Sashe 60
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zama tayi tare da ɗaga hannuwan ta sama tana mai addu'a tunda ga ƙasan zuciyarta har zuwa kan bakinta,ya Allah ka zama gatanmu kajiɓanci lamuranmu Ni da dukkanin musulmi masu tsoronka,ya Allah ka sakawa waɗanda aka aka zalunta ya Allah ka war ware mana ƙullin da aka ƙulla mai wuyar kwancewa,ya Allah ka tsare mu daga sharrin kiɗan shaiɗan ka kiyaye zuciyoyin mu daga faɗa wa halaka katsare mu da aikata saɓonka, Allah kakiyaye mu da aikin na dama kasa kar mu tozarta a duniya da lahira, Amin Ya Allah.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 37 ```
Wayar tace tashiga neman ɗauki, cikin nutsuwa ta shafa addu'o'in ta, tare da janyo wayar ta kara a kunnen ta,cikin girmamawa tace"Alhaji wallahi wani ɗan saɓani aka samu amma yanzu zan kuma gwada wayar tata idan batayi ba sai na koma ɓangaren nata!'ta ɗaya ɓangaren Alhaji Baba yace"kizo ai na samu wayar tata tuni ke muke jira, Hajiya Babba tace"to madalla gani nan tafe!'bayan ta ajiye wayar tare da tafiya dan amsa kiran megidan nasu, suji abinda yake faruwa da sammakon nan kuma.
Tana dosar coridon da zai sada ta da falon Alhaji Baban ta fara jiyo tashin Muryar Dady Mansur, a ranta tace"sababbe kaci kanka wato ma shine sanadin tarasu da wannan safiyar,to Allah Ubangiji ya shirya,ta faɗa tare da yin sallama cikin falon,amsawa sukayi gaba ɗaya kana sukayi gaisuwa a tsakanin su,cikin nuna halin dayake ciki na tashin hankali ya gaida Hajiya Babba, Dady Habib ma dake zaune ƙasan ƙafar Alhaji Baba yana ja masa yatsu ya gaida ta cikin tsananin biyayya, Hajiya Babba ta amsa fuskarta cike da ƙauna da kuma alfahari da yaron nasu wanda ya ya ƙwace girman Mansur tunda ya zubda girman to su sun ɗauka sun bawa Habib.
"Ɗan gyaran murya Alhaji Baba yayi tare da cewa kai Mansur tun yaushe ne baka ga shi Sayyid ɗin ba?cikin ƙara san zafafa abun yace" Nabil yace"sam baiga ya shigo jiya ba, ma ana dai bai kwana gida ba,da farko ma yayi tunanin yana sashena sai da aka idar da Sallah kana nake ce masa ina Sayyid,to shine yake sanar dani,gashi tun alokacin nasa aduban duk inda akasan yana zuwa amma babu wani labari!'ya ƙara sa maganar cikin yanayin fargabar abinda zai faru da ɗan nasa, Alhaji Baba yayi gyaran murya kana yace"to Ni dai aganina Sayyid ba yaro bane da za ace ya ɓata,sai dai wani abu daban dan haka Ni aganina mu jira zuwa jimawa idan bai dawo ba sai mu ɗauki mataki!'inno tace"gaskiya Alhaji Ni dai ashawarata gara ayi saurin fara neman yaron nan tun da kasan duniyar yanzu ta zama abin tsoro,ba zai yiwu ace har sai wani lokaci mu fara ne man sa ba,kuma dai kaga yaran nan duk runtsi sai sun kwana a gida,barantana muce sun saba yin irin haka!'tana ajiye maganar ta Hajiya Babba,ta ɗauka ita ma dai shawarar da ta bayar ke nan kamar yadda inno tace" ita kuwa Hajjah tayi musu kara amatsayin ta na kakar Sayyid,dan haka batace komai ba baya ga fatan Allah ya baiyana shi da gaggawa,Dady Habib yace"yanzu yaya katashi muje mu bayar da cikiyar sa gida jen ƴan uwa da abokan nan sa,idan ba a ganshi ba zuwa gobe sai mu sanarwa ƴan sanda,tun da yanzu bamu da tabbacin ɓata yayi kaga bai kamata muyi saurin sanar da ƴan sanda ba!'Alhaji Baba yace"to madalla hakan yayi, Allah Ubangiji ya kareshi aduk inda yake ya dawo mana dashi cikin ƙoshin Lafiya,Amin suka amsa gaba ɗayan su,daga nan Dady Mansur da Dady Habib suka fita dan fara aiwatar da abin da ya dace,Hajjah da Inno ma tashi sukayi suka koma sashen su kasan cewar yau turakar ta uwar gida ce Hajiya Safiya buzuwar Agadez.
