← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 120

Sashe 108

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kiran da yaji a wayar sa dake soke gaban rigar sa ita ta fara dawo dashi hankalin sa,amma duk da haka bai saki Bintu ba,a hankali ya zare bakin shi daga nata,tare da zuba mata ido,hannu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya,leƙa fuskar ya shigayi tare da cewa duk bakya buƙatar waɗan nan eye Bint?janye jikin ta tashiga yi a ƙoƙarin ta nasan guduwa,domin ita sam bata gane inda maganarsa ta dosa ba,riƙeta yayi ganin zata gudu yace"baki bani amsa ba,ko sai anjima zaki gaya min?da sauri ta daga kanta kamar zatayi kuka, murmushi yayi tare da sumbatar dogon hancinta,kana ya saketa,sai da taje bakin ƙofa kana ta ɗan dakata tare da juyowa tace"kayi sauri ka fito kazo falon Alhaji Baba saboda ina buƙatar ganin farincikin Ammi da Oga Abdallah!'tana gama faɗa tayi waje da gudu fuskarta dauke da murmushi,zubawa kofar idanu yayi hannuwan sa zube cikin aljihun shi,ɗan shafa cikinsa yayi dan shi sai yanzu ne ma yake jin yunwar gashi kuma su kaɗai ake bukata a falon Alhaji Baba,kafin ya samo mafita sai ga Bintu ta dawo hannun ta ɗauke da plat wanda yake shaƙe da jelof ɗin shinkafa da uban kifi wanda kusan rabin abincin kifine,sai ƙamshi take gwanin da ɗi da burgewa,har tazo gaban shi ta janyo dan Centre ɗin tsakiyar falon ta ajiye yana kallonta,sai da ta ɗago taga kallon da yake mata,sai kuma ta tura baki tare da cewa wai miye ne haka da kallo?bai bata amsa ba sai zama da yayi yana maida duban shi kan abincin,cikin kasalar da ganin ta ke saukar masa yace"abun burgewa mata tana son mijinta yaci abinci kamar kinsan yunwa nakeji!'kamo hannun ta yayi ya zaunar da ita kan cinyar sa tare da cewa ke kinci abincin ne?girgiza kanta tayi,bai ce komai ba ya shiga miƙa mata abincin bayan ya ɗebo a spoon,Bata son yawan yi masa gardama hakan yasa ta buɗe bakinta ya shiga bata abincin,sai da ya tabbatar ta koshi kana shima yaci,yana gamawa ya ɗaga ta yana cewa muje Bint kar muga dakarun Alhaji Baba akanmu!' dariya tayi kana ta zagaya hannun ta ta saƙalo hannun shi,a haka suka fita dan zuwa falon Alhaji Baba.

Kamar yadda akayi a farko haka yanzu ma kowa ya hallara har da ƙari,saboda yanzu da akwai Alhjin Nafisa da kuma Hajiyar ta Ladidi,kowa ya nutsu,shigowar Abdallah da Bintu kawai ake jira,yayin da Hajjah take cikin wani irin hali duban farko zaka san cewa a kwai tsoro da tarin fargaba a tare da ita, Anty Nafisa ma tun da ta ga zuwan baban ta da kuma Hajiyar ta cikinta ya kuma durar ruwa,cike take da tashin hankalin abinda zai biyo bayan abinda ta shuka,

Hannun su rike dana juna sukayi sallama,wanda su sun manta a yanayin da suke,sai da Bintu taga kallon da Inno take watsa mata kana ta ankara,da sauri ta zare hannun ta daga nasa,can wajen Ummin ta ta nufa ta zauna tare da kwantar da kanta a kafadar ta,shi kuwa Abdallah daga nan gefan Dady Mansur da Dady jafar ya zauna,Alhaji Baba ne ya bawa Abdallah umarni da ya buɗe taro da addu'a,bayan sun shafa addu'ar ne Alhaji Baba ya dubi Abdallah tare da cewa,har yanzu kai muke bi Abdallah meye abu na gaba da zaka gabatar mana dashi?wayar Safwan ya kira yace"ku shigo dashi!'baiyi minti ɗaya da kashe wayar ba,akayi sallama a ƙofar falon tare da sako kai alokaci ɗaya.

