← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 120

Sashe 4

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhj balarabe,mutumne kamili, me tsananin riko da addini, me kokarin bin dokokin' Allah yana da, kyauta base lokacin zakka yake kyauta ba, kullum hannunsa abude suke akwai temakon addini, Yana kyautatawa iyalinsa balle kuma iyayensa,shi mutum ne me San gaskiya da fadin ta dan haka yake da farinjini cikin al umma talakawa sunyi kokarin jan ra ayinsa dan yatsaya musu amatsayin gwam nan jiharsu amma fir yace!" shi baze saka kansa aharkar da zatasa ya kauce hanya ba, dole haka suka hakura.

Awannan tsukinne malam habu da matarsa nana sukace !"dole zasu koma gida, dan duba bayan ragowar yan' uwa, sede Kuma ashe ajali ne ya kirasu jirginda suka hau gaba daya ya tarwa tse' asakamakon birki da ya kwacewa matukin,

"hakika alhj balarabe yaji mutuwar iyayen nasa, sede dole ce, Kuma rigace ajikin kowa yadda, mukazo haka zamu koma.

Rayuwa taja, shekaru sun tafi, alhj balarabe ya samarwa yayansa in gan taccen ilmi na zamani da na boko.

"ya' aurar da nana karama ga dan babban amininsa,
salisu se sakina da ya aurawa yaransa rufa' i

Alokacinne kuma'aka gama, gina babban estate
dinsa wanda yakeso ya tasar da zuri' arsa ya hade su guri guda,duk kuma asannan ne yaje ya taho da danginsa na kasar maroko dan cika burin mahaifansa .

"Baffansa 'kani ga malam habu, se kanwarsu wadda ta kasance' auta' adakinsu, sune danginsa najiki tare da iyalansu.

"Baffa ali duk da ya tsufa amma' da dan kwarinsa ,
Se matarsa inna hafsatu,
da da yayansa biyu,bab ban shine sa' an alhj balarabe sunansa hashir yana da matarsa daya yayansa uku se kaninsa me bi masa Mas' udu Shima matarsa daya da yaya hudu ahmad da, sadi se kuma nadiya da maryam.
anan yazo ya hadesu' awaje daya kowa da bangarensa, ya bawa ko wannensu abunyi,kana kuma yayansu ya sanya su amakarantu ya basu' ingantaccen ilmi babu nuna san kai ya dauki yayan yan' uwansa tamkar nasa na cikinsa.

Yayan hajiya yagana wadda' ake mata lakabi
da hajjah sune nana karama, sakina hafsa, bilki, mansur, habibu

Se yayan hajiya zainab ita kuma ana mata lakabi da inno, yaranta hudu mata sadiya,amina, zakiya, asiya

Yayan safiya yar agadex wadda ake mata lakabi da hjy babba,sune' abubakar, hasana da husaini, se aliyu, usman,

A yanzu gaba daya wadan nan iyali suna hade guri daya banda matan da sukayi aure awaje.

Tofa anzo gun, ku gyara. zama domin jin me ake shiryawa,ake kullawa? suwaye masu shiryawar ? suwaye bosa bosan cikin estate din alhj balarabe?

A, fage na gaba zamu zakuloka fatash dole ka fito muganka mujika ehe

har yanzu ba'asoma wasanba.

Dattijon bauci fafin bintu
anya kuwa kana da gaskiya? ammafa bani na fada fans din, KUDURAR ALLAH ne....

Comments........
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GsLlgKf7MsD3M4Hoo7U65P

💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 4 ```

'Ya'yan alhj balarabe kaf
dinsu, su goma sha biyar ne,maza takwas mata ta-
ra, sai kuma na 'Yan uwansa hashir da mas'-
udu guda uku-uku,

