Sashe 52
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bintu ta bita da wani mugun kallo tare da cewa insha Allah Asirinki ya kusa tonuwa da ɗai ɗai zaku fara girbar abinda kuka shuka wannan alƙawarin da na ɗauka ne!' hannun ta ta ɗora kan ƙirjinta tare da cewa Bintu ki kwantar da hankalin ki ki cire tsoro wannan yaƙin ba zai yiwu da tsoroba dole ki zama jaruma a filin daga.
Taufiƙa ta kalli Farida tare da cewa idan kin san zaki lalata mana shiri ka wai ki bari tunda kina tsoron Abdallah, Ni dai nasan bazai kasheni ba kuma na gaya muku muna gamawa zamu gudu gidan Nana Babba!'Siddiƙa cikin yanayin tsoro tace"wallahi Ni dai babu Ni bazan dakar masa mata ba,saboda tun kafin ta zama matarsa idan mukayi mata abu rama mata yake ballantana kuma yanzu,dan haka Ni dai babu ruwana!'Taufiƙa ta kuma kallon Farida tare da cewa ke kuma fa meye ra'yinki? dake Farida kusan halin su ɗaya da Taufiƙa shi yasa batare da jin ko maiba ta amince da shirin da sukayi dan tarfa Bintu suyi mata shegen duka,daga nan su bar gidan sai komai ya lafa.
Kallon ta take cikin tsananin baƙin ciki da tsana mara misali, ji take da zata samu dama da itace mace ta farko da zata fara ganin bayan ta, to amma yanzun ma bata fidda ran watarana wannan matar da har yanzu bata san ko wacece ba, zata kwashi kashinta a hannun ta ba,matar da take sanye da niƙab ta duƙa gaban mahaifiyar Bintu tace"lallai idan na bari kika cigaba da rayuwa a haka baƙaramin adalci nayi miki ba saboda ko ba komai zaki dinga jin labarin ɗiyarki kafin kiji labarin mutuwar ta wanda Ni kuma dashi ne zan samu damar gamawa dake dan nasan yadda kike son ɗiyarki da mijin ki zaki iya haɗiyar zuciya duk ranar da kika samu labarin barin su duniya!'Allah ba zai nuna miki wannan ranar ba sai dai keda zuri'r ki ku wula ƙanta amma ba dai kiga bayana nida ahlina ba,kuma ki sani cewa zalunci baya ƙarko dolene kuga ƙarshenku,kuma yaran da kuka zalunta sune zasu ga bayanki ke da duk wani me irin halinki, insha Allah Bintu ta fi ƙarfin shu'mancin ki saboda tana tare da Allah kuma shine zai zama garkuwar ta ya kareta a duk inda take!'wani gigitaccen mari ta watsa mata tare da cewa, mu zuba Ni dake da duk wanda yake son kawo min cikas akan samuwar cikar burina,bazan ƙyale ko da ɗan cikina bane in dai har zai kawo min matsala cikin burina ballantana kuma ke bafulatanar jeji sakarya kawai!'laila ta kuma ɗaga muryar ta tare da cewa bazan daina faɗar abinda ke raina ba kuma idan kin san wuta to tabbas Bintu ita zata zamar miki wuta me azabtar da rayuwarki kafin kije ki tarar da ta gaske me azabtar dake a lahira,in dai har bakiyi gaggawar tuba daga munanan aiyukan da kike aikatawa ba!'kuma ina mai kuma sanar da ke ki ƙyale ɗan uwana domin babushi cikin al'amarinki!wata muguwar tsawa matar me niƙab ta daka mata tare da cewa to idan baki sani ba ki sani ɗan uwanki shine babban jigo shine mutum na farko da idan na sassauta wa zan yi babban kuskure a rayuwata, ko dan baki san yaƙin da nasha gurin ƙwato ku daga hannun waɗan can mutanen ba?Laila ya kamata ki saduda ki zubda makamanki, ko karɓarku da nayi a hannun waɗan nan matsafan iya haka ya kamata ki jinjinawa shu'mancina ki san cewa Ni ba abar sa in sanki bace!'Laila tace" Aikuwa tun da kika kasa gane mutanen da suka ɗauke mu kika kasa gano babban shu'umin da kuke takara dashi wajen yaƙin neman Abu ɗaya to kuwa tabbas baki kai inda ya kamata kikai ba, kamata yayi kije cikin ESTATE ɗin ku ki binciko wannan takadarin da ya buwayi ahlinku tukun na, sannan kizo ki kama ƙananun ƙwari irin mu,kuma gashi duk kirarin da kike yiwa kanki kin kasa sanin inda mutum daya yake wanda dole shine zai haska miki hanyar samun cikar burinki, kinga kuwa kina da babban aiki agabanki tunda baki san inda ALHAJI Abubakar yake ba,kuma Allah ba zai taɓa baki nasara ba,dan haka ki sani wannan abun da kike kamar bulayi kike kina lalube a cikin duhu!'cikin matuƙar jin zafin maganganun Laila ta fita daga akurkin ɗakin, yayin da ta bada umarnin ci gaba da azabtar da Laila.
