← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 120

Sashe 71

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin taka tsan tsan Dije ta gayawa Bintu duk yadda sukayi da uwar ɗakinta,sai dai ta ƙara mata da alwashin da taci da kuma alƙawarin da tayiwa Bintun duk suna nan sai ma abinda ya ƙaru,tace"Bintu dole ne mu tashi tsaye mu bada himma dan bankaɗawa waɗan nan mugayen mutane asiri,dole kuma musake yin ɗamara akan wadda mukayi da dan cimma nasara, Bintu da akwai mugaye da yawa acikin gidan nan don bazaki taɓa gane fuskar kowa ba,amma yanzu dole mu gane mu sakawa kowa ido,kar kiji cewa kin yadda da wane saboda haka bazaki bibiyi al Al'amarin sa ba, Bintu idan da hali Hatta inno da Hajiya Babba da Hajjah mu saka musu ido da duk wani motsin su,ba kuma wai na faɗi haka dan ina zarginsu bane a'a sai dai kin san Hausawa sunce idan allurar ka ta ɓata duba ta har cikin teku,nima zanyi nawa yin duk wata hanya zanyi bi dan ganin na samu abinda zan iya shaida wannan muguwar matar dashi!'Bintu tace"yauwa Mama Dije abinda zakiyi ƙoƙarin gano wa kenan ina ga sai mun fi saurin gano ko wacece A cikin gidan nan!'dije tace"Bintu ke dai kiyi abin da nace kiyi,saboda wannan aikin agurina yana da wahala kuma akwai hatsari,dan zata iya fuskantar cewa har yanzu ina nan akan bakana na yaudarar ta, kinsan wan can ma ganowa tayi da kanta,kuma da kike wannan batu ma Bintu idan kuma ba acikin estate ɗin nan take zaune ba fa,abin fa ba ƙarami bane saboda Ni har yanzu bata bani wata ƙofa da zan gane komai akanta ba, wannan matar ta iya takunta yadda bakya tunani shi yasa na gaya miki kar ki bar kowa da kuke tare hatta wannan nafisar ma ki kuma banƙaɗa cikin ta baza muka sa samun wani ɓoyayyan abu daga gareta ba!' Bintu tace"har Ammin Rahima?wani irin murmushi Dije tayi tare da cewa Bintu ke yarinya ce bazaki fahimci komai da nake son ganar dake yanzu ba,amma dan Allah kiyi abinda nace dake,na fiki daɗewa acikin gidan nan kuma tunani na da naki ba ɗaya bane,ko har yanzu baki yadda dani bane?cikin sauri Bintu ta girgiza kanta tare da cewa"kiyi haƙuri mama Dije ba haka nake nufi ba amma insha Allah zanyi abinda kikace fiye da yadda kike tunani!'dafa ta Dije tayi tare da cewa yauwa yariyar kirki, sannan ki dinga yi mana addu'a kinji domin komai baya tafiya dai dai sai da taimakon Ubangiji!'jikin Bintu ne yayi sanyi sai taji kamar ta faɗawa Dijen halin da take ciki a kwanakin nan sai dai kuma babu halin haka tunda har yanzu Dijen bata san komai akanta ba bata san ita wacece a cikin wannan gurɓatattun mutanen da suke son kawo ƙarshen suba,dan dole ta ƙirƙiro ƙaryar da ta sharawa Dijen tace"insha Allah inayi kema ki dingayi min addu'a mama Dije!'Dije amsa mata tayi cike da son ƙara mata ƙwarin gwiwa, duk da cewa ta fahimci cewa akwai abinda Bintun take ɓoye mata,amma dai ta ƙyaleta har zuwa ranar da zataji ta gamsu da ita A zuciyarta,sai da ta rakata har can waje kana sukayi sallama bintun ta nufi sashen Hajiya Babba cike da nazarin maganun Dijen.

