← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 120

Sashe 112

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka Dady Habib yake da idanun sa wanda bai taɓa tunanin zaiyi shiba, wannan lamarin shi kaɗai ya karya lagon sa,tabbas idan yace ya ya taɓa jin makamancin wannan tashin hankalin yayi ƙarya, cikin kukan yake cewa Hajja kin cuceni,me yasa baki barni na taso a hannun dan gin uwa ta ba koda kuwa za a dinga yimin girin uba?yanzu duk taran mutanen nan da da suka kasance ƴan uwana yanzu na zama bare acikin su kenan?maganganun da yake yi har sai da takai da cewa wasu sun fara tausaya masa karma Dady Mansur yaji labari,dan abun shi yawa yayi masa ya mutukar razana da jin wacece Hajjah da iri n abinda ta shuka,kallon Habibu yake cike da haushi da kuma tausayi Sa dai shi kansa yasan cewa Habibu ba abin tausayi bane,saboda ya cutar da mutane masu yawa arayuwar sa,wanda kuma alhakin sune ya fara bibiyar sa,tun da gashi har ƙaddarar sa ta juya sama ta koma masa ƙasa,tabbas duk wanda bai ji tsoran Allah ba ɗaiɗaicewa tana tare da rayuwarsa,Dady Habib yana cikin halin nadama wadda ta zame masa ƙeyar baya, yaji an damƙi hannun shi yana ɗagowa yaga Safwan ne da ankwa a hannun sa da alamu dai zai koma inda ya fito ne,dan Nana ne kaɗai ya fi dacewa dashi kafin ya fara ganin sakaiyyar Allah,saboda tsananin tashin hankali da zaucewar tunani bai iya yin musu ba haka ya tashi ya bishi idanun sa na zubar da zafafan hawayen nadama.

Duk wanda ka gani afalon Alhaji Baba zakayi tunanin mutuwa akayi masa mai shiga jiki,sai dai kuma sam ba haka bane tsabar damuwa da tashin hankali da kuma tsinkewa da al'amuran duniya ne,Hajiya ladidi da akayi komai agaban idanun ta,tuni jikinta yayi sanyi nadama ta shigeta,tare da fara itgfari akan abun da taso yiwa rayuwarta,Alhajin Nafisa ne ya ɗan ja numfashi kana yace"ai wannan al'amari wanda ya shafi ahline,bai kamata kuyi kirana ba,duk da dai ban san dalilin Alhaji Baba nayin haka ba!'Alhaji Rufa'i ne ya ɗan share gumin dake saman goshinsa,kana yace"ai Alhaji kaima wannan zama ya shafeka matuƙa,kawai dai Alhaji ya ɗan shiga cikin wani yanayi ne da ya kamata ya keɓe kansa shi yasa bai iya tsayawa yayi maka bayani ba,to amma tunda wakilan sa suna nan na kuma su ai nahin waɗan da abin ya faru akansu to ai ina ganin za a iya sanar da kai komai!'ya rufe bakin sa yana mai duban inda Abdallah yake kwance idanunshi a lumshe dan bazaka taɓa iya fahimtar halin da yake ciki ba,Dady jafar ne ya karbi zancen dan yana ganin waɗan nan ahlin yanzu dole ayi musu uzuri dan suna cikin halin da a yanzu bazasu iya wata doguwar magana ba,har sai lokacin da zuciyar su ta fara mantawa da gagarumar ƙaddarar data keto cikin rayuwar su,babu wanda ya motsa ko yayi wani ƙwaƙwƙwaran tari,har sai da Dady jafar ya dire ƙarshen labarinsa da yake bawa Alhaji munir na abinda gudan jinin sa Nafisa ta aikata,sai gashi shima yabi layin kurame,dan tunda ya ɗora tafukan hannun sa akan fuskarsa,bai ce komai ba har na tsawon wasu mintuna,sai daga can ne kuma ya saki ajiyar zuciya tare da cewa,kuyi haƙuri dan Allah kuyi Allah ya huci zuciyarku,bansan da irin bakin da zan rarrashi zuciyarku ba,haƙika Nafisa tayi min ƙarshen tozarci a rayuwata,ta kuma aikata mummunan kuskuren da bazai taba kankaruwa ba!'yana maganar yana share hawayen da ya kasa hana su zubowa,miƙewa yayi ya bawa su Alhaji Hashir hannu kana ya nufi hanyar waje yana cewa Umar kayi haƙuri ka'ida dukkan iyalanka,amma bance sai ka yafewa Nafisa ba,kabbarta taje ta koyi darasin rayuwa,kuma karki sake ki nufo gida na,ki haƙura dake har abada!'wani irin kukan ihu Anty Nafisa ta saka tana magiya wa Mahaifinta da ya yafe mata ya bawa Umar hakuri,amma ina tuni shi yayi ficewar sa,yana ƙara goge ƙwallar idanunsa,Abba Umar ne yace"Abdallah ya kira Safwan ya tafi da Nafisa dan barinta ba tare da ankoya mata darasi ba hadarine, Abdallah kuwa kamar jiran umarni yake haka ya kira Samuyal,yace"yazo cikin falon,yana shigowa ya zo gaban Abdallah ya duƙa kansa a ƙasa yace"Oga kafin inyi abinda ka umarceni inaso na fara karɓar kalmar shahada a bakinka,domin naje nayi bincike akan addinin Musulunci na kuma gamsu cewa shine addinin gaskiya,dan haka ina so ka musuluntar dani!'gaba ɗaya falon ya ɗauki kabbara, Abdallah kuwa bazan iya ce muku ga halin farin cikin da ya shiga ba,ba tare da wani jinkiri ba,ya bawa Samuyal kalmar shahada,yana faɗa har saida ya maimaita sau uku,kana aka kuma yin wata kabbarar, Abdallah yace"wane suna kake so?kai tsaye yace"Abubakar!'dady ya miƙa masa hannu cikin murmushin farin ciki,yace"Alhamdulillah masha Allah, Ubangiji ya sa musulunci da musulmai su amfane ka,ya kuma baka ikon kiyaye DOKAR sa!'da Amin suka amsa kana Abdallah ya bashi umarnin ya tafi da Nafisa har sai ya nemeta.

