Sashe 48
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Lokacin da aka kawo mata take away ɗin tuni ta daɗe da tashi tayi wanka ta mayar da kayanta, dan haka ana kawo mata ci tayi ta ƙoshi,daga nan kuma sai duk tsoro ya rufeta ta kalli ko ina taga ita ka ɗai ce,sai tsoron ya kuma kamata tuni ta fara ruwan hawaye daga ƙarshe ma ta saki kukan gaba ɗaya,da taji motsi sai ta zabura acikin wannan halin ya shigo ya sameta wanda ita saboda rigima ba tasan yashigo ba kukan ta kawai takeyi tamkar wanda yake mata daɗi,ɗan tsayawa yayi yana dubanta wai ita kuka baya mata wahala ko yanzu me akayi mata kuma oho? ɗan tsaki yayi wanda shi ya ankarar da ita, da gudu ta miƙe zata gudu yayi saurin sa mata doguwar ƙafarsa aiko tuntuɓe taci ta zube ƙasa tana riƙe ƙafar cikin tura baki tace"to Ni me nayi maka kuma naga dai kai kabani tsoro!'harara ya zuba mata batare da yace"mata komai ba ya wuce dan shiga ɗaki, da gudu ta tashi tabi bayan sa,ɗan juyowa yayi yayi mata kallon ki kiyayeni ɗan marairaice wa tayi tare da cewa Wallahi Oga Abdallah tsoro nakeji!'ki shirya zamu koma gida da sauri tace"nan ba agida muke ba wane gidan kuma zamuje? ESTATE ya faɗa tare da cigaba da tafiya,tunda ya faɗi kalmar estate jikinta yayi sanyi zuba masa ido tayi har ya shige ɗakin sa, A hankali takoma ta shiga ɗakin da take ta ɗauko mayafin abayar jikinta, falon ta dawo ta zauna tare da zuba ta gumi anya kuwa zata iya ci gaba da rayuwa a cikin wannan ahlin? anya zata iya cigaba da zama ana ƙulla mata sharrin kisa?idan kuma basu karɓe ta bafa? inno fa ga Hajiya Babba itama tasan duk sun tsaneta yanzu kallon makashiya suke mata, ta tuna lokacin da ƴan sanda suka tafi da ita babu wanda yayi yunƙurin ceton ta babu wanda ya nuna alamun ya yadda da abinda ta faɗa,ya zatayi ta iya zama da inno cikin halin tsana da ƙyama? tabbas a wannan lokaci baza iya duban idon inno da Alhaji Baba ba, ga kuma Hajiya Babba matar da tabata yadda a rayuwa, kallon ƙofar ɗakin da yashiga tayi haka kuma zuciyar ta na cigaba da tunzura ta akan ta tashi ta gudu tun kafin ya fito ya mayar da ita cikin wannan gida mai kama da ramin macizai a wajen ta, cikin sanɗa ta miƙe batare da ta yadda tayi wani motsi mai ƙarfi ba, da sauri ta gangara ƙasa cikin Sa'a ta samu ƙofar falon babu security cikin hanzari ta fita, dai dai lokacin kuma mai gadin ya zaga baya, dalilin kenan da tasamu damar fita batare da kowa ya lura da ita ba.
Cikin hanzari ya fito falon ganin bata nan sai ya ɗan ƙonƙosa ƙofar ɗakin nata jin shurun da yayi yasa ya shiga yana mai tunanin yanzu haka kuka take tunda ba gajiya take dashi ba idan tanayi har wata jiniya take masa da ado dan ya kuma yin daɗi,zubawa ɗakin ido yayi tare da ɗan kasa kunnensa ko zai ji motsi a banɗaki sai dai har kusan mintuna biyu baiji motsin komai ba, takawa yayi A hankali ya isa bakin toilet ɗin saida ya ɗan kasa kunnensa kana ya tura ƙofar,ga mamakinsa bata cikin toilet ɗin,da sauri ya fita tare da sauka babban falon ya shiga dubawa ko wane ɗauki daidaita duba kiching da sauran guraren dake cikin falon amma duk neman sa baiji koda motsinta tsorone yafara kama shi karfa a shigo har cikin gidan nan a sace yarinyar nan,a hankali ya fara kiran sunanta tun yana faɗa a hankali har ya koma ɗaga muryar sa amma shiru a yadda ya lurama babu kowa cikin gidan fita yayi can wajen get,sojan me gadin ya shiga ƙwalawa kira kamar zai dake shi,da sauri ya ƙara so inda yake jiki na rawa gani ranka shi daɗe!' cikin fusata Abdallah yace"wa kagani ya shigo gidan nan ko ya fita? cikin rawar jiki mai gadin yace"wallahi yallaɓai babu wanda ya shigo sai dai bansani ba ko lokacin da nazaga baya wani ya shiga!'wani mugun kallo Abdallah ya watsa masa tare da cewa ka tabbatar idan banga yarinyar nan ba saikayi na damar sakaci da kayi na barin aikinka kuma kabar get abuɗe! daga haka ya koma ya shiga mota tare da yimata wata irin wuta,ganin haka yasa mai gadin ya kwasa da hudu ya buɗe masa get,da wani irin azababban gudu ya fita zuciyarsa tamkar zata kama da wuta har ya rasa wane irin tunanin zaiyi, ita ta fita da kanta ko zuwa akayi aka tafi da ita?cikin wannan tunanin ya hango kamar Bintun tare da maza biyu sun zagaye ta da alama ma kukan nata na fama takeyi, cikin sauri ya taka burki tare da fita daga motar wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya saki lokacin da ya tabbatar da cewa Bintu ce.
