Sashe 63
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bintu kuwa ta riga ta gama shirya masa karin sa tsaf tare da shirya masa bisa dinning table,ɗakinsa ta nufa dan kimtsawa duk da basu kwana cikin sa ba, kuma bata da tabbacin dawowar sa, sai da tayi sallama cikin siririyar muryar ta da ta bada wani sauti saboda yanayin da take ciki na damuwa,sai hakan yabawa Abdallah wani salo acikin kunnuwan sa,ganin sa A ɗakin cikin shirinsa na fita yasa ta ɗan yi turus tunda batayi tunanin yana ciki ba,ɗan duƙawa tayi ta gaida shi,amsawa yayi ba tare da ya ɗauke kaifafan idanuwan sa akanta ba,hannunta tashiga murzawa,kanta a sunkuye,gaba ɗaya jinta take atakure cikin wani yanayi saboda kallonsa gareta,batasan meyasa yake mata wannan mayataccen kallon ba,da taga dai abin bana ƙare wa bane sai ta shiga ƙoƙarin yaye bedsheet ɗin dan canzawa,ƙarar zummm zummm da sukaji shiyasa su duka waiwayawa dan kallon inda wayar take,zaro ido tayi dan ganin wayarta ake kira,ita sam ta ma manta anan bar wayar,shi kuma Abdallah da ya dawo daga masallaci ya ɗauka ya shigo da ita ɗakin,sakin bedsheet ɗin tayi tare da matsawa kusa da Abdallahn daya tsurawa wayar ido,a tsorace ta raɓa ta gefan sa tare da riƙo hannun sa dayake ƙoƙarin ɗaukar wayar dashi,ɗan dubanta yayi fuskarsa babu walwala,girgiza masa kai tayi idanunta har sun cika da ƙwallah,bai saurareta ba ya ɗauki wayar tare da danna amsa kuwa,Muryar Anty Nafisa ce ta daki kunnuwan su,wata irin ajiyar zuciya Bintu ta sauke jin ba mutumin jiya bane,miƙa mata yayi,yai mata alamun ta amsa,cikin sanyin jiki, tace"inajinki Anty Nafisa!'Haba Bintu baki san irin tashin hankalin da nashiga ba tsakanin jiya da yau na rashin samun wayar ki, ga kuma babban tashin hankalin dayake tunkarar rayuwata koma nace ya tunkara,yanzu ina son ganin ki ɓangare na da gaggawa,ki hanzari dan Allah Bintu ki taimaka min ina cikin tashin hankali!'cikin saurin baki Bintu tace"Tom yanzu zanzo Anty Nafisa karki damu gani nan zuwa!'yauwa sai kinzo!'tana kashe wayar Bintu ta samu kanta da shigewa jikin Abdallah da yake sauraran maganar su da Anty Nafisa,wani irin numfashi take saukewa mai nuni da cewa tayi matuƙar razana,lumshe idanunsa yayi,lallai wannan mutumin sai sun dage da addu'a akan sa dan ya fahimci yayi matuƙar razana Bintu,to dama duk mutumin dayake mu amala da jinnu ai ya zama abin tsoro ballantana ga yarinya ƙaramar kamar Bintu,ɗago kanta yayi tare da cewa muje na rakaki,jinjina kanta tayi tare da sakin sa,gani tayi ya buɗe wannan jakar ya zaro mata dogon hijabi kalar blue mai tsananin kyau,miƙa mata yayi ta karɓa batare da wani bincike ba dan yanzu ba wannan ne agaban ta ba,sawa tayi sai yayi matuƙar yi mata kyau da haska farar fuskar ta wanda har sai da Abdallah yaso kasa ɗauke idon sa akanta,cikin tura baki da kuma gajiya da yawan kallon sa tace"to muje mana,hararar borin kunya ya sakar mata kana yayi gaba binsa tayi da sauri suka fita daga ɗakin.
