Sashe 23
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda suka shigo farfajiyar gidan idanunsa suke kan hanyar ɗakin nan, in dai kuma idanunsa ba gizo sukayi masa ba sai yaga kamar giftawar inuwar mutum ta can bayan ɗakin, har Yahya ya buɗe masa ƙofa bai sani ba saida yahyan yace" sir Bismillah! kana ya zuro dogayan ƙafafuwan sa da suke sunƙe cikin wani arnan takalmi sau ciki sai sheƙi yakeyi,taku yake me cike da zallar ƙasaita kai kayi zatan sarkine, ko mai na Abdallah abin burgewane da ƙayatarwa,dai dai hanyar da zai ɓullah ya shiga ɓangaren inno sai ga Dady ane,(Alhaji mansur)kamar an jefoshi,ɗan kaucewa Abdallah yayi tare da cewa Barka da yamma Dady!' washe baki yayi tare da cewa Abdallah ne?ya naganka yau ka dawo da wuri? Abdallah bai samu damar bashi amsaba sai ga Dady nan ya ƙara so(Alhaji Habib)da murmushi A kan fuskarsa,yace"yana ganku anan ba shiga zakuyi bane?gaba ɗaya suka shiga falon inno bakunansu ɗauke da sallama,
Inno suna zaune ita da Bintu harda ma Hauwa'u,ta amsa tana cewa sannunku kamar duk tare kuke!' Alhaji Habib yace"A'a inno duk Haɗuwar ƙoface yana maganar yana zama,ga mamakin Bintu da inno kai Harma Hauwa'u da tunda ya shigo ta daina gane na kusa da ita,zama yayi shima yana gaida inno da sannu da gida, Abinda suka sanine haka kawai bai cika zaman falon inno ba idan ya shigo ƙarƙarinsa ya gaidata ya wuce part ɗinsa,mamakin bai gama sakin su ba saida yasa tsadaddiyar muryarsa yace" ke ki kaimin wannan falona!' yadda yayi maganar bazaka taɓa fahimtar da wa yake ba ko kuma kayi tsammanin idanunsa abuɗe suke, saboda kansa jingine yake A jikin kujerar yayin da idanunsa suke A lumshe tamkar mai bacci,Hauwa'u ce tayi saurin tashi taƙarasa har inda yake, tasa hannu zata ɗauki jakar laptop ɗin kenan yace" bake nasa ba! cak Hauwa'u ta da kata yayin da wani irin haushi da takaici ya turnuƙeta,haka ta koma mazaunin ta jiki a saluɓe,
Bintu kuwa tun sanda yace da Hauwa'u bake nasa ba, jikinta ya shiga baburashin dan ita kwata kwata bata san abinda zai kusanta ta dashi, dan ita kaɗai tasan irin bugun da zuciyar ta keyi da yadda take rikicewa duk saboda tsoronsa,A hankali ta miƙe kamar an zare mata lakar jikinta,zuwa tayi ta duƙa ta ɗauki jakar yayinda zuciyar ta kamar zata yi tsalle ta faso ƙirjinta,sai da ta raba kanta daga kusa dashi kana taji komai nata ya dawo daidai.
