Sashe 40
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Acan cikin ɗaki me wayar ya cigaba da cewa,kin ɗauka zaki iya yau dararmu,ai base kin kasheshi bane Asirinki zai rufu Ni awaje na Asirinki a tone yake,kinyi tunanin ban san me kike ciki ba to babu abin da ban sani ba game da rayuwar da na baki dan ki salwantar da ita amma kika yau dare ni,dan haka kisa ranki a inuwa ina nan tafe gareki dan yanzu ba ta taki nake ba babban aikine agabana!' ɗif aka datse kiran,hannu Abigirl ta ɗora aka zatasa kurwa sai karaf ya buɗe ƙofar ya shiga.
Kallo yake binta dashi sai dai bai nuna mata yaji wayar da sukayi ba,cikin hikimarsa ta cikakken ɗan sanda wanda ba kowane yasan da hakan ba da gashi sai ɗan sa Abdallah,yace"lafiyar ki kuwa naga kamar zakiyi kuka, ko da wata matsalane?cikin ajiye wani wahalallan numfashi tace" dama mutuwa akayi mana A can garin mu yanzu zan shirya na tafi!' ta faɗa tana miƙewa ko ina nata rawa yakeyi saboda ruɗewa da tashin hankali, Dady jafar yace" to ai sai mu tafi tare nima na tarar da jana iza!'wata zabura ta kumayi kunsan dai yadda al'amarin su yake sam babu nutsuwa, a'a kabari zan je Ni kadai baza A bar gidan babu kowa ba!' ka faɗa ya ɗage cikin ransa yana cewa duk inda kikaje zaki dawo kitarar da tuhumar ɗanki Oga Abdallah,a fili kuma yace" shike nan amma gobe zaki dawo ko? cikin rashin san doguwar magana ta amsa masa da A,fita yayi dan yaga gaba ɗaya bata cikin hayyacinta.
Gaba ɗaya tunanin sa ya tafi akan da wa Abigirl take waya me ta ƙulla dayake shirin komawa kanta? wa kuma take san kashewa? tabbas waɗan nan amsoshin suna gurin Abigirl kuma da sannu zata tono su da kanta da bakinta.
Kwata kwata Oga Abdallah bashi da hutu yanzu,ka'in da na'in ya shiga zurfafa bincike A kan ahlin nasa, sai dai wani abu guda da yake tunani bai wuce yadda zai nemi karin bayani daga gurin Bintu ba,dan yayi yaƙinin cewa yarinyar ta san abubuwa da yawa wanda shi bai sani ba,to amma ta yaya zai saka yarinyar mutane cikin irin wannan haɗarin,anya idan yayi haka bai zalunci rayuwar ta ba bayan itama da tata matsalar ta ƴan iskan yaran gidan,to amma fa dole bashi da wata mafita sai hakan domin Bintu ita kaɗai ce zata iya keta ɗakin nan,furzar da iska yayi daga bakinsa ya zaiyi wannan ita kaɗai ce mafita agareshi amma dolene ya ɗauki matakin kare rayuwarta duk da cewa yasan Allah ne me rayuwar,amma ko mai yana da sanadi,dan haka zai jarraba.
Kiran da yasamu daga Alhaji Baba shi ya katse masa dogon tunanin da yayi zurfi acikin sa,cikin takunsa na ƙasaita yayi sallama A falon Alhaji Baba,mamakine ya kamashi ganin Dady jafar da sauran yaran Alhaji Baba wanda sukayi wan can zaman dasu, sai kuma ƙarin Taufiƙa da aka samu,gai dasu yayi cikin girmamawa,kana ya samu guri ya zauna, Taufiƙa kuwa tamkar zata cinye shi saboda kallo, ga kuma farin cikin da take ciki kasan cewar itace Ummul aba'isin haɗa wannan taron.