Misalin ƙarfe bakwai na yamma ya dawo saboda yana son jin ƙarshen tattaunawarsa da Bintu, dan yasan baƙaramin aikin tane da ta gama abinda takeyi ta yi bacci ba,sai da yayi sallar isha kana ya nufi ɓangaren inno,yana dab da shiga hanyar da zai kashi ɓangaren wan da dole sai ka wuce ɓangaren wannan ɗakin kafin ka ƙara sa saboda shi wannan ɗakin ya kasan ce a tsakiyar ɓangarorin, sai ya zamana duk ɓangaren da zaka shiga sai ka wuce ta ɓangaren ɗakin,
Kamar iska haka yaji wuce war Abu, juyawa yayi sai kuma yaga giftawar inuwar mutum al'amarin da yasa shi dakatawa daga niyar sa ta shiga ɓangaren inno,zubawa wajen ido yayi tare da ƙara nutsuwa ko zai kuma ganin wani abun, amma shuru kake ji sai da ya ɗauki kusan mintuna uku kafin ya bar wajen,amma zuciyar sa cike take da san ganin zahirin wannan inuwar,hakan ne yasa yaƙara sauri dan haɗuwa da Bintu tare da fatan Allah yasa batayi baccin nata na fama ba.
A dai dai lokacin Bintu ta gama duk wani abu da ya dan ganci ogan nata,yayin da su Taufiƙa kuma tuni sun canja shirin su saboda sunyi tunani dukan Bintu ba mafita bace domin abin kansu zai'iya dawowa,wani yaron maƙotan su na ESTATE suka kira ya samo musu karara a makarantar su, dan haka sun shiryawa Bintu mugunta ta rashin mutunci kuma sun fasa barin gidan a cewar su dole su kalli rawar duskon da Bintu zatayi a cikin wannan dare,lokacin da suka zuba mata tana kiching dan haɗawa Oga Abdallah abincin sa,
Tana shiga ta zame kayan ta, tare da waɗawa toilet, batare da tunanin ko maiba ta dauki sosanta wanda shima sai da suka zazzaga masa karara bayan wanda suka saka mata cikin bahon wankan,zuciyar ta ɗaya ta shiga cuɗa jikin ta, kaɗan kaɗan ta fara jin ƙaiƙayin sama sama tun tana daurewa har taji dai abin kamar gaba yakeyi,sauri tayi ta ɗauraye jikinta tare da ɗaukar tawul ta ɗaura,fita tayi daga toilet ɗin tana sosa dukkanin jikinta cikin ƙanƙanin lokaci ta fara fita daga haiyacin ta,gwanin tausayi haka ta shiga goga jikinta a bangon ɗakin ta rasa inda zata tsoma ranta gashi duk inda ta sosa sai ya tashi yayi wani irin ja kamar wanda zai tsatstsafo da jini,kuka ta farayi sosai tana kiran sunan Allah.
