Sashe 95
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta ɗaga wayar da tun ɗazu tana hannun ta dan ta kasa ajiye ta gani take kamar labarin wani abun zai iya wuce ta,cikin sauri tace"ya akayi ina fata dai komai ya kammala?bansan amsar da aka bata acan ɓangaren ba sai kawai ta sheƙe da dariya cike da farin cikin samun nasara akan burin rayuwarta,tace"Barka" inawa kaina Barka kafin nayi muku Barka da arzikin dake bunku yadda kuka cika min burina nima zan cika muku alƙawarin da nayi muku dan haka yanzu ina jiran shaidar kashe su da kuma asusun bankin ku!'kashe wayar tayi ta bar su da sakin baki gaba dayan su wayar suke kallo yayin da suka shiga tunanin yadda za ayi su tura mata shaidar kisan da tasaka su aikata,sai dai kuma abunka da ƴan ta adda waɗan da suka saba aikata kisa a kowane lokaci kuma su ajiye record saboda wata rana,shi yasa basu sha wuyar turawa Nafisa fake ɗin gawar Abba Umar ba,sun tura mata kuma shirin su yayi daidai da irin ƙwaƙwalwar Anty Nafisa dan bata gane komai ba tunda ita dai taga gawar mutum kuma taga ƙonannen gida bata da wata damuwa,take ita ma ta tura musu kudaden su, zuciyarta fes bata da wata sauran damuwa sai ta cin duniyar ta da tsinke.
Cikin sauri ya gaida Hajjah ba tare da ya zauna ba,hakan ne ke nuni da irin saurin da yake dan fita daga gidan, zuba masa ido Hajjah tayi ganin yadda yake ta share gumi ga kuma yawan kallon agogo da yake yi,cikin tsare shi da ido tace"wai Mansur saurin me kake yi ne haka,gaba ɗaya ka kasa zama ba daban Ni nayi kiran ka ba ma ina ga bazaka zo ba!'ta faɗa tana daɗa tsare shi da mahukuntan idanunta,cikin ɗan sosa kai yace"wallahi Hajjah da inda zani kuma zuwan yana da muhimmanci!'tace"shi wajen bashi da suna?girgiza mata kai yayi yana ƙoƙarin tashi,ba tace"masa komai ba sai ido da tabi shi da shi.
Yana fita ya shiga mota wanda da alama bashi kadai ne cikin motar,kasancewar duhu ya farayi shi yasa ban kula da wanda ke zaune a bayan motar Ba,figar ta yayi da matsiyacin gudu,itama cikin sauri ta shiga motar ta tare da figarta a tsiyace,tana cewa Mansur bazan bari ka tseremin ba dole sai na ga inda kakai Abubakar kuma sai na kwato shi a yau ba sai gobe ba!'ta faÉ—a tana É—an danna wayar ta,wanda da alama kira takeyi,cikin sakanni kuwa aka daga wayar,ba tare da ta saurari wani zance ba tace"ina fatan kuna nan inda nasa ku tsaya!'daga can aka amsa mata kana tace"yauwa to gamu nan yana fitowa kubishi Abaya Ni kuma zan biyo ku kar ku sake ku bari ya tsere muku haka kuma kar ku bari ya fuskanci ana bin bayan sa!'daga haka ta kashe wayar ta ci gaba da bawa motar ta wuta.