Me sace Sayyid yake nufi?anya kuwa ba wani abune da ya dan ganci bin sahun ta ba? tabbas dole ne ta dawo da Dije cikin gidan nan tunda tasan itama Dijen bata da wani garanti akan ta bata san ko ita wacece ba,amma Dijen ce lamarin ta akwai sa shakku wanda hakan ne yasa tasa akayi nesa da ita daga estate ɗin gaba ɗaya, dan taga kamar tana shirin munafun tar ta ita da shegiyar yariyar nan,ga shi kuma rashin Dijen na son ya dameta,dan rashin ta shi yake sawa duk wasu abubuwa suke faruwa batare da sanin ta ba,gashi Sayyid ɗin ma ga dukkan alamu dai yafaɗa tarko, yanzu ya za ayi tasan waɗan da suka kama Sayyid idan ƙama shin akayi?tabbas a kwai ƙura,wata zuciyar tace da ita toke meye na far gaba bayan kin tabbatar da cewa Sayyid bazai iya bada baya nai akanki ba,tunda bai sanki ba,nunfashi ta ja mai tafe da ajiyar zuciya tana mai ƙara gaskata abin da zuciyar ta ta sanar da ita akan lallai su Alhaji Nasir su suka ɗauke Sayyid saboda suna tunanin yana aiki tare da wani akan buƙatar su,wanda basu san waye ba,shine suke son su sani ta hanyar ƙwamushe shi Sayyid ɗin,kuma suna tunanin zasu samu hanyar sanin inda Abubakar yake,wani ɗan murmushi tayi wanda alamun tane kawai ya nuna hakan,fulawar dake gaban ta Koriya shar ta cikin lambun da take ciki tasa hannu ta ɗan tsinka,tare da cewa Alhaji Hashir Alhaji Nasir Alhaji Kabir da sauran tawagar ku tabbas kunyi ta banza, domin ina da tabbacin babu abinda zaku iya ganowa game dani,saboda ban bar wata sheda da zata sa mai nemana ya sameni ba,kwayi ku gama ku dawo musu da ɗan su,Ni kam na riga nayi nisan da babu mai kamoni,(hmmm Allah mai kowa mai komai shi yake da ikon kamaki koma zai kamaki cikin ƙudurar sa,tafi-tafi dai ita dama akewa ai ƙarshen ta ƙasane)cikin ƙwarin gwiwa ta bar lanbun.
Duk tabi ta birkita É—akin duk wani waje da tasan yana ajiye muhimman abubuwan sa saida ta duba,É—an dakatawa tayi tana mai cizan yatsan ta tare da bin ko ina na cikin tangameman É—akin da ido,cikin sauri ta nufi wata Æ´ar jaka wadda baza ta wuce girman jakar mata ta rataya wa ba,buÉ—e jakar tayi tare da zazzage ta gaba É—aya tana mai fatan samun abinda take nema,takardun da suka faÉ—o ta shiga dubawa da É—aÉ—É—aya yayin da kuma bugun zuciyarta ke kuma tsananta,saboda tsananin tashin hankali da fargabar abinda ta gani rubuce cikin takaddun,goge idan ta ta kumayi saboda ta kuma tabbatar wa ba gizo yake mata ba,tabbas wannan sa hannu ne na mijinta akan ya mallaka wa É—iyar sa gidan mansa dake cikin garin na Abuja,ta kuma buÉ—e wata itama ya sa hannu akan ya mallaka wa É—iyar sa wani babban mension da bai daÉ—e da gama gina shi ba,sai ta ukun ita kuma kamfanin sa na auduga ya bata,hannu ta É—ora aka tare da zunduma wani ihu,da sauri ta rufe bakin tana mai fashewa da wani irin kuka mai tada hankali.
