← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 120

Sashe 8

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukane irin kukan nan me wahala wanda haryi take tamkar zata shide tun tanayi da karfinta harya zamana karfinnata ya kare sai wani irin Jan ajiyar zuciya me tsananin karfi, ita dai tana ji tana gani tasan fafin nata bai mutu ba, to amma me? gaba daya jikinsa asake yake babu inda yake motsi ajikin nasa,sai'idanunsa daya kafesu awake daya kwayar idanne kawai take jujjuyawa sai kuma numfashi dayake fitarwa sasa-sama, amma bada ban wadannan alamu ba to dashi da gawa basu da maraba, hannunsa ta kuma rikewa tana jijjigawa cikin dasheshshiyar muryarta da bata fita , tace" fafi Ina rokaka da allah katashi karkamin haka bani da kowa sai kai ina zansaka kaina? ta inazan fara nemansa ?a'ina yake? wayeshi ? fafi duk bansani ba, bani da nutsumi bare da bara, ni ban san komai ba akan rayuwata,fafi bazan iya ba ,bansan ta ina zan fara fuskantar wadan nan cukurkudaddun al'amuran ba,wayyoni kam bansan ina zan nufa ba fafi kayi min magana mana kaji fafi kace wani abu bintun kace agefanka tanai maka magiya, kaji tausaina mana ko 'ka'kane kaji fafina!'maganganu take iri da kala da na hankali da na tsantsan yarinta,sai dai kuma duk abanza baisan ma tanayi ba, abinka da lungu ba wasu jama'ane dayawaba,ba kuma tayi tunanin neman taimako ba, dakyar ta iya tashi tayi sallar isha tare da nafilar wuturi,zazzabine mai zafi ya rufeta ga wani wahalallan ciwan kai dayake neman bara mata kan gida biyu.

..ABUJA..

Sai da tayi zaman kusan awa daya afalon tana jiranshi batare kuma da ta kosa ba, har saida ya gama yangarshi kana ya fito.sansanyan kamshin sa ne yasanar mata da zuwanshi,anutse yake takawa har zuwa inda luntsumemiyar kujerarshi ta zama take, zama yay tare da mike sambala-sambalan kafafunshi ya kwantar da kanshi saman kujerar yana mai lumshe manyan idanunshi,shiru falon yayi bakajin komai sai karar na'urar sanyaya waje, ahankali mom tadan muskuta cikin taka tsantsan,dan yanzu wani babban motsi zatai yace zai bar mata wajen ba kuma tare da ta fadi abinda ya zaunar da'ita tsawon awa daya ba,cikin kokarin kalato jarumta tace"son dan allah kasaurari abinda zan fada maka ka kuma fahimceni, tasan bazai tankata ba, dan haka taci gaba da cewa"kasan ni maman kace bazan taba son abinda zai cutar da kai ba ina neman alfarma awajenka inaso awannan karon kabani martabata ta mahaifiyarka ka mutuntani kayi min biyayya kasani farin ciki akaro na farko arayuwarka!' ahankali yake bude manyan idanunsa wanda suke cike da bacci da kuma gajiya,d'an tashi yayi zaune, yana d'an taune lip dinshi kana ya fara motsasu ahankali yace"mom please I'm very tried if you finish the talking I need a space!'yadda yake fitar da salon maganar ma abin kallone balle ka saurari muryar dake fita dai-dai cikin wani hadadden turanci,mom cikin sauri da son ta karasa maganarta tace"basai ka koreni ba fatash yanzu zan baka falonka amma kabari na isar da sakona!'shiru yayi mata dama tasan da haka,dorawa tayi da cewa fatash aure mukeso kayi na samo maka mata dan nasan zakace baka da girl friend!' wani irin rikitaccen kallo yake binta dashi idanuwan nan sun kara girma yayin da fuskar ta kuma hadewa tamkar hadarin da zai zubda ruwa,tuni jikin mom yashiga bari saboda idanuwan fatash masu hukunta mutum aduk lokacin da yaso ba tare da duka ko zagi ba,sun shiga hukuntata tako 'ina tsabgarta suke ,saida ya tabbatar ta ladabtu kana ya janyesu tare da mikewa ya nufi bedroom dinsa ba tare da ya tankata ko kuma duban inda take ba,da sauri akuma rikice ta bar apartment din nasa gaba daya, tana maijin babbar faduwa agareta da tazama shashashar uwa mai tsoran danta

....Bauchi....

