Sashe 70
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajjah ta zubawa Taufiƙa ido A yayin da ta gama ratta ba mata jawabin ta, cikin kuka da wani irin baƙin ciki dake tasowa tun daga ƙarƙashin zuciyar ta,wani ɗan murmushi Hajjah tayi kana tace"yaro dai yarone,to yanzu Ni me kike so nayi miki da kika kwaso uban kaya kika dawo nan,ko so kike na kira shi Abdallah n nace masa gaki ya aure ki? Taufiƙa ta kalli Hajjah da jajayen idanun ta da suka rune saboda kuka,tace"Hajjah dan Allah ku taimakamin wallahi zai iya yadda idan kuka gaya masa saboda kema kin san Yah Abdallah yana da biyayya,tunda itama waccen ƴar matsiyatan bashi ita akayi kuma yakarɓa,nima idan kuka ce masa ya aureni wallahi Hajjah zai yadda, na yadda zan zauna da Bintu Ni dai kawai kusa shi ya aure Ni dan Allah Hajjah!'ta faɗa tana mai saukowa ƙasa ta riƙe ƙafar Hajjah tana wani irin kuka kamar ankashe mata duka dangin ta,kafin Hajjah tayi magana Dady Habib dake shigowa falon yace"Hajjah ya kamata a duba lamarin yarinyar nan kar taje ta shiga wani hali akan abinda zamu iya bata!'shuru Hajja tayi cike da yin dogon nazari akan maganar Dady Habib,can taja numfashi tare da cewa.....
Fatimah y AdamâœðŸ½
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 42```
Kai yanzu Habibu kana ganin wannan shine adalci?sunkuyar da kansa yayi kana cikin ladabi yace"Hajjah gani nayi kamar idan akai hakan shine hankalin ta zai kwanta, tunda kinga itama waccen yarinyar bashi ita akayi ina ga itama Taufiƙan idan aka bashi zai karɓa yayi biyayya!'wata irin harara Hajjah take zuba masa tun kafin ya ida maganar tasa,yana direwa kuwa ta ɗauka cikin faɗa tace"amma kai kam Habibu wallahi baka da kirki, wannan sankan har ina,saboda su bare ne a cikin mu shine zamu ƙuntatawa zuciyar su,wato tunda yayi biyayya a wan can to wan nan ma sai abashi koda ran sa baya so,ita kuma ƴarku a faran ta mata saboda itace ƴar dangi,to ba dani za ayi wannan sakarcin ba,kuje can kai da ita da wanda zai biye mata ku ƙaraci shirman ku amma banda Hajjah a ciki!'ta faɗa tana ƙoƙarin tashi dan barin falon gaba ɗaya,har ta bar falon bata bar mita ba, Taufiƙa kuwa gaban Dady Habib ɗin ta rarrafa tare da sakar masa wani ɗan kukan yaudara koda zai taimaka mata tunda taga alamun haka atare dashi,ɗago kansa yayi,kana ya dafa kanta cikin san kwantar mata da hankali yace"haba Taufi meye abin daga hankali? bayan ga ɗan uwanki nan Alhaji Baba ya baki,meye aibun Sayyid?cikin kukan da ya kuma ƙwace mata tace"Dady wallahi Ni bana son Sayyid a tunda can amatsayin abokai muke dan haka yanzu bazan iya zaman Aure dashi ba,dan Allah ka taimakamin ka sanar da Alhaji Baba halin da nake ciki,saboda kai ka ɗaine yake sauraran maganar ka, kuma kana gani Sayyid ɗin shima ya gudu saboda baya sona!'kul kar na kuma jin wannan maganar A bakin ki, wa yace miki Sayyid guduwa yayi? Sayyid ɓata yayi kuma insha Allah muna saran ganin sa anan kurkusa kar ki ƙara wannan maganar kinji,ki yi haƙuri maza tashi ki tafi ɗakin Hajjah tunda bakya son wajen innon ki kwantar da hankalin ki ki dai na yawan koke koken nan!'tashi tayi tana layi kamar wadda tasha wani abun,ta dai jine kawai amma ba dan ta yadda ba,itafa bata jin zata haƙura da soyayyar Yah Abdallah,saboda sonsa acikin jininta yake,da kallo Dady Habib ya bita cike da tausayi,dan tabbas da yana da damar da zai aura mata Abdallah da ya aura matashi ko dan samun nutsuwar ta
