Sashe 10
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bintu kiyi hakuri abinda kikeso kiji daga gareni bazai samuba dan nima bansan komai ba amma abinda zan gaya miki yanzu shine fitilar da zai haska miki hanya, abu dayane zuwa biyu shine asalinki da kuma inda zaki nufa!'
Dafarko dai bintu banine mahaifinki wanda ya haifeki ba amma uba nake agareki dan ciki daya muka fito nida mahaifiyarki uwa daya uba daya nine babba sai ita mu kadai iyayenmu suka haifa!' mu cikakkun fulanin adamawa ne,iyayenmu ba yan boko bane amma sun samar mana da ilmin boko dana addini mu bamasu kudi bane amma muna da rufin asiri dan bamu nemi komai mun rasa ba nayi karatun digree dina a maleshiya anan ne muka hadu da umar balarabe wanda yazamo amini agareni,ko da muka gama karatu bamu bar zumunci ba,har bikinsa naje nayi kwana biyu sai da aka gama na dawo. daga nan nima ban jima ba akayi bikina da yar uwata asma'u alokacin Ina aiki a wata babbar kotu dake nan cikin yola.
Bayan shekaru kusan biyar Allah bai bamu haihuwa ba daga ni har aminina umar sai dai umar yafini shiga damuwa nine nake yawan bashi baki da yaci gaba da addu'a ,yana yawan cemun shi dai aure zaiyi da zarar yasamu matar da yakeso.
Ana cikin hakane kanwata lailatu ta dawo daga makaranta, kasancewar akano take karatu a b.u.k tana zaune a hostel, tunda umar yake zuwa bai taba haduwa da Laila ba sai alokacin da ta kare karatunta, ranar da tayi exam din karshe aranar tayo gida tunda umar ya dora idonshi akan Laila shike nan yawada zazzafar soyayyarta,tun daga lokacin umar baya cikakken sati bai biyo jirgi yazo yola ba tun muna jin tsoro nida ita da iyayenmu har muka saduda, ba komaine yasa mukejin tsoron dangantakar umar da Laila ba illah tsananin kishi mai matukar zafi kuma na hauka wanda matarsa nafisa ke dashi agabana tasha alwashi iri da kala munana akan duk wadda tayi gangancin auren mata miji dan umar natane ita daya, wannan shine babban dalilin dayasa bamason wannan alaka ta soyayya. ana cikin wannan halinne kuma mahaifinmu ya rasu,bayan wasu yan watanni da rasuwar ne umar ya kuma dago da maganar sa da Laila wanda ni atsammanina ya hakura ashe wai mutuwar bafface tasa ya danyi shiru da zancen.
Babban kuskuren da muka aikata alokacin ganin nine alwalin Laila yasa mukayi ganganci, nazo na kalallame hajjo mahaifiyarmu da zance mukace babu wanda zaisan da auren har sai ankwana biyu, umar ya kawo hujjar cewa idan alhj baba yasani kamar nafisa tasanine dan haka ayi auren daga baya sai ya kaita gida ya nunata yadda alokacin nafisa babu yadda zatayi dasu dole ta dangana,
Haka kuwa akayi. aure tsakanin Laila da umar ya dauru, ya siya musu gida mai shegen kyau anan cikin yola suka tare duk sati yake zuwa yayi kwana biyu ya koma bansan me yake gayawa mai dakinsa nafisa idan zauzo .
Haka rayuwa ta shuda har tsawon watanni biyar, alokacin matata asma'u ta haifa mun tagwaye harsuyi wayo. cikin ikon Allah Laila tasamu ciki acikin watansu na shida da aure, bazan iya kwatanta miki murnar da mahaifinki yayi ba domin ta wuce gaban kwatance, ahaka suka reni cikin atare cikin so da kauna har ya'isa haihuwa,aranarne mummunar kaddarar ta same mu kuma shine mafarin komai, lafiya kalau Laila ta haihu dama nace agida na zatayi wanka gaban hajjonmu dan haka daga asibiti can muka nufa dake umar saiwashe gari ne juma'a kenan zaizo dan haka nace kar agaya masa har sai yazo......