Zumbur tayi ta mike tana mai nanata kalmar innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un,agigice tashiga laluben fafi saboda mummunan mafarkin da tayi, wanda bata fatan ya zama gaskiya,sai dai kuma ga dukkanin alamu mafarkinta nema yake ya zama zahiri dan bil hakki take neman fafi adakin amma yace daukar ni idan kin ganni babushi babu alamar sawunshi,loko da sako tamkar wani allura haka take bi tana dubawa acikin gidan, ta daina gane komai bata ganin komai tamkar wata zautacciya haka ta koma ,bata tunanin komai kawai hange da duba take a'ina zataga fafi har kiran sallar asuba tana abu guda sunturi kawai take tana shiga tana fita ita daya bata da mataimaki sai allah gwanin kuka gwanin tausai rayuwa tayi mata duhu kwakwalwarta da tunaninta duk sunjuye.

..…ABUJA....

Ayau asabar misalin karfe takwas na safiyar ranar, pastor david ya gama shirinsa tsaf dan kaiwa amininsa alhj habib ziyara da kuma isar da muhimmin kuduri da tarin manufofi acikin zuciyarshi wanda shine babban dalilin zuwanshi cikin estate din na alhj balarabe, ya dade yana bibiyar ahlin na alhj balarabe dan samun kusanci me karfi atsakanin sa da yayan gidan, yakuma dace yasamu abinda yakeso, dan ya 'kullah 'ka'k'karfar alaka tsakaninsa da alhj habib, hatta yaro karami indai a estate yake yasan pastor david sai dai a idanunsu pastor david ba Crista bane dan da sunan musulmi yaje musu, dady jafar shine sunan da ake kiransa dashi acikin ahlin alhj balarabe.

Fakin yayi acikin katafariyar farfajiyar dake shashin alhj baba,bayan ya rurrufe kofofin motar da key din dake hannunsa, kai tsaye ya nufi katuwar kofar glass din da zata kaika har cikin falon alh baba,kafin ma ya taba madannin jikin kofar tuni ta wangale dan tuni CCTV ta nuna zuwansa.

Yana shiga ya zube gaban alh baba yana gaishishi cikin tsananin girmamawa,alh baba yace tashi jafaru kazauna Allah yayi muku albarka!'ya amsa da amin baba muna godiya Allah ya kara girma yajikan magabata!'alhj baba ya amsa cikin jin dadi hakanan yake ganin kimar alhj jafar da mutuncinsa yana kuma girmama alakarsu sosai ya daukeshi tamkar d'an cikinsa,cikin mutumtaka da kamala alhj baba yace da alhj jafar, nayiwa duk wani wanda yakamata atattauna dashi magana dan haka yanzu zasu karaso baki dayansu!' yan halak kuwa yana rufe bakinshi sai gasunan kusan duk atare, kasancewar yau weekend kusan kowa yana gida danshi alhj balarabe duk yayansa yan bokone kalilanne suke kasuwanci acikinsu.

