Sashe 62
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ta shiga ja da baya, ƙoƙarin samawa kanta gurin tsira take,saboda gani take a yadda yake ɗin nan tsaf zai iya bata kashi,to me ya ɓata masa rai haka?ko zan can mahaifinsa da akayi masa ne?tana ƙoƙarin silalewa taji yayiwa hannunta wani irin riƙo wanda har sai da ta saki wani marayan ihu,kallon sa tayi idanun ta cike taf da hawaye,kawai ji tayi ya janyo ta jikin sa tare dayi mata wata iriyar runguma mai cike da jin kewar wani sashe na rayuwar sa,rungumar da yayi mata runguma ce irin wadda mutum yake buƙatar lallashi,runguma ce irin wadda take nuni da halin da mutum yake ciki,samun kanta tayi da kwanciya luf cikin jikin sa wanda har baka iya gano ta aciki saboda lulluɓin da yayi mata,wani irin ɗumi taji saman wuyanta wanda yasa ta ɗan ɗagowa ta na fuskantar fuskar sa,ga mamakin ta Abdallah ne yake hawaye,wanda hakan ya kuma kiɗimata,tabbas duk abinda zai sa Oga Abdallah hawaye ba ƙaramin abu bane,kallon fuskar sa take tamkar tana san gano amsoshin ta cikin ƙwayar idanun sa, A hankali yasa hannu ya maida fuskarta kan ƙirjin sa tare da ƙara tsaurin riƙon sa A gare ta.
"Cikin wata iriyar murya mai matukar sanyi da sanya kasala,yace"Bint!innalillahi kalmar da ta ambata kenan can ƙarƙashin zuciyarta,a yayin da taji wani irin yanayi ya lulluɓeta tare da wata iriyar kasala da wani irin sanyi da yagame dukkan sassan jiki da ɓargon ta,tunda take bata taɓa jin wanda ya kirata da wan nan suna ba,bata kuma taɓa jin wani ya kirata da wannan sigar da Abdallah ya kirata dashi ba,kuma bata taɓa shiga wani baƙon yanayi dan wani ya kirata ba sai yau, yau ɗin ma yanzu A cikin wannan lokacin,to ko dan bai taɓa kiran sunan ta bane yasa taji haka?ƙara kiran sunan ta dayayi ne yasa ta ida shiɗewa dan wannan karon kasa jurewa tayi sai da ta kuma shigewa cikin jikin sa tare dasa dukkanin hannuwan ta ta rungumo shi ta hanyar zagayo dasu ƙugun sa,ta kuma shiga murza kanta akan ƙirjin sa tana wata irin sheshsheƙa wan da ita kanta batace ga dalilin yin hakan ba,lumshe kyawawan idanun sa yayi masu kama dana mai jin bacci,cikin lokaci ƙan ƙani ya dinga jin wata nutsuwa na saukar masa abinda ya tokare masa a maƙoshi ya dinga faɗawa,sunkuyo da kansa yayi ya cusa hancin sa a wuyanta yana shaƙar wannan masifaffen ƙamshin da yake barazanar tafiya da tunanin sa,a wannan yanayin gaba ɗayan su wani nannauyan bacci mai cike da nutsuwa yayi awan gaba dasu batare da sun shiryawa hakan ba.
"Dariya yayi cike da farin ciki,kana ya dubi tsayayyen mutumin da bashi da maraba da gawa,yace"ka gani ko ABUBAKAR saina watsa farin cikin waɗan nan ƴaƴan naka masu taurin zuciya,saina gama tsorata rayuwar su da barazana da tsafi na kuma mai dasu wawaye san nan na kawo su nan na na buɗe bakin ka agaban su ka gaya min inda ajiyar take,kai kuma A gabanka zan saka kawunan su cikin injin tsafi,wanda dole hakan zai sa ka buɗe baki ka gaya min inda aka ɓoye ajiyar zan gani shin riƙe amana yafi ɗanka da ƴar ɗan uwanka?dama na gaya maka zan yi ta ajiyar ka domin akwai ranar da kai da kan ka zaka tona abinda ka binne, ƴaƴan ka sune zasu zama garkuwar da zanyi amfani da ita dan nasaka tilas ka faɗa ko kaƙi ko kaso,duk da yanzu ma inada dama amma bazan yi ba saina jagwalgwala rayuwar su da tunanin su,yaro ke nan Abdallah kun kawo kan ku da kanku inda zaku zubda hawaye,agaban idanun ku baban ka zai faɗan abinda na daɗe ina binsa ya faɗa yaƙi faɗa,kuma agaban idanunka zan ƙarasa rayuwar sa dan bashi da wani amfani an riga anman ta da babin sa na rufe tunani kowa babu mai iya furta sunan sa sai maƙiyan sa,wata dariya ya kuma sheƙewa da ita yana cewa da kyau rashi kasheku tun farko yamin rana dan dana kasheku to da Jack Bai kawo min wannan mafitar ba,akan wannan burin ban san adadin rayukan da na kashe ba ƴan mata da samari da jarirai,dan haka ina da tabbacin burina ya kusa cika na mallakar duniya.
