Sashe 46
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tacan ɓangaren Alhaji Baba kuwa A safiyar yau ne ya A kuma cikin masallaci bayan idarwarsu daga sallar asuba ya umarci liman da yasanar da akwai ɗaurin auren da za A gabatar yanzu in Allah ya amince, tare da miƙawa Abba Umar kuɗi dubu ɗari biyu cif tare da ce masa Umar inaso kazama wakilin wannan marainiyar Allah Bintu nasan kai kaɗai ne zakayi min biyayyar yin haka batare da son jin ba asi ko kuma gar dama ba!' Abba Umar wanda ya sauka da asubahin ranar daga tafiyar da yayi duk da dai ba da ɗewa zaiyi ba, yasa hannu biyu ya amshi kuɗin da mahaifinsa yake miƙa masa,haka nan ya tsinci zuciyar sa cikin wani irin maɗaukakin farin ciki tamkar anyi masa bushara da aljanna,sauran yaran Alhaji Baba da ƴaƴan ƴan uwansa da jikokin sa da duk wanda yake zaune cikin wannan ESTATE kuma yasan abinda ya faru da Abdallah da Bintu saida ya shiga cikin tsananin mamaki da kuma tashin hankalin wannan al'amari,basu taɓa tsammanin cewa Alhaji Baba bai yadda da abinda yaji kuma ya gani akan gubar da Bintu ta zubawa Abdallah ba,sai gashi ya basu wani irin rikitaccen mamaki da ɗaurawa Bintu da Abdallah aure.
A wannan rana ta juma'a da misalin ƙarfe bakwai nasafiyar ranar mutanen da suke cikin ESTATE da maƙota da masu gadi da direbobi da ma sauran manyan mutanen da Alhaji Baba duk ya riga yasanar musu, wanda wasu sai bayan idar da salla suka dinga shigowa wanda daga cikin su har da manyan Aminan sa su Alhaji Nasir Wanda su basu san kiran nasa na meye ba sai da suka zo,duk sun shaida Auren Fatima Bintu Zahra da kuma angonta Abdallah Jafar,kai wannan rana na kuma sakan kan cewa, imani ya kuma ratsani na kuma sallamawa ubangi ƙadiran Ala manyasha'u, na kuma jinjinawa ƘUDURARSA, da ikon sa tare da buwayar sa, abinda yaso ya kasan ce ko ta yaya sai ya kasance Alhaji Umar ya ɗaura Auren ƴarsa ta cikin sa da hannun sa batare da shima yasani ba,batare da sanin kowa ba Allah ya zartar da ƙudurar sa da buwayar sa.
Wani irin farin ciki Alhaji Baba yake ciki dashi kansa bai san adadin sa ba, Abba Umar kuwa bayan farin cikin da ya tsinci kansa aciki hakanan sai tsohon mikin sa ya kuma tashi, can dakin mahaifiyar sa ya nufa ya sauke mata damuwar sa kamar yadda yasaba,ita kuma ta tarbe shi da tsantsan soyayya da tausayi wanda yake tsakanin uwa da ɗanta,duk da cewa itama tana cikin wani irin hali na damuwa da kewar gudan jininta da kuma farin cikin wannan Aure ji take kamar ta taka rawa saboda tsananin farin ciki,tana shafa kansa tana murmushi mai ɗauke da kishiyoyin ma'anoni, cikin taushin lafazi take cewa, Allah Ubangiji yasa Auren nan yazama sanadin wani haske da zai baiyana nan ba da jimawa ba cikin wannan ahlin, Allah Ubangiji yasa wannan Aure daka ɗaura ya zama sanadin kawo farin ciki A rayuwarka data ahlinka, Allah Ubangiji yasa wannan Aure yazama shine sanadiyyar ruguza duk wani ƙulli da aka ƙullashi acikin gidan nan!'da Amin Amin yake ta amsawa yanajin wani farin ciki da tun faruwar al'amarin bai kuma samun makamancin sa ba,(to nima dai ina yi muku fata da addu'ar ɗorewar farin ciki da kuma bayyanar gaskiya mu kuma Allah ya kawo mana ƙarshen masifun da suka addabi kasarmu ya kawo mana kuma farin ciki A cikin al'ummar mu yatabbatar mana da shugabanni masu adalci Amin Ya Allah)
Tofa FANS Taufiƙa sai ku zama cikin shirin abinda zai faru idan taji wannan labarin
Ko ya Abdallah da Bintu zasu ji idan suka sami labari? yaya Bintu kuwa zata karɓi aikin da Anty Nafisa ta bata?to wai ya zaman Aure zai kasance tsakanin waɗan nan taurari?Samira kuwa zata sami nasara akan Alhaji Sama'ila?kai dama sauran manyan tambayoyin da suke ƙulle acikin wannan rikitaccen labarin wanda da sannu zan warware muku zare da abawa dan haka sai ku shirya ku kuma kimtsa yan zu akasoma.
