Sashe 16
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jiki asanyaye aunty nafisa ta karasa kan kujerar da ta tashi tare da zubawa bintu dake durkushe kan kafafunta Ido, abubuwa masu tarin yawa take kissimawa azuciyarta, sam zuciyarta taki yardan mata da bintu, sai dai kuma abun babu sauki sarayar da bukatar hajiya ladidi, hakan yana nufin dai dolenta ta zauna inuwa daya da bintu,wani zazzafan huci ta furzar, sannan ahankali ta daga kanta tana duban hajiyarta da ta zuba mata ido, tana mai karantar zuciyarta,hajiya ladidi tace"kyale ki nayi ki gama fita daga rudani da kuma kokwantan da zuciyar ki tashiga, wanda nima saida hakan ta faru dani ayayin da naci karo da wannan ko daddiyar fuskarta, sai dai kuma inaso duk wannan mu ajiyeshi agefe dan bai da wani amfani agaremu, zurfafa tunani akan zahra bashine damuwata ba, damuwata shine yadda zatayi mana aiki batare da faduwa ko samun akasi ba, ina fata kin fahimceni dakyau? ahankali aunty nafisa ta zare ta gumin da ta tafka, tare da cewa shike nan hajiya duk abinda kikace haka za ayi!' murmushi hajiya ladidi tasaki, kana ta juya tana fuskantar bintu yayin da take kara kokarin tsuke fuskarta, tace" kee" kisaurareni da kyau kiji abinda nakeso na gaya miki da farko dai zan tambayeki shin kina san rayuwar ki?afirgice bintu take duban hajiya ladidi, yayin da jikinta ya shiga rawa cikin zuciyarta tace" shike nan wayyo fafina bintunka ta shigo hannun yan yankan kai shikenan tawa takare!'wata masifaffiyar tsawa aunty nafisa ta daka mata kee" mahaukaciyar inace kinaji ana maki magana kina ji kina kallon mutane da wannan dakwalayen idanun naki masu kama da na mayu, nutsuwa zakiyi ki saurari umarnin da zamu baki, indai kuma har kina san cigaba da rayuwa aduniya, dole kibi umarninmu wannan shine ma'anar tambayar da hajiyata tayi miki, doluwa shashasha kawai!'ta karasa maganar tare da dora mata wani zazzafan kallo, mai cike da tsantsar tsana ta babu gaira ba sabar.
Hajiya ladidi ta dora mata da zaiyano mata bukatarsu akan abinda sukeso tayi musu agidan da zasu kaita aiki, wani irin gumi ne yashiga ketowa bintu tako'ina yayin da zuciyarta tashiga wani irin tsalle tamkar zata hudo kirjinta ta fito, to me hakan yake nufi? ta addanci, zuciyarta tayi saurin bata amsa,to Ina makomar rayuwarta?Ina imaninta da tausayinta? Ina addinin ta na cikakkiyar musulma? Ina makomarta awajen ubangiji?Ina burinta nasan binciko mahaifiyarta da fafinta? ina burinta nasan tarwatsa makiyansu da tona musu asiri? lallai ni Fatima bintu ina cikin tsaka me wuya,anya ba gara su kasheni ba, da na aikata wannan mummunan aiki?to yaya zanyi?meye mafita agareni? tsinkayar muryar hajiya ladidi tayi akanta tana cewa tashi ku tafi inkin gama nazarin da bazai amfanekiba!'atsorece ta dago kanta cikin wani irin kuka tace hajiya dan Allah kimin rai..kafin ta kuma samun damar bude bakinta aunty nafisa ta dauke fuskarta da wani irin gigitaccen mari, wanda take agurin ji da ganin ta, suka dauke na wasu yan dakiku,aunty nafisa ta dora da cewa, indai har kikace gaddama zaki mana
to tabbas rayuwar ki tana cikin hatsari, dan haka tun kafin na kara miki wanda yafi wannan ki goge wadannan shegun hawayen naki ki kuma shanye kukanki dan gaba zai miki amfani!'hajiya ladidi tace da kyau nafisa ni nasan ban haifi lusara ba, aikinki yanayin kyau yadda ya kamata kutafi kawai bani da haufi akan bar miki ragamar komai ahannunki!'tace karki damu hajiyata ko mai zai tafi daidai kamar yadda kikeso! bintu kuwa tun marin da aunty nafisa tayi mata tare da koro mata jawabai da manyan gargadi tayi dif sai zuciyarta dake wani irin zafi da tururi tare da wani irin tsanar aunty nafisa, sai dai tayi kokarin rarrashin zuciyarta kafin ta samarwar kanta mafita,kallo daya aunty nafisa tayi mata,aiko cikin sauri da rawar jiki tare da matsananciyar tsoron aunty nafisan ta juya ta fita daga dakin, yayin da nafisan ta bi ta abaya tana mai Jan wani dogon tsaki wanda ya shiga har tsakiyar kwakwalwar kan bintu.
Suna fita hajiya ladidi ta dannawa Alhaji munir kira, tace Alhaji kayi hakuri na zartar da hukunci ban rigaya nasanar dakaiba!'ta can bangaren cikin yanayinsa na nutsuwa yace me ya faru ladidi?tace dama nafisace tazo yanzu tace Alhaji baba yana nemanwa inno 'yar aiki shine nace tunda ga zahra kuma yarinyar tana da nutsuwa me zai hana su karbeta, to kuma nafisan tana ganin ta ta dage wai dan Allah abawa inno din, saboda yarinyar ta shiga ranta da gani zatai hankali,nace tabari ka dawo taki, tace nai maka waya!'shiru tayi tana sauraransa,yace babu damuwa indai bazata takuraba kuma babu tsangwama, shikenan sa iya tafiyar? daga haka ya yanke wayar,ta wani tabe baki tana kwaikwayonsa kamar agabanta yayi maganar,babu damuwa indai bazata takuraba, kuma bazata tsangwama ba!'taja wani dogon tsaki waikai na Allah to muma ai bamuce bazamu tuba ba amma ba yanzu ba.