Lokacin da suka fito falon,tsayawa tayi tare da ɗan daga murya tace" baza ka karya bane?girgiza kansa kawai yayi yana cigaba da tafiya,cikin gunguni tace"kawai sai asa mutum yayi wahala kuma aƙi ci wannan ai al mubazzarancine,sarai yaji abinda tace"har zai fita sai kuma yaji ba zai iya fita bai karya ba ɗin kamar yadda ta faɗa gaskiya ne idan yayi haka yayi almu bazzaranci juyawa yayi ya nufi dinning table ɗin, zama yayi ya ɗan zuba chips kaɗan kana ya haɗa tea shima kamar na shan jariri, kallon tea din da ya haɗa tayi kana ta ɗan matsa gaban sa tare da ɗaukar ruwan zafin ta ƙara a cikin cup ɗin da ya zuba,ɗan kallon ta yayi ta gefan ido batare da yace"mata komai ba,ɗauka yayi ya ɗan sha kaɗan kana ya tura mata gami da yi mata nuni da ta ɗauka ta sha,tunawa da tayi akwai abinda ke gaban su yasa ta ɗauka ta shanye dan itama yunwa takeji,miƙewa yayi ya wuce gaba tabi bayan sa
Taufiƙa ce zaune ita kaɗai a falon kamar tana jiran wani abu,idanunta yana kan ƙofar falon Abdallah,wanda hakan ne yaba ta damar kallon su yayin da suke fitowa,dukkan su babu wanda ya lura da Taufiƙa shi yasa suna kusan tsakiyar falon Abdallah ya ɗan dakata saboda jurwayen shayin dayagani gefan bakin Bintu,tana ƙarasowa kusa dashi ya dakatar da ita ta hanyar kama kafaɗun ta ya juyo da ita ya zamana tana fuskantar sa,kallon sa takeyi cike da alamun tambaya a kan fuskarta,kafin ta gama tunanin dalilin tsayuwar tasu,taji tattausan yatsan shi saman leɓanta yana goge mata shayin da batasan da zaman sa ba,
Taufiƙa kuwa yadda kasan idanun ta zasu faɗo ƙasa saboda kallon da ta kuresu dashi,zuciyarta kuwa kamar zatayi bindiga ta faso haka takejin ta,
Bata gama fita daga wannan tashin hankalin ba, taga Abdallah ya ɗora bakin sa saman na Bintu wanda yayi hakane saboda ankara da Taufiƙan da yayi da kuma irin kallon tashin hankalin da take musu,sai hakan ya bada wani salo na musamman Bintu kuwa kamar zata shiɗe saboda tsananin firgici da mamakin abinda Abdallah yake yi mata,shi kuwa Abdallah har ya manta manufar da tasashi aikata wannan ɗan yan aiki ga Bintu,shan bakin yake tamkar wanda yasamu alewar minti,wani irin kukan baƙin cikine ya ƙwacewa Taufiƙa wanda shine sanadin dawo da Abdallah cikin haiyacin sa,ɗan tsuka yayi tare da jan hannun Bintu da ta rasa inda zata tsoma kanta saboda kunya da takaicin wannan rashin kunya ta Oga Abdallah,bata iya kallon inda Taufiƙa take ba ta bishi kamar raƙumi da alaka suka fita daga falon,suna fita ya nuna mata hanya dayi mata alamun ta ƙara sa,shi kuma yaja ya tsaya yana son yaga kulewar ta dan tuni ya fahimci yadda tsoron mutumin nan yayi tasiri a zuciyarta,tafiya take A hankali tana waigen sa har dai ta ƙure ta kai hanyar da zata kaita part ɗin Anty Nafisa.
Sai da yaga ɓacewar ta san nan ya nufi wajen motocin sa inda Yahya yake dakon jiran fitowar sa.