Duk wannan diramar da sukayi hankalin Dady ane yana kansu, yayin da Alhaji Habib suke ɗan tattaunawa da inno,inno ta dawo da hankalin ta kan Abdallah yayin da take ce' masa yaya dai Abdallah naga ka dawo da wuri ince dai lafiya?ɗan motsawa yayi kana yace" inno ai yanzu zan dinga dawowa da wuri saboda na ɗauki hutun Asibiti yanzu ina ɗan wani aikine dan haka wataran ma babu inda zani zama zanyi muyi hirar soyayya!'yana gama faɗa inno ta ɗauka da wata shewa irin ta dattijan da sukaji daɗin wata magana, tace"haba ɗannan kamar bansan halinka ba,kaine zaka zauna nan kayi hira sai dai kaita lum-lumshe idanuwa kana taɓa waya!'murmushi kawai yayi batare da ya kuma tankawaba dan wannan ma da yayi ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba, muryar Dady ane ya tsinkaya yana tambayar sa wane aikine kuma zakayi shi a gida dan fi'ili? Alhaji Habib ya tari numfashinsa da cewa haba yaya bai kamata ba dan yace yana da aiki sai kaji ko wane irine? Afusace ya miƙe ya na nuna shi da yatsa yace" mansur ka dai nayi min katsalandan A cikin lamurana, ban isa na tambaye shi bane ko yaya?kana ƙoƙarin fa kadinga ganin ka zubda min da girma a gaban yara amma babu damuwa!' yayi ƙwafa tare da ficewa daga falon,inno ta dubi Alhaji Habib tace dan Allah Habibu ka daina shiga dabgarsa kasan dai ɗan uwan kane yadda Allah yayi mutum babu yadda za ayi wani yace zai canja shi!'numfasawa yayi kana yace" wallahi inno idan nayi kamar zan dinga ƙyale yaya mansur da halinsa sai naji sam bazan iyaba saboda yana zubarwa da kansa ƙima a idon mutane ba daga nan gida ba har can waje!'tace"to addu'a zamuci gaba dayi masa Allah Ubangiji ya shirya mana shi da dukkan zuri'a baki ɗaya!'da Amin ya amsa kana ya miƙe yace inno bari na shiga wajen Alhaji Baba!'to madalla afito lafiya, yace" Amin gami da fita daga falon.
Yana zaune har suka gama faɗe-faɗensu suka fita bai ɗaga kai bama balle yasan sunayi,kamar jira yake dama su fita shima ya tashi yana cewa inno bari na ɗan huta kafin magriba! Inno tace au duk kun gudu? itama wannan daga aike shine ta sulale ta gudu, ita kuma wannan dama bata da amfani ta nuna Hauwa'u da tayi kamar bata falon saboda takaicin abin da yayi mata da kuma haushi da tsanar Bintu,binsa tayi da wani mayen kallo,yayin da shi kuma ya shiga sarrafa dogayen ƙafafunsa kan tattausan carpet ɗin dake malale bisa kafcecen falon,ba ita ta ɗauke idan ta daga kansa ba har sai da taga shigarsa falonsa.
Ita kuwa Bintu dama tuntuni take neman hanyar guduwa,dan ta ƙagauta ta ji abinda takardar nan ta ƙunsa,tana zuwa kuwa ta zaƙulo takardar ta warwareta gaba ɗaya......
More comment...
More, typing........
Fatima y AdamâœðŸ½
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 18 ```
Ga abinda ke cikin saƙon, Bintu inason ganinki kuma kema nasan kina buƙatata dan haka daga yanzu ki fara shirin yadda zamuyi mu haɗu,dan bazata yiwu A cikin gidan nan ba, dole kisan yadda zakiyi ki fita daga gidan nan, Ni kuma daga yau zan fara tunanin inda zamu haɗu,sai dai matsalar ɗaya ce ke baki san ko ina A cikin garin Abuja ba,shiyasa ban san inda ya kamata na samu wanda bazakiyi wahalar ganewa ba,amma dai ko meye ma kikasance cikin shiri,da kuma lura dan gidan nan haka yake zaki ga kamar babu mai lura dake amma abun ba haka yake ba, koda ƙwarone yashigo ESTATE ɗin ALHAJI BALARABE,to shakka babu Ana biye dashi, sai dai bazaki taɓa gane hakan ba,ina mai ƙara tunatar dake da ki lura sosai.