Alhj balarabe Yana da abokai ko nace aminai guda uku, wa'yanda yayi matukar yadda dasu abokaine na amana matuka da gaske,
alhj kabir me auduga da alhj nasir sai alhj shams,
amintar dake tsakanin su
ne yasa har suka hada au
re tsakanin 'ya'yansu,
alhj kabir 'ya'yansa uku namiji daya mata biyu, sai alhj shamsu shi yaran
sa biyu'amma 'kananu ne kasancewar basu fara
haihuwa da wuri ba sai bayan shekara goma sha biyar, sannan allah ya ba
su yara biyu duk maza,
alhj nasir ma babban dan
sa guda daya ragowar guda biyu duka yarane shima tunda'aka haifi' ila wato isma'il saida aka ja shekaru kana aka samu kannensa,

Ayanzu haka alhj balarabe ya dan man
manyanta tunda har an fara aurar da jikoki
amma baza ka taba gane
haka ba, saboda tsufan alhj balarabe tsufane me kyau, wanda yake cikeda jin dadi gami da kwanci
yar hankali, dan da 'kau yake,to baffansa Ali ma yake nan babu wata ta
waya atare dashi sai na tsufa bare kuma shi da yake da manya 'ya'yan banki,

Nana karama babbar 'ya agurin alhj balarabe ya aurarta ga dan amininsa
alhj kabir me suna salisu suna zaune suma acikin garin abj da yaransu hud
u khadija, haulat da Fa'iz
da kuma ahmad,
sai sakina da rufa'i yaran babanta alhj balarabe su
kuma suna kano shi ya ke rike da shagonsa na daban gari,'ya'yansu biyar
mata biyu maza uku,

Sai hafsa ita kuma tana maidugu a 'bangaren mahaifiyarta tayi aure yaranta hudu itama duka mata rukayya fauziya kal
tume da amina (amna)

Sai Kuma bilkisu da nura hashim,yaransu uku najib da najiba sai hauwa'u,

Habibu da saratu hashim
yaransu hudu duk mata,
farida zainab da sakinatu

Husaini da nadiya mas'u
d 'ya'yansu biyu mace da namiji,

Ahmad da hasana yaran su uku duk maza nabil nazir da Kuma najib,

Amina da bashir yayansu
su kuma kananu ne basu haihu da wuri ba yaransu hudu,

Zakiya kuma da dan alh nasir wato isma'il suma
basu taba haihuwa suna nan cikin anguwar metama sule,

Acikin 'ya'yan alhj balarabe
e wadan dan sune sukayi auren zumunci,

Abubakar shine da mafi soyuwa azuciyar mahaifinsa, kuma babba awajen mahaifiyarsa hjy babba,
daya tashi sai bai tsaya, a ko'ina ba sai jihar gombe ya auro san kace ciyar bafulatanar matarsa zulaihat, kyakykyawar ba fulatanar gombe me kyak kyawan asali da tushe, ta kuma shigo cikin zuriya r alhj balarabe, taketa zaz zago masa kyawawan 'ya
'ya maza har guda biyar cur sai auta rahima, su shida ke nan, ayan zu haka biyar ne awajensu,
mu'azzam muhamud abdurrahim da abdulsha-
kur da Kuma auta rahima ,

Sai asiya itama tana kd da nata iyalin guda hudu

Mansur abokiyar aikinsa ce me suna rabi'a yayan su uku Yar kanoce aikine ya kawota abj take zaune gurin yayanta,

Aliyu Kuma kanwar aboki nsa ce" yayansu hudu maza biyu mata biyu

Shi kuwa umar hjy zainab
(inno) itace" ta hadashi da ' yar' aminiyarta hjy ladidi me suna nafisa,

Hjy ladidi ' yar' salin garin minnace, aurene ya, kinki mota ya kawota garin abj
da yarta guda daya tilo nafisa ba sai nace muku nafisa ' yar gata bace ku kanku zaku fada, kasan
cewa kowa yasan yadda d'a guda daya yake agun iyayensa to irin wan nan son akewa nafisa agidansu,
""itaka kadaice'acikin suru kan alhj balarabe bata taba haihuwa ba ko batan wata kuwa,

