← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 120

Sashe 75

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shiga zauren malam bayan anyi musu iso,ji tayi kanta yana juyawa har tana ƙoƙarin faɗuwa da sauri Abdallah ya tarota jikin sa,suka zauna, cikin girmamawa Abdallah ya gaida Malam,daga nan basu sake cewa komai ba,bayaga tsurawa Bintu ido da malam yayi yana nazarin al amarin ta,can ya ja dogon numfashi kana yace"Abdallah kayi tunani mai kyau da ka kawo yarinyar nan,saboda akwai al amari mai girma wanda yake a lullɓe tare da baiwar ta,ɗan sihiri ne yayi tasiri ajikin ta amma da baka kawota da wuri ba abin zai iya girmama!'shiru yayi na ɗan wani lokaci kana yaci gaba da cewa,yarinyar nan sai da aka sha wahala kafin wannan sihirin yayi tasiri ajikinta,kuma damar da aka samu akanta shiyasa baza a zaunaba ake kuma binta da abun,amma dai har yanzu ba ayi nasara akanta ba,saboda jikin ta ya ginu kuma tana cikin kariyar ubangiji,dan haka yanzu baza musha wahala akanta ba!'wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Abdallah ya sauke,yana kallon fuskar Bintu da bacci yayi awan gaba da ita,Tofi malam yayi mata tare da addu'oi sai magunguna da ya haɗa mata da yadda zata dinga amfani da su,ya miƙawa Abdallah tare da cewa gashi nan insha Allah kafin kazo karbar wasu ta samu lafiya, Allah Ubangiji ya daɗa karemu daga sharrin maƙiya, Abdallah ya amsa da Amin kana ya ajiye wa malam sadaka,ganin yawan kuɗin shi kuma yace"ba zai karɓa ba sadaka kawai yake buƙata,badan Abdallah yaso ba ya kwashe kuɗin sa kana sukayi sallama ya ɗauki Bintu kamar wata ƴar tsana ya nufi mota da ita,yana saka ta cikin motar ta buɗe idanun ta,gyara zaman ta tayi tare da kawar da fuskarta can gefe,suna fara tafiya wayar Bintu ta kuma yin alamar shigowar saƙo, wannan karon ma shine ya ɗauka,wan nan karon saƙon Dije ne,inda take sanar dasu ta fito ta kuma gaya musu inda Bintu zata zo ta same su,cikin sauri Abdallah yace"da Yahya maza faka motar nan kajira mu anan zamu dawo!'a kuma lokacin ne samuyal ya kawo masa a daidai ta,lokaci ɗaya naga Abdallah ya sauya kama wasu kaya ya saka baƙaƙe tare da wata hular gashi babu abin da zai sa ba zaka ce masa tsoho ba,dan sak ya juye wata suffar da ban,Bintu dai saboda tsabar mamakin sa tsayawa tayi tana kallon sa baki buɗe,ɗan ɗage mata gira yayi lokacin da suka haɗa ido da ita,tura baki tayi tare da cewa kai ka ɓoye kanka Ni kuma a ina zaka ɓoyeni?bata ankaraba taji ta cikin jikin sa yayi mata mayafi da rigar dake jikin nasa,cikin wata irin murya yace"anan zan ɓoyeki Bint duk San da kike buƙatar ɓuya kizo Ni zan ɓoyeki nayi miki rumfa yadda babu wanda zai ganki balle ya cutar dake!'wani irin rawa jikinta ya shigayi saboda wani shauƙi da ya lulluɓeta wanda ita karan kanta bata san komeye ba, ta dai samu kanta da matukar jin daɗin kalaman ogan nata wanda har saida ta kuma cusa fuskar ta tana shaƙar sassanyan ƙamshin sa me canja mata tunani,gaba ɗaya sun shiga cikin wani yanayi na matuƙar shauƙi,amma su duk basu san da haka ba, Bintu tana ganin kamar yadda yake matuƙar tausaya mata ne yasa takejin kanta a wannan yanayin,yayin da shi kuma yake ɗaukar haka amatsayin tausayi da kuma kasantuwar ta ƴar uwar sa ta jini wadda a yanzu ita kaɗai ke gare shi wadda zai kalla ya bigi ƙirji yace"ga ƴar uwar sa,ƙarar da wayar Bintu tayi ne ya dawo dasu cikin hayyacin su,cikin sauri ta ƙwace kanta daga riƙon da yayi mata tare da rarumar wayar tana karawa a kunnen ta, muryar Dije taji cikin faɗa faɗa tana cewa Bintu wai me kika tsaya yine?Ni fa har na kusa ƙara sawa wajen!'cikin rawar murya Bintu tace"ga,,, gamu nan mun taho!'kar ɓar wayar yayi daga hannunta bayan ya kashe,miƙa mata wata doguwar riga yayi baƙa me hula yace"maza saka kar mu ɓata lokaci!'karba tayi ta zura kana suka fito,a tunanin ta samuyal ne zai tuƙa nafef ɗin amma sai taga saɓanin haka,dan Abdallah wani mamakin ya kuma barinta dashi dan shine ya zauna a mazaunin draver ya kuma tada nafef ɗin,ganin ta tsaya taki shiga ya sashi cewa bazaki shiga ba kin san dai ba jiran mu zasuyi ba!shiga tayi batare da tace masa komai ba,sai dai zuciyarta cike take da mamakin sa da kuma tambayoyi.

