← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 120

Sashe 81

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Abdallah yana fita daga gidan officce suka wuce shida Yahya,bai daɗe da shiga officce ɗin ba sai ga Dady jafar, murmushi Abdallah yayi yace"Dady kafi Ni busy yanzu naga alama, tunda gashi har ina yin kwana biyu ban ganka ba!'wani irin murmushi Dady jafar yayi wanda yake nuni da tsan tsan farin cikin da yake ciki,farin cikin da yake ciki baya rasa nasaba da yadda yaga rayuwar Abdallah ta fara sauyawa kuma ga alamu sun fara nunawa suna samun nasara akan abinda suka saka gaba,cikin murmushin da yakasa gushewa akan kamilalliyar fuskar sa,yace"to ai naga ƴata Bintu ta fansheni tana kula min dakai yadda ya kamata,godiya mara adadi da yarinyar kirki!'ga mamakin sa sai yaga wani ɗan matashin murmushi ya baiyana akan fuskar Abdallah,a hankali ya lumshe idanun sa tare da jinginar da kansa a bayan kujerar,haka nan ya dinga jin maganar Sayyid na dawo masa daki daki,(taƙi bani dama saboda tana da matukar kamun kai da nutsuwa hakan ne yasa ko fuskar da zan yi mata wasan banza ban samu ba)kalaman da suka burgeshi sukayi masa daɗin sauraro ke nan daga bakin Sayyid, Dady jafar ne ya katse masa tunanin sa da cewa,to Malam Abdallah ina sauraron ka kayi min bayanin nasarar da muka samu tare da cigaban da aka kuma samu,ka kuma bani labarin da kace zai matuƙar bani mamaki!'ya ƙarasa maganar cikin ƙara dai daita zaman sa tare da taro nutsuwar sa kan Abdallah,

"Cikin nutsuwa Abdallah ya gaya masa ko wacece bintu,cike da matsanancin mamaki haɗe da farin ciki,Dady ya taso ya rungume Abdallah tare da cewa,ikon Allah kaga ƘUDURAR ALLAH ko Abdallah, wato duk abinda Allah yaso tabbas sai ya faru, wannan abin akwai al ajabi amma ikon Allah ya wuce ga haka,!'Dady ya daɗe yana jin jina wannan ƙudura ta ubangi,yayin da soyayyar musulunci ta kuma kafuwa cikin ransa da zuciyar sa,ya kuma gasgata Allah da Manzon sa,ya kuma godewa Allah da ya kawo masa Abdallah cikin rayuwar sa da har ya zama silar zamowar sa cikin musulunci,hawaye ne ya shiga zubo masa saboda tsabar imani da tsoran Allah yace"Alhamdulillah alakulli halin, Allah na gode maka da wannan baiwa da rahama da kayi min Allah kashirya waɗanda suka ɓata, Allah ka ƙarawa Annabi daraja, Allah ka tsare zuciyoyin mu daga ruɗin duniya da ƙyaleƙyalenta ka kare mu daga faɗawa cin haram ka karemu daga cutar ƴan uwan mu,ka tsare idanuwan mu daga kallon abun da ba namu ba, Allah ya Ubangiji ka tonawa azzalumai asiri kasa suji kunya a duniya ka kuma sa su gane gaskiya ka shirya su idan masu shiryuwa ne!'amin Abdallah ya faɗa nima nace Amin Ya Allah,daga nan suka tattauna sauran maganganun da ya kamata Dady jafar ya sani,daga nan suka gangaro kan maganar Abigirl inda suka tsaida magana akan cewa zai sa aje ataho da ita,yayi wa ma aikacin su na can wanda yake kula da shige da ficen Abigirl waya ya sanar dashi zai sa azo ataho da ita,daga nan suka fara jiran zuwan sakamakon Samira.

