← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 120

Sashe 14

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsit kakeji falon yayi ai tuni kallo ya koma sama ,mai sakin baki nayi mai zaro Ido nayi kan uban nan Allah mai kudura da irada tsarki ya tabbatar ga ubangijn da ya halicci wannan kyakykyawar surar cewar hauwa'u kenan da takasa kawadda da idanunta akan abdallah da yasamu wata kujera can nesa dasu ya zauna, zaman nasa ma kansa abin kallone, dukkanin su suka hadiye wani kakkauran miyau da ya daskare akan harshinansu,najib ne yay karfin halin cewa kai dalla dubesu duk kun wani rikice da ganinsa sai kace baku gansa jiya ba!'amna ce tai zakal tace" kai ya najib kaima ka rikice da ganinsa bare kuma mu mata, kuma jiyan ince kinbari yay aga fuskarsa tunda ya sunkuyar da ita har akatashi ataron bai dagoba!'rahima da zuciyarta take mata wani irin mugun bugu tace" kai amna baki sani ba dai irin wadannan ko kallo zasuyi basa bari afahimta, dan haka baki da hujja akan cewa bai dago ya kalli kowa ba!' abdurrahim ne ya kallesu cikin jin haushin maganganunsu yace"yanzun dan Allah wannan tarbiyace? kudinga yi da mutum agabansa kuma babu wanda yay tunanin gaidasa, karfa ku manta da jawaban Alhaji baba koma kai tsaye nace" umarninsa akan mubi Yaya abdallah domin shine babba ayanzu da zai tsawatar mana!' fa'iz ya harareshi gami da cewa to uban tsari kai yanzu gaidashin kayi? komu cewa akayi maka bazamu gaidashin ba me tarbiya!'yakarasa zancen
da mikewa kai tsaye ya nufi kujerar da abdallah yake hakimce akai, ya kwantar da kansa idanunsa alumshe tamkar bayajin muhawarar da ake tafkawa akanshi,sallamar da fa'iz yayine yasashi dan bude idanunsa, nutsuwa fa'iz ya kumayi ganin tsabar kwarjinin abdallah, amsa sallamar yayi kamar wanda yake koyan magana,dan durkusawa fa'iz yayi tare da cewa barka da asuba ya abdallah!'barka dai ya fada asaman labbah danma fa'iz din yana kallon bakinsane da tabbas cewa zaiyi bai amsa ba, ahankali kuma suka dinga tasowa daya bayan daya suna gaidashin cikin kula da taka tsantsan tamkar ansanar musu halinsa sai dai kuma atabangarensu ba komaine yasasu wannan nutsuwar ba illa tsabar kwarjini da kamala irin nasa da kuma rashin ganin fuskar wasa,

Tunda ya zauna ya hanasu sakewa karshe ma ahankali suka dinga zare jiki suna guduwa daga falon ba fada ba duka balle harara su da kansu sukaji sunyi tsarara abdallah yana zaune aguri suma suna zaune babu mai iya wannan karfin halin duk cikinsu,sai dai yan matanfa yau hirarsu ta canja zani dan gaba daya ayinin ranar hirar abdallah ce abakunansu karma amna da hauwa'u da kuma farida yar Alhaji habib suji labari...

Da dai matar nan taji bintu takiyi mata shiru sai ta kuma juyowa afusace ta kwaza mata wata azababbiyar tsawa wanda nan take bintu ta kuma rikicewa, tsoro ya kuma da baibaye zuciyarta, saboda ta kaici matar figarta tayi sukayi ciki bintu kuwa binta kawai take batare da tashiryawa hakan ba saboda matukar tsoro,suna shiga tafkeken falon mai matukar haduwa da tsaruwa,wani dattijo wanda akiyasce zai iya kaiwa shekara hamsin da bakwai,yace'haba ladidi kiyi mata ahankali mana bakya ganin yarinyace karama,kinsan da nafisa ta haihu da yanzu kina da jikan da ya girme mata sosai!'sakin hannun bintu tayi tana cewa haba Alhaji ya daga ganin yarinya akwararo zakace lallai sai munshigo da'ita kai kana ganin kafurin kyau irin na yarinyarnan kasan ba abin arziki ta fito shukawa ba dan bana raba dayan biyu karuwancine ya fito da ita sannan gaka ganinta kaga balarabiyar karuwa!'
Alhaji munir yace" ashsha haba ladidi bazaki daina aibata yayan al'umma ba kenan kullum Ina gayamiki Amma bakyaji, ki bar ganin daya kawai kika haifa...kafin ya karasa ta tari numfashinsa da cewa kaga ni banason wannan mugun bakin naka kaima dai yarkace na gani idan kayi mata baki ta lalace bani kadaice da asaraba harda kai ehe,!' jinjina kansa kawai yayi batare da yakuma cewa da 'ita komaiba, dawo da hankalinsa yayi kan bintu da kukanta ya mutu tun sa'ilin da kamilalliyar fuskar Alhaji munir tayi mata maraba,cikin nutsuwa yace yarinya ya sunanki? cikin Jan ajiyar zuciya ta wanda yaci kuka ya koshi tace"zahra ta sami kanta da canja suna wanda itama baza tace ga dalilin yin hakan ba, ya kuma cewa to zahra daga Ina kike kuma me ya zaunar dake kofar gidana kusan awanni hudu?bintu kasa tayi da kanta ganin irin buhu-buhun harar da hajiya ladidi take aikamata,tagane daga dazu zuwa yanzu matar da aka kira da hajiya ladidi bata kaunarta, itama kuma hakanan taji matar bata kwanta mata ba, Alhaji munir ne ya katse mata tunani da cewa muna jinki zahra!'hajiya ladidi tai zaraf tace"yo ba dole tayi shiruba tana kirkiro karyar da zata shimfida mana!' Alhaji munir yayi mata kallon ki kiyayeni ladidi.........
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

