Sashe 42
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da taga fitar sa kana ta koma ɗakin cikin sauri ta shiga dubawa, cikin Sa'a kuwa tayi karo da wayar ga alamu ma manta ta yayi,ɗauka tayi ta koma ɗakinta,lambar Dije ta fara gwadawa cikin sa ar datake da ita yau, wayar ta shiga,haba mama Dije hankalina ya tashi da rashin jinki gashi bani da wata hanyar da zan ganki!' cikin nutsuwa Dije tace"Bintu muna cikin masifa matar nan ta fara ganewa muna ƙulla wani abu Ni dake, Bintu rayuwar ƴaƴana nakeji shiyasa kika ga na ƙulle hanyar haɗuwa dake!'cikin tashin hankali Bintu tace"yanzu kina nufin kin karya alƙawarin da kikayi min? Dije taja wani sheshsheƙa tare da goge zufar dake sauko mata kana tace"Bintu ban karya ba kuma bazan karya ba,ina daiyin ta katsantsan ne saboda rayuwar marayun Allah, wannan matar shu'uma ce Bintu ta iya takunta, yanzu abinda nakeso na gano shine wai shin acikin gidan nan take zaune ko kuma daga cikin ahlinsa ne wanda basa zaune a gidan nan? daga nan zamu san yadda zamuyi mugano abinda suke wannan san zuciyar akansa dan tabbas a kwai wani abu daya dan ganci dukiya me razana zuciyar mutum a cikin estate ɗin nan!'jin kamar za a shigo ɗakin dan ta manta ba tasa key ba yasa tace"to shike nan mama duk abinda ake ciki ki kirani!'tayi saurin kashe wayar tare da cusa ta cikin zanin ta.
Da wuri ta gama girkinta ta kai ta jera saboda bata san su haɗu da Oga dan tasan ita mai laifice A gurinsa,haka kawai take jin faɗuwar gaba jikinta duk a san yaye yake,shiyasa ko da Rahima tazo suka zauna A falon inno kasa gane mata tayi,tace"Bintu wai ko baki da lafiya ne duk na ganki wani iri? cikin faɗuwar gaban dake ƙara kusan tarta tace"wallahi Rahima kaina ne tun ɗazu yake sarawa kamar zai rabe biyu!'ayya sorry bari na kama maki sai kije kisha magani!'kama mata kan tayi kana ta miƙe tare da cewa bari na wuce sai Allah ya kaimu gobe!'Bintu tace"ki gaida min da Ammi na gode,daga haka sukayi sallama,zama tayi A falon ta kasa tashi har su Taufiƙa suka sameta,basu ce mata komai ba suka wuce ɗakin su, Sayyid ne ya shigo yana ganin Bintu ya fara washe mata baki zama yayi kujerar dake fuskantar ta ya shiga yi mata surutai bata tanka masa ba dan ita kaɗai tasan halin da take ciki,a haka Oga Abdallah ya shigo ya same su bai kalli inda suke ba ya wuce part ɗinsa,yana shiga ko ɗakin bai ƙara sa ba ya wuce dining dan wata muguwar yunwa ya dawo da ita,savin kansa yayi ya fara cin haɗaɗɗen tuwan farar shinkafa da miyar ɗanyen kubewa wanda taji ragargajejjen naman kaza sai ƙamshin daɗi takeyi.
Acan falo kuma Bintu ta gaji da surutun Sayyid tashi tayi ta barshi ba tare da ta tanka masa ba tun zamansa,sai da ta shige kana ya ankara da wayar ta ɗauka yayi da niyar miƙa mata saƙon dayaga ya shigo wayar ne ya saka shi da katawa tare da zaro idanu cikin tashin hankali da firgici...
Bintu kuwa tana shiga ta wuce wajen taga ta ɗaga labulen,dan samun iska ko zataji sanyi,takarda ta gani saƙale ajikin tagar da sauri ta ɗaga tare da warwareta,innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un da gudu ta fito daga ɗakin cikin tsananin tashin hankali...
Turƙashi wani kaya sai amale,wane saƙo Sayyid ya gani A wayar Bintu?me saƙon wasiƙar Bintu ya ƙunsa da ya tayar mata da hankali haka?wane tashin hankali ne yake shirin faruwa da Bintu da har take jin faɗuwar gaba? amsar na cikin nest page insha Allah
AlÆ™alaminâœðŸ½
Fatima y Adam
More comment.....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 29 ```
Karo sukayi da Sayyid sauri tayi ta ɓoye takarda hannun ta tare da yagata ƙananu, bin yagaggiyar wasikar yayi da kallo,kana cikin sanyin jiki ya miƙa mata wayar tare da wani irin kallo na tsantsan tuhuma,karɓar wayar tayi hannun ta na rawa,da sauri ta wuce shi bata re da ta tsaya duba wayar ba.
Paper da ta zubar ya tsaya ya tattara duk da bazai fahimci komai aciki ba haka yayi gaba dasu batare da nasan abinda zaiyi dasu ba.