"Wayyo rayuwa me yasa zakiyi min haka? Ni Nafisa naga ta kaina ashe shukar dusa nakeyi ban sani ba,me yasa banyi irin tunanin da Bintu tayi ba tun kafin zuwan wannan rana,kuka takeyi sosai tana san batu tamkar wata zararriya,anya zata yadda duk wannan wahalar da tayi ta tashi abanza,waifa wannan ke nan data gani,bata san iya adadin waÉ—an da yasaka hannun ba,dole tayi wani abu tun kafin ta zama asararriya dan kuwa ta rasa wannan uwar dukiya ta Umar ba iya asara tayiba ita kanta ta zama asararriyar,kwashe su tayi gaba É—aya tana mai aiyanawa dole ta sami Bintu dan ita ka É—aice zata kawo mata mafita akan wannan al amari.
Ita ba sa hannun ne a yanzu ya dame taba,ƴar dayake iƙirarin ya bawa itace tafi damunta,to wai shin wace ƴar yake nufi?a i'na yasame ta a ina ya gano ta?idan ya gano ta yanzu tana ina?to ya akayi hakan ta farune dama matacce Yana dawowa?ko dai Umar tunani ya fara zautar shi?idan kuwa hakane ya zama dole agareta ta binciki Umar dan sanin inda ya dosa da kuma abinda yake nufi da mallaka wa gaibu dukiyar da ta jima tana farauta.
Hello Samira!'daga ɗaya ɓangaren Samira tace"ya naji muryarka kamar ba dai-dai ba?Samira akwai matsala amma ki ɗan yi haƙuri zan kiraki,yanzu ina kan hanyata ta zuwa guest house zamuyi miting, ko da yake anjima mu haɗu kawai sai muyi magana!'daga haka ya kashe wayar dai dai kuma lokacin ya ƙara so gidan su da suke haɗuwa dan zaman tattauna matsalar su.
Samira ta dubi oga Abdallah tayi masa alamun ko ya fahimci wani abu? dake wayar a amsa kuwa ta sakata,Safwan ne yace"kema dai kin san bazai wuce tashin hankalin an riga su ƙwamushe Sayyid ba,kuma zasuyi tunanin waɗanda suke tare dashi ne suka ɓoyeshi dan kar su sami damar samun bayanai daga Sayyid ɗin,samuyal yace"hakane sai dai ina ga tunanin su zai iya canjawa!'Abdallah ne cikin yanayin ƙasaitar sa ya ɗan motsa bakinsa kana yace"basu da wannan damar tunda muna tare dasu ta ko ina ko kun manta lawan ayanzu shine drivern Alhaji Nasir?mun mamayesu ta ko ina ga kuma Samira dan haka duk ta inda zasu ɓulla mu zasu gani!'Samira ta ɗora da cewa,kuma bana tunanin zasu iya canja hanyar da suke kai a yanzu domin mun riga munyi musu shigar sauri,mune muke juya tunanin su,koda sunyi tunanin hakan to tabbas Nice zan kuma ɗora su a hanya ta yadda zamu samu dukkanin abinda muke so!'Abdallah yace"mu saka ido akan motsin kowa domin ayanzu munzo gaɓar da zamu fara han kalta da motsin kowa ta hakane kuma zamu damar ɗora zargin mu akan duk wanda muka ga wata alama atare dashi,sace"Sayyid zaiyi matuƙar ɗagawa wanda suke sakashi aiki, kuma tanan zamuyi ƙoƙarin gano ko waye domin bibiyar sa.
Hmmm Abdallah da sauran rina A kaba fa, gano wannan shu'umai sai andage da addu'a dan sun san takan ɓadda kama cikin mutanen kirki, sai su saka ɓaƙar fuskar su cikin fararen fuskoki yadda fararen fuskokin zasu haska su a kasa gane ɓakin fuskar tasu to Allah dai ya baku nasara Abdubint.