Sashe 117
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maganar Bintu ce ta dawo da ita daga tunanin da ta lula,tace"Ya Abdallah sauke Ni haka ka gaji,zo muje muci girkin inno!'yadda ta faɗa ɗin haka yayi, sauke ta yayi tare da nufar kulolin a hankali ya fara savin ɗin su a plat ɗaya,sai kuma Bintu duk daji babu daɗi abinda sukayiwa Taufiƙa hakan ne yasa ta ɗan dubeta a sanyaye tace"Anty Taufiƙa bazaki zauna bane?jin haka da tayi daga bakin Bintu sai tayi saurin durƙusawa kasa tare da kama hannun Bintun cikin kuka wanda ke tafe da hawayen nadama tace"dan Allah ƴar uwata ki haƙuri ki gafarceni!"cike da mamakinta Bintu take dubanta,kama hannunta tayi suka miƙe janta tayi har zuwa falon kana suka zauna, cikin sanyin murya Bintu tace"Anty Taufiƙa shin wane irin tuba kikayi?cikin kukan Taufiƙa tace"wallahi wallahi wallahi kinji rantsuwa har uku ta musulmi,nayi tuban da bazan kara komawa ga aikata ko wane irin zanuɓi ba,Bintu rayuwarki ishara ce ga mutane masu san zuciya kuma abar koyi ce,ƙaddararki ƙaddara ce wadda take cike da darussan rayuwa ga mutumin da ya gane,dan haka na tuba na janye duk wani batuna zan auri Sayyid dan uwana tunda shi Allah ya zaba min matsayin abokin rayuwa!'cikin farin ciki Bintu tace"Alhamdulillah masha Allah Allah shine abun godiya,kana ta ɗan gyara zamanta tana cewa Anty Taufiƙa ki sani cewa duk wanda yayi imani cewa a kwai wuta kuma akwai aljanna dole ne ya kiyaye kansa daga fadawa daga halaka ta sharrin shaidan wanda zata kasance masa azaba a gurin ubangiji,muna aikata kuskure mai girma a cikin rayuwar mu wanda sam hakan bai kamata ba,duk wanda ya dauki burin duniya ya saka a ransa to kuwa tabbas yayi ƙawance da shaidan,domin shi shaidan babu abinda yake so irin yaga ana aikata saɓo,manzan Allah s.w.a ya tambayi shaidan cewa shin mai yake sawa ƙashin bayansa ya karye? sai yace,yaga ana tuba dan komawa turbar gaskiya,
San nan a kwai lokacin da mala'ika jibrilu yazo yana bawa Annabi a,w,a labarin jahannama har yazo kan ƙofar wuta ta bakwai,irin azabobin da Annabi yaji za ayiwa waɗan da suka kasance a cikin wannan ƙofa sai da ya suma,bayan ya farfaɗone yake cewa da maka'ika jibrelu dama akwai wata al umma ta da zasu shiga cikin wuta? shin zaka bani labairin waɗan da zasu shiga cikin wan nan ƙofa?sai mala'ika jibrelu yace"masu manyan zunubai ne wadan da suka koma ga ubangiji basu tuba ba sune zasu shiga wannan kofar wutar!'wa iya zubilla alla ka kiyashemu da ita,dan haka duk wanda ya tuba daga wani aiki na saɓo da yake aikatawa ba ƙaramin rabone dashi ba,kin ga yanzu ke kin dace muna fatan dacewa har acan ƙiyama!'cak taji an ɗaga ta sama,ƙamshinsa da taji ne ya kuma tabbatar mata da cewa shine,duk da tasan shine kadai zai iya yi mata haka, yace"princess mun gode da wannan ta ƙaitaccen wa"azin haɗe da tunatarwa Allah yasaka da Alkhairi ya bamu dacewa da kuma babban rabo na Alkhairi,yanzu muje ki karya ki bar amaryar Sayyid itama taje gida ta fara shirin sabuwar rayuwa mai cike da daɗi da sirrika da kuma ɗumbin lada gurin Ubangiji!'sai kuma Taufiƙa taji duk tana jin kunyar Abdallah dan haka ta miƙe cikin sanyin jikin da kalaman Bintu suka ƙara saukar mata, cikin nutsuwar da da bata da ita, ta ce dan Allah