Wannan abun da yafaru na karɓar kalmar shahadar Samuyal shi ne ya sanyaya musu zuciya har aka samu damar tattauna abinda ya faru,sai dai har yanzu babu wanda ya kula Hajjah hatta da ƴaƴan ta sunƙi duban inda take, addu'oi masu yawa aka gabatar kana kowa ya fara watsewa jiki a sanyaye,Dady jafar ne ya ciro madaukar da yasaka ya bawa Dady Mansur saboda waɗan da basa nan,domin wannan zaman yana da muhimmanci ace duk wani ahlin ALHAJI BALARABE ya san abinda ya faru acikin ESTATE ɗin sa,

Hajjah kam ta zama tamkar wata mujiya dan kaf ƴaƴan ta waɗan da suka sami halartar taron basu koma ɓangaren ta ba kowacce sai ta wuce gidan mijinta,domin a halin yanzu basa jin zasu iya fuskantar mahaifiyar tasu,duk da cewa itama Nana ƙarama da mijinta a cikin maha intan,to amma dai tanajin gwarashi tunda har ya samu yafiyar wanda suka zalunta,Abba Umar kuwa matarshi ya janye suka nufi sashen sa,Dady Abubakar ma Ammi yabi, dukkanin su suna maijin sabon farin ciki tamkar a lokacin suka mallaki junan su,inno dai itace ta wuce dasu Hajjo bangaren ta,ita kuma Hajiya Babba sai ta janye Bintu saboda dalilinta na cewa sai sunyiwa BINTU auren gata,dan haka da ga yau tabar zaman ɗakin Abdallah,Dady jafar kuwa kai tsaye yacewa da Abigirl ta san inda dare yayi mata dama shi yanzu basu da wani haɗi da ita,ya daiyi mata taimako daya ya bata kuɗin mota ta tafi garin su.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 61 ```