Kaf mutanen falon sai gasu a tsaye,daga mai murza idanu sai mai zaro su dan san da ɗa tabbatar da abinda idan nasu yake gani,A hankali Alhaji Baba ya shiga takowa har zuwa inda Dady Abubakar yake tsaye cikin kyakkyawar shiga ta kamala kai baka ce shine wanda yayi tsawon shekaru ba tare da yasan inda kansa yake ba,kama hannun sa yayi cikin nasa jikin sa har rawa yake gwanin tausayi, zuba masa idanu yayi sai ga hawaye shar suna tsartuwa daga idanun Alhaji Baba jarumin namiji,sai ga Hajiya Babba ma tazo saboda ta kasa daurewa tsayawa daga nesa ga Ni take kamar zata iya yin saken da zata kuma rasa ɗan nata,ita kanta Hajiya zulaihat alkunya tayi amma idanun ta tamkar zasu faɗo ƙasa saboda kallon Abubakar kuka take yi mai tsanani wanda yake tafe da wani irin kewa da shauƙi,duk ƴan uwansa dake zaune a falon babu wanda yake son ko ƙifta idanun sa yayi dan kar ya buɗe yaga babu Dady Abubakar,Abba Umar ne yazo da sauri tare da cewa, Alhaji Baba yayane fa ko baku gane shiba?bai sauraren su ba ya tafi ya rungume ɗan uwan sa tare da sanbatun farin cikin sake kasancewar sa acikin su, cikin ƙanƙanun lokaci falon ya dau sautin kukan mutane,Hajiya Babba kuwa kama su tayi gaba ɗaya shida Umar ɗin ta rungume ta kasa cewa komai sai wani irin murmushi wanda yake haɗowa da wasu zafafan hawaye,shafa kawunan su takeyi kamar baza ta sakesu ba,A hankali Alhaji Baba ya zaresu daga jikin ta shima yayi musu kamar yadda tayi,duk kan su sun rasa bakin magana sai zubar hawaye ,cikin nutsuwa yajasu suka koma inda yake a zaune daga nan yabawa sauran ƴan uwan sa damar raɓar Abubakar ɗin dan nuna farin cikinsu na dawowar sa,cur cur haka zaka ga duk wanda suka rungumi juna ya koma yana hawaye kai abun dai gwanin tausayi,rarrafawa yayi har gaban inno matar da ta so shi ta nuna masa kauna tamkar ita ta haifeshi,ɗora kanshi yayi bisa ƙafafunta,hannun ta tadora a kansa tana mai cigaba da zubar hawaye,A hankali tace"Abubakarina Allah ya nufi ganawar mu,yau ƙudura ta hadu da irada,ƙudurar Allah ce take ta wanzuwa acikin wannan zuri'a tamu,dama inaji ajikina zuwan Bintu da Abdallah cikin ESTATE ɗin nan haskene da warwarewar duk kanin matsalolin mu,na daɗe inajiran wannan rana mai ɗumbin tarihi a garemu, Allah ya karemu ya kuma shiga tsakanin nagari da mugu!'ɗagowa yayi cikin san kwantar musu da hankali,yace"inno ku daina kuka godiya ya kamata muyiwa Allah da ya nufemu da sake haɗuwa!'A hankali Bintu ta tashi taje har gaban Ammi ta kama hannun ta ta miƙar da ita,kowa sai ya maida kallonshi kanta,bata tsaya da Ammi ba sai a gaban Dady Abubakar,hannun shi ta kama ta haɗa dana Ammi idanun ta cike taf da hawaye tace"duba nan Dady kar kamanta da macen da ta ɗauki tsawon shekaru idanun ta na tsiyayar da hawayen rashin ka da na gudan jininta,Ammi kenan macen da tashaƙi ɓacin ran da ya kusa illata rayuwarta, duk saboda kai,Ammi ki kawar da fulako ki tarbi Dadyn mu,saboda abinda ke zuciyar ki ya wanku,abinda ya tsaya a ƙahon zuciyarki ya faɗa!'kuma takawa tayi taje ta kamo hannun Abdallah, tana zuwa ta haɗa dana Ammi da Dady Abubakar cikin hawayen tausayin su,tace"ya Abdallah inaso kayi farin ciki kamar yadda kasani, kaji irin abinda naji lokacin da ka haɗani da Ummina da Abbana,kaima yau gaka ga Dady ga kuma Ammi,ta ɗan kalli Ammi da ta zuba mata ido tana san fahimtar inda zancan BINTU ya dosa tace"Ammi ga nan Ya Abdallah shine ɗanki da suka ɓace lokaci ɗaya da Dady,wata irin zabura Ammi tayi sai kuma ta koma tare da riƙe hannun Abdallah kamar zata ɓallashi, Allahu Akbar tabbas naji ajikina kullum fatana kenan abinda nake tunani akan ka ya zama gaskiya, Alhamdulillah,yau haske ya baiyana duhu ya yaye,yau ranar farin ciki ce a cikin wannan ahlin,ta faɗa cikin zubar da wasu zafafan hawaye wanda zamu iya kiran su dana farinciki,