Dady jafar ya kalli Abdallah cikin gajiya da shiga wannan uban surƙuƙin dajin,yace"anya kuwa Abdallah ba yaudarar mu yayi ba? Amma ace dan Adam ne yake shiga gurin nan babu gida gaba babu baya!'abdallah ya dage kanshi tare da cewa tunanina kawai shine halin da Bint take ciki!'daga haka basu kuma magana ba har suka zo wajen da yayi daidai da zanen kwatan cen da yake kan wayar sa,ɗan slow suka farayi tare da yin ƴan dube dube saboda ko bukka basu gani awajen ba bare gida,gashi kuma inda aka zana taswirar akwai gida a wajen,tsayawa sukayi tare da zubawa dajin ido wanda yayi tsit baka jin kukan komai sai na tsuntsaye,kamar daga sama sukaji ance, sannun ku da zuwa ɗan zaki,munayi maku maraba kaida jajirtaccen uban riƙon ka,ku fito daga cikin mota ai kun zo inda kuke nema!'daga haka gurin ya kuma ɗaukar shuru kamar yadda yake a farko,da ambatan Bismillah da addu o in tsari suka fito daga cikin motar,ga tsananin mamakin su suna fitowa suka ga tafkeken gidan da babushi a farkon zuwan su,ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauko Dady Abubakar dake san ƙame kamar gawa,suka shiga cikin gidan ba tare da sun tsagaita da ambatan Allah jalla wa'azza ba.
Wani fili suka fara tararwa kafin su dan gana da ƙofar da suka gani tana kallon su,itama kai tsaye suka shigeta ba tare da jin tsoro ko wani ɗar atare dasu ba,sosai suka shiga gidan da yake da wani irin zurfi ga wani irin duhu da ya mamaye gurin gaba ɗaya, da taimakon Allah kawai suke samun inda zasu jefa ƙafafunsu,gajiya sukayi da shiga inda basu sani ba kuma basu da tabbacin akwai mutane agurin,suna tsayawa haske ya gauraye wajen,bin ko ina suke da kallo cikin mamakin mutanen da suka gani agurin,kallon juna sukayi kana suka maida kallon su kan mutanen da suke zaune wasu kuma a tsaye,da wasu irin jajayen kaya ajikin su sai zane dake kan fuskar su,zasu kai kimanin su ashirin da ɗoriya,babu wanda ya tanka acikin su duka, sai daga can baya akayi magana da cewa Barka da zuwa ɗan zaki tabbas kacika ɗan halak wanda ke saka Alkhairi da halacci,ga kuma soyayya mai tsanani wanda bantaɓa jin ta ko ganin irinta ba,maza ka miko min mahaifin ka Ni kuma na miƙa maka matar ka!'Abdallah yace"ba haka mukayi da kaiba,dole sai naga lafiyar Bint kafin na baka mahaifina!'wata shegiyar dariya ya sheƙe da ita kafin yace"yaro kar ka manta fa fada ta ka shigo dan haka gaddama ba taka bace,kawai kayi abinda na saka ka inda ba haka ba zan nuna maka ƙarfin iko na,ko dake ma bar shi dama na sha alwashin ta hanyar ku zan samu cikar burina dan haka yanzu agabanka mahaifinka zai buɗi baki ya sanar dani inda suka ɓoye wannan dimon ɗin!'take ya shiga yin wasu siddabaru duk da yasan ba lallai ne yayi ba,yana kuma daga inda yake ba tare da ya fito su Abdallah sun ganshi ba,kafin ƙiftawar ido Dady Abubakar ya fara wani irin jijjiga kafin wani lokaci jikin shi ya saki yana fitar da wani irin numfashi,da sauri nanu ya fito daga inda ya ɓoye cike da mamakin farfaɗowar da ABUBAKAR yayi ba tare da yayi masa wani aiki ba dan siddabarun da yayi yanzu gwadawa kawai yayi tunda yanzu bashi da karfin siddabaru kamar da.
Cike da tsananin mamaki Abdallah ke kallon shi cikin rawar baki ya nuna shi tare da cewa"Dady Mansur kai ne dama?Dady jafar yace"haba Abdallah me na gaya maka ai Ni ban yi mamaki ba saboda duk wasu alamu sun gama nuna Mansur a fili!'
cikin wani taku irin na taƙama ya ƙaraso gaban Dady Abubakar wanda ya buɗe idanun sa tsaf yana bin Mansur da wani mugun kallo,hannu yasa ya ɗago habarsa yace"dan uwa yau fa ka dawo mutum ina tayaka murna,ya faɗa yana jifan su da wani shu'umin murmushi, Abdallah kuwa kallon da yakewa Dady Mansur hatta Dady jafar saida ya nutsu dan son gano ma'nar kallon.
