Sashe 97
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daya daga cikin yaran ne yayi saurin kunna wutar, sai dai hakan baiyi rana ba, dan sun rasa Hajjah da Abubakar ko ƙurar motar basu gani ba,hakanne ya kuma hargitsa zuciyar Dady Habib tare da tunzura shi cikin ɓacin rai yace"karku bari kowa ya bar gurin nan!'Dady Mansur yace"yanzu Habibu akan abin duniya zaka kashe ƴan uwanka?kuma meye dalilin ka na saka fuskata amatsayin mugu?wani kallon baka da wayo yayi wa Mansur kana yace"an gaya maka Ni mara wayo ne irinka?zagaye shi ya shiga yi kana ya cigaba da cewa Mansur baka san yadda kayimin amfani arayuwata ba, na samu damar fakewa A bayanka Ina aikata mugun nufina,duk da nasan kasan komai akan abinda nake aikatawa,hakan yasa da yawan mutane suke zarginka suna maka wani kallo,dalilina nasaka fuskar ka kuwa shine ko da zan kashe Abdallah da ubansa da kuma wannan uwar tona tonan matar sa,zasu tafi ne da sanin kaine ka kashe su bazan mozanta azukatan su ba ko acan ƙiyama zasu bada shaida akaina,kai kuma kisan su ya rataya akanka!'tir wallahi tur da wannan jahilin tunanin naka,ilmin ka bai AMFANA maka da komai ba indai har ƙwaƙwalwal ka zata zana maka yiwa Allah wayo,shin karatun da akai maka bai shiga kanka bane kokuwa idan Alhaji Baba ya turaka makaranta laɓe kake yi?gaskiya na tabbatar da cewa kai ba karamin sunduƙi bane mai karkataccen tunani!'tau kakeji ya ɗauke fuskarta da wani lafiyayyan mari,zabura Abdallah yayi wani ya rikoshi amma dake zuciyar maza ta ɓaci antaɓa rabin rayuwar sa,da hannu ɗaya ya kama hannun mutumin da ya riƙe shi jikake ɓass ya karya shi, cikin sauri ya ƙaraso inda su Bintu suke da mutumin da ya saita maƙoshinta da wuƙa,cikin azababban fushi yace"ba gaskiya ta faɗa ba da zaka mareta, Dady Habib da yake fitar da wani irin huci na tsananin ɓacin rai yace"idan yasake ya ƙaraso inda take na baka dama ka farka maƙogwaranta!'yake fadawa wanda yake rike da Bintu.
Cak Abdallah ya tsaya jin an riko hannun sa ta baya, muryar Dady Mansur ce ta shiga kunnuwan sa yana cewa karkaje Abdallah kana nan tsaye Allah zaiyi mana maganin sa idan yafi ƙarfin mu ai baifi ƙarfin wanda yayi shiba!'a hankali Abdallah ya koma ya jingina da bango mafi kusa dashi,idanun sa akan Bintu da take ta kallon sa gani yake kamar kallon tuhuma take masa na Kasancewar ya kasa yin komai na taimakonta,shi ne yasa duk yaji zuciyar sa ta kasa nutsuwa,da barin ta a hannun wannan ƙasurgumin dan ta adda,ga yadda yake jin zuciyar sa na masa suya saboda kusan cin Bintu da wannan ƙaton,
A hankali Dady Habib yasa hannun sa ya ɗaye fuskar da yasaka, yana cewa babu amfanin zama da wannan a yanzu tunda kun gane shirin,sai kuwa ga fuskarsa ta zahiri ta bayyana,babu wanda yayi mamakin haka a cikin su sai Bintu tunda ita bata taɓa sanin anayin fuskar wani asakaba,cikin ƙosawa Abdallah yake ɗan duban agogon hannun sa wanda yake traking ɗin in da mutum yake,lumshe idanun sa yayi wanda sai buɗe su yayi yaga mutane zagaye dasu an dasawa kowannen su bindiga,wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke,Muryar wani jami'in tsaro ne ya karaɗe wajen da cewa kar wanda ya motsa duk wanda ya motsa kuwa saina fasa kansa da bindiga! cikin mamaki Dady jafar yace"to me yakawo ku nan?ina tunanin gurin da ake aikata laifuka irin ku suke zuwa?to nan kuma naga tattaunawa ce tsakanin zuri'a ɗaya Dady jafar ya faɗa cikin nuna pretending!'Safwan da ya ɗorawa Bintu bindiga yace"babu ruwan mu da abinda kuke tattaunawa binciken mune ya nuna mana da akwai matsala babba a ta ɓangaren nan, dan haka gaba dayan ku abin tuhuma ne!'ya faɗa yana tafiya da Bintu wajen da Abdallah yake tsare da bindiga,yayin da Dady Mansur da Alhaji Rufa'i da basu san shirin su Abdallah ba hankalin su duk ya tashi,haka kawai Habib zai shafa musu jakar tsaba,cikin tsari da sanin makamar aiki suka dinga fita da