← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 120

Sashe 65

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana fita Bintu ta ƙwatar da kanta jikin gadonta tare da lumshe idanun ta,tana mai tasbihi ga Ubangiji tare da ƙara gine masa akan baiwa da Ni imar da yayi mata,ita da kanta tana mamaki idan ta duba taga yadda take juya rayuwar Anty Nafisa,duk da ba ason ranta ba,amma Allah mai ƙudura ya ɗora mata shakkar Bintu tare da bin duk abinda ta faɗa mata cikin hikimar sa tasan fidda gaskiyar mai gaskiya,gashi dai yabata ƙwaƙwalwa da tunanin abinda ta tsarawa Nafisan kuma har hakan ya zamo mata alheri,tunda gashi ta sanadin shawarar da tabawa Anty Nafisa ta san abubuwa da yawa wanda su yakamata tasani tuntuni amma bata sani ba saboda wani abu da Ubangiji ya ɓoye wanda babu wanda yasan shi sai shi mai kowa da komai,sai kuma wani irin farin ciki da ya mamayeta saboda kasan cewar ta samu mahaifin ta a raye, kuma wanda ya kasance kamili cikin wannan har gitsatstsen family mai abubuwan al ajabi iri da kala.

A hankali Hajjah ta ɗora hannun ta saman kan ɗan nata, tare da cewa Habibu me yake damun kane? tun ɗazu kazo ka sanyani gaba da tagumi idan da wata matsala ba sai ka faɗa min ba!'ta ƙare maganar cikin yanayin damuwa da da muwar ɗan nata,ɗagowa yayi kana yace"wallahi Hajjah ba komaine yake damu na ba sai lamarin Yaya Mansur,na rasa me yasa idan zaiyi abu baya tunanin mai zai je ya dawo?cikin san jin abinda ya aikata Hajjah tace"me kuma yayi sababben?cikin jin takaicin abun yace"zuwa yayi har sashen Baffa Hashir ya ci masa mutumci wai yasan sune suka ɗauke masa Sayyid, to maza suyi gaggawar fito masa da ɗan sa ko ya ɗauki matakin da bazai yiwa kowa daɗi ba!'ya ƙarasa maganar yana ɗan huro iska ta bakinsa,shuru Hajjah tayi saboda tsabar takaicin halin ɗan nata,Dady Habib ne ya kuma cewa Ni abinda ya bani mamaki ma bai wuce yadda ya ɗorawa ɗan uwan mahaifin namu sharrin satar mutum ba,ko ta ina hakan zata faru?kuma duk yara sa wanda zai ɗauka sai Saiyyid ɗan Mansur mutumin da kusan shine ya raineshi da hannun sa,Hajjah da sai yanzu ta iya furta wani abu tace"anya kuwa Mansur baya shaye-shaye?idan kuwa har baya shan komai to tabbas yana da taɓin hankali,saboda abin nasa ya wuce makaɗi da rawa,kuma wan nan magana har gaban Alhaji dan wannan hauka ne da rashin kamun kai!'Dady Habib yace"nima abinda nayi tunani ke nan shi yasa na fara sanar dake dan kar yaje yayi abinda zai ɓata musu zumunci!'hakane Habibu Allah yayi maka albarka ya kuma shiryaku baki ɗaya kai da ƴan uwanka,da Amin ya amsa cikin jin daɗin addu'ar mahaifiyar tasa.