A wannan daren baccin Dady Mansur ragaggene,dan ko mama sarah bata kaishi shiga tashin hankali ba ita da takasan ce uwa,babu irin alwashin da baici ba akan duk wanda yasamu da hannun sa akan sace masa gudan jinin sa ba,babu wanda baiyi zargi ba daga kan Baba Hashir har zuwa kan waɗannan mugayen munafukan aminan Alhaji Baba ɗin,koda yake duk tafiyar su ɗaya dasu Baba Hashir ɗin,shi yanzu tunanin sa kawai yadda zasu bashi ɗan sa batare da sun cutar masa dashi ba,tunda shi dai bashi da wani laifi ko wata masaniya akan duk wani abu da suke nema,tom dan mai zasuyi masa garkuwa da Sayyid duk yawan jikokin Alhaji Baba Amma su rasa wanda zasu ɗauka sai ɗan sa,juyawa yayi tare da ƙara gyara kwanciyar sa yana kuma Allah Allah gari ya waye dan yasan matakin da zai ɗauka tun kafin su cutar masa da yaro.
"Anty Nafisa ma kusan haka abin yake agurin ta, kai ita ko da runtse bata runtsa ba, yadda taga rana haka taga dare,ji take kamar ta janyo safiya dan ta samu damar ganawa da Bintu,ji takeyi ganawa da Bintu kamar shine mafitar matsalar ta,shawarar Bintu itace abinda take buƙata,domin kuwa shawarar Bintu ce zata bata damar tunkarar Umar da abinda ke kai kawo azuciyar ta,zuwan ta ɓangaren inno kuwa ya zama dole ko da kuwa innon zata zargeta akan yawan ganawarta da Bintun.
"Kiran sallar da aka ƙwala cikin danƙareran masallacin dake cikin ESTATE ɗin shi ya ta dashi daga baccin da ya kwashe shi batare da ya shirya ba,a hankali ya buɗe idanun sa da sukayi masa nauyi,bai sauke su ko ina ba sai kan kyakkyawar fuskar Bintu da ke ƙwaƙume cikin ƙirjin shi,zuba mata kaifafan idanun sa yayi masu matukar kyau da sheƙi,kallon abubuwan da suka faru a daren jiya yake tamkar a fai fan majigi,ganin ko mai yake tamkar shirin Film,lamarin Bintu ya matuƙar gigizashi da ɗaure masa kai,in dai har kunnen sa yaji masa dai dai ba kuma mafarki yake ba,to hakan yana nufin Bintu jikar ALHAJI BALARABE ce ƴar cikin ahlin sa kuma jinin sa mafi kusan ci da shi ƴa awajen Baffansa, Umar ƙani ga mahaifin sa,jika a wajen Hajiya Babba,to shi abinda bai gane ba dama Abba Umar ya taɓa haihuwa ne,shi dai yadda ya sani Anty Nafisa bata taɓa haihuwa ba kuma a iya sanin sa ita kaɗai ce matar da yake da'ita,dafe kan sa yayi wan da yake masa wani irin sarawa saboda tsananin ruɗani da kwan cewar tunani,ya shiga cikin duhu matuƙa da wannan al amari,ƙara kallon Bintun yayi yana ji tamkar ya tasheta yanzu ta war ware masa wannan curku ɗadɗen al'amarin,zame ta ya farayi daga jikin sa saboda yaji ana ƙoƙarin ta da Sallah,gyara mata kwanciya yayi saman faffaɗar kujerar tare da gyara mata dogon gashin ta da yarufe mata fuska,cikin hanzari ya ɗauro alwala ya fita bai nufi sashen Alhaji Baba ba dan dana yanzu ba kullum suke tafiya tare ba,a cewar Alhaji Baban wai yanzu ya zama magidanci ba zai dinga jiran sa ba dan kar ya makarar dashi,a lokacin murmushi kawai yayi yana aiyanawa a ran sa ko mai zai sa ya makara a masallaci oho, to kuma tun kan aje ko ina gashi shagwaɓɓiyar yarinyar nan tana saka shi fara makara, tun da duk ranar da ta kwana sashen sa sai dai yayi gaggawar alwala,da wannan tunanin ya isa masallacin.