Cikin gwaninta da ƙwarewa yake jan nafef ɗin har suka zo inda Dije ta kwatanta musu,sai dai daga can baya ya tsaya da nafef ɗin, juyowa yayi yana duban Bintu cikin bata ƙwarin gwiwa yace"ga ta inda suke can na sanki kina da dabara ba sai nayi miki bayanin yadda zaki ɓoye kanki ba!'jinjina kanta tayi tana ƙoƙarin fita,kama hannun ta yayi kana A hankali yace"Bint ki kula kinji,kiyi addu'a nima zanyi miki ki,ba tsayawa zakiyi sauraran wani abuba kawai ƙare mata kallo zakiyi,koda Allah zai sa ki ki iya gane ta a duk yanayin da kika ganta!'fita tayi da sauri ta nufi wajen da take da yaƙinin cewa su Dije suna gurin,guri ya samu ya ɓoye kan sa, sai dai ji yake kamar yabi bayanta,amma dai haka ya daure ya shiga Binta da addu'oi na kariya da neman nasara,

Lokacin da tazo dab da gurin sai ta shiga sanɗa da raɓewa ta yadda babu wanda zai iya ganin ta,cikin ikon Allah ta samu nasarar zuwa inda suke,waje ta samu mai matukar tsaro ta ɓoye kanta amma saida ta tabbatar da cewa zata iya ganin su sosai batare da ta samu matsala ba,zubawa matar ido tayi tana lura da duk wani motsinta da takunta, yayin da zuciyar ta kuwa ji take tamkar zata faso ƙirjinta ta fito saboda tsabar kiɗima,har yanzu tsoron gano wannan mata yana tare da ita,sai dai yayi sauƙi saboda samun ƙarfin gwiwa daga Abdallah,

Matar ta tsurawa Dije idanunta ta cikin niƙaf,tana daɗa karantar yanayin ta,can dai tayi wani murmushi ta cikin niƙaf ɗin ta,kana tace"anya Dije babu abinda kike shiryawa nifa har yanzu ina kokwanto a kanki!' sai kuma tayi shiru tare da ɗan yin taku biyu zuwa uku,kana ta da kata,cikin nutsuwa da taka tsantsan dije tace"ranki ya daɗe babu wani abu da nake shiryawa face abinda kika sakani,aikin da kika sakani shi kawai nakeyi!'to Dije idan haka ne ya labarin mutumin nan shin kun samo shi ne ko har yanzu ita ma ya gagareta?Dije tace"ranki ya daɗe muna kan hanya kuma insha Allah mune da nasara mun kusa kawo ƙarshen komai ina tabbatar miki da cewa bazan kuma bari mu haɗu ba har sai na samo miki ko wanene wannan mutumin!'dariya tayi wadda ta shiga kunnen Bintu,kana tace"yauwa Dije yanzu ne hankalina ya kwanta da aikin da kike min kuma na samu tabbacin kina yin abinda ya dace,dan haka Ni kuma zan zuba ido na saurari ranar da zaki kirani ki sanar dani ko wanene wannan shu umin mutumin!'daga haka,ta cigaba da taku dan barin wajen tana cewa saboda yardar danayi miki yau Ni zan fara barin wajen nan Dije na baki amanar rayuwata!'ba tare da ta saurari abinda Dijen zata ce ba ta yi hanzarin ƙara sa fita daga gurin wanda har saida ta taka ƙafar Bintu ba tare da hankalin ta ya kai kanta ba.