ya Abdallah ka yi hakuri ina fata zaka dinga kallona kamar Rahima dasu Shakur!'jinjina kanshi yayi cikin jin dan tausayin Taufiƙan yace"kar ki damu Allah ya kaimu ya kuma yafe mana baki ɗaya!'suka amsa ita da Bintu daga nan ta fita daga falon Bintu ta ɗan daga murya tana cewa sai munzo shan biki dan nima ban yafe nawa ba sai anyi mun!'tana dariya a hanyar ta ta ƙarasa fita tace"ai ke angama da babinki tunda komai yayi daidai,shine ƙarshen maganarta da ta faɗa ta kai waje,
Zaunar da ita yayi kan cinyar sa ya fara bata abincin,ganin kamar bata son ci,sai kawai ya shiga ɗurawa abakin shi sai ya tauna sai ya ɗura mata,tamkar dai cin abincin tsuntsaye,(wai ko Ni nan Fatima ƴar uwar Bintu ban taba tunanin Abdallah ya iya irin wannan salon soyayyar mai kashe gaɓɓai ba sai yau)a haka suka gama daga nan kuma ya sunkuceta suka koma daki,
Inno tayi matuƙar mamaki da yadda taga yanayin taufiƙa,ta shigo cikin fara a da walwala,dan haƙiƙa ita kanta tafi jin sakewa da rashin nauyin zuciya a yanzu da ta sauke nauyin damuwarta ta kuma nemi gafarar Bintu,zama tayi gefan inno da take Binta da kallon mamaki,cikin sanyin murya ta gayawa inno abinda ya faru da kuma hirarasu da Bintu ta ɗora da cewa inno dan Allah kema ina neman yafiyarki san nan zanje na gayawa Alhaji Baba da kaina cewa na haƙura da auren Ya Abdallah a ɗaura da Sayyid ɗin!'inno ɗaga hannunta sama tayi tace"Allah na gode maka da wannan hasken Alkhairin da yake ta shigowa zuriyar mu,duk a sanadin su Bintu wan Nan shi ake kira da ɗan Hakin da ka raina, Allah yayi muku albarka ya baku zuri'a mai albarka ya kuma ciga ba da nuna mana hanya mai kyau, ya bamu ikon binsa cikin tafarkin musulunci,Amin Taufiƙa ta amsa zuciyarta fes babu sauran damuwa.
A cikin wannan kwanakin ne ake ta shirye shiryen auren jikokin Alhaji Baba,yayin da su Bintu suna can suna shan soyayya duk da dai har lokacin Abdallah bai kuma neman wani abu a gurin ta ba,saboda so da tausayi,ita kuwa sai zuba sangarta da taɓara takeyi, amma fa Abdallah yana da burin maida Bintu makaranta,in Sha Allah,babu abinda yafi burge shi a gurin Bintu sai irin tsananin ibada da miƙa lamura ga Allah duk abinda zatayi sai ta saka Ubangiji a ciki, komai zata aiwatar sai kaji tana addu'a ko tasbihi da ya riga ya zauna abakinta,to dake shima Abdallah ba baya bane sai suka haɗu suke raya rayuwarsu da yawan ibadu ga sadaka da taimako,wan nan duk halinsu ne wanda suka koya daga gurin iyayensu,
Yau ake ɗaura auren su Taufiƙa da su Hauwa'u,abin yayi amarshi sosai,kaf iyalan Alhaji Baba babu wanda babu,a ranar da yamma akayi ƙayatacciyar walima,Amare sunyi kyau har ba a magana, Bintu tamkar ka saceta ka gudu fans din ƙudurar Allah kuwa kamar kiyashi haka suka cika babban holl ɗin ESTATE duk wanda ka kalla bakinta har kunne sunci atamfarsu mai zaiba sai wawar kajin walima suke su maman hamra da su Ummu banat kai harda su saudee iyayen rawar ƙafa,su Maryam cika ga su fati nan duk anci gayu an ƙafe aguri ɗaya ana muzurai,gasu nan dai da yawa mutanen idan nace zan lissafo su abun zai ci lokaci, Allah sarki yayata maman nuur tana wajen su Ummi Laila ana shirin kai Amare da ita,kai abu dai yayi kyau haka taro ya watse lafiya,daga nan kuma su Alhaji Baba suka wuce gidan su Anty Samira a ƙa ɗauro aurenta da Dady jafar,Ni kaina bazata akayi min wannan abu baƙaramin daɗi yayi ba, Abdallah zan iya cewa yafi kowa farinci,ikon Allah ya wuce da haka to mu dai sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya ya kawo ƙasantar dakuna,
