Sashe 110
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tana yin shuru Dady jafar ya ɗora musu da tarihin musuluntar sa da yadda akayi ya fara zargin Abigirl, da yadda akayi suka binciko asalin Abdallah har sukayi dabarar kawoshi gidan dan aiwatar da aikin sirri,gaba ɗaya falon aka ɗauki kabbara masu share hawaye nayi masu kuka nayi,wanda da yawa labarin Abdallah ne ya ɗimauta su ya kuma gigizasu har yasa su zubda hawaye,Bintu kuwa numfashinta har ɗaukewa yake,saboda matsanancin kukan da take na tausayin rayuwar Abdallah,haka Dady Mansur da Dady Abubakar da Abba Umar da su Ammi Ummi Hajiya Babba da inno kowa kuka yakeyi da kuma Allah wadai da wannan baƙin azzzlumin can ƙarƙashin zuciyar su kuma suna jin bazasu iya yafewa mai wannan alhakin ba, Abdallah kuwa gaba daya neman kasa riƙe kansa yake saboda yadda kukan BINTU ke kiɗima tunanin shi,idanun shi suna kanta so yake kawai ta ɗago kanta daga jikin Ammi dan yasamu damar rarrashinta koda da ido ne,a jikinta taji cewar yana kallon ta hakanne yasa ta ɗago kanta a hankali ta ɗora rinannun idanunta akan kyakykyawar fuskar shi,sai kawai taga ya lumshe idanun shi haɗe da budesu duk alokaci ɗaya,kana ya shiga yi mata nuni da ta share hawayenta,yanzu lokacin kuka ya ƙare,yana gama yi mata nunin sai ya tallafe fuskarsa a cikin tafikan shi yana ci gaba da yi mata wani irin narkakken kallo,wanda tuni ya tafiyar da gajiyarta da kuma damuwarta,hannu tasa ta shiga share hawayen tana ci gaba da kallon sa ƙasa ƙasa dan bata jin zata iya shigar da idanun ta cikin nasa,kamar yadda taga alamun yanaso suyi,Muryar Alhaji Baba ce ta katse musu hirar kurman da sukeyi,cikin dishashshiyar Muryar da kanaji kasan cewa tayi kuka, yace"baiwar Allah muna sauraren ki har yanzu baki sanar damu wanda duk ya kitsa wannan munanan aiyukan ba!'a hankali ta ɗaga hannun ta tayi nuni da inda Dady Habib yake rakuɓe kamar ɓeran da mage ta tarfa....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 60 ```
Kowa sai ya maida hankalinsa saitin da take nunawa, cikin fatan kar abinda yake zargi ya kasance Alhaji Baba yace"ban fahimceki ba? kiyi mana bayani sosai yadda zamu fahimta!'ya ƙare maganar tasa cikin bugawar zuciya da fargaba, Abigirl ta buɗe bakinta cikin yanayin tsoro tace"gashi nan Habibu shine mutumin da na karɓi Abdallah a wajen sa!'ɗuf falon yayi lokaci ɗaya,A hankali Alhaji Baba ya shiga jan innalillahi'wa'inna ilaihi raji'una,kansa a ƙasa yana tsiyayar hawayen da ya kasa daurewa rashin zubar su,a halin yanzu kuwa bazan iya ce muku ga misalin halin da Dady Habib da Hajjah shuke ciki ba,ƙwaƙƙwaran motsi an rasa wanda zai farayi a wajen, wannan shine ana zatan wuta a maƙera,su Baffa Hashir sunyi matuƙar girgiza da jin wannan batu,dan aduk bulayin su da hasashen su basu taɓa kawo Dady Habib a cikin mummunan tunani ba,inno da Hajiya Babba kuwa gaba ɗaya idanun su yana kan Hajjah,Dady Abubakar ne yaga gara kawai ya ƙarasa musu da abinda basu sani ba ayi ta taƙare,dama mahaifinsa kawai yakeji,amma yasan Alhaji Baba a ko da yaushe mai tawakkali ne da haƙuri da ƙaddara,dan haka cikin nutsuwa yayi gyaran murya tare da cewa, Alhaji Baba ka gafarce Ni ka kayi haƙuri kuma da duk abinda zaka ci gaba da ji har lokacin da komai zai dai-dai ta!'ɗan shuru yayi kana ya cigaba da cewa,tun tsawon lokacin da aka nemeni aka rasa agidan nan,ina kusa daku kuma A cikin gidan nan,cikin damuwa da kaicon rayuwar da ɗan uwan nasa ya saka kansa a ciki, ya basu labarin duk abinda ya faru iya wanda ya faru acikin tunanin sa, har kawo lokacin da Bintu da Abdallah sukayi nasarar fito dashi zuwa yanzu da ya dawo cikin ahalinsa,yana ajiye numfashi Dady Mansur ya ɗora da nashi labarin kamar yadda ya sanar da Hajjah,
Da ƙyar mutanen dake falon nan suke iya jan numfashi saboda tsananin mamaki da tu ajjubi,babu kama abun da su Alhaji Nasir suke faɗa kenan,sunji kakansu a san duniya,Nana ƙarama kuwa kuka take sosai da jin abinda ɗan uwanta ya aikata,da yawan ƙannen sa da kuka sukeyi da jin matsananciyar kunyar Ahlin Hajiya Babba, Alhaji Baba ne ya ɗago kansa bayan yaci nasara akan zuciyar sa da idanunsa,da kallo ya dunda bin ƴaƴa da jikokin nasa,kana kuma cikin wata irin murya mai kama da wadda aka shaƙe, yace"Alhamdulillah masha Allah,Ni kuma jarraba ta akan ka take Habibu,to wai duk akan wannan diamon ɗin ake wannan ta asar acikin ahlina ba tare da na sani ba? Ni kam wane irin uba ne?Habibu mai na rageka dashi da har kake ƙoƙarin gina jikinka da haramun kake son kashe ɗan uwanka da ɗanka?ko dan baka san zafin ɗa bane shi yasa kake raba tsaka nin iyaye da ƴaƴan su?ka rabani da ɗana shi kuma ka rabashi da ɗan sa,ita kuma Laila ka rabata da iyayen ta,ka rabata da ƴarta, duk da cewa ba kaine ka fara rabasu da farin cikinsu ba,Habibu ka bani mamaki na dade banji makamanciyar rayuwa irin taka ba!'ya ɗan tsagaita da maganar yana jan wani wahalallan numfashin da yake ne man gagarar yin shi,kana ya cigaba da cewa,Habibu me kake nema?anya kuwa diamon kaɗai ya isa ka salwantar da rayukan ƴan uwanka?