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 9 ```
Misalin karfe biyu na dare muna daki nida asma'u na dinga jiyo ihun kuka,zunbur muka tashi hankali atashe nida asma'u, tabbas kamar daga dakin su Laila nake jiyo ihun kuka da hayaniya , cikin sauri na fita, har asma'u ta biyo bayana, nace" da'ita ta koma ta kula da yan biyu karta sake tafito duk runtsi!' ba dan taso ba ta koma dakin, da sauri na zare key din dakin na rufe su, cikin sanda na doshi dakinsu Laila.
Ina zuwa bakin kofar dakin na tsaya cike da tsoro da tarin fargaba, muryar Laila najiyo tana cewa" dan Allah kurufan asiri kubar mun yarinyata mahaifinta ko ganinta baiyi ba baisan ma'an haifeta ba!'muryar wani kato na kumaji ya daka mata tsawa yace" ke angaya miki ita kadai mukazo farauta?to harda ke uwarta da kuma wanda yai sanadin kulla alakar aure atsakanin ku wato munafukin yayanki, dolene yau dukanku ku ba kunci lahira!'yana kaiwa nan azancensa, kawai ni dai naga Laila ta fito aguje sabe da jaririyarta,cikin sauri na danki hannunta adai-dai lokacin naji wani yana cewa maza ku bisu karku bari su sha, ni kuma zanji da wannan tsohuwar!' wato hajjon mu ban tsayaba duk da haka sai dai addu'a danayiwa hajjona da kuma iyalina akan Allah ya karesu daga sharrin wadannan mutane da bamu san daga Ina suke ba.
Allah ya bamu sa'ar fita daga cikin gidan, abinka da tsakiyar dare gari yayi tsit baka jin komai sai haushin karnuka,arewa muka nausa muna gudu iyakacin karfinmu amma abin mamaki mutanan nan suna biye damu, laila ta gaji iya gajiya dan haka na karbeki muka cigaba da nausawa cikin surkukin daji,bayan wasu bishiyoyi muka samu muka fake ganin yan ta addan nan na kokarin cimmana, gashi kuma da alamu karfin Laila yana gab da karewa yasa muka rabe abayan wasu ciyayi ganin mun bace musu yasa suka tsaya suna dube-dube,ji nai wani yana cewa kai washa gaskiya mutanen nan sunyi nisa kawai mucewa oga mun aikasu munjefawa namun daji gangar jikinsu sunyi fati!'sauran suka amsa masa da hakan yayi shashirgi!' dan suma sun gaji, muna jin komawar su sai da muka ja wasu mintoci kana muka fito,Laila duk tayi laushi ga danyen jego,kai tsaye muka dauki hanya batare da munsan inda muka nufa ba.
Mun dade muna bulayi acikin dajin kafin muci karo da wata 'yar karamar rugar fulani anan muka ya da zango, baffa jauro shiyay mana masauki, ganin Laila da danyen jego yasanya kan kace kobo yasa matarsa inno tayi mata duk abinda ya dace dan gane da masu jego tayiwa yarinyar wanka ta gasa mata cibiya,akabamu abinci mukaci muka koshi,cikin kankanin lokaci muka dawo haiyacinmu, sai da muka nutsu sannan na bawa baffa jauro labarin abinda ya koromu daga gida, ya jinjina al'amarin tare kuma da tunanin suwaye wadan nan mutanen?zuwan kansune ko kuma turosu akai?mun kasa tsayar da tunanin mu akan kowa dan haka muka tattara al'amuran muka barwa Allah.