Tsit kake jin estate din tayi,kowa yana ɓangaren sa ga kuma ƙaruwar Amare da aka samu duk da cewa suna da tazara sosai tsakanin su da iyayen nasu, haka tsakanin su da juna ma a kwai tazara me yawa,dan haka za kayi tsammanin kowa a guri daban yake,tamkar yadda a kayiwa kowacce amarya itama Bintu haka akayi mata basuyi duba da cewa ita ta daɗe da aureba,zaune take bakin haɗaɗɗan gadonta da yasha shimfiɗu na alfarma kai kace gadon sarautane,sallama yayi tare da shigowa ɗakin fuskarsa tamkar wata ɗan daren goma sha huɗu,kana kallon sa kasan cewa yana cikin farinciki mara misaltuwa,takowa yayi cikin nutsatstsan takunsa mai cike da iko kamar wani saraki,zama yayi a gefan ta tare da dage mayafin lafayar da aka yane dukan fuskarta,cikin taushin muryarsa yace"Alhamdulillah!'kana ya sunkuyo da fuskarshi daidai saitin tata,yana binta da wani narkakken kallo mai cike da shauki,cikin sanyi da lallaɓa ya janyota cikin jikinshi yana sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya,tallafeta yayi gaba ɗaya cikin jikinshi yana bin ko ina na jikinta da sunsuna,shigewa jikinshi ta kuma yi tana matsarshi saboda yanayin da take tsintar kanta aciki aduk lokacin da ya kusanto jikinta,ɗago kanta yayi mata ana bin lumsassun idanunta da eye lashes ya kwanta yayi zara zara,har shensa ya kai saman idanun ya shiga lasa tamkar ya samu alewa,wani irin numfashi taja tamkar wadda zata shiɗe,bata gama da wannan yanayin ba,ta tsinci bakinshi cikin nata,yana yi masa wani irin tsotsa tamkar wanda yake shirin tsinke harshen gaba ɗaya,sai ga Bintu na tallafar ƙeyar Abdallah domin taimakawa bakunansu wajen daɗa kusantar juna,a hankali ya shiga ware lafayar jikinta yanayi yana scuizin ɗin jikinta da tafukan hannunshi,saida ya warwareta gaba ɗaya kana ya buɗe idanunshi da suke lunshe tare da zare bakinshi daga nata,kallon shigarta data ɗimauta shi yake,wata fitinanniyar rigar bacci ce wadda akayi mata ado da bakin less baƙa kuma iya kacinta cinya,abunka da fara sai ga Bintu na walwali cikin rigar,wanda take Abdallah ya kuma rikicewa tsumammiyar ƙaunar ta ce takuma tashi tare da shawa awa da ɗokin kasancewa da ita,yana kwadayin kara zuwa wannan burnin na fadama,yana son ƙara zuwa gurin nan da tunda ya shige shi har yau daɗinsa bai bar cikin ƙwaƙwalwa da gangar jikin shi ba,duk da cewa bai je ko ina ba, bai kuma kai inda ya kamata ace ya kaiba,amma dai a yau yana fatan zuwa ƙoramar Bintu mai wuyar mantawa, cikin kunnenta ya shiga raɗa mata wasu kalamai wadanda suke neman zautar da tunaninta kalaman da bata taɓa tunanin zata jisu daga gwarzon maza irin Abdallah ba,kalaman da bata taba sanin cewa Abdallah zai iya fadawa wata mace su ba,lallai ta taki sa a ta zama mace mai sa a arayuwarta,da abun yayi mata yawa kawai sai ta yi masa wata irin runguma da ita kanta bata san taya tayi hakan ba ji take yi kamar ta maida shi cikin zuciyarta kowa ya huta,tana sonsa tana kishinsa tana kuma mararinsa,