Bayan gaishe-gaishe atsakanin su ne kuma alhj baba ya dubi alhj jafar yace"to jafar kace kana neman alfarma agurin ahlin gidan nan, kuma baza ka nema ba harsai na tara maka manyan yarana maza wanda dole sai da saninsu za'a'iyazartar da wani abu muhimmi acikin gidan nan,to gasu dan haka muna sauraronka!'alhj jafar yayi gyaran murya tare da gyara zamanshi kana yace"baba dama wata alfarmace nakeso ayimin acikin gidan nan wanda wannan alfarmar ba wani abu bane illa inaso d'ana abdallah zai dawo gidan nan da zama,wata zabura da alhj mansur yayi ita ta dakatar da dady jafar daga maganar da yakeyi, cikin wasiwasi da matukar shakku daddy jafar ya zuba masa ido dan yanaso ya karanto abinda yake kasan zuciyar mansur, alhj baba ne yace"munajinka jafaru kayi shiru!'numfasawa dady jafar yayi san nan yaci gaba da cewa"baba abdallah wani irin rikitaccen mutum ne kuma miskili me wuyar sha'ni,nayi-nayi ya fito da matar aure yakiya hasalima baya saurarona haka mamanshi duk wanda zaiyi magana ta bayan kunnenshi take wucewa,shiyasa na zauna nayi tunani me kyau akan abdallah naga dacewar kawoshi cikin ahlinka ko da bai samu macen da tayi masa ba zai dauki darasin rayuwa,kuma zai iya canjawa daga yanayin da yake ciki da kuma matsananciyar damuwar dayake ciki tunda nan wajene na jama'a da hada-hadarsu!'ya kare maganar yana mai tsurawa fuskar dady ane ido dan ganin yadda yake ta antaya masa harara tamkar idonsa zai fado,gyaran murya alhj baba yayi kana cikin nutsuwa yace"jafaru kan wannan dan batun ne kace sai na tara jama'a kamar gangamin daurin aure?kana ganin ko habibu kasamu da maganar nan bata isa ta wadatar ba?dady jafar ya sunjyiyar da kansa yana mai neman afuwa gurin alhj baba yace"baba ayi min gafara nayi kuskure amma naga kamar sai hakan yafi asanar da masu hakki!'alhj baba ya junjina kai,sannan yace"babu damuwa jafaru ni dai ta bangarena na amince abdallah jikana yazo ya zauna da yan uwansa, kuma duk yarinyar da yaga tayi masa indai babu maganar wani akanta to na bashi ita ya aura!juyawa yayi yana mai kallon yayan nashi da kuma yan uwanshi alhj Hashim da alhj mas'ud yace"idan da wani mai magana zai 'iya!' dady ane da dama kiris yake jira, ya zaburo cikin yanayinshi na zafi da ya shiga jikinsa yace"baba nifa Ina ganin kamar hakan bai dace ba bamusan manufarshi ta kullah wannan munafurcin ba to inba gulma ba haka kawai za'akawo katan gardi ace wai ya zabi mata bazai iya zuwa ya zaba ya koma inda ya fito ba!'ya karasa maganar cikin huci da hakilo shi adole baba ya fahimceshi, alhj hashir wanda suke kira da baffa ya dan numfasa kana cikin taushin murya da kamala irin ta manyan dattijai masu daddako, yace" haba mansur ya kana gima kana abun kananan yara duk ga kannenka nan zaune babu wanda yay irin wannan abun sai kai, dan allah ka dinga nutsuwa karka zama babban kobo meye abun tada hankali acikin wannan maganar, ka nutsu ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru sai alkhari insha allah!'abba mas'udu ma yace" hakane zancen ka yaya shi mansur baya daukar abu da sauki ne kamar yan uwansa, shiyasa kake jawowa kanka abubuwa da yawa ka nutsu dan Allah haka mansur kajiko!' ya fada cikin rarrashi da san kwantar mai da hankali,shi dai dady ane yayi shirune kawai dan anfi karfinsa amma ba dan yaji hankalin nasa ya kwantaba, Abba two wato alhj habib yace"to yaushe d'an namu zai karaso danni har na 'kagu naga zuwansa cikin ahlinmu!'ya fada yana sakar wa dady ane wani kayataccen murmushi tare da dage masa gira na irin to ya kagani din nan,dady jafar yayi dariya yace karka damu aboki insha Allah yana nan tafe!' Abba Ali yace" kaga sai asha shagalin biki dashi tunda yanzu baifi saura sati biyu ba bikinsu fa'iz!' abbi husain ne ya karbi zancen da cewa"tabbas zaisha hayaniya dan bikin mutum takwas ba wasaba!'nan dai suka cigaba da dan tattaunawarsu daga karshe kuma kowa ya nufi sabgarsa, dady jafar ma gida ya nufa kai tsaye da kudurin tunkarar abdallah da maganar komawa ahlin estate.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*
Chapter 8 · 0% Book details