Ita kuwa Bintu tun lokacin da ta fito ta shati hanya batayi wata tafiya mai nisa ba wasu samari irin ƴaƴan manyan nan sangar tattu suka tare ta wai suna sonta, shine take ta fama dasu kan su rabu da ita sai kuka take amma sun ƙi rabuwa da ita acikin wannan yanayi Abdallah ya ƙara so ya samesu, Bintu tana ganinsa ta gudu bayan sa tare da cukyikyi sa tana sheshsheƙar kuka,ɗaya daga cikin sune yace" kai kuzo mu tafi wannan daga ninsa mijin tane!'ɗayan yace"ai inaga dai tabbas matar sace kawai mu fece!'Abdallah dai yana kallonsu bai kuma ce dasu komai ba ya juya da sauri tabi bayansa,buɗe mata motar yayi ta shiga sam ya kasayi mata magana saboda takaici, yarinyar nan tana bashi ciwon kai da yawa.
Ganinsu a tan game man get ɗin ESTATE yasa ta kuma sakin kuka cikin tashin hankali tace"Ni kabarni na tafi bazan koma wannan gidan nakuba bazan iya rayuwa da mutanen cikin sa ba,dan Allah ka rabu dani na gode da taimakon ka bazan taba mantaka cikin rayuwata ba, wallahi idan nakoma kasheni zasuyi,ga su inno ma duk haushi na suke ji kowa bai yadda dani ba, kuma Ni bani bace wallahi ban san komai ba!' kuka takeyi sosai wanda har sai da yaji wani iri can cikin zuciyar sa,cikin wata irin taushin murya yace" da ita ki daina kuka ba wanda ya yadda da abinda ya faru har inno ma duk sun fahimce ki!',da sauri ta goge hawayen fuskar ta cikin farin ciki wanda ya nuna tsantsan ƙuruciya da yarintarta, tace"da gaske inno ta yadda dani Hajiya Babba ma ta amince ban aikataba?gyaɗa mata kai yayi kawai yanajin tamkar wani abu na faruwa da zuciyar sa sai dai bai san komeye ba,A hankali ya fita ya zagayo ya fito da ita tare da kama hannun ta, ji yayi ance kar kasake ka dawo mana da wannan annobar cikin ahlin mu bazamu zauna da ita ta dinga kashemu da ɗaɗɗaya ba, ka mai da ita inda ka ɗauko ta dan shi kaɗai ya fi dacewa da ita!' wani irin kallo mai cike da tsana ta kaici haushi shi Abdallah ya kewa Dady Mansur,batare da ya kulashi ba ya cigaba da tafiya dan shi baisa wannan mutumin cikin sahun masu hankali ba,haka ya barshi agurin yana kunfar baki tamkar wani zararre.
Cikin nutsuwa yayi sallama falon Alhaji Baba,wani irin ƙayataccen murmushi Alhaji Baba ya saki ganinsu Abdallahn,yace"maza ku ƙaraso ƴan albarka Allah Ubangiji ya haskaka rayuwarku dan alfarmar shugaban mu Annabi Muhammad s.w.a.atare suka amsa masa da Amin Ya Allah, bazan iya misalta muku farin cikin Bintu ba ganin tabbas maganar Oga Abdallah ta tabbata, ga wata irin ƙauna ta bawan Allah da take ƙara mamaye jinin jikinta,gaidasa sukayi cikin girmamawa wanda bai bari sun ƙara wani magana ba ya ɗauko kuɗi a ɗaure cikin wata kyakykyawar leda wanda zaka iya hango abinda ke cikin ta, yace"matso nan jikata Faɗima!'matsawa tayi gabansa ya kuma kiran Abdallah shima ya matsa gab da Bintu hannun su Alhaji Baba ya kama ya haɗa dana juna ya sarƙesu daga bisani ya miƙa wa Bintu wannan kuɗin na hannun sa tasa ɗaya hannun ta karɓa cike da wani irin faɗuwar gaba wanda bata san dalili ba lokaci ɗaya jikin ta ya hau rawa,Muryar Alhaji Baba ce ta ratsa dodon kunnuwansu,Fatima karɓi wannan, sadakin Auren ki ne da Abdallah Allah Ubangiji ya baku zama lafiya ya kawo haske cikin rayuwarku.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 32 ``