← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 120

Sashe 79

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A ranar nan ne dai kuma Abdallah yayiwa gidan sirri tsinke wanda tunda aka kai masa Sayyid aka ajiye bai waiwayen shi ba sai yau ɗin,zama yayi agabansa bayan Faisal ya saka masa kujera,kallon Sayyid ɗin yake wanda duk ya fita daga haiyacin sa duk da cewa ba dukan sa ake ba, kuma ba A hana shi ci da sha ba,kawai dai babu maganar wanka sallah dai ko ba yayi dole yayi ta,sai dai babu sakewa kuma ɗakin da aka saka shi aciki babu haske ko kaɗan,waɗan nan abubuwan sune suka sauya Sayyid tamkar ba Sayyid ɗan gayu da wanka ba,zuba masa ido yayi bayan yasa an haska masa wajen da wada taccen haske, Sayyid ɗin shima kallon sa yake cike da mamakin dama shine yasa aka kawo shi gurin nan,ɗan ɗage girar sa yayi kamar yadda ya zame masa jiki,kana yace"kayi mamaki ko? Sayyid yace"me nayi maka kuma da ka rabani da jin daɗi na?sai da Abdallah ya shaƙi ƙamshi,na ɗan wasu sakanni,kana yace"tambayar ka zanyi me by kasamu amsar taka tambayar acikin tambayar da zanyi maka, Sayyid bana so kayi min gaddama,saboda aikina na gaggawa ne,idan kuma har kana son fita daga gurin nan kaje kaci gaba da shaƙar iskar duniya kusa da mahaifin ka to ka gaya min gaskiya karkayi min karya!'kawar da kai Sayyid yayi tare da cewa me kake so ka tambaye ni?in dai na sani zan baka amsa!'ɗan tafa hannu Abdallah yayi tare da cewa yauwa kasamawa kanka lafiya,kana yace"waye yasaka shiga rayuwar Bint?kallon sa yayi da alamar bai gane Bint ɗin da yake nufi ba,gane hakan ne yasa Abdallah cewa Bintu my wife u understand,wani kafurin murmushi Sayyid yayi kana yace"au cewa zakayi bagidajiyar ƴar aikin inn...kafin ya kai ga ƙarasa abin da yake son faɗa Abdallah ya ɗebe shi da wasu mahaukacin marika hagu da dama wanda Sai da duniyar ta tsayawa Sayyid gaba ɗaya, lokaci ɗaya hancinsa ya fara zubda jini,cikin kakkausar murya Abdallah yace"tare da nuna shi da yatsa,kar ka sake ka bari wannan ruɓaɓɓen bakin naka ya kuma furta ƙazaman kalamai akan kyakykyawa mai kyakykyawar aniya kamilalliya mai kamilalliyar zuciyar matata,bana son raini ka mutunta Bintu tamkar yadda zaka mutunta iyayenka,koma fiye da haka,domin na tabbata tafisu kyan zuciya da mutuncin da za a mutunta ta,amsa kawai nake buƙata a gurin ka ba wasu ban zayen kalaman ka ba,ina sauraren ka,kabani amsar abinda na tambaye ka,saboda ina da abinyi!'ya faɗa yana duba tsadadden agogon dake ɗaure A tsintsiyar hannun sa,cikin wahala da nadamar shiga hurumin Abdallah da yayi Sayyid yace"nima ban san ta ba,a flazer muka haɗu da ita ta bani kwangilar sawa Bintu ido da kawo mata rahotanni akanta,amma wallahi ban san ta ba!'kamar ya baka santa ba?baka ga fuskar ta bane ko kuma kaga fuskarta sanin tane bakayi ba?girgiza kai Sayyid yayi cikin fitar da wahalallan numfashi yace"niƙabi ne a fuskarta, da ɓaƙar doguwar riga ban gane ko mai atare da ita ba,ban san komai A kan ta ba!'to meye manufarka ta karɓar tayinta? Abdallah ya tambaye shi cike da takaicin wawancin sa,nima saboda ina da manufa akan Bintun shi yasa na karɓa!'meye manufarka akanta? Abdallah ya kuma jefa masa tambaya,sunkuyar da kansa Sayyid yayi kana cikin rawar murya yace"sonta nake taƙi bani dama saboda tana da matukar kamun kai da nutsuwa,hakan ne yasa ko fuskar da zan yi mata wasan banza ban samu ba shi yasa Ni kuma nake jin haushin ta,kuma shine dalilin da yasa nayi saurin karɓar tayin matar saboda nima na ida manufata akanta,kamar dai ranar da ka ƙwace ta a hannuna!'ya ƙara sa faɗar maganar cikin fargaba,ji yake kamar Abdallah zai iya maimaita masa irin dukan da yayi masa ranar, wani ɗan huci Abdallah ya furzar batare da ya kuma cewa komai ba ya miƙe daga kan kujerar yana ƙoƙarin barin ɗakin,cikin saurin baki Sayyid yace"dan Allah tunda na gaya maka abinda kake so ka fitar dani daga nan gun!'Abdallah yace"da sauran lokaci daga haka ya ficewar sa ba tare da ya saurari surutan da Sayyid ɗin keyi ba.