Duk abin da ya kamata yayi ya gama sai dai kuma shiru kake ji Bintu ba ita ba alamar ta duk da dama yasan bawuyacin Abune tazo ɗin batare da ya kira taba,cikin azalzalar da zuciyar sa keyi masa ya yunƙura ya tashi,wata zuciyar tace masa mene ne dan kashiga dakin Bintu bayan tariga ta zama mallakinka, ɗan dafe kansa yayi tare da runtse idanunsa, haka nan yake jin wani irin yanayi atare dashi kamar ana taɓa wani ɓari na jikin sa,me ya hana yarinyar nan zuwa ne?ɗan takawa ya farayi har yaje bakin ƙofar sai kuma ya tsaya yana jin nauyi inno ta ganshi wanda shine dalilin da yasa ya kasa yi mata waya ta turo masa Bintun dan kar tayi wani tunani na daban ko ta fassara hakan da wata manufa,har ya juya zai koma amma sai yaji ba zai iya aikata hakan ba,dan haka ya juya tare da buɗe ƙofar yafita kai tsaye hanyar ɗakinta ya nufa wanda da ba dan yana ganin shigar taba da bazaice ga ɗakin ba.
Kuka tayeyi sosai har da birgima duk ta yi wata iri shikansa tawul ɗin da ke jikinta gab yake da fita saboda duk cinyoyin ta a waje suke,gashi har ta rasa inda zata sosa, da ta sosa nan kafin ta ɗauke hannu wani ya fara,kai duk wanda yaga Bintu a wannan lokacin sai yaji ƙwalla cikin idanun sa.
A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar tare da saurin faɗawa ɗakin saboda kukan Bintu da ya fara cin karo da shi cikin kunnuwan sa,a hankali ya ɗan lumshe idanunsa saboda yadda yakejin kukan can cikin jikinsa da zuciyarsa,ci gaba yayi da buɗe ƙofar har ya buɗe ta gaba ɗaya ganin da yayiwa Bintu cikin wannan halin shi ya gusar masa da duk wani tunani da rayuwar da ake yi cikin gidan da rikicin ahalinsa, cikin wani irin taku mai cike da ƙarfin izza wanda ya haɗu da fushin da yasame shi cikin wasu sakanni ya ƙarasa inda take kwance tana burgima tare da soshe soshe,durƙusawa yayi agabanta cikin wata irin murya me cike da sirri kan da har yanzu bai gane su ba,yace"me yasameki? Bintu da batasan da shigowar Oga Abdallah ba tayi wata irin zabura tare da afka masa kana cikin wata irin murya irin wadda take nuni da halin raɗaɗin da mutum yake ciki tace"wayyo Allah Oga Abdallah ka taimakamin jikina ko ina ciwo ƙaiƙayi ciwo zafiii!'ta ƙarasa faɗa cikin wani irin yanayi tare da ƙara shigewa jikin sa tana ƙara mustsika jikinta a cikin nasa, cikin wani irin yanayi da ya saukar masa alokaci ɗaya yace"ƙaiƙayi kuma a ina kika samo ƙaiƙayin!'cikin kuka ta kuma cewa wanka nayi ina cikin yi naji jikina yana ƙaiƙayi!'ta faɗa tana mai ɗaukar hannun sa tare da kaiwa jikinta tanaso ya sosa mata,shi kuwa Abdallah gaba ɗaya yanayin sa ya sauya da wani irin fillin da bai san daga ina ya taho masa ba, mamaki ne ya rufe shi to kuma me ya kawo ƙaiƙayi cikin toilet ɗinta?jin yadda tasakar masa wani azababban kuka yasa shi aje wannan tunanin a gefe ya fara neman hanyar magance wa Bintu wannan ɗan yan muguntar da akayi mata,
Ɗaukar ta yayi cak tare da nufar ƙofa da sauri ya fita daga ɗakin yana dab da shiga falon sa yaji muryar Inno tana cewa Abdallah lafiya kuwa me ya faru da Bintu?cikin sauri yace" mata inno ƙaiƙayi aka sa mata cikin ruwan wanka!'bai saurari innalillahin da innon take zabgawa ba ya shige falonsa da Bintu ɗauke a hannun sa,