yaran Dady Habib,sai da aka fita dasu gaba ɗaya sai shi kaɗai yayi ragowa, Abdallah yasa hannu ya ture hannun wanda ya ɗora masa kan bindiga kana yashiga takawa A hankali tamkar wani Basarake da yake kan ganiyar mulki,gaban Dady Habib ya ƙaraso tare da zuba duka hannayen sa cikin aljihunan dogon wandon jins dake jikin sa,wani irin kallo ya fara watsa masa wanda Dady Habib yajishi har cikin hanjin cikin sa,ganin Abdallah agaban sa baƙaramin kyarmar jiki yasa shi ba,tabbas kwarjinin Abdallah abun tsorone ga maƙiya da kuma marasa gaskiya,Dady Habib baisan sanda ya sunkuyar da kansa ƙasa ba,ya kasa haɗa idanu da shi,wani zazzafan huci Abdallah ya furzar kana cikin maganarshi mai fita ɗai ɗai da kuma salon iya sarrafa harshe,yace"Habibu ga ranarka nan, sakamakon ka kuma yana nan tafe,gashi dai ɗan zaki yazo har fadarka kuma zai tafi da kai cikin ƙasƙanci,kuma mutuncin da kake dashi zai zube a idon duniya,ina nan kuma zan aiko maka da ragowar mutanen ka da kuke aikata shirka dan babu wanda zai tsira a cikinku da izinin Allah!'yana gama faɗar haka yayi musu alama da su tafi dashi,hankaɗa ƙeyarsa Safwan yayi suka fita dashi cikin ƙasƙancin da yake gudu,bakin sa dai bai mutuma alwashi yake ci iri da kala akan sai ya ga bayan zuri'a Hajiya Babba gaba ɗayan ta.
Da wani irin gudu haɗe da kuka-kuka dariya dariya Bintu tazo ta waɗa jikin sa,ba su Dady jafar ba hatta Ni da nake sakaɗe abayan kofa sai da naji ajiyar zuciyoyin da suka sauke atare kamar an irga musu,riƙeta ya kuma yi ajikinsa yana shafa gashin kanta da duk ya watse a gadon bayanta,Dady jafar ne ya dubi Dady Mansur tare da cewa Mansur afuwa fa, saɓanin fahimta ne!'murmushi Dady Mansur yayi kana ya kama hannun Dady jafar yana cewa babu komai baka da laifi kai mutumin kirki ne, da duk mutane zasuyi koyi da halayenka da tabbas ansamu ƙaruwar jin dadi da zaman lafiya!'fita sukayi suna ƙara maida maganar.
A hankali ya kamata suka fara takawa yanayi yana duba lafiyar jikinta duk da ta tabbatar masa da cewa babu abinda ya same ta ko sukayi mata sai marikan da tasha,motar da su Abdallah suka zo da ita shine ya shiga shida bintu sai Safwan da zai ruƙasu,su kuma su Dady Mansur suka shiga wadda suka zo shida Alhaji Rufa'i da Dady jafar,cikin nutsuwa suka jero motocin suka fito daga wan nan mugun wajen.
A hankali ta matsa jikin sa tare da saƙala hannunta ta bayansa,ta kwantar da kanta A ƙirjinsa,ji take kamar wadda ta shekara ba tare da shi ba,ɗan tura ta yayi yana cewa matsa tsamin datti kikeyi!'a zubure ta ɗaga kanta tana kallon sa,sai kuma ta shiga ƙoƙarin ƙwace wa daga gareshi,riƙe ta yayi yana sakin wani sassanyan murmushi wanda yake fitowa tunda ƙasan zuciyar sa,da ta kasa ƙwacewa sai ta ɗago kanta dan yi masa magana,,,amma ina hakan ba ta samu ba sakamakon jin ya haɗe bakinsa da nata,a hankali cikin wani irin salo na ƙwarewar da bai san a inda ya sameta ba,yake sarrafa harshenta acikin bakinshi,tun tana son ƙwacewa har ta haƙura ta bada kai bori ya hau,sai da ya hango fuskar Safwan ta cikin miro kana ya ankarar da shi abinda yake gaban yaran sa,zare bakin sa yayi daga nata yana binta da wani kasalallan kallo,rufe fuskarta tayi akirjinsa tana tura baki,cikin gunguni tace"me yasa to kayi wannan bayan wari nakeyi?bai amsa mata ba sai kallon da yake ci gaba da yi mata,ganin haka kawai sai ta canja maganar ta,ta da cewa yanzu da Hajjo ta tafi da Dady ina zata kaishi?karfa ta kai shi ESTATE,bayan bamu shirya komawarsa yanzu ba?dan sunkuyawa yayi ya sumbaci goshinta kana yace"kar ki damu shi yasan yadda zaiyi zaiyi mata bayanin komai!'da wannan maganar ta gamsu duk da dai tanajin wani abu aranta game da tafiyar tasu,cikin sanyin murya ta kuma cewa dashi dan Allah ka kai Ni gidan Hajjo Ina son daukar wayana,kuma,,,,katse ta yayi da cewa shuru Malama da surutun!'tura baki tayi amma dai bata kuma cewa komai ba,