƙara tura mata haushi.

Tabbas idan taufiƙa tace"maganganun Bintu basu taɓa ta ba tayi ƙarya,sosai kanta ya kulle tare kuma da san neman ƙarin haske ga kalaman Bintun wanda suke kama da magana mai harshen damo,a kwai manufa A cikin kalaman Bintun,cikin mutuwar jiki da zuciya taja jikinta ta shige ɗakin su.

BaTaufiƙa ka ɗai ce ta shiga halin rikicewa da kalaman Bintun ba,hatta da Abdallah da Hajiya Babba da ta kawo kai dan sanarwa inno kiran gaggawar da ya same su daga Alhaji Baba sai da ta shiga wani yanayi na matukar zurfafa tunani,kasa shiga falon tayi ta koma saboda bazataso wani yaganta cikin wannan hali na kiɗima ba.

Tun dawo war sa daga masallaci da ya wuce tiraning sai lokacin ya shigo, wanda shigar sa ke nan kunnuwansa suka fara jiyo masa kalaman Taufiƙa, tsaki yayi zai wuce saboda bai ga amfanin sauraren shashan cin Taufiƙan ba,amma kafin ya saka ƙafar sa cikin falon sa ya tsinkayo ɗaɗdaɗar muryar Bintu tana maida wa Taufiƙa Raddi cike da kar sashi da kuma san zuwan wata rana mai ɗinbin tarihi agareta,tabbas shima ya shiga halin rikicewa da wannan sabon Al'amarin, tabbas ya daɗe yana tunanin abinda Bintu takeyi bai ci ace wai dan taimakon musulunci kawai take ba, idan yayi duba da ranar da ta bashi tabbacin zata taimaka masa da dukkan rayuwar ta,tabbas ranar ya hangi yadda wutar fansa ke ci a tsakiyar idanunta,to ga kuma wannan kalaman nata masu shige da har shene damo,meye gaskiyar tarihin wannan yarinya meye gaskiyar,abinda ya kawota ahlin nan?kai akwai wani abun da Bintu ta ɓoye wanda ita kaɗai tasan shi sai Ubangijin ta,ta yaya zaiyi ya gano wannan gaskiya da ta ɓoye masa?anya kuwa Bintu bata da alaƙa da ahlin ALHAJI BALARABE?dafe kansa yayi A yayin da yake zama ƙasan carpet ɗin dake malale tsakiyar haɗadɗan falon nasa,tare da runtse idanun sa,wai meye yasa abin mamakin cikin gidan nan baya karewa?kafin ya gama da wani al amarin wani ya taso, tabbas al al'amari Bintu wani babban al amarine da dole sai ya nutsu dan gano shi,kuma shi kaɗai zaiyi wannan binciken batare da sa hannun kowa ba kuma zai bar shi a matsayin sirrin zuciyar shi,

Hajiya Babba tunda ta koma ɓangaren ta take kaiwa da kawowa itafa a rikice take da wannan al amari na Bintu, tabbas A kwai wani ɓoyayyen sirri da Bintu take ɓoyewa,to me yasa takejin wani irin sabon kusanci A cikin jikinta game da Bintun? kuma tanaji ajikinta komeye agame da Bintu to Alheri ne,(Hajiya Babba macece mai matuƙar dogon hange da baiwa mai tarin yawa to ba wani abin mamaki bane dan shaidar Bintu jikar tace ta baiyana acikin jikinta da zuciyar ta duk da ita bata taɓa kawo wannan tunanin ba) amma tabbas tanaji ajikin ta Bintu haske ce ga ahlin ta kuma madubi mai haska baya,
Chapter 59 · 0% Book details