Abinda ya faru shine Taufiƙa ta gama yankewa kanta shawara akan tazo tasamu Alhaji Baba ta sanar dashi tana san Ya Abdallah tunda ta ga haɗa aure yake, ita dai ya haɗa ta dashi matsayin mijinta,Alhaji Baba murmushi kawai yayi tare da ɗaga waya yakira duk wanda suka san wan can zaman na Sayyid,farinciki ne fal ranta dan tasan tunda haka ta faru kamar ta samu Abdallah ta gama,kiran Bintu bai dame ta ba tunda tasan itama zai sanar da ita wanda ya zaɓa matane.
Gyaran murya Alhaji Baba yayi kana yasa Abba Hassan ya buɗe taro da addu'a,bayan sun shafa ya kuma yin gyaran murya kana yace" nasan zakuyi mamakin kiran ku da nayi cikin gaggawa,to amma ta wani ɓangaren ba abin mamaki bane idan mukayi la'akari da cewa abu yana iya taso mana batare da mun shirya masa ba,dan haka yanzu ma abinda ya faru kenan, ina so nasanar daku zan haɗa auren Taufiƙa da....
Muje nest page
Fatima y AdamâœðŸ½
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 28 ```
Da Sayyid ko bayan raina na bar wannan wasiyyar!'wani irin kallo Taufiƙa take bin Alhaji Baba dashi,maƙoshin ta kuwa ya bushe ƙamas da ƙyar take iya haɗiyar yawu,maganar da yaci gaba dayi ce ta kuma sawa take tashiga wani irin tari me ƙarfi,yayin da Alhaji Baba yaci gaba da cewa, Bintu kuwa zan bada aurenta ga Abdallah, mutanen da suka shiga shock akan maganar nan ta Alhaji Baba suna da yawa,kamar dirar mikiya haka sukaji saukar zancen yayin da Bintu ta shiga matuƙar ruɗani da mamakin wannan haɗin na Alhaji Baba ta ya wannan haɗin zaiyi dai dai? Alhaji Baba bai san irin masifar da yasakata ba, yanzu ji take har ta gwammaci auren Sayyid ɗin, A hankali ta maida dubanta kan uban gayyar, kansa A ƙasa yake bata fahimci ko mai a yanayin saba amma ta tabbatar a yanzu jiyake kamar yayi aman zuciyarsa, Alhaji Baba ne yaci gaba da cewa, wannan haɗin yayi min har cikin zuciya ta Abdallah kai kaɗai nake buƙatar jin ta bakin ka!'cikin nutsuwarsa da ba ta yadda za ai ka fuskanci halin da yake ciki,yace"Alhaji Baba ni bani da ja akan umarnin ka kai naka faɗa ne Ni kuma cikawa ce tawa,dan haka na amince da umarnin ka!'shiru falon ya ɗauka na wasu ƴan daƙiƙa kana Alhaji Baba yace"to masha Allah Allah yayi muku albarka baki ɗaya Batula ke kuma fa ko kina da abun cewa? da sauri ta gyaɗa kanta,yace to me kike buƙata?cikin tsan tsan biyayya da kawaici tace"Baba dama Anty Taufiƙa ce take son sa, Ni kuma na amince ka haɗani da Sayyid ɗin!'tunda aka fara maganar nan banga Abdallah ya kalli ɓangaren da Bintu take ba sai yanzu,amma cikin sakanni har ya janye fuskar sa ba tare da kowa ya ankara da hakan ba, Alhaji Baba yace"a'a Bintu ke Allah ya bawa itama ga wanda Allah ya bata nan!' ya nuna Sayyid da shi kam ko ajikin sa zan iya cewa laba asa a haka yanayin sa yake,cikin wani irin kuka na fitar hayyaci Taufiƙa ta shiga yiwa Alhaji Baba magiya da rokon ya warware haɗin ta da Sayyid amma ina ko saurarenta baiyi ba,inno ce ta daka mata tsawa tare da cewa ke kam wai Taufiƙa wace irin macece haka mara aji da kunya?to tashi maza kibawa mutane waje idan an kaiki gidan Sayyid ɗin kiyi duk abinda kika ga ya dace da rayuwarki shashashar banza da ta wofi!'Dady Mansur ne ya tashi fuu ya fita yayin da duk suka bishi da kallo,Dady Habib ne ya kalli Alhaji Baba tare da cewa Baba yaushe akasa ranar auren? kai tsaye Alhaji Baba yace"sati me zuwa in Allah ya kaimu!'daga nan su Hajiya Babba suka saka albarka sukayi addu'a kowa ya watse,
