← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 120

Sashe 37

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duk takun da zaiyi sai yaji bugun zuciyarsa ya ƙaru, yana kusan tar wajen ajiye motocin yana jin jikin sa na wani irin rawa da sanyi tamkar ana zuba masa ƙanƙara, A hankali yasa hannu zai buɗe motar amma sai yaji ya kasa, haka nan zuciyarsa ke sanar dashi da wani mummunan abu na shirin faruwa,to A ina kuma A kan waye? ɗan jim yayi yana sauraren bugun da zuciyarsa keyi,waywayawa yayi yana fuskantar ɓangaren su Sayyid kasan cewar ataɓangaren gurin ajiye motoci ɗakunan su suke,hakanan yaji kamar ana ingaza zuciyar sa da ya shiga ɓangaren, A hankali yake takawa yayin da duk taku ɗaya bugawar zuciyarsa ke tsanan ta,bai tsaya ba har sai da ya dangana da ƙofar ɗakin ɗaya daga cikin samarin,har ya ɗora hannun sa kan mariƙin ƙofar sai kuma yashiga tunanin abinda zai kaishi me zaiyi A wajen idan yashiga mai zaice da mamallakin ɗakin? dan haka zuciyarsa ta umarce sa da barin gurin.

Bintu kuwa ta gama yin laushi ta kuma sadaƙar yau ƙarshen rayuwar tane yazo, dan tabbas Sayyid ya ɓata mata rayuwa baƙin cikine zai sa ta haɗiyi zuciya ta mutu,duk yaji mata ciwo ya kuma yayyaga mata kaya,lokacin da hannunsa ya taɓa lallausar fatar jikin Bintu ji yayi ya kuma ruɗewa idanunsa sun riga sun rufe baya sauraren kalaman Bintu na magiya wan da suke shige da waƙe saboda yawan jaddadawa,numfashin ta sai ƙoƙarin kumcewa yake saboda tsananin jigata da wahala da kuma yawan kukan da tasha,wani irin murmushi yayi na ganin yana dab da cimma burin sa.

A dai dai lokacin kuma da Abdallah yake ƙoƙarin juyawa dan barin wajen,tamkar mayen ƙarfe haka yaji an fixgi zuciyar sa zuwa ga ɗakin da yake kusa da wanda ya fasa shiga.

Yana gab da san cin ma manufarsa yaji tamkar duniyar tana juyawa dashi, yayin da kuma ya kasa tan tan ce duniya da lahira saboda wani irin mummunan naushi da ya bakunci fuskarsa wanda take haƙoran sa guda biyu suka biyo bayan naushin, kafin ya dawo haiyacin sa ya kuma ji anyi sama dashi tamkar ƴar tsana an wurgashi kusuwar ɗakin in da ya faɗo ƙasa tamkar kayan wanki, Abdallah dukan Sayyid ya shigayi tamkar ba ɗan Adam yake duka ba,hatta Bintu da bata hayyacin ta sai da taji tsoron kar Oga Abdallah yaje yay kisa, Sayyid ɗin ma ya daina motsi amma yaƙi daina dukan sa, A hankali ta rarrafa jiri na san yadda ita,tana kusan tar inda yake jiri ya ɗebeta ta tafi luuu, zata faɗi, babu shiri yay wurgi da Sayyid dake hannun sa ya tafi ya tarota, waɗawa tayi jikinsa numfashin ta na ƙoƙarin ɗaukewa,rigarsa ya cire ya rufa mata kana yay mata ɗaukan jarirai yabar ɗakin da ita.

Cikin mota ya sakata ya kwantar da ita kana ya shiga ya figi motar da gudu kamar zai tashi sama,har yanzu bayajin yayiwa Sayyid hukuncin da yakamata,zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinsa haka yake ji saboda tsananin ɓacin rai,tabbas ba iya abinda ya kamata yayiwa Sayyid ba kenan dole ne yasa ayi masa horo mafi muni A rayuwar sa wanda sai yaji dama ba A haife shi ba.

Da wannan tunanin yazo haɗaɗɗan gidan sa wanda yake A area 2, unguwar kanta abin kallo ce balle kuma gidajen dake cikin ta,guri ya samu yayi pakin bayan sojan mai gadin ya ɓuɗe masa get,buɗe bayan motar yayi ya ciro Bintu da har yanzu bata farfaɗo daga suman wahalar da ta tafi ba,ɗaukar ta yayi A kafaɗarsa ya nufi cikin gidan da ita.

Duk kansu A falon ya samesu shi ko kula da motocin su baiyi ba saboda baya cikin nutsuwarsa,gaba É—aya binsa sukayi da kallo batare da kowannen su ya iya yi masa tambayar dake zuciyar saba,har sai da ya shige É—akin dake cikin falon da ita, kana suka shiga kallon junansu amma duk da haka basuce komai A junansu ba suna dai jira su gane koma meye dan sun san dai da wuya Oga Abdallah yayi musu bayanin abinda bai shafe su ba.

Sai da ya fara shafa mata ruwa ta farfaɗo daga suman da ta tafi, kana ya saka mata ruwa saboda ƙwarin jikinta ya dawo duk da sai da sukayi artabu duk tabi ta cukwikwiye ta wahal dashi kafin ya soka mata allurar ruwan, saida yaga bacci ya ɗauke ta kana ya canja wasu kayan ya fita falo dan tattauna wa da yaran sa, bai ce musu komai akan Bintu ba dama suma basu sa ran zai faɗa ɗin ba,sun tattauna abubuwan da suka shafe su da kuma yadda zasu fuskanci wannan gagarumin yaƙin da suka tasa A gaba, kowa ya bashi ɓangaren da zai fuskanta yayin da ta ɓangaren Alhaji Salisu shima suka canja tsari dan yanzu A maimakon bibiyar Alhaji Salisu zatayi, yanzu Alhaji Sama'ila zata bi dan ƙulla alaƙar soyayya,duk da cewa yasan su Alhaji Nasir basu san da wannan shirin ba tunda daga shi sai Samira sukayi maganar A wan can ranar cikin office dinsa batare da sauran yaran nasa ba,sallamar su yayi batare da yayi musu ƙarin bayani a kan Bintu ba.