Tunda ya fita Bintu tana ɗakinta bata leƙa ko ina ba saboda bata jin fita ko ina ga kuma addu'oin da malam ya bata su ta yini tana yi,ko inno tunda suka haɗu da safe bata kuma ganinta ba,sai dai innon tana leƙawa ɗakin Bintu dan tabbatar da lafiyar ta,sai bayan sallar azhar ne ta fito falon dan samun abinda zata sakawa cikin ta,tana fitowa taci karo da bayan matar da take shirin shiga part ɗin Alhaji Baba,ta cikin ƙofar dake falon inno,zubawa bayan matar ido tayi zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri wacece wannan da ta shiga ɓangaren Alhaji Baba?wata zuciyar tace mata wacece take da ikon shiga idan ba inno ba,dafe ƙirjinta dake dukan tara-tara tayi,cikin sauri ta nufi ɗakin inno dan ganin ko tana cikin ɗakinta,sai dai abinda ya kuma tada hankalin Bintu sam bata ga inno a cikin ɗakin ta ba,hatta da toilet sai da ta duba amma bata ganta ba,kanta ta dafe,cikin tsinkewar zuciya tace"nashiga uku wacece wannan me irin takun matar nan da yanayin bayan ta, tabbas daga bayan matar nan ƙirar waccen shu'umar matar ta gani,to me hakan yake nufi?ji tayi kamar tabi matar sashen Alhaji Baba, Allah na roƙeka kar ka tabbatar min da abinda idanuwa na suke gani, Allah kar kasa zargi na ya zama gaskiya,haba inno anya kuwa zata iya aikata haka ta faɗa cikin yanayin ?tana son shiga falon Alhaji Baba Amma tana tsoron kar tayi mugun gani,wayar tace, ta fara haske alamar saƙo ya shigo, buɗe saƙon tayi tare da karantawa,Anty Nafisa ce take sanar da ita cewa gata nan zuwa yanzu da muhimmin saƙo gareta,kafin ma ta sauke idanun ta daga kan wayar taji ƙarar rawar falon tana ringin,hakan ne ya nuna mata ƙofar falon a rufe take,cikin jan jiki ta ƙara sa bakin ƙofar tare da cewa,waye?Anty Nafisa tace"nice Bintu buɗe min da sauri nasan inno bata nan saboda sai da na shiga ɓangaren Alhaji Baba na tabbatar tana can!'wani irin kakkauran miyau Bintu ta haɗiye wanda take taji bakinta ya gauraye da wani irin ɗaci, jikinta ya mutu murus, ta tabbata zarginta ne yake son tabbata,ke nan inno ce ta shiga falon Alhaji Baba, innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un,allahumma ajirni filmusi bati wakalifni khairan minha,abinda ta ambata kenan taji sauƙin abinda ya tokare mata a wuya,matsawa tayi Anty Nafisa ta shige ta mayar da ƙofar ta rufe,cikin sanyin jiki tamkar wadda bata da laka haka tabi Anty Nafisa zuwa cikin ɗakinta.

Ganin irin tafiyar da takeyi ne yasa Anty Nafisa janyo hannun ta tare da rufe ƙofar har da saka key,kana ta je ta zuge window ta ƙara gyara labulen window ɗin,dawowa tayi ta kama hannun Bintu dake tsaye tana binta da ido cike da mamakin ta ga kuma wan can Al'amarin da har yanzu bai sake taba,zaunar da ita tayi a can ƙarshen gadon tare da zama a kusa da ita, Bintu dai har yanzu kallo take binta dashi ta kasa ce mata uffan,kama hannun ta Anty Nafisa tayi cikin matuƙar tashin hankali da neman taimakon Bintun tace"Bintu nazo gareki ne dan nasanar dake abinda ban taɓa sanar da kowaba, kuma sirrin rayuwata wanda cigaba da rufuwar sane kaɗai garkuwata,Bintu asirina yana neman tonuwa a gurin wanda bana fatan har duniya ta naɗe yaji sirrin nan,kamar yadda kika gayamin Bintu nayi amfani da shawarar ki kuma na aikata hakan,sai dai a maimakon samun nasara faɗuwa ce ta zomin domin kuwa allura ce take son tono garma,tsaf ta gaya mata yadda sukayi da Abba Umar,ta ƙare da cewa wannan dalilin ne yasa naji dolene nazo na sanar miki abinda baki sani ba dan ki samo min mafita wadda zan samu na tsira da mutuncina da kuma dukiyar Umar!'shuru ta ɗanyi tana haɗiyar miyan da ya daskare a maƙoshin ta,ita kuwa Bintu har yanzu cigaba tayi da saka mata ido,yayin da takewa Allah godiya cikin ranta dan tasan tasirin addu'a ne ya kawo mata ƙarshen Nafisa dan tabbas da zarar ta bankaɗa abinda ta shuka da bakinta to ta gama da ita fallasa ta ba zai zamar mata aiki mai wuya ba, wannan shi ake kira da dana sani wanda kamar shi ta fara hangowa a idanun Nafisa,sai dai lokaci ya ƙure mata,don kuwa a yanzu dana sani ce ta zame mata ƙeya.

Kamar yadda kika sani sunana Nafisa Æ´a É—aya tilo a wajen Hajiya ladidi,shi yasa suke bala in sona,karma Hajiyata taji labari dan tafi Alhaji na ririta Ni da fifita soyayyar ta akaina,tun Alhaji na ganin gata ne take min har abin yazo ya fara damun sa,gashi Hajiyata bata jin maganar sa ko É—aya,wan nan dalili ne yasa shi zuciya ya kaini makarantar kwana,
Chapter 79 · 0% Book details