← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 120

Sashe 6

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

'Dakine guda acikin estate din ta can wani bangare na musamman wanda ba kowane yakebi ta hanyarba, babu wanda yasan meye' acikin dakin da kuma mamallakan dakin,sai dai kuma wani abun mamaki babu wanda aka taba gani ya bude dakin ko kuma yabi ta hanyar,da dakin yake,
dayawa-yawan zuciyoyi nakai komo da taraddadi akan dakin, haka kuma zuciya da gan- garjiki suna son kai kansu inda wannan dakin yake, amma kash,hakan ya kasa samuwa daga dukkanin bangarorin dake son sanin abunda aka 'kunshe acikin dakin da kuma amfanin zamansa anan, kai harma da mamallakan dakin.
Adai-dai kuma wannan lokacin ne dije me aikin hjy madina matar mansur, tafito da wani kullin abu ahannunta sai yan dube-debe take kai kana ganin yanayinta zaka hango rashin gaskiya aidanunta,cikin sanda ta nufi can baya inda wannan dakin yake, alhj mansur da tun fitowarta ya hangota a lokacin da yake fitowa daga bangaren alhj baba(alhj balarabe)cikin sauri da azama ya mara mata baya dan ganin abinda take kokarinyi,abinka da namiji kakkarfa nan da nan ya taddata,cikin wata iriyar gugitacciyar tsawa,yace"ke dijeeee karki sake ki kara wani taku daga nan inda kike!'dije cikin tashin hankali da rawar jiki ta tsaya tare da juyawa dan ganin wanda yake neman fasa mata 'ya'yan hanji da wannan' razananniyar tsawar ,ganin uban dakinta tsaye yana aika mata da wani' shakurarren kallo me cike da gargadi da barazana,yasa ta kara kidimewa,da sauri ta karaso inda yake tsaye tana mai cewa"yallabai agafarceni wlh sani akayi bada niyar kaina nazo gurin nan ba, cikin tsareta da ido alhj mansur yace" dije.wani irin gan-gancine yakaiki ga zuwa gurin nan? kinsan kuwa komu bama iya zuwa hanyar nan amma ke kike kokarin saida ranki akan kudi!' wayasaka ki wannan aikin? kuma mezakiyi anan din?san nan meye wannan ahannunki? yayinda dady babba(alhj mansur) yakewa dije wadan nan tambayoyi ita tuni ta dade da antayawa' zuzzurfan tunani na yaya zatayi ta tseratar da rayuwarsu ita da yarta,tabbas idan bata kai wannan ajiyar inda akasata takaiba tana cikin tsaka me wuya,sannan kuma shima kaiwar wani tashin hankalinne wanda shima ya hada da rayuwarta, san nan fadin wanda ya aikota shima yana dai-dai da rasa rayuwar danta, to yanzu meye mafita agareta?kai suwaye anan gurin? ta ji wata murya daga bayansu ayayin da me maganar take nufosu saida ya karaso san nan ta fahimci waye alhj habib ne wanda ake masa lakabi da Abba 1,cikin nutsuwa ya dubi dady babba wanda yake ta faman muzurai yana wani hade rai,yace dashi yaya meke faruwane anan?cikin hargagi dady babba yace"kawai kaje babu ruwanka bana san saka ido da munafurci,Abba ane yayi murmushi cikin sanyiwa dan uwan nasa biyayya yace"yaya kayi hakuri ba Ina nufin wani Abu bane mara kyau amma kayi hakuri,dije kuwa hamdala tayi ganin ta samu hanyar kubuta daga wadan nan razannun tambayoyi daga uban gidanta,cikin sanda ta fece daga gurin ba tare da sun ankaraba.
cikin fada-fada da yanayinsa na rashin hakuri yace"ai dama habibu dole ka bani hakuri tunda kasan baka kyauta mun,duk abinda zanyi idanka yana kaina ka daukeni tamkar wani mara gaskiya Ina amatsayin yayanka kuma babba acikin gidan nan idan ka dauke yaya nana da sakina da hafsa kaf gidan nan nine babba amma bani da damar da zan aiwatar da abu ya zauna acikin gidan nan, saika kai karata gurin alhj baba, to Ina mai tabbatar maka billahillazi idan baka fita harkata ba zaka ga abinda zai faru, babu ruwana da ciki dayan da muka fito dan wani lokacin rufin asirin da dan uba zaiyi maka dan ciki dayan bazai yi maka shi ba!' yana zuwa nan not azancen sa ya kada babbar rigarsa ya juya afusace ya bar Abba ane tsaye da tsananin mamaki da takaicin halin dan uwan nasa.