Har ya gama shirin sa bata tashi daga baccin da takeyi na bayan asuba ba,ɗan tsayawa yayi akan ta tare da zuba mata ido,tunanika ne suke ta kai kawo cikin ƙwaƙwalwar sa,a yanzu babu abinda yafi buƙata kamar yagano wanene wannan mutumin sai kuma iyayen Bintu wanda yake ganin kamar duk hanya ɗaya ce zata kai su ga cimma wannan nasarar,kallonta yake tamkar wanda ke son samo amsoshin sa a kan fuskar ta,a hankali ta shiga buɗe idanunta saboda A can cikin jikinta taji kamar ana kallonta,tana buɗe idanun nata kuwa suka shige cikin na Abdallah,da sauri ta ɗauke kanta saboda yadda taji gaɓoɓinta na amsawa da wannan sihirtaccen kallon da Abdallah yake mata,a hankali ta ɗan motsa bakin ta tare da cewa"Barka da safiya!'sai A lokacin ya ɗauke kansa daga tsumamman kallon da yake mata,tare da amsawa asaman laɓɓan sa kamar wanda akayi wa dolen amsawa,tashi tayi tsaye tana ƙoƙarin fita daga ɗakin,cikin miskilar muryar sa yace,"baki sanar dani dawowar Dije ba!'juyowa tayi batare da ta kalli cikin idanun sa ba, tace"to ya akayi kasani!'bai bata amsar tambayar ta ba sai ɗora mata da yayi da cewa,ki tabbatar kin samu keɓewa da ita yau,ina son sanin abinda ke tare da ita duk da cewa ina zatan Alkhairi,ki kula da kanki!'binsa kawai tayi da idanu tasan dai mutumin nan ba zai daina kasheta da mamakin sa ba gara kawai ta haƙura da ɗorawa kanta nazarin al'amarin sa,sauri tayi tabi bayan sa lokacin da taga ya sa kai ya fita daga ɗakin.
Yau kam har lokacin hira ta samu da inno,a cikin hakane ta samu damar gaya mata tana son zuwa gaida su Hajiya Babba da Hajjah,cikin kulawa inno tace"amma dai kin tabbatar kin sanar da mijinki ko?kai inno wai mijina!'cikin dariyar yarintar Bintun inno tace"au da meye idan ba mijinki ba?tura ɗan ƙaramin bakinta tayi tare da zura dogon jijabin ta,bata cewa innon komai ba saboda ita har ga Allah haushi takeji idan inno ta ambaci Oga Abdallah da mijin ta, wannan mai shegen nunƙufurcin,itafa tana ji bata taɓa ganin dariyar sa ba,gara dai suyi su kashe gobarar da take gaban su kafin daga baya su san yadda zasuyi da Auren da aka ƙaƙaba musu basa so daga shi har ita,da wannan tunanin ta nufi ɓangaren Hajjah, wannan karon bata ko kalli sashen da ɗakin yake ba balle taji son zuwa gurin.
A hankali tayi sallama bayan ambata umarnin shiga,Hajjah ce zaune hakimce akan luntsumemiyar kujerar ta sai Dady Mansur da Dady Habib,wanda kallo ɗaya zakayi musu kasan cewa rayukan su duka aɓace yake,jikinta ne yayi sanyi da ganin su A cikin wannan yanayin sai kuma wani irin kallo da ta kasa gane ko na mene,da Dady Mansur yake mata,Hajjah ce tace"a'a Bintu ƙaraso mana kuma kin tsaya sai kace wata baƙuwa!'ta faɗa tana nunawa Bintu gurin zama kusa da ita,takowa tayi A hankali har ta zauna a inda Hajjah take nuna mata sai dai amai makon kan kujerar sai ta zauna ƙasan kujerar,cikin rawar murya ta fara gaida Hajjah kana ta gaida Dady Mansur da Dady Habib,shuru tayi yayin da zuciyar ta tashiga wani irin bugu wanda ta rasa na mene ne, Hajjah ce ta dubi Dady Mansur tace"na dai gaya maka karna kuma ji kaje wajen wani daga cikin ƴan uwan mahaifinka kayi musu rashin ɗa'a kaje kawai ka cigaba da addu'a Allah ya baiyana mana shi a duk inda yake,ku tashi kuje Allah yayi muku albarka ya shirya mana ku baki ɗaya,amsawa sukayi atare wanda hakan yasa Bintu ta ɗago kanta dake sunkuye da wani irin sauri tare da bugun zuciyar da zai iya yi mata illah,sai dai kafin tayi tunanin wani abu har sun fita daga falon,bayan su tabi da wani irin kallo mai cike da razani da tsoro da kuma san gano wani abu da ya ƙulle mata kai.