Tun da suka zo suna bakin gurin sun rasa inda Mansur yashiga basu san ta hanyar da yabi ba,domin su dai basu ga gida ko wani waje dake nuna alamun da mutane a wajen ba,tashin da tashiga ba mai misaltuwa bane, wannan aishene ta tasamu yanzu kuma tana shirin ganin rashi,to ina wannan shu'umin ya shiga da har ya ɓace musu,gashi dai tabbas basuyi kuskuren hanya ba,daga ita har yaran nata cirko cirko sukayi suna jiran tsammani.
Æangaren Abba Umar kuwa,sai da suka É—an samu nutsuwa,kana yake bawa Hajjo labarin abinda ya faru tsakanin sa da mutanen nan masu kashe su,yace"Hajjo na fahimci cewa kudi shine matsalar su dan haka sai na siye su dashi kamar yadda aka basu aikin kisa akan su to barin aikata kisan ma bazai gagara su barshi ba,dan haka sai nace dasu ya fadi farashin da akabasu Ni kuma zan ninka musu sau biyar,yadda dai ya sanar dani za abasu dubu É—ari biyar dan haka ni kuma nace zan basu miliyan biyar, su rabu dani kuma suje su cewa wanda ya saka su sun yi abinda aka umarce su,to kinji dalilin da yasa basu kashe mu ba!'Hajjo tace"ikon Allah idan kana da kuÉ—i babu abinda zai gagareka haka kuma idan kana dasu kana cikin tashin hankali, Allah dai yasa mu dace!' da Amin suka amsa shida Asma'u.
A ɓangaren su Safwan kuwa sunyi abinda ogansu ya umarce su,dan kuwa cikin kankanin lokaci suka kama su Alhaji Hashir da tawagar su,lokacin da Alhaji Sama'ila ya ga Samira acikin jami'an tsaro na farin kaya,sai da ya suma,Samira ce da kanta ta zuba masa ruwa ya farfaɗo amma yana kuma haɗa ido da ita sai ya kuma shekawa,da ta kuma zuba masa ya farfaɗo zai koma kenan ta daddage ta sheƙa masa marika har guda biyu hagu da dama,wani irin ƙayataccen murmushi ta saki na samun nasara da cin gari,tace"Sama'ila sakarai ko da yake sakarcin ka ya matuƙar taimakamin,dan da baka kasance wawa ba da nasan ba lallai ne nasamu nasara kamar yadda nasamu yanzu ba!'zuba mata ido yayi idanun sa na ruwan hawaye ga wani irin yaji kamar zasu waɗo ƙasa,ta cigaba da cewa,Ni ɗin ƙaryace gabaki ɗaya na gaibuce labarina gaibune amma awajen ka,rayuwata tare da kai ka ƙaddara amafarki kayita yayin da gaskiya ta bayyana a farke,kuma ƙaryarka ta ƙare a farke,dariya tayi irin ta tura haushin nan,kana ta miƙe daga durkusan da tayi a gaban sa,tana cewa Sama'ila na gode fa da aikin da kayi min nasaka wahalafa da yawa to amma dai babu damuwa tunda gashi yanzu soyayya tayi rana,tunda ta ƙure ƙaryar masu ƙarya!'daga haka suka fita daga ɗakin da aka lodasu,wani irin ihu Alhaji Sama'ila ya saka tare da rushewa da wani irin kuka mai cike da nadama da takaici,sauran kuwa basu da bakin magana duk da suna so su magantu saboda tonuwar asirin da Sama'ila ya jawo musu,da kuma zubewar mutuncin su,gemai gemai dasu an watsa su a kurkuku kamar wasu karnuka,hmm kaɗan ma kuka gani dan indai akan ha inci da hassada da yaudara ne to baku ga komai ba kwarankwatsa dubu....