Runtse idanunta tayi cikin raɗaɗin da ƙafar ta take mata da kuma fargabar kar ta ganta, ga kuma ruɗaninda ta shiga na san tan-tance inda tasan me wan nan dariyar tabbas kamar taso ta gane Muryar matar duk da cewa ta rufe Muryar,haka kuma takun ta shima ya tsaya mata kai da duk yanayin jikin matar,tabbas tasan wannan mata kuma a cikin astate take rayuwa,lallai Dije tayi gaskiya kuma tayi babbar dabara da kawo wannan shawara,dan kuwa tabbas idan taga matar nan zata shaida ta Ali wane yanayi,sai dai kuma ta ina zata fara karaɗe ESTATE dan binciko ta?wata zuciyar tace ke Bintu biyota bai zama abu mai wahala a gareki ba sai duba ta a inda kike rayuwa,ko kin manta kina da jarumin maza kuma gwarzo a kusa dake,dan haka babu abinda zai gagareki a wannan karon kune da nasara,da wannan tunanin ta fito daga maɓoyar ta,wanda sai alokacin ne Dije ta san Bintu tazo,fita sukayi bayan sun tabbatar da tafiyar matar.

Daga ɓangaren Abdallah kuwa kaɗan ne ya rage zuciyar shi bata buga ba,shi da yacewa Bintu kar ta zauna me ya kaita daɗewa a inda shu'umar mata kamar wannan take,yana ƙoƙarin Binta sai kuma yaga fitowar matar cikin sauri ta tari a dai daita ta shiga suka bar gurin,da sauri ya fito daga maɓoyar sa,yana tunkarar wajen sai kuma yaga Bintun sun fito ita da Dije,Dije tace"Ni bari na samu nafef na wuce dan ba zai yiwu mu tafi tare ba!'jinjina kansa yayi tare da duntso kuɗi cikin aljihun rigar sa ya miƙa mata,karɓa tayi tare da yin godiya,ganin Bintu na ɗingi sawa yasa shi ɗan duban ƙafar tata,cikin alamun tambaya ya kalleta,tuni hawaye suka fara zuba mata cikin shagwaɓar da take halittar tace, tace"ba itace ta take min ƙafa ba!'kawar da kansa yayi tare dacewa to muje gida ayi miki allurar tetonos tunda wajen yayi jini kuma Allah yasa bata ganki ba!'ya faɗa yana ƙara haɗe fuskar sa,shuru tayi batace masa komai ba amma dai ta ƙudurta a ranta babu allurar da zata tsaya yayi mata,

A inda sukabar su Yahya a nan suka same su, nafef ɗin ya bawa samuyal,kana suka shiga motar, kayan jikin sa ya cire ya dawo Abdallahn sa na ainahi wanda har saida ya bawa Bintu dariya, sosai take jin dariya idan ta tuna shigar sa ta ɗazun wanda alokacin bata samu damar yinta ba saboda yanayin da suke ciki,kawai kallon ta ya tsaya yanayi saboda yadda yaga dariya tana mata kyau,ita kuma ganin ya zuba mata ido, sai ta bar dariyar tare da haɗe fuska wai dan karma ya ga fuskar da zaice zaiyi mata allura idan sun koma gida,wani ɗan murmushi ne ya suɓuce saman leɓan sa amma bai bari ta gani ba,ya gano ta sarai yasan abin da take yiwa gudu kuma allura ce sai yayi mata ko me zatayi,a haka suka karasa estate ɗin.
Chapter 75 · 0% Book details