Baffa jauro yace"amma yanzu ku dan dakata zuwa wani lokaci kafin ku koma!'nace"hakane baffa yanzu komawar mu gida bazai yuwu ba saboda bamusan masu neman rayuwar mu ba koda yaushe zasu iya kara farmakar rayukan mu!' ranar da kika cika kwana bakwai na rada miki sunan hajjonmu wato fadima amminki tana kiranki da hajjo ni kuma ina kiranki da bintu dan nace" bazan boye miki suna ba ko dan tunawa da mahaifiyarmu wadda bamusan halin da suke ciki ba haryau.
Bintu nida mahaifiyarki muka baki ilmi na boko da na addini ko wanda yake zuwa makaranta bazai nuna miki ilmi ba,saboda kina da basira da kwakwalwa me.saurin daukar abu duk wani littafi da ake koyawa amakaranta mun koya mikishi haka ta bangaren addini duk wani littafi da aka koya manashi saida muka koya miki kama daga hadisi fiqhu akbari sira umdatul ahkam bulugu zaduzzau jaini da dai sauransu kuma alhamdulillah baki bamu kunya ba.
Haka muka cigaba da rayuwa arugar baffa jauro bamu da wata matsala sai na tunanin gida da halin da su hajjo suke ciki, kina da shekara biyar muka fara shirin komawa gida sai dai kuma wani babban tashin hankalin ya kuma da katar damu,Laila ta gayamun tana wasu irin mafarkai mara dadi tana yawan mafarki da wasu mutane wadan da sam ita bata sansuba arayuwarta suna yawan zuwar mata awani irin suffa marakyan gani mun kasa gane inda mafarkin ya dosa,cikin wannan yanayin da amminki ta fada yau dadi gobe sai Allah baffa jauro baya zaune baya tsaye da nemar mata magani, ahaka muka kuma share wasu shekaru biyar din har me faruwa ta faru.
Tunda Allah yasa muka shiga rugar baffa jauro Allah ya dora masa kaunarki, bintu dan haka baffa jauro yayi miki gata ya tsaya tsayin daka ya kula dake ya dafaki da kayan tsari kullum ta Allah da irin kalar rubutun da zaiyi miki ko tofi wanka kuwa ba dai ayi miki shi da ruwa normal ba sai anzuba masa abubuwa na tsari sauka kuwa kinshata bansan iya adadi ba, bintu kedin kudurar Allah ce kuma da sannu zaki zamewa wasu takalmin kaya!' babu wani abu da zaiyi tasiri akanki ke din kin riga kin gagara, anyi miki kuma ankoyar dake shiyasa bana shakka akanki domin duk wanda yanemi kariya da taimakon Allah to tabbas ubangiji yana tare dashi.
Mafarkan da mamanki takeyi har nema suke su zautar da ita, dan har azahiri take ganin mutanen dasuke neman rayuwarta suna razanata, kalmar da suke yawan nanata mata shine, ta haifo abinda yake shirin rusa rayuwarsu sun kasa taba bintu ko inda take basa iya kalla, dan haka zasu dauke ta zasu rabata da ke so suke suyi maganin matsalarsu tun kan abin ya gagaresu, baffa jauro yayi iyayinsa amma dake kaddara tariga fata babu tsumi ba dabara dole abinda Allah ya nufa sai ya faru. kuma abincikensa yace"wadannan mutane ba jinnu bane sai dai kuma mushirukaine ma'ana manyan matsafane dasu kayi kaurin suna a har karsu ta shirka, haka muka dukufa da addu'a babu dare babu rana, sai dai kuma babu yadda zamuyi kaddarar amminki ahaka Allah ya shiryota.
Awata safiyar juma'a ne muka tashi da gagarumin tashin hankali dan mun nemi Laila sama ko kasa mun rasata,na shiga tsananin rudani da tashin hankali kuka ya gagareni sai hadiyar zuciya kema da bawani wayo ne dake sosai ba saida kika tashi hankalinki kullum sai kinyi mana kuka akan mukaiki gurin amminki alokacin shekarunki basu fi tara zuwa gama ba, har yau har gobe ban dena kukan rashin yar uwata tilo danake matukar kauna ba.