Tunda suka fara tafiya bintu ta kunshe kanta tana Jan sheshsheka ahankali sabo da tsoron aunty nafisa, ahaka har suka karasa dan kareren estate din na Alhaji balarabe, ahankali bintu ta dago kanta tana bin mikakken titin dake shinfide, tamkar titin da zaikaika wani gari daban ba cikin estate ba,sunyi yar doguwar tafiya kafin su ratsa ta wani karamin titin wanda shine yasadasu da manya-manyan gidajen dake jere reras hagu da dama gwanin ban sha'awa,motar na tsayawa bintu tayi kokarin fitowa, sai kuma wani tunani ya zo mata karfa taje ba gidan bane fitowarta ya zama matsala, a'yan awannin da sukai da aunty nafisa ta fahimci jiran kiris take yi akanta, tasamu damar cimata mutumci harma da guzurin matuka, dan hakan zuciyarta cike take da tsoro dan hakika batasan me yakamata tayi ba, kafin takai ga samun mafita taji anyi mata wata kyakykyawar figa, hadi da ingizata, da kyar tasamu damar dafa jikin motar wanda shine ya taimaketa daga mummunar faduwar da take shirinyi, ahankali ta dago kanta da manyan idanunta da suka cika da ruwan hawaye, takalli aunty nafisa dake kallonta tamkar ta jawota tayi ta dukanta,cikin huci tace" mata tunda so kike na fito dake gashinan na fito dake saiki wuce muje!'jiki asalube bintu tabi bayanta zuciyarta cike da tsanar aunty nafisa, tana kuma aiyanawa aranta kome zasuyi mata sai ta gudu tunda su ba Allah bane.
Wani Abu aunty nafisa ta danna ajikin kofar, sai ga kofar falon ta bude, hauwa'u da amna da rahima ne afalon,babu wata hayaniya dasukeyi kamar da, saboda yanzu basa samun damar watayawa abangaren inno kamar da,zaman ma basosai akeyi ba, sai dai su amna din saboda jarabar da suka dorawa kansu ta mahaukaciyar soyayyar abdallah,
Sallamar aunty nafisa suka amsa tare da zubawa bayanta ido,rahima ce tace" waw aunty nafisa a'ina kika samo mana balarabiya?gaskiya wannan ko acikin larabawan ita mai kyauce!'aunty nafisa taja tsaki!' gami da cewa ke kam rahima kin ga takanki da surutu daga ganin abu sai ki fara zuba!'amna tace"kai aunty nafisa wallahi yarinyarce me kyau!'tace to aikwa barni na zauna kafin ku isheni da wadannan tambayoyin naku!'ta fada yayin da take samun gefen kujerar da hauwa'u ke zaune ta zauna, kana tace"hauwa'u Ina inno ?dan kifi wadannan taron yarintar hankali!' hauwa'u da hankalinta ke kan wayarta, tun kallo daya da tayiwa bintu bata kara daga idonta ba, tace"aunty nafisa kinsan ni ba komaine yacika yimin kyauba dan wani kyan ma ni tsoro yake bani, kamar dai wannan tayi nuni da inda bintu take atsaye har yanzu ba abata damar zama ba,aunty nafisa tayi wani kayataccen murmushi tace" yauwa yargidana duk muna gari daya kenan,amma dai yanzu bari na kira inno tukunna!'gani me akasamomin aketa nemana? inno ta fada yayin da take kawo kanta cikin falon, aunty nafisa tace" yauwa inno karaso kiga abinda nakawo miki!'karasowa tayi tana cewa to gani abani in abun dadine!'rahima tace" ke kam dadina dake shegen kwadayi to ba abun ci bane!ta fada ayayin da take juyawa gurin bintu dake kame atsaye kamar sojiya, kafafunta har sun fara rawa saboda gajiya, tace" me kyau zo ki zauna kinji Allah sarki mun barta atsaye tun dazu!'ta karasa maganar cikin tausayawa,sai alokacin inno ta lura da bintu data zauna adarare taki bari su hada idanuwa da aunty nafisa,inno tace" nafisa kar dai har kinsamo mana 'yar aikin?gashi kuwa kin gani inno!' cewar aunty nafisa,inno tace masha Allah yarinya karaso nan, meye sunanki? ahankali bintu tace" zahra!'cikin farin ciki inno tace kai masha Allah nafisa kinyi kokari yarinyar tana da nutsuwa da gani kuma zatai tarbiya,daga Ina aka samota nafisa Ina iyayenta? aunty nafisa tace inno wannan fa da kike gani marainiyace gaba da baya bata da kowa kishiyar maman tace ta kareta wai ta gaji da ciyar da ita, shine fa tazo garinnan shi kuma alhajinmu ya samota akofar gida dan ya taimaka mata!'inno ta kalli bintu tace 'yar nan kin tabbatar gaskiyar labarinki kenan? bintu ta daga kanta idanunta na zubar da hawayen tausayin kanta, inno tace" to taso ki biyoni ta dubi aunty nafisa tace" nafi bari na gabatar da ita gun babanku!' gyada kanta tayi tare da cewa to inno amma ni zan wuce gida bazaki sameni ba!'inno ta amsa mata da cewa shikenan nafi Allah yayi albarka!'ta amsa da amin!' tana mikewa dan fita alokaci daya kuma tana aunawa bintu kallon gargadi, inno tace" taho muje kinji!' ahankali tabi bayan inno cikin takunta na nutsuwa nutsuwa,