Kamma lallan guri ne me cike da nutsuwa, sam babu yawaitar jama a agurin saboda gurine na manyan mutane waɗan da suke buƙatar sirri dan hakane ba kowa ake bari ya shiga ba sai isu-isu manyan,Samira da Alhaji Sama'ila suna daga cikin mutanen dake zaune cikin gurin a kuma keɓantaccen guri,ga yanayin damuna da muke ciki wanda shine ya kuma ƙawata gurin da ƙamshin ƙasa dana furanni,zaune suke a kan ƙawatattun kujerun da suka zagaye gurin gaban su ɗan tebur ne wanda yake ɗauke da kayan sanyi kala-kala, Alhaji Sama'ila ya dubi Samira wadda ta nutsu ta kasa taɓa komai saboda ƙagauta da tayi taji abinda ta fi buƙatar ji a yanzu, murmushi yayi tare da cewa'haba My dear ki ɗan sha wani abu mana duk kinbi kin sawa kanki takura,ɗan murmushi tayi tare da ɗaukan drink ɗin da ya zuba mata,bata son ya fahimci wani abu atare da ita, shi yasa tayi saurin kawar da ɗokin dake kan fuskarta da yanayin ta,bata kuma ce masa komai akan abinda ya kawo su ba, sai da yagama jan ranta kana ya ɗan gyara zaman sa, tare da cewa,

Samira zan fara da baki labarin asalin dangantakar dake tsakanin mutane huɗu,dan ki fahimci yadda abin yake tun farko, Alhaji Balarabe da Alhaji Nasir da kuma Alhaji Shamsi sai Alhaji Kabiru,asalin su aminai ne waɗan da suka haɗu ayawon fatauci,wato neman kudi,daga baya ne bayan kowa ya samu abinyi sai duk suka watse,amma abin Allah shine A lokaci ɗaya suka kuma haɗuwa da junan su,acikin garin Abuja ke nan,daga nan ne suka ɗora da amintar su wadda har tafi yadda suke a baya, dukkanin su babu wanda bai tara dukiya ba,sai dai amma arziƙin Alhaji Balarabe na daban ne acikin su,lokacin da suka fara ankara cewa Alhaji Balarabe yayi musu zarra,shine lokacin gina ESTATE, estate shine mafarin komai shi ya haddasa komai,tun daga lokacin ya zamana abokan nasa sun fara gane abinda yake zuciyar su na tsananin hassada da ɓakin ciki,abin yayi matuƙar tasiri a zuciyar su,amma basu taɓa nunawa Alhaji Balarabe ko mai ba hasalima nunawa suke sun fishi farin ciki da duk wani ci gaba da zai samu,tun daga lokacin suka fara haɗuwa su biyu suna mitin ɗin yadda zasu dinga cutar Alhaji Balarabe ta wajen kasuwan cin su,to amma dake shi zuciyar sa cike take da aminci da kuma kyautatawa talakawa,sai hakan bai girgiza komai a cikin dukiyar sa ba,duk kuwa da irin yadda mahaifina suke yagar dukiyar Alhaji Baba tamkar babu gobe,sai daga baya suka kuma samun karuwa saboda sun gano manufar su ɗaya da ɗan uwan Alhaji Baba wato Alhaji Hashir,dan haka sai abu ya kuma cin uban na baya ha inci suke masa batare da arziƙin sa na raguwa ba saima karuwa da yake samu Ako da yaushe,mutum ɗaya ne yasan abinda suke aikatawa shine Alhaji shamsi saboda shi babu hannun sa acikin duk wani abu da suke aikatawa Alhaji Baba,A lokacin yaso faɗawa Alhaji Baba abinda ke faruwa sai kuma yayi tunanin idan yayi hakan tabbas zasu iya cutar da shi da kuma Alhaji Baba,tunda ya fahimci cewa sunyi nisa acikin san duniyar su,idanun su ya rufe,tabbas idan yayi ƙoƙarin dakatar dasu ko ya sanar wa da Alhaji Baba zasu iya yin komai A yadda ya fahimcesu,sai kawai ya ƙyalesu tunda har yanzu babu abinda ya ragu ko ya samu tawaye daga dukiyar Alhaji Baba sai ma arziƙin nasa da yake kara haɓaka.

A haka lokaci yaja suna kan wannan ƙadamin har zuwa yanzu da salon tafiyar ya sauya,
Chapter 81 · 0% Book details