Ɗago jajayen idanun shi yayi da shi kaɗai yasan irin azabar radaɗin da zuciyar shi take mishi,girgiza kanshi yayi tare da yin magana cikin wata razanniyar murya,wadda take cike da nuna tsananin da yake ciki,yace"Alhaji Baba duk kaine ka jawo wannan ƙiyayyar da nakewa dan uwana,saboda fifita shi da kayi sannan gashi Ni ban taɓa haihuwa ba,a asalima likitoci sun tabbatar min da cewa bazan taɓa haihuwa ba, sannan tun ina yaro Nakasance mutum mai san duniya da ganin nafi kowa kuma ansoni fiye da kowa,sai dai kash duk ban samu hakan ba,dalilin da yasa na fara cusawa zuciyata neman kuɗi ta kowace irin hanya,da ɗin da ɗawa kuma ga abokai ƴaƴan manya wanda ake sakar musu da dukiya ina tare da su,a hankali burika na kullum da ɗuwa suke ina girma burina yana da ɗuwa,gan da bikina sai katsam na haɗu da abokina Saddam wanda shine sanadin duk wani arziki nawa da kuma kaucewa ta,tun da yakawo mun tayin sama ar sa,banji ko dar ba na karɓa saboda alokacin nayi nisa idanuwa na sun gama rufewa,tun daga lokacin na faɗa harkar tsafi nayi tsundum har mukami aka bani,babu wanda zai iya gane halin da zuciyata take ciki saboda na iya taku na,nasan ta kan yaudara,da wannan halin da rufe zuciyar kowa,na saka ƙaunata da yarda a zukatan dangi da ƴan uwana,na samu arziki wanda bazai kwatan tuba sai dai kuma ban bari kowa ya fuskanci daular da nake ciki ba,a hankali nake tafiyar da al amurana cikin dabara da salo na wayo,da kuma sihirin da nakeyi,sai kuma katsaham rana ɗaya na samu labarin diamon ɗin nan wanda nasan idan nasame shi na gama shahara a duniya tunda yanzu sunan da nayi a harkar tsafine kawai kuma har kar sirri ce,Ni kuma burina bai gama cika ba sai na ganni ina damawa da manyan ƙasashe da ƙusoshin masu kuɗi wanda sukayi suna a faɗin duniya,amma sama ar da nakeyi ba zaiyuwu na cika wannan burin nawa da itaba tunda arziƙin nawa ma na kasa bayyana shi saboda gudun zargi,labarin diamon kuwa da yazo kunne na,shine ya sa na fara jin cewar burina zai iya cika ta sanadin sa,dan haka banyi ƙasa a gwiwa ba,nayi duk yadda zanyi cikin shu uman cin tsafi na sace Abubakar,daga baya na sace ɗan sa Abdallah saboda,a nawa tunanin gani nake idan Abdallah ya girma zai iya gadar mahaifinsa ta wajen mallakar diamon ɗin, sam na manta da cewa yana da ƴan uwa,saboda idona ya rufe da tsanar Abubakar da ta shafeshi,sai kuma daga baya muka gano zulaihat ɗin na da wani cikin,alokacin na riga na gama shirya yadda zanyi,da sabon dan fasaha haifa sai kuma ta haifi mace, ƴaƴan Abubakar kaf ɗin su Nine sanadin tarwatsasu,saboda yadda nake razanasu tare da mahaifiyar su,akan rayuwar su,a haka suka rayuwa cikin tsoro da fargaba har dai sukayi aure,mahaifiyar su ta turasu can wata duniyar dan kar a salwantar mata dasu,kamar ma ba a haiyacin sa yake ba haka ya cikagaba da zaƙulo magana yana haɗar duk wani abu da yayi hatta da irin matan da suka kashe da ƙananan yara da sukayi aiki dasu,bai ɓoye ba sirrin su kaf na cikin ƙunya sai da ya faɗa ya daɗa da faɗar inda suke zaman mitin da sunan dajin da suke aikin tsafinsu.