Tunda ta shiga ɗakinta take kuka wanda ita kanta tasan na tsorone yaza ayi ace wai Oga Abdallah shine wanda zata aura, har yanzu gani take kamar A cikin mafarki to ya zatayi da nauyin da yake kanta? tabbas tasan akwai ƙura ga Anty Hauwa'u ma da bata nan idan ta dawo tasan kashe ta zasu haɗu suyi kawai, wannan tunanin ne ya hana ta sakat duk tabi tayi sanyi,
Watsi take yi da duk abinda yazo hannun ta, Siddiqa sai haƙuri take bata amma tamkar tunzura ta takeyi cewa take wallahi sai naga bayan yarinyar nan sai dai duk kowa ya rasa,tsinanniyar yarinya ƴar mitsiyata almajira macijiyar sari ka noƙe wallahi bazan ƙyale ta ba kai kuma Sayyid ko dame kake taƙama bazan aureka ba,idan kuwa hakan ta faru sai na kasheshi na kashe kaina kowa ya huta!'Siddiqa ce ta kama ta da ƙyar tana cewa zama zakiyi munemi mafita ba wai kizo kinayi mana hauka ba, dan wannan abin da kike bashine zai rage miki raɗaɗin dake cikin zuciyar ki ba!'da wannan kalamin ta samu kan Taufiƙa ta nutsu tana maida ajiyar zuciya.
Cikin tashin hankali Hajiya ladidi ta tashi daga kashin geɗen da tayi tare da ƙara manna wayar akunnenta tace"aure kuma wani irin aure? Nafisa kina cikin hankalin ki kuwa yaza ayi maganar auren Zahra batare da sanin mu ba?ji tayi daga bayan ta Alhaji munir yace" Ni ai nasani kece dai baki sani ba!'kashe wayar tayi da sauri tare da juyawa tana fuskantar sa,tace"amma dai ko gayamin ayi ko ba dan neman amincewa ta ba tunda nasan ban isa ba!'Alhaji munir yayi dariya tare da cewa to yanzu baga shi kin sani ba,miƙewa tayi ta bar falon,
Tana shiga ɗakinta ta danna masa kira bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka, dariya kawai taji yasa tare da cewa nasan komai akan zan cen auren, ina so ki cire hannun ki daga kan wannan yaƙin dan yanzu yaƙin ya dawo na cikin gida ki zuba ido kiyi kallo yanzu wasan zai fara!'ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa yauwa har naji sanyi da hankalina ya tashi saboda ban san yadda zaka ɗauki maganar ba!'yace"kar ki damu ai hakan shine dai dai agurin mu!'daga haka suka katse kiran,Hajiya ladidi tace"wayyo Zahra inaji ajikina kece zaki zama silar warwarewar matsalolin mu.
Ta mai maita saƙon Anty Nafisa ya kai sau goma,ta kuma karantawa A karo na sha ɗaya, Bintu har yanzu banji amsarki ba lokaci yana ƙurar mun kiyi gaggawar yiwa kanki da rayuwar ki sulhu bana son ki ƙara kwana uku ba tare da kin bani sakamakon buƙata ta ba!'share gumin da yake ta tsatstsafo mata tayi, kana ta samu guri ta zauna tare da zuba tagumi,matsalolin da suka sakata gaba sun fara neman zautar da ƙwaƙwalwar ta domin yanzu babu wani tunani dayake shiga yake fita A kan ta ko mai yatsaya mata cak,ji take kamar ta zauna tayi ta zunduma ihu,duk wata dabara ta ƙwace mata,