Taufiƙa kuwa tashin hankalin da tashiga babu misali kuka take da idanun ta, tana jin fargabar tabbatar maganganun inno wanda gashi tunkan aje ko ina ta fara gani,wai Abdallah datake tunanin ba zai taɓa kallon macen da tafi Bintu ba, amma wai shi ne yakewa Bintu irin wannan sumba mai tada hankalin lafiyayyar mace,tunda haka ta faru tabbas abinda yake faruwa cikin ɗakin yafi haka,macen da ta raina kamar Bintu itace ta samu kiss ɗin miji kamar Abdallah,me yasa inno bata ƙaunar ta?har take mata bakin da yake neman tabbata,wai shin ya zatayi da soyayyar Abdallah ne?anya kuwa ba ƙas ƙantar da kanta zatayi taje tanemi soyayyar sa ba? tunda tabi ko wacce hanya taga babu riba,kawai abinda yafi mata a yanzu shine ta gwada kissa ko zata dace,da wannan shawarar ta goge hawayen ta, tare da komawa ɗakinsu ta ɗauko wayar ta dan ƙara neman sani a kan hanyar ƙwatar saurayi ta hanyar kissa.
Tafe take tana ɗan waige waige, kasancewar safiya ce sosai shi yasa baka jin motsin kowa,sai na kukan tsintsaye,duk da cewa Bintu a tsorace take amma hakan bai hanata ƙarfin halin bi ta wajen ɗakin nan ba,kai tsaye taji tana muradin zuwa wajen koda bata shiga ciki ba ganin ƙofar ma zai iya zama abu mai muhimmanci,tafi-tafi saiga Bintu ta tsallaka inda babu mahaluƙin da yataɓa tsallakawa, wanda koda tsautsayi yasa ka tsallaka tabbas sai wani abu ya sameka,(a cewar su kenan masu gurin)ɗan dakatawa tayi agurin saboda wani abu da taga gilmawar sa kamar mutum,cike da mamaki ta fara ƙoƙarin tunkarar wajen da taga gilmawar,saboda yadda abin ya bata mamaki tunda tasan dai ance babu wanda yake iya zuwa wajen, to in dai hakane kuwa bai kamata taga wata alama ta mutum ba,da sauri tasa hannu ta toshe kunnuwan ta saboda wannan kiɗimammiyar ƙarar da ta taɓa ji a wan can karon wan nan karon ma ita ta kuma sake ji har taso tafi ta wancan karon, yayin da ta dinga ji wajen yana juyawa da ita,haka kuma tana ji tamkar ana son janta zuwa cikin wannan ɗaki ta ƙarfi,ƙara toshe kunnuwan ta tayi tana ciccijewa saboda a yanzu ta tabbatar da janta ake zuwa cikin wannan ɗakin sirrin...
Bintu Allahu Ya kareki daga sharrin masu sharri ya kuma baku ikon bankaÉ—o mana abin da ba ason bankaÉ—uwar sa,
Fatima y AdamâœðŸ½
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 39 ```
Har Yahya ya tada motar tare da fara yi mata wuta,cike da azama Abdallah ya dakatar dashi,cikin sauri ya fito daga cikin motar,haka nan yaji zuciyarsa bata amince masa da tafiyar Bintun ba,tamkar ana ingizashi haka yaji yana son ganin ta,dan jikin sa ya bashi ba lafiya ba tun daga yadda zuciyar sa take wani irin bugu da sauri da sauri,dafe saitin zuciyar sa yayi lokacin da yaji tayi wani irin bugawa da ƙarfi,ƙara ɗaga ƙafafun sa yayi dan san isah inda zuciyar sa ke kai shi,
Wata gigitacciyar ƙara Bintu ta saka lokacin da taganta gab da ƙofar ɗakin,wanda ƙarar da tayi tamkar acikin kunnen Abdallah ne,da wani irin sauri mai haɗe da gudu ya nufi inda yake jin sautin ihun na Bintu,lokacin da ya hango Bintu cikin wannan halin baƙaramin tashin hankali ya shiga ba, ƙoƙarin tsallakawa yake yi amma hakan ya gagara,(karku manta fa Bintu ce kawai take da damar shiga gefan ɗakin nan saboda fuwacewa ta Ubangiji da kuma taimakon Baffa Jauro).