Da gudu ta ƙara sa ta tankoɓe hannun sa dayake shirin kai wa bakinsa, kallon ta yake cike da mamaki,ita kuma abincin tabi da idanu,cikin wani irin tashin hankali da ruɗani tace"kaci abincin? cikin mamakinta yace" ke meye hak...murɗawar da cikin sa yayi shi ya hanashi ƙara sa tambayar da yaso yi mata,ƙara riƙe cikin yayi cikin jin matsanan cin ciwo, Bintu wani irin kuka tasaka mai tsuma zuciya,kafin ta ankara Abdallah ya faɗo daga kan kujerar dayake kai yana wani irin juyi na tsananin azaba,riƙe shi tayi tana cigaba da kuka cikin matsanancin kuka tace"wayyo Allah na shiga uku yazanyi da rayuwata Ni Bintu wa zai fitar dani daga wannan mugun zarge?Allah kafitar da Ni banji ba bangani ba,bani da laifin komai ga bawanka da baiyi wa kowa laifi ba suna san ganin bayansa me yasa kuke san kasheshi me yayi muku? saboda tashin hankalin da take ciki har bata san lokacin da suka baiyana a falon ba Dady Habib ne yayi saurin cicciɓar Abdallah yana cewa maza muje asibiti Yakamata mu fara kaishi kar gubar tafara aiki har tayi ajalin sa!'Dady Mansur yace"kuje Ni ina nan saboda na kira police,inno kuwa dasu Taufiƙa harda Hauwa'u da bata jima da dawowa gidan ba,Dady jafar da Dady Habib ne suka tafi dashi asibiti, Bintu kuwa gaba ɗaya kukan ma ta neme shi ta rasa, sai yaune ta tabbatar ashe duk kukan da takeyi abaya na rahmane ashe kukan ma akwai ranar nemansa? Alhaji Baba ta kalla da tunda ya shigo ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa,baice uffan ba,Hajiya Babba kuwa cikin nutsuwa ta ƙarasa kusa da Bintu ta dafa kafaɗarta wanda sai alokacin Bintu ta kula da ita,tace"Bintu gaya mana abinda ya faru kinji? ki kwantar da hankalin ki!' Dady Mansur yace"haba Hajiyarmu ai ba anan zata amsa tambayoyin ba sai taje can police station tukun dan mu baza ta gaya mana gaskiya ba!'Hajjah tace" kai bana san shashanci,ka bari yarinya tayi mana bayanin abinda ya faru kafin zartar da ko wane irin hukunci!'Hajjah ce tai mata magana a wannan karon cikin taushin lafazi tace"Bintu,gaya mana abinda ya faru? rawar murya ta farayi saboda ita bata san me zata ce ba,amma dai kawai zata faɗa musu gaskiya duk da dai tasan Allah ne kawai zai ƙwaceta daga wannan mummunar zargi,cikin tashin hankali tace" wallahi ban san komai ba Hajjah ɗakina na shiga na tarar an ajiye min wasiƙa,da na duba wasikar sai naga an rubuta an saka guba A cikin abincin Abdallah wallahi shine na fito da gudu dan nazo naga ko baici abin cin ba na zubar shine na haɗu da Sayyid ya bani wayata!'Dady Mansur yace"to lauya munji wannan ƙaryar shi kuma saƙon da Sayyid ya gani anturo miki fa? cikin mamaki tace" wane saƙo Ni ba wani saƙo da aka turan,(sanadin karbar wayarta da Abdallah yayi sai tayi tunanin tunda haka ta fara faruwa gudun tsautsayi gara ta goge duk wani saƙo dake cikin wayar,shi yasa Sayyid bai ga ko wane saƙo ba sai wanda aka turo A lokacin kuma da ɓoyayyar nomban)Bintu tayi mamaki ƙwarai dan bata san ta bar wani saƙo a wayar ba, Sayyid ɗin ne yace"Hajjah A karɓi wayarta a duba in dai bata goge ba za A ga saƙon wallahi ba sharri nayi mata ba!'Hajiya Babba ce ta karɓi wayar da kanta kana ta lalubo saƙon wan da bata sha wahalar ganin sa ba saboda dama Sayyid bai fita daga kan enbox ɗin ba,ga abinda saƙon ya ƙunsa Bintu kin tabbatar kin zuba masa gubar nan? bana so yau Abdallah ya kwana a duniya,shike nan abin da aka rubuta,wani irin juwa da layi Bintu ta shiga yi kan ka ce me sai gata yaraf aƙasa babu alamun numfashi,Abin mamaki babu wanda yayi ƙoƙarin tallafawa Bintu saboda dukkanin su sun shiga shock da jin wannan al'amari mai girma,wayar Dady Mansur ce tayi ringin ɗagawa yayi tare da cewa to to gamu muna ciki bari nasa a shigo daku!'kashe wayar yayi yana cewa maza jeka Sayyid kashigo da inspector lawan,da sauri ya fita dan shigowa dasu har zuwa yanzu babu wanda aka samu d yayi wani abu kan suman da Bintu tayi, Alhaji Baba ne ya miƙe tare da fita daga falon,har haɗa hanya yake kamar zai faɗi saboda har yanzu baya cikin nutsuwarsa, Siddiqa ce tayi saurin kamashi dan ta taimaka masa ita ta raka shi har part ɗinsa,
Sai da su inspector lawan suka shigo kana Dady Mansur ya ɗauki ruwa ya sheƙawa Bintu A fuska, ajiyar zuciya ta saki kana ta buɗe idanunta da sukayi mata nauyi, Dady Mansur yace"to gata nan ku tafi da ita na gaya maka kisan kai take ƙoƙarin yi yanzu dai yaron yana asibiti bamu san halin da yake ciki ba duk abinda ya kamata zakuji daga baya!'wata ƴar sanda ce ta ƙara sa kusa da Bintu tare da kama hannun ta,batare da wata gaddama ba Bintu ta bita saboda tariga tasan bata da sauran kalamin kare kai ko da da akwai ma baza su yadda ba,suna kallo aka tafi da Bintu ba tare da sun iya dakatar wa ba,jiki A saɓule suka fita daga falon zuciyoyinsu cike da tunanika iri-iri.