Nabil ne yazo zai shiga ɗakin sa ya hango Sayyid A sheme kamar matacce da gudu ya ƙarasa cikin ɗakin ya ɗagoshi cikin tashin hankali, ya shiga jijjiga Sayyid da ko motsi baya yi dan kuwa matuƙar buguwa ya bugu,da gudu ya fita bai tsaya ko ina ba sai sashen Dady mansur,kiran da sukaji Nabil ɗin na kwarara musu shi ya fito da su A tuɗe kowa da irin tambayar da ya kewa Nabil, bai tsaya basu bayani ba kawai yaja hannun Dad suka fita yayin da mama ta shiga binsu Abaya cikin tashin hankali,

Lokacin da suka ga halin da Sayyid ya ke ciki gaba ɗaya ruɗewa suka kuma yi,dan ita mama ta kasa daurewa kuka ta saka tana faman sanbatun tambayar waye yay mishi haka waya keson kashe mata yaro? haka dai take ta jefo zantuka cikin fitar hayyaci, Dady Mansur kuwa saɓa shi yayi A kafaɗarsa ya nufi wajen mota dashi cikin tashin hankali mara misaltawa duka nufi asibiti.

Inno ta shiga ɗakin Bintu yayi sau ashirin, tun tana kasa magana har ta fito da tashin hankalin ta A fili bata san sanda ta fara tambayar su Taufiƙa ko sunga gilmawar Bintu ba,amma duk cikin su babu wanda ya bawa tambayar muhimmanci, saima cewa Taufiƙa tayi inno ki daina neman yariyar nan,dan ba yau ta fara wannan halin ba ke ce dai sai yau kika lura!' wani irin kallon takaici inno tabi Taufiƙa dashi batare da ta iya furta mata komai ba, ta ɗaga wayarta dan ta kira Rahima ta tambaye ta ko suna tare da Bintun.

A hankali take buɗe idanunta da sukayi mata nauyi,tun tana ganin dishi dishi har suka buɗe tarwai,wata gigitacciyar ƙara ta saka tana ƙoƙarin fizge ƙarin ruwan dake hannun ta,gaba ɗaya ta fita haiyacin ta, A tsorace take gani take kamar har yanzu tana dakin Sayyid,A hankali ya turo ƙofar ɗakin ya shiga waya saƙale A kunnensa da ga dukkanin alamu da inno yake wayar dan naji ya na cewa ta farka karki damu idan mun dawo zanyi miki bayani!' daga haka ya katse wayar yana mai ɗora mata rikitattun idanun sa masu saukarwa da mutum nutsuwa,aiko take Bintu ta nutsu ta daina ihun da takeyi amma ba ta daina kukan ba,zare mata ruwan yayi kana ya juya da niyar barin gurin,riƙo hannunsa tayi gami da ƙara sakin wani marayan kuka,ɗan tsaiki yayi gami da juyowa A matuƙar fusace dan dama har zuwa lokacin bai gama hucewa ba,cikin tsananin fusata da ɓacin rai yace"meye ne kuma zan miki Ni nakai ki ɗakin nasa da zaki na cikan kunne da ihu?idan da banzo ba me kike tunanin zai faru?duk wannan tsoron naki amma bai hanaki shegen shige shige har sai kin kai kanki inda ake neman rayuwar ki!' cikin kukan tace Ni bani naje ba jana yayi ta ƙarfi ina cikin tafiyana!'ɗan tsuka yayi gami da zare hannun sa daga nata,cikin shagwaɓaɓen kukan nata ta kuma cewa dashi Ni dai yunwa nakeji!'sai ki tashi ki girka!' ya faɗa yana mai kawar da kansa gefe,tura ɗan ƙaramin bakin ta tayi tare da cewa" to ai Ni bani da lafiya!' bai saurareta ba ya fita daga ɗakin,shiru tayi cikin mamakin Al'Amuransa meyasa duk sanda take buƙatar taimako shi yake zuwa ya taimake ta? wani lokaci me kirki wani lokacin kuma akasin haka, tana cikin wannan tunanin har ya dawo hannun sa riƙe da take away miƙa mata yayi, hannu tasa ta karɓa tare da tashi zaune cikin sanyin murya tace" na gode!'bai dai tan ka matan ba ya kuma fita daga ɗakin,baki ta taɓe tare da buɗe take away ɗin ta.

Inno ta samu kwanciyar hankali jin Bintun tana tare da Abdallah,sai dai zuciyarta da take tayi mata saƙe saƙe akan bintun, ko me ya faru da marainiyar Allah? ko ma dai meye dole ta ajiye ta barwa safiya.

Sayyid kuwa yana can hannun likitoci suna kula dashi yayin da Alhaji Mansur yake Allah Allah Sayyid ɗin ya farka domin yaji uban da yayi masa wannan mummunar rauni har da cire haƙora, tabbas ba zai taɓa yadda ba dole sai ya ɗauki fansa wanda zata kasan ce ta ramuwar gayya.
Chapter 37 · 0% Book details