Cike da razana da bayyanannen tsoro take duban nafisar, san nan cikin dan daga sauti tace'" nafisa kina da hankali kuwa? kinsan abinda kike shirin aikata mana kuwa!'sai kuma ta dan sassauta, cikin kwantar da murya tace" haba nafisatu yaya kike son bata rawarki da tsalle kinsan kuwa babban tashin hankalin da zamu dauwama aciki in dai ki kai saken da wannan' sirrin ya tonu,to bari in fada miki abinda har yanzu baki sani ba, alhj balarabe estate ta wuce duk inda kike tunani, ta wuce zatan me zato, a'iya tuggu da makirci, kowa yana' iya takunsa baza ki taba gane abinda ke cikin zuciyoyinsu ba,dan haka ki sake sabuwar damara indai har abinda kike fada gaskiyane!'ahankali nafisa ta dago kanta dake sunkwiye, idanunta sun kumbura sunyi ja tamkar garwashin wuta,tace'" mama na kasa!' damuwata tayi girman da bazata iya boyuwaba, Ina cikin mummunan tashin hankali aduk sanda naga dare yayi gari zai waye, damuwata 'karuwa take duk sanda na tuna lokaci yana zuwa da zan iya rasa umar,tsorona karuwa yake' aduk sanda na tuna, bansan wane rana bane wane lokacine, da wane yanayine wan can rudadden al'marin zaizo me cike da sarkakiyar da warware shi sai wanda ya kullah shi,mama ayanzu inajin garamun mutuwata da zuwan wan nan rana bazan iya kallon idanun umar ba, dana sani mama da na hakura da saukar KUDURAR ALLAH da ban kasance ahalin da nake ciki ayanzu ba!' ta karasa maganar da sakin wani rikitaccen kuka me bayyana abinda yake can cikin kasan zuciya,ita kanta mama kukan take yi wanda yake cike da cunkushewar zuciya na rashin tunanin mafita.

Pastor David hause

Kallo take masa me cike da tsoro,takowa yake gabanta cikin wani kakkarfan taku wanda duk takunsa daya ji take yana tafiya da bugun zuciyarta,fuskarsa me tsananin kyau da haiba da kuma tsananin kwarjini, ahade staf babu alamun murmushi bare dariya da dama ba al'darsa bace,tsayawa yayi akanta batare da ya tanka mata ba,dama tasan za'a rina da yaya ma tasamu yazo din,kallansa tayi sai dai ta rasa ta inda zata fara magana,tamkar ba itace me kururuwa da fade- fade akwanakin ba,daga kafarsa da yayi daniyar Bari wurinne yasa tayi hanzarin dawowa hayyacinta,tare da saurin kama tattausan hannunsa, san nan cikin rawar murya tace"FATASH...cikin wata murya me tsananin dadi wanda ta hade da yanayin fushi da muskilanci sai ta hadu ta bada wani daddan sauti,yace"don't coll me FATASH I'm doctor ABDALLAH,daga haka ya maida bakinsa ya tsuke tamkar bashine yayi maganar ba,cikin tsananin rudani da tashin hankali take kallallonsa, ga tarin maganganu da tashirya yi masa amma ta gagara furta masa Koda kalma daya saboda tsananin kwarjini da tarin ilhamomi da allah yay masa cikin kudurorinsa,tana kallo ya wuce cikin nisatstsan takunsa me cike da wani salo me burgewa, har ya bacewa idanunta, anan ne kuma takece da wani irin kakkarfan kuka me cike da ta kaici da tarin da nasani.

FATASH. saurayine dan kimanin shekaru talatin zuwa talatin da daya, kyakykyawan gaskene fari amma ba tas ba, wata irin kalace dashi me wuyar samu, yana da saje wanda ya kara kawata kyakykyawar fuskar tashi,dogone me dogayen gabobi saidai kuma ba siriri bane acike yake babu rama ajikinshi,fatarshi cike take da gargasa me laushi yana da kyan tsari kwarai abangaren halitta,ta bangaren halayya kuwa zan iya cewa fatash murdaddan mutumne, tun yana karami iyayensa basu Isa su gane inda ya dosa ba, muskiline na karshe wanda baza kataba cewa ya ma taba magana ba ko dariya,yana da matukar zurfin ciki bai yadda da kowa ba sai kansa yana da tsentsami ta ko wane bangare,bai iya so ba baisan ya ake yi ba, shi dai kawai yaje asibitinsa ya yini aiki ya kwana aiki bayasan damuwa ta surutu, shiyasa baya shiga sabgar iyayen nasa musamman mamansa,tun yana yaro yake da muradin wani abu wanda ako da yaushe ake haska masa acikin mafarkinsa tun bay gane ba harya fahimta, kuma yasa aransa sai yabi wan nan hasken,tun yana shekara goma sha uku iyayensa suka kaishi can u.s dan yayi karatu dan kaucewa abinda suke zatawa yaron nasu, sai dai kash basu nan tuni Alllah ya saukar da KUDURAR sa akan fatash ba ya saukar da haskensa akansa,allah me kudura buwayi gagara misali, yayi cewa FATASH baze tashi cikin duhuba,zuwanshi u.s yasamar masa da nutsuwa ta yadda zai guda nar da rayuwarsa cikin haske, yashiga neman malaman addini manya-manya ya kuma dace,ashekarun da yayi a u.s ya haddace alkur'ani me girma ya haddace manya- manyan littattafan addini,ayanzu fatash yayi nisa kuma bazai taba jin kiran da mahaifan NASA suke masa ba.
Chapter 6 · 0% Book details