Bintu tana gama karanta wasiƙar ta koma cikin toilet tayi ploshin ɗinta,kana ta fito ta kwanta saman gadonta gami da rufe idanunta, cikin hasasowa kanta dabarar fita daga gidan batare da ankarar wasu manyan ƙayoyin gidan ba, wayarta dake kan bed side ta ɗan kalla har ta kawar da kanta sai kuma ta tashi da sauri tare da rarimo wayar saboda wata dabara da zowa ƙwaƙwalwarta A lokaci ɗaya,cikin sauri ta shiga latso lambar Hajiya ladidi,batare da jan wani lokaciba ta ɗaga kamar dama jiran kiran takeyi,yaya dai Zahra Ina fatan jin bayani mafi daɗi daga gareki!' cikin zumuɗi tace Hajiya wallahi an samu sai dai kuma akwai ƴar matsala!'Hajiya ladidi tace" ki gayamin, nasan ko wace irin matsalace bazata fi ƙarfina ba!' cikin murmushin samun nasara Bintu tace"Hajiya na samu hanyar haɗuwa da dije, dan ta bani baya nai akan matar da take yiwa aiki, sai dai tace bazamu haɗu acikin gidan nan ba dole sai dai mu fita can wajen gari domin haɗuwa,to kuma tayi min bayanin cewa kar na bari agane akwai wani shiri tare dani shine tun ɗazu tunanin da nakeyi hanyar da zan samu na fita batare da wata matsala ba!'Hajiya ladidi ta sauke wata Ajiyar zuciya tace" Zahra ai wannan ba wata matsala bace baga Nafisa ba ki kwantar da hankalinki zaki fita cikin salama batare da zargi ko bincike ba!' A hankali Bintu ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya,kana tace"to shike nan Hajiya na gode!' Hajiya ladidi,tace" ai nice da godiya!' daga nan suka ajiye wayar, Bintu tayi wani sassanyan murmushi,kana afili tace" Hajiya nice da godiya irin wannan aiki da kike min dole na gode miki.
Zagaye falon yake hannayen sa goye A gadon bayansa, inuwar mutum da ya gani ta wajen ɗakin nan shine abinda yake taɓa zuciyar sa, tabbas yana ganin wannan binciken shine zai bashi wahala a dukkanin sauran binciken da yasa A gaba,to amma dai ba zai taɓa karaya ba,yana da tabbacin samun nasara akan kowane mara gaskiya.
Alhaji Farouk ne zaune A gaban mahaifiyar sa Hajiya Babba,daga dukkanin alamu ma kuka yakeyi,cikin damuwa da alhinin halin da ɗan autanta yake ciki, cikin ƙauna da tausayi irin ta ɗan da ake matuƙar so,tace"autana kayi haƙuri banaso wani ciwon ya daɗa kamaka bayan ciwon zuciyar da kake dashi dan Allah Farouƙu ka daina wannan damuwar nima da fa karkamanta kwatankwacin irin damuwarka ce dani, amma nayi haƙuri na fauwala wa sarki Allah na miƙa masa komai A hannunsa shi zai yi mana maganin dukkan masifun da suka kewaye mu,banaso kaci gaba da nuna damuwar ka ne saboda nasan idan maƙiya zai koma kanka, amma idan ka ɓoye damuwarka wa maƙiyanka zaka samu salama baza A kuma ƙoƙarin cutar min da kai ba,kaji autana!'ta ƙarasa maganar cikin lallami da shaukin ƙauna da tausayi,ɗago kansa yayi yayin da idanunsa sukayi jawur kamar garwashi,cikin dishewar murya yace"Hajiya ina matuƙar ƙoƙari sosai,idan banzo gabanki nayi kuka na rage raɗaɗin dake cikin zuciyata ba tabbas wata rana za'a shigo miki da gawata, ke kaɗaice wadda zan iya zama gabanki inyi kuka kuma ki rarsheni koda ace bakisan silar damuwar tawaba, ballantana ke ka ɗaice kikasan damuwar dake binne cikin raina!'ya ajiye maganar cikin jan wata sheshsheƙa dake nuni da tsananin damuwar da mutum ke ciki,A hankali Hajiya Babba ta ɗora hannunta akansa tana shafawa tare da cewa, hakane Farouƙu,na gamsu da maganar ka,Ni dai fatana da addu'a ta Ako da yaushe shine Allah ya nunamin ranar tonan asiri ya nuna min maƙiya da idanuna ranar da za ayi walƙiya aga idanun kowa,ya kuma kawo mana haske da farinciki A cikin ahlin ALHAJI BALARABE!'Amin Hajiyata Amin ya Allah.