Fatima y AdamâœðŸ½
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 31 ```
A wannan rana zuciyoyi da yawa sun baƙanta wasu kaɗan daga ciki kuma sun faranta,taɓan garen,inno dai har yanzu zuciyar ta tana cikin zulumi da wasi wasi zuwa yanzu ta fara hararo tabbas A kwai wata maƙarƙashiya cikin al'amuran Bintu, da akwai wani ɓoyayyen sirri wanda bakowane yasan da shiba domin idan ba haka ba meye ruwan ahlin ALHAJI BALARABE da rayuwarta? meye yasa ake binta da sharri da makirci haka alhalin babu hurumin ta cikin mugayen al'amuran gidan, tabbas da A kwai wani ɓoyayyen sirri wanda insha Allah ita kuma sai ta binciko shi tare da taimakon Allah, amma bazata zuba idanu alalata rayuwar marainiyar Allah ba,tayi farin ciki da wannan Aure amma ta wani ɓangaren tana jin wata irin fargaba tanaji kamar wani abu zai iya samun Bintu ta rasa me mutanen gidan nan suke nema haka da kowa idansa ya rufe da salon mugunta da makirci na rashin imani idan ba rashin imani ba kamar Bintu za'a ɗorawa alhakin kisa har kuma a rufeta,ga kuma Abdallah da ba dan Allah yasa da sauran shan ruwan sa ba da yanzu batun wani ake bana saba, kai Allah ya kare mu daga sharrin zuciya ya tsare imanin mu.
Ita kuwa Hajjah ƴar duk inda ta daɗi sha ce,bata zauna da Bintu ba bare tace" ga abinda zata iya aikatawa da wanda baza ta iya ba,kawai dai ita tana tsakiya babu ruwanta da duk wani al'amarin da yake gudana A cikin ESTATE ɗin ita abin da ya dameta shine damuwar ta, ba ruwanta da shiga shirgin da ba nata ba ko ba asata cikin saba,amma tana da zafi idan kataɓota,kuma bata fiye ɗaukar matsalar wani matsayin tata ba,amma idan ka zauna da ita tana da fara'a dan zan iya cewa duk cikin matan Alhaji Baba ta fisu sakin fuska da wasa da jikoki shiyasa dayawa jikokin nasu sun fiyi mata wasa akan su Hajiya Babba da Inno,kuma tun yaran gidan suna ƙanana idan sukayi laifi itace mai hukunci,shi yasa ta wani ɓangaren suke bala in tsiron Hajjah,dan haka yanzu ma tuni ita ta manta da batun Bintun sai da taji sanarwar Auren ne take cewa to shi Abdallah yaji sauƙine? Jabir da shi ya kawo mata tsegumin ya bata amsa da yaji sauƙi,daga haka bata ƙa ɗaga zancen ba sai fatan Alkhairi da tayiwa Auren.
Ita kuwa Hauwa'u dama tuni tasawa zuciyarta dan gana, dan taga yanzu faɗan yafi ƙarfin ta na manyane sai dai ta koma gefe ta taya Taufiƙa yaƙin tunda ita taga zata iya amma zata bada gudummawa wajen ƙuntatawa rayuwar Bintu ita yanzu tuni ta haƙura ta amshi soyayyar Nabil da ya daɗe yana mata naci, ya fiye mata kwanciyar hankali akan taje inda ba asan da ita ba balle akai ga batun so.
Hajiya zulaiha ta kai ta kawo yafi sau goma gaba ɗaya kanta ya ɗaure da wannan al'amarin,ta zurfafa tunani sosai akan Bintu kuma tabi duk wasu hanyoyi dan ganin ko zata kama Bintu da wani laifi amma bata gani ba, tabbas yarinyar nan ta shiga komar magauta akwai ayar tambaya fa meyasa suke bibiyar ta kamar yadda suke bibiyar duk wanda ya kasan ce ahlin ALHAJI BALARABE wanda yake da masaniya akan ɓoyayyen sirrin nan?gaskiya abin nan da matuƙar ɗaure kai ita yanzu sanadin wannan muguwar rayuwar da ake yi A cikin ESTATE ɗin nan yasa duk ta hana ragowar ƴaƴanta zaman cikin gidan ko wanne ya lula wata ƙasa shida iyalan sa Rahimace kawai ta rage mata a gabanta,anya kuwa da wanda aka cutar a cikin ahlin nan sama da ita, ansa ta rabu da yaranta wanda suke sune sanyin idaniyarta abin alfahari agareta duk saboda kar acutar mata dasu ko arabata dasu kamar yadda aka rabata da hasken zuciyarta da kuma mijinta abin alfarinta me share mata hawaye a koda yaushe da yawan lallashin ta,wani irin kuka ne ya kufce mata mai azabar raɗaɗi,me cike da kewa ta rashin masoya guda biyu.