Aunty hasana (maman nuur)wannan page din nakine kiyi yadda kikeso dashi Ina kara mika dunbin godiyata agareki Allah ya kara mana zumunci Amin ya Allah

```Page 12 ```

Alhaji munir ya juya yana dada fuskantar bintu tare da cewa Ina saurarenki zahra!'bintu cikin tsoron hajiya ladidi, tace"ni marainiyace iyayena duk sun mutu kuma a bauchi muke zaune, Ina zaune wajen kishiyar mamana na tsawon shekara daya da babana ya rasu, itace cina shana duk da Ina azabtuwa ahannunta,katsaham rana daya ta tada balli akan ta gaji da wahala dani alhalin babu dangin iya bare na baba dan haka saina bar mata gida wai itama tashi zatayi ta koma garinsu, hakan yasa na bar gidan da garin ma baki daya, Ina fita na nufi tashar garinmu dake bamu da nisa sosai da kafa naje, lokacin da na isa cikin tashar naji ana cewa Abuja dan haka kawai sai na hau motar Abuja ba tare da nasan kowa ba idan nazo, wata matace ta biya min kudin mota da muka sauka take tambayata inda zani ta ragemun hanya kasancewar anzo daukarta amota, shine kawai sai sunan anguwar nan ya fadomun da suka saukeni sai ta kuma taremin napep yakaraso dani nan, akofar gidan nan ya ajiyeni shiyasa na zauna awurin tun dazu har kawo yanzu da kasa aka shigo dani!' tayi saurin yin kasa da kanta ayayin da takawo nan akaryar da tasamu kanta da iya shararowa, Alhaji munir cikin tsananin tausayawa yace" ayya zahra karki damu insha Allah zaki zauna damu na dan wani lokaci kafin muyi shawara da mai daki na akanki!' bintu ta hada hannuwanta biyu tace"Abba na gode Allah ya saka maka da alkhairin sa ya kara tsawon kwana!' cikin tsananin jin dadin addu'ar ta yace"amin amin,!'tare da juyawa gurin hajiya ladidi da tayi wani irin sakalo tana kallonsa cike da mamaki da kuma takaicin wannan abu da ya aikata batare da neman amincewarta ba, batare da ya kula da kallon takaicin da take masa ba yace ladidi dan Allah kuje kisa iya talatu tayi mata duk wani abu da ya kamata, kama daga abinci wanka dakin da zata zauna,da duk dai abinda zata bukata awannan lokacin, yanzu zansa bawa driver yaje store yasamo mata kayan da zata bukata!'ya gama maganar da dauke kansa dan baya bukatar ta kawo masa wani buwaginta akan abinda ya bukata, hajiya ladidi ta saki wani dan murmushi, wanda da gani kasan da wani abu aranta,cikin ranta take fadin haba Alhaji nice fa ladidi idan kasan wata ai bakasan wata ba, bana aikata komai sai da manufa kuma wannan abun dakayi ni kaiwa danni zai amfana,

Ganin yadda yabawa banza ajiyartane yasa ta mike ba dan ranta yasoba a fuskarta, kallon bintu tayi da wani irin kallon tsana ta rasa da lilin da yasa taji bata san yarinyar, ita kanta ta fara da sawa kanta ayar tamba tabbas akwai dalili amma babu kira mai zai kawo gawayi,ganin takiyiwa bintun magana yasa Alhaji munir yace" da bintu tashi maza diyata kuje kinji Allah yayiwa rayuwarki albarka!'bintu ta amsa da Amin tanajin kaunar mutumin da ganin girmansa da kuma mutuncinsa arayuwarta, sumi-sumi tabi bayan hajiya ladidi tamkar zakace kyat ta arta na kare.

Can side din yan aiki suka nufa,wani daki taga hajiya ladidi ta konkwasa, wata dattijuwar matace ta fito daga dakin, tana yin arba da hajiya ladidi jikinta ya fara bari, kokarin rissinawa take hajiya ladidi ta dakatar da'ita cikin takama da izza, tace" talatu ga yarinya nan kiyi mata duk abinda ya dace!' daga haka bata kara ko'alif ba ta juya tai tafiyar ta,daga bintu har talatu bin bayanta sukayi da kallo,har sai da tabacewa idanunsu kana suka juyo alokaci daya suna duban juna, ahankali bintu ta durkusa har kasa ta gaida baba talatu,baba talatu ta'amsa cike da jin dadin girmamawar da bintu tai mata,sannan tace muje ciki kiyi wanka kafin nan na kawo miki abinci,bintu tace"na gode!'kana suka shiga cikin dakin na baba talatu, bayan ta nuna mata bathroom din sai ta fita dan samo mata abinda zataci,
Chapter 14 · 0% Book details