A hankali ta buɗe idanun ta tare da addu'a a bakinta,falon ta shiga bi da kallo,sai alokacin ta tuna abinda ya faru da sanadin kwanan su afalon,mai da idanun ta tayi ta rufe,tanajin wata iriyar kasala da wani irin fargaba cikin zuciyarta,tabbas kalaman mutumin nan sun tsorata ta,duk da bata fahimci wasu kalaman nasa ba,,tashi tayi taje ta ɗauro alwala kana ta nufi ɗakinta,zuciyarta cike da saƙe saƙe,da neman mafita ga kuma tsoron mutumin nan da san gano ko waye,tunda har yasan ko ita wacece ya kuma san inda aka ɓoye iyayen ta dole ne ta jajirce domin yaƙi da azzalumi irin sa dolene ya fito mata da iyayen ta, tabbas ya sauƙaka mata wahala yanzune yaƙin zai fara zafi tun da ta fara sun suno hanyar da zata samu kubutar da iyayen ta,to Abdallah kuma fa?hakan yana nufin da shima akwai tashi ƙaddarar mai kama da tata ƙaddarar?to idan hakane me yasa sai su?kuma meye dangantakar ta da Abdallah? lallai tana buƙatar waɗan nan amsoshin nata daga bakin Oga Abdallah, tunda ta fuskanci matsalarsu ɗaya,kuma ya riga yaji komai babu batun yi masa ƙunbiya ƙunbiya cikin tarihinta,dama tana tsorone dan kar wani acikin baƙaken mugayen suji su farmaki rayuwar ta,to amma yanzu tana da yaƙinin bata da wata da bara illa ta tonawa Abdallah sirrin ta,tunda ta tabbatar da shine wanda fafinta ya sanar da ita zai taimaketa,oho yanzune ta gano dalilin da yasa fafi yake yawan ce mata shima yana buƙatar ta akusa dashi domin tare zasu haɗu suyi yakin warware mugun ƙullin da yake sarƙafe da rayuwar Ahlin su,da wan nan tunanin ta shiga ɗakinta dan gabar da sallar asuba,
Baiyi mamakin rashin ganin ta a falon ba,kai tsaye ɗakin sa ya shige dan shirin fita,dan baya tunanin ko karyawa zai tsaya yi,so yake yaje ya haɗu da Dady jafar ga kuma batun Sayyid duk da bai shiryawa ganawa da Sayyid ɗin yanzu ba,kuma bayajin zai sakeshi a ƴan kwanakin nan so yake ya haɗa faɗa gagarumi wanda zai kuma haska masa hanya,dan yasan abinda ya zama dole ne Dady Mansur ya tunkari wadan da bai yadda dasu ba yake kuma zarginsu da batun Sayyid, shi kuma da wannan dama zai kuma amfani dan gano mutum ƙwaya ɗaya da yafi addabar su ya kuma ɗauke mahaifinsa abin tunƙahonsa,duk da yana ganin ba lallai ne yasamu abin da yake so ta wannan ɓangaren ba,amma kuma tunanin sa ya bashi tunda duk abu ɗaya suke nema babu aibu dan yabi wannan hanyar hakan ma zai iya bashi wata hanyar ko yaya take tunda shi jam'i,in tsaro baya raina shaida ko mai ƙan ƙantar ta.