Yakamata musan meye halaiyar alhj balarabe,

Alhj balarabe mutum ne me tsananin addini da ku ma amfani dashi yana da
tausayi da hakuri haka kuma ya' iya mu' amala da mutane yana da san kyautatawa' al 'umma, ya gina makarantu da masallatai babu adadi, ga asibitocin da ya gina dan kawai tallafawa marasa karfi da Kuma marayu,
wannan dalilin ne talaka
wa su kaso ya tsaya musu
amatsayin gomnan jiha
amma sai yaki fur, acewa
rsa" bazai taba iya shiga abinda zaisa yasa 'bawa mahaliccinsa ba,
da wannan' hujjar tasa suka hakura badan sun so ba,

Alhj balarabe baisan
wace irin waina ake toyawa a,cikin estate dinsa ba,zuciyarsa daya yake kallan kowa baya kuma
tunanin ana aikata wani
mummnan ta adi,

Yana can hadadden ban
garensa shi da matansa
dattijan da jin dadi da da ula suka boye tsufansu,

Inaso makaranta kuyiwa labarin KUDURAR ALLAH
kyaykywar fahimta, shine dalilin da yasa na fayya- ce muku sunayen ' ya'yan alhj balarabe da kuma wadànda suka rabeshi,

Hali,dabi'a da Kuma manufa duk suna cikin labarin,

CIGABAN LABARI

...…..Estate.....

Wani kimtsetstsen falo ne me matukatukar gir
ma da kyau wanda yaji kayan more rayuwa da dima- diman kujeru masu
tsananin kyau da burge-
wa,babu wasu yawan tar-
kace acikinsa bayan sai-
tun kujeru kala biyu sai kuma run dumemiyar placzima tv,

Wani sanyayyen kamshin
turaren wutane tare dana
air freshener, wanda suka hadu suka bawa falon wani ni'imtaccen kamshi me san yaya zuci
ya,

Saidai duk wannan ni'ima hakan bai hana damuwar
hjy zulaihat kassara ruhin
ta ba,
""cikin tsananin damuwar dake cin zuciyarta tasa hannunta ta dafe saman
kanta dake barazanar barin gan-gar jikinta sabi da tsananin sarawar da yakemata,

Rahima dake tsaye akarshen matakalar da zata sadaka da falon ta
bangaren hagu,yayinda hjy zulaihat ke ta bangaren gabas akan 'kawatattaun kujerun dining table din da ya ma
maye gurin,ayanzu kanta a,kife yake dan haka batasan rahima ta zoba,
sai kawai ji tayi andafa kafadarta, cikin tsananin
tsoro da firgita!' ta dago kanta, ganin rahima ce yasa ta saki wata 'kak'kar
far ajiyar zuciya, kana' ta
yi saurin goge hawayen da suka 'bata kyakykya-
war fuskarta tare da 'kirkiro murmushi akan fuskarta.

Hannun rahima ta kamo tare da kokarin boye damuwarta, tace" rahima
'yanmatan Abbie ba ki koma bacci ba?
rahima da tacika da tausayin ' ammin tata,
tace" ammina yaza'ai na
iya bacci bayan kina nan
cikin wani'mugun yanayi
da tsananin damuwar da
take neman hargitsa farin cikina,
"taci gaba dacewa" ammi tun ban mallaki hankalin
kainaba nake ganinki cikin wannan damuwar,
kuma duk sanda natam
bayeki saikice mun bahurumina bane, ammi
meyasa? ta fada cikin zubar da wasu zafafan hawaye,

""Cikin nutsuwa irin ta mata masu tsananin hakuri ammi tace"rahima
kinutsu kidena wannan ihun haka!dan wani zai' iya shigowa ya Kuma fuskanci halin da muke
ciki,hakan Kuma bakara
min hatsarine agaremu ba dagani harke!
wannan damuwar da kike
gani' atare dani sirrin rayuwata ce"kuma jinsa ga wani fansane garayuwata da kuma rayuwar wasu,dan haka inaso kikama kanki da
dakyau ki adana wadàn nan shir mammun tambayiyin'naki!takarasa maganar da wani irin hada rai dan karma rahima tasamu damar
ragargazo mata wasu tambayiyin,
Chapter 4 · 0% Book details