Alhaji Baba kuwa tunda ya shige ɗakinsa ya saka fuskarsa gabas ya shiga miƙa lamuaransa ga Allah,bayaso yayi wani abu da zaisa ace ya zama daga cikin mutane marasa tawakkali da yarda da ƙaddararsu, wannan dalilin ne yasa ya tsaya tsayin daka domin nemarwa kansa nutsuwa,tabbas yasan ko bai fada ba an san cewa dole ya koka da irin wannan lamari da ya samu ahlinsa, amma kuma yanzu dole ne ya zama mai godiya ga ubangiji domin kuwa yanzu ba dabarar sa ce tasa ya warware masa matsalolin ba,yana ji cewa yanzu lokacine da ya kamata ya ƙarfafa zuciyarsa ya janyo farinciki dan farincikin iyalansa,dan kuwa yasan kasancewar sa cikin walwala shine zai basu damar mantawa da mummunar ƙaddarar da ta same su,tun da su sukayi hakuri ai yana ganin shi ba komai bane,ganin cewa su ne jigon waɗan da akayiwa laifin tare da cuta mafi muni, wannan tunanin da yayine yasa shi sakin wani ɗan murmushi tare da faɗin Alhamdulillah aka kulli halin, Allah ya karemu daga sharrin zuciya ya mana tsari da shaiɗan,ya kuma bamu farinciki mai ɗaurewa ya kuma kawar da duk wani abu da zai ƙara cutar da rayuwar iyalina!'Alhaji Baba yayi ƙoƙari sosai gurin cire abinda Hajiya Babba tayi masa a ransa tare da kitsa irin hukuncin da ya kamaceta,Habibu kuwa bashi yayiwa laifi ba Allah yayiwa laifi mai girma, laifinda ya faɗa cewa ba yayiwa bawansa a fuwa akan waɗan nan abubuwa, laifin wani akan wani laifin shirka,to shi kuma Habibu duk ya aikata waɗan nan laifukan,ba zaice yaji daɗi ba dan Habibu ya kasance ba ɗan shi ba,saboda ya riga ya sawa ranshi Habibu ɗan sa ne dan haka yanzun ma bata sauya ba,sai dai yabishi da addu'ar fatan shiriya da neman sassauci gurin Ubangiji.

Tsakanin Dady Abubakar da Abba Umar ban san wanda yafi wani dokin amarcewa ba,dan kuwa tunda suka kule a ɓangaren su babu wanda ya kuma jin ɗuriyar su,suna can suna sabunta soyayyar su,Nafisa kuwa ba zan iya misalta halin da ta shiga ba,saboda rashin tsuntsu da tarko,kuma gata a kulle cikin gurin da ko tafukan hannayen ta bata iya gani,gurin da bata taɓa tunanin zata zoshiba,(to dama Nafisa ai ƙarshen mugun abu kenan, Allah dai ya tsare mu daga masu irin halin ku)

ESTATE ɗin tayi shuru tsawon kwana biyu,kafin kuma su koma da walwalar su, Abba umar tuni ya maida su Hajjo gidan da ya kaisu kasancewar gidan babban gidane,sai ya miƙa wa Fafi takardun gidan yace"ya bar masa ya cigaba da zama da iyalan sa,ƴan biyu kuwa tunda suka ƙyalla idanu suka ga ƴar uwar su Bintu shike nan suka samu nayi duk da cewa sun girmewa Bintun,Hassan ya zama macen dole a cikin su,sunƙi barin estate ɗin gaba ɗaya sun tare anan sunce sai angama bikin Bintu zasu koma gida,fafi dai yana can shima shida ma'unsa ana sabunta soyayya.

Yayin da duk ake wannan budurin Abdallah yana can yana fama da soyayyar da a yanzu yake kokarin gasgata ta,ya rasa dalilin da yasa a ka hana Bintu dawowa sashen sa,shi kuma tsabar miskilanci ya kasa tambayar ko Ummi Laila ce,wadda a kwana biyun kusan kullum yana bangarenta,haka yake sunturin zuwa wajen Alhaji Baba ko da zaiyi masa maganar Bintu amma shuru kake ji,sai yayi tunanin ko dai baisan abinda yake faruwa bane?tun yana daurewa zuciyar sa har ya fara bin iyayen nasa maza amma,duk yawan zaman da zasuyi tare baya jin maganar Bintu abakin su,to wai me ake nufi da wannan abun ne?sai kuma ya shiga fargaba kar dai ko Dady jafar ya faɗa musu abinda yace"akan cewa da yayi idan komai ya daidaita zai saketa ta auri wanda takeso,tunawa da hakan yasa yaji zuciyar sa na bugawa da ƙarfi,kamar zata faso ƙirjinsa ta fito.
Chapter 112 · 0% Book details