Kallon ta take ta cikin miƙab ɗin dake sanye a fuskar ta,kallon da take mata kallone na tsana da ƙyashi, da kuma uwa uba baƙin cikin da take son yi mata na toshe mata hanyar samun burinta,tunda taƙi gaya mata inda Abubakar yake wanda ita kuma tayi yaƙinin cewa Laila tasan inda Abubakar yake kawai dai taurin kaine ya hanata faɗa mata,wanda tasan a ƴan kwanakin nan zata sauke mata shi,sunkuya wa tayi ta danƙi gashin kan lailan tare da cewa zaki iya gaya min ko har yanzu baki shirya ba?karfa ki manta kece kika dawo dani kan hanyar da da na kauce mata,wanda dama shine sanadin satoku daga wan can gurin amma sai wani dalilin ya sha kaina na sauka daga kan hanyar da nake da farko, amma sai gashi cikin tabbatuwar samun nasara ta sai ya zamana ke ɗin ke kika dawo da tunani na,to amma me yasa bazaki yi min abinda nake so ba?nace miki in dai kika gayamin suwaye mutanen dasuka ɓoyeku da kuma inda suka ɓoye Abubakar,to nayi miki alƙawarin zan kula da rayuwar Bintu ba zan bari wani abu ya cutar da ita ba!'tana direwa Laila ta ɗauka da cewa ke baki isa ki kare rayuwar wasu ba,tun da kema baki iya kare taki ba,kuma Bintu bata buƙatar kariyar wani bawa kariyar ubangiji take buƙata kuma ta riga tasamu,dan haka sai ki bi wani sarkin Bintu ta riga tafi ƙarfin shu'umancin ku gaba ɗayan ku macuta azzalumai insha Allah ƙarshen ku yana nan zuwa,Ni na gaya miki sai kun to zarta ke da duk wani mai kwatankwacin irin mugun halinki!'kafin ta gama rufe bakin ta matar ta ɗauke ta da wani mahaukacin mari,tana wani irin huci kana tace" ki kiyayeni Ni ba A faɗa ina faɗa,sai kinyi nadamar waɗan nan kalaman naki,dani kike zancen,daga haka ta fita daga ɗakin tamkar kububuwa,tana mai jin baƙin cikin yadda takasa samun abin da takeso,duk faɗi tashin da tayi kuma take kan yi,ko a iya binciken neman Abubakar ta tsaya ya isa a jinjinawa namijin ƙoƙarin da tayi,saboda ita farko neman ABUBAKAR takeyi amma sai tayi kacibus da su Laila,wanda sam da farko batayi niyar ɗauke su ba,amma sai ta canja shawara ta yaudaresu da nufin taimakon su zatayi sai da suka bata labarin su kaf ba tare da sun ɓoye mata komai ba,tun alokacin ta so su gaya mata ko waye ya ɓoye su sai kuma tayi rashin sa a suka gano nufinta,shine dalilin da yasa ta kwashe su gaba ɗaya ta killace da nufin zata iya gane ko waye ta hanyar neman su Lailan da zaiyi,amma sai taji shiru wanda hakan ne ya kuma tabbatar mata da cewa wannan mutumin baƙaramin shu'umi bane,saboda ya kulle duk wata hanya da zata sa agane shi, wannan shine dalilin da yasa tasan tarihin Laila da fafi kuma shine dalilin da yasa take faman ajiye dasu tsawon shekaru,gane Bintun bai yi mata wahala ba tunda tayi binciken ta yadda ya kamata,to kuma sai gashi itama Bintun tana yaƙin neman mahaifiyar ta,abu ɗaya ne yasa ta rabu da Bintu shine tana so ta gano musu wannan mutumin,da zarar tasame shi ita kuma lokacin zata samu kyakkyawar dama akan su su duka,dole tana buƙatar sanin waye wannan mutumin saboda shi kaɗai ne yake da fawar riga ta samun abinda take nema kuma tana ganin kamar Abubakar yana hannun sa,shi yasa take da tabbacin su Laila sun san inda yake tunda sun zauna tare da mutumin,duk da cewa ita bata yar da da wani zuwa wajen boka ba tafi yadda da kaifin basirar ta to amma alokacin sai da ta dangana da wani hatsabbin boka wanda shine ya bata tabbacin anan aka ɓoye Abubakar sai kuma gashi a maimakon ta samu Abubakar sai ta samu su Laila,wan nan abin shi yake matuƙar ci mata rai, kuma tana da tabbacin sun sani amma shegen taurin kansu ya hana su faɗa mata gaskiya,amma babu komai tunda ta haifi ɗiyar da zata nuna mata komai, batare da tasha wahalar da tasha a baya ba,

Tun da ya shiga office ɗin bai huta ba,saboda aiyukan da ya tarar,sai dai lokaci lokaci tana yawan faɗo masa a rai,da tunanin ko ya take?ko wane hali take ciki yasan ta da shegen tsoro,shi yasa duk yake jin damuwa aransa,yana fatan dai Allah yasa bata cikin firgici, wayar dake salular dake cikin office ɗin ce tayi ringin ɗaga wa yayi tare da amsawa da ok ya ƙara so!'ajiyewa yayi tare da cigaba da duba wasu manyan fayal dake gaban sa,sallama akayi tare da turo ƙofar officce ɗin, Abdallah ya amsa sallamar yana mai ƙurawa mutumin da yashigo idanu dan san tuna inda yasan shi,har mutumin ya zauna Abdallah bai ɗauke idanun sa daga kansa ba,cikin tsuke fuska Abdallah yace"me ya kawoka officce ɗina? ƙoƙarin tashi yake ya bar officce ɗin saboda fes ya tuna fuskar mutumin idan bai manta ba wannan mutumin yana daga cikin tawagar su Alhaji Nasir,to me yake nufi da zuwa har cikin officce ɗin sa?Alhaji Rufa'i kamar yasan tambayar dake zuciyar Abdallah yace"Abdallah ka tsaya ka saurare Ni a kwai tarin manufofi da kuma ma ana da muhimmanci cikin wannan ziyarar tawa, wanda banyi wannan ziyarar kai tsaye ba har sai da na nemi izinin Dadyn ka jafar!'tabbas kuwa Abdallah sauraran Rufa i Abune mai matukar mahimmanci,dan haka ina baka umarni daka tsaya ka saurari abinda yazo dashi!'Dady jafar ne yake wannan furucin a yayin da yake sako kansa cikin Officce ɗin na Abdallah,zama yayi ba tare da yayiwa Dadyn nasa musu ba sai dai zuciyar sa cike take da mamakin yadda akayi zai samu wani abu mai muhimmanci daga bakin ɗaya daga cikin abokan gabarsa, wanda shi dai baya raba ɗayan biyu cewa yaudara ce,amma dai bari ya saurare shi ɗan yaji shi kuma da wace irin al mara yazo ko kuma tatsuniya...

Tuna sarwa Alhaji Rufa'i shine babban yaron Alhaji Baba dake kula da kasuwan cin sa na Kano,kuma shike auren daya daga cikin Æ´aÆ´an Alhaji Baba wato sakina,kuma É—aya daga cikin Æ´an kungiyar su Alhaji Nasir,

To gashi dai yayi tattaki yazo har inda Abdallah yake, kome yakawo shi? Wannan duk sai mun haÉ—u cikin nest page....

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 40 ```
Chapter 65 · 0% Book details