Tun Bintu ba ta ɗaɗe da fita ba Anty Nafisa ta shigo ɓangaren innon,tunda ta tabbatar Bintun bata nan shike nan ta ɗorawa hanya idanun ta,tana son ganin shigowar Bintu, sai dai har ta shafe awa ɗaya babu Bintu babu alamar ta,to amma tayiwa kanta alƙawarin bazata bar sashen ba sai da mafitar damuwar ta,gashi ta kasa tambayar inno inda Bintun ta tafi,har innon sai da taso fahimtar kamar ba anutse Nafisan take ba,sai ta ɗan shiga yi mata nasiha kamar yadda ta saba yi mata alokuta da dama,a tunanin inno har yanzu wannan damuwar ce aranta ta rashin haihuwa,duk da ta ga abin yayi sauƙi yanzu sosai bakamar lokutan baya ba,da take yawan riskar Nafisan cikin wani irin yanayi na matukar damuwa,to da taga inno tana son ranfota ne yasa ta ɗan nutsu,sallamar Bintu yayi dai-dai da wata ɓoyayyar ajiyar zuciya da Anty Nafisa tayi,gaishe da ita Bintu tayi,daga nan tayi shigewar ta ɗaki ba tare da ta kuma kallon inda Nafisan take ba.

To ga dai biki kuma babu zanin ɗaurawa, Bintu ta dawo amma ta rasa hanyar magana da ita,tunda tasan cewa magar da zasuyi da Bintu ba ta mintuna bace,kuma maganar sirrice wadda ta shafi wani ɓangare na rayuwarta,to kuwa ta yaya zata iya yin wannan sirri inno tana cikin falon nan A zaune?tunanin tane ya tsinke lokacin da taji wayar inno na ringin,dawo da hankalin ta kan inno da ta ɗaga wayar tayi tana cewa to Alhaji gani nan zuwa!'runtse idanunta Nafisa tayi tare da yin hamdala ga Ubangiji abinda take daɗewa batayi ba sai idan takama,(sai dai kuma ba tasani ba wannan taimakon da ta samu daga Ubangiji ba na kowa bane sai na Bintu saboda Allah yana tare da ita akan niyar ta ta Alkhairi,da san taimakon bayin Allah)

Inno tace"to Nafisa zan je Alhaji na kirana kuma gashi Bintu ta shige ƙurya bare ki samu ɗan taya hira!'da sauri Anty Nafisa tace"kije kawai inno bari na bita ɗakin, na rasa me yasa har yanzu Bintu bata sake dani ba,ko dan bamu cika zama guri ɗaya bane oho mata,ta faɗa tana miƙewa dan ƙara sawa ɗakin Bintun,inno ma dake ƙoƙarin shiga sashen Alhaji Babba ta ƙofar dake cikin falon ta tace"to ina ga dai haka din ne yanzu sai kije ki rutsata dan kiji dalili!'cike da farin ciki Nafisa ta faɗa ɗakin Bintu wanda ko sallama bata samu damar yi mata ba, Bintu na tsaye jikin windon ɗakin nata,har yanzu tunanin ta yana akan muryar nan datake tai mata kai kawo a cikin kunnuwa, ta kuma ci alwashin sai ta nemo shi kowaye indai yana cikin estate ɗin nan,ga kuma babban aikin da Dije ta bata, ko tayata zata fara bincikar inno da Hajiya Babba da kuma Hajjah?ita dai tasan bata zargin ko ɗaya daga cikin su,to amma idan tayi la,akari da maganar fafi ɗinta sai taga cewa wannan fa ita ce shawara mai kyau kuma abar bi,tabbas Dije tayi dogon tsinkaye,shigowar Nafisan ce ta dakatar da ita daga tunanin ta,juyawa tayi tana kallon Nafisan cike da jin tsanar ta acikin zuciyar ta tare yin tur da mugun halinta,zama tayi tare da cewa Bintun zo ki zauna saboda maganar mu bata buƙatar tsayuwa!'