Zubawa ƙeyar Bintu ido Hajjah tayi cike da tunanika bar katai,ita kuma wannan kome yake damunta? ta faɗa cikin zuciyar ta ganin yadda alokaci ɗaya duk ta firgice kamar wadda taga wani abin tsoro,ɗan dafa kafaɗar Bintun tayi dan san dawo da ita cikin hayyacin ta,a tsorace ta waigo ganin Hajjah ce yasa ta sakin wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciyar da takasa ɓoyeta, Hajjah cikin nuna tsananin damuwa da halin da taga Bintun tashiga tace"Bintu lafiyarki kuwa koda wani abun da yake damunki?ta faɗa cikin nuna kulawar ta,da sauri Bintun ta girgiza kanta tare da cewa,dama gaidaki nazo nayi bari na wuce ɓangaren Hajiya Babba!'ta faɗa tana miƙewa tsaye, Hajjah tace"to da sauri haka ko ɗan hira bazaki tsaya kimin ba tunda ita waccen kasan da tayo muku ƙaura bacci bazai barta tayi hira ba!'batare da Bintu ta nuna san sanin wa take nufi ba,tace"ai zan kuma dawowa!'Hajjah tace"to shike nan ki gaida Innon da kuma mai gidan naki da kika fishi kirki!'kafin Hajjah ta kai ƙarshen zan canta tuni ta nemi Bintu A falon ta rasa,riƙe baki tayi cike da nazarin Abin da Bintu ta gani afalonta ya razana ta haka.
Tafe take dan zuwa sashen da Dije tayi mata kwatance,dan zuwa wajen Dijen,sai dai yanzu kwata kwata ba a nutse take kamar farkon fitowar ta ba,kafinta ta shiga ɓangaren Hajjah kenan,wai me yake faruwa da ita ne?ko dai zarar da ita ake son yi?me yasa yanzu take jin kamar mutumin nan yana kusa da ita?me yasa Muryar sa keyi mata gizo?wai wannan wane irin shu'umi kuma azzamin mutum ne,me yasa yake son cutar da ita ta hanyar son juyar mata da tunani? da wannan rikitaccen tunanin ta ƙarasa sashen da Dije take aiki,tayi sa a kuwa Dijen ce ta buɗe mata ƙofa,baƙaramin farin ciki Dije tayi da ganin Bintu ba,duk da cewa tana cikin ɗan yanayi na tsoron kar wani ya gansu,kama hannun Bintu tayi tana ƙoƙarin kaita cikin ɗakinta, Dady Mansur dake kallon su,cikin ɗaga murya
yace"ina zaki kai min wannan annobar? cikin sauri suka juyo yayin da Bintu jikin ta ya shiga rawa haka kuma hankalin ta ya kuma tashi da jin muryar da taji yanzu ta kuma sake jinta,wai waye wannan ɗin ne?muryar Dije ce ta katse mata dogon tunanin da ta waɗa akan wannan al'amarin dake son zarar mata da tunani,Dije tace"a'a yallaɓai dama inno ce ta aikota zan bata saƙon goro da na kawo mata tsara ba!'bai ce mata komai ba sai wani kallo da yayi musu su duka kana yayi ƙwafa tare da fita daga falon,kallon juna sukayi kafin Dijen ta kuma jan hannun Bintu da sauri suka faɗa ɗakin ta.