Dady Habib kuwa tamkar zararre haka ya koma yana zaune amma duba ɗaya zakayi masa kasan cewa baya hayyacin sa,cewa yake yi nayi sake nayi sake yau gashi ƘUDURAR ALLAH ta baiyana,Dady Mansur dake hankalce da shi da Dady jafar sune kawai suka fahimci halin da yake ciki ga kuma maganganun da yakeyi,wanda basu ji abinda yake cewa ba,amma dai tabbas alamu sun nuna Dady Habib yana cikin wani yanayi na tsaka mai wuya,kowa a cikin falon nan farinciki yake, amma banda waɗan da suka shuka suke jiran girbewa,idan ka duba zuciyoyin su tamkar ƙabari haka suke,su kuwa su Alhaji Hashir sun shige cikin masu taya ɗan uwan su murna da samun ɗan sa da jikokin sa,tunda su sun samu salamar yafiyar wanda suka yiwa kuma nasu ƙullin makircin bai kai na su Dady Habib ba, wannan dalilin ne yasa suka samu nutsuwar zuciya.

A hankali Abdallah ya rungume mahaifiyar sa ya haɗa da Dady,Rahima da ta ƙaraso itama ta rungume ɗan uwanta,ɗago idanunshi yayi ya ɗorasu kan rigimammiyar fuskarta kamar yadda yake faɗa,nuni yayi mata da ta share hawayen fuskarta, murmushi ne ya suɓucewa Ummi da sauran waɗan da suka kula da abinda Abdallah yayiwa Bintu,ita kuwa Bintu umarnin mijinta tabi tasa hannu ta goge hawayen da suka ɓata kyakykyawar fuskar ta,zama yayi ya zaunar da Ammi da Dady Abubakar,kana ya koma mazaunin sa,fuskar sa ɗauke da wani ɗan maƙalallan murmushi,shuru falon ya kuma ɗauka yayin da zuciyar Dady Habib ta cigaba da bugawa da sauri da sauri, zufa kuwa tamkar wanda ake sheƙa masa ruwan zafi.

Abdallah ya buɗe baki zaiyi magana kenan, sai Dady Habib ya riga shi cikin yanayin fita daga haiyaci da tashin hankali na birnin kunya, yace"me zakace? me kuma yayi saura?kai dai wan nan yaro bakaji da kyauba,na tabbata dama zaka zama annoba arayuwata shi yasa tun farko naso wan can shegiyar ta kashe min kai,amma sai ta munafunceni saboda wata manufa tata,to gashi nan dai itama bata tsira daga tarkonka ba, wallahi bazan ɓoye muku ba na tsaneka kai da mahaifinka da wannan tsinanniyar yarinyar me kwana ido biyu,duk kece kika jawo komai!'ya faɗa yana nuna Bintu da kamar zai je ya rufeta da duka,a tsorace kowa yake kallon Dady Habib,Alhaji Baba kuwa bakinsa buɗe da tsananin mamaki yake duban ɗan nasa,haka jama ar da basu san komai akan abinda ke faruwa ba, Abdallah kuwa waya ya yiwa Safwan tare da bashi umarnin a shigo da Abigirl,ci gaba yayi da kallon Dady Habib da ya kasa zama sai muzurai yakeyi yana kuma faɗar maganganun da tun ba a fahimta har mutane suka soma fuskantar inda tashin hankalin nasa ya dosa.
Chapter 108 · 0% Book details