"A hankali ta ƙarasa kusa da Anty Nafisan ta zauna,shiru sukayi na wasu sakanni kana Anty Nafisa tace"Bintu kefa nake jira tun ɗazu kuma yanzu nazo kinyi min shiru!'to me zance dake yanzu?ta tambaye ta batare da wani shakka ba,me kike nufi ne Bintu?ɗan gyara zamanta Bintu tayi tare da ƙara yin ƙasa da murya tace"Anty Nafisa kin san yanzu duk shawarar da na baki ba zatayi kyau kamar ace nasan mafarin lamarin ba,amma duk da haka yanzun ma ba zan kasa ko mai a kan haka ba!'yauwa Bintu na san bazaki kasa yin kyakykyawan tunani akan matsala ta ba,kuma na gaya miki babu komai dana rufe miki da dawani abun kin san bazan ɓoye miki ba!'ta faɗa cikin san Bintu ta gasgata maganar ta,wani ɗan murmushi Bintu tayi wanda kana ganin sa kasan na yaƙe ne,kana tace"hanya ɗaya ce zaki bi dan mijin ki ya gaya miki abinda yake sirrin sa,hannu tasa ta ɗan shafa fuskarta kana taci gaba da cewa,in dai har kin san ya yadda dake ya kuma yadda bazaki taɓa cutar dashi ba,kuma da akwai amana da gaskiya a tsakanin ku to kawai ki tunkare shi kai tsaye ki tambaye shi,ina mai tabbatar miki da cewa indai yayi miki waɗan nan abubuwan dana lissafa to wallahi zai gaya miki batare da ya ɓoye miki komai ba!'shuru tayi ganin yadda Nafisan take mata wani irin kallo wanda kamar ma bata san tanayi mata shiba,can dai da ƙyar tace"Bintu kina da hankali kuwa ta yaya zan san duka waɗan nan abubu wan alhalin ban shiga zuciyar sa na gani ba,ban san meye a zuciyar sa game dani ba, ban kuma san wani irin kallo yake min ba, ban san wane irin zargi yake min ba? gaskiya Bintu ki sake tunani!'tsura mata ido Bintu tayi kana tace"Anty Nafisa ya akayi KIKASAN yana zarginki?bayan kuma kin ce baki san ta yadda za ayi kisan wane irin kallo yake miki a cikin idanuwan sa ba?tuni Anty Nafisa ta diririce gaba ɗaya Bintu yariyar cikin ta ta saka ta a kwana tamkar wadda take tuhumar ta da laifin kisa,ganin irin rikicewar da tayi ne yasa Bintu ta kuma tabbatar da zarginta tabbas a kwai Babban abinda Nafisa take ɓoyewa wanda kuma zai iya taimaka musu sosai cikin tafiyar su,kuma tayi alƙawarin sai ta faɗa mata kome taƙe ɓoyewa,yanzu zata bar ta da wannan sai kuma zama na biyu,miƙewa tayi tare da cewa,Anty Nafisa Ni zanje kiching ke kuma kije kiyi tunani akan shawarar da nabaki idan ta karɓu sai ki aikata ta,idan baki gamsu da ita ba,sai mu canja wata Kinga Nima sai na samu damar ƙara yin nazari,kinga dole sai kin yi haƙuri akan wannan aikin saboda ya ban banta da sauran ayyuka,su waɗan can na san komai shi kuma wannan sai dai nayi lalube,daga haka ta fita daga ɗakin batare da ta jira abinda Nafisan zata iya faɗa ba,ita ma tashi tayi jiki a saluɓe ta koma ɓangaren ta cike da tunanika iri-iri.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 43 ```

Tana shiga kiching ɗin ta fara ƙoƙarin ɗaurawa ogan nata sanwa, sai dai gaba ɗayan ta bata jin ta dai dai saboda tunanin da ya cika mata ƙwaƙwalwalwa, ƙoƙarin ta kawai a yanzu gano me wannan muryar,duk da cewa yanzu duk wanda yayi magana ji take kamar waccan Muryar to amma da izinin Allah hakan ba zai sa ta kasa gano me ai nahin Muryar ba.
Chapter 71 · 0% Book details