← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 120

Sashe 61

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can kuma ɓangaren su Alhaji Hashir tare da Alhaji Kabir,sai Baba nura da Sama'ila da kuma,Salisu,yayin da Alhaji rufa'i ya kasance shine kaɗai babu acikinsu,kuma waɗan nan mutane sun kasan ce duk alhalin su ne suke musu wannan faɗi tashin, wato Alhaji Nasir da ɗan sa Sama'ila Sai Alhaji Hashir da ɗan sa Baba nura,sai kuma Alhaji Kabir shima da ɗan sa Salisu, dukkanin su sun yi zurfi cikin nazarin wannan lamari da ya taso musu,cikin dogon tunanin da Alhaji Nasir yayi yace"anya kuwa bamuyi gangan cin fita daga lamarin yaron nan Abdallah ba?nifa ina ganin kamar dasa hannun sa cikin wannan lamari!'Alhaji Sama'ila ne yayi saurin tarar sa da cewa haba Abba tayaya Abdallah yasan da wannan shirin namu balle har ya ɓullo mana ta haka? Ni ina ganin fa wannan fa bashine abinda Abdallah yake nema awajen mu ba dan haka ka daina sako shi cikin wannan sabgar!'Baffa Hashir yace"maganar Sama'ila akan hanya take Ni nafi tunanin mutanen nan sun ɗauke Sayyid ne kawai saboda suma sun gano muna bibiyar sahun su,dan haka sun ɗauke shi sun ɓoyeshi saboda kar mu samu wasu bayanai a tare da Sayyid ɗin!' wannan shine gaskiyar maganar cewar Alhaji Kabir kenan,kuma ina da tabbacin basu ka ɗai bane me amfani da Sayyid daban yake, kawai Ni aganina mu cigaba da bincike mubar maganar Sayyid, abu me mahimmanci agurin mu shine sanin inda Abubakar yake,dan haka mu cigaba da wannan binciken ta hakan zamu kuma gano waɗanda suke da irin manufar mu!tafi suka ɗauka gaba dayan su cikin nuna gamsuwa da batun na Alhaji Kabir,da wannan shawarar suka sami matsaya a tattaunawar su ta yau.

Kaf Alhaji Sama'ila ya zaiyanawa Samira tattaunawar da sukayi awanni biyu da suka wuce,tare da ƙara wa da faɗin to kinji shawarar da muka yanke akan wannan al'amari,Samira ta ɗan ja ajiyar zuciya tare da cewa shawararka tayi wannan ma Abune mai kyau da Yakamata musani, dan haka idan kuna da buƙatar taimako na hanya A buɗe take!'murmushi yayi tare da cewa ki kwantar da hankalin ki Samira lokacin buƙatarki yana nan zuwa!'itama murmushin tayi tana mai ɗaukar ice cream ɗin dake gaban ta, haka suka cigaba da ɗan tattaunawa cikin ƙara bugun cikin sa ba tare da ya gano hakan ba.

Alhaji Mansur fa yatashi hankalin sa,saboda har yanzu da rana take faɗuwa baiji wata alama da ke nuna masa cewa Sayyid zai dawo ba,ya tashi hankalin kowa dake cikin ESTATE da wan nan shegen kwakwazon nasa da rigima, to dama ya lafiyar kura, Hajjah ce tayi kiran sa ta zaunar dashi tare da yima sa nasiha yayi hakuri za aga Sayyid ɗin, amma tamkar tura shi takeyi,gajiya tayi ta sa masa ido dan fadan da yafi ƙarfin ka dole ka maida shi wasa,

Ta auna kiran Bintu yayi so goma amma wayar yaƙi shiga, gashi duk sakanni tashin hankalin ta da ɗa girmama yakeyi,idan ta zauna ji take kamar ko mai zai iya zuwa ya faru,neman taimakon Bintu take cikin gaggawa,so take ta samu mafita kafin dawowar Umar,so takeyi ta samu hanyar da zata ɓullo masa dan Sanin abinda take ƙwaɗayin sani,gashi bata son yawan zuwa ɓangaren innon dan gudun shiga cikin zargi,amma dole nan da zuwa safiya tasan abinyi.

Ta ɓangaren Abdallah kuwa yayi mugun saka ido akan al amuran da suke tafiya a cikin estate ɗin,amma abin da yake bashi mamaki har yanzu bai ga wata shaida da zai nuna masa wani yana da ɓoyayyiyar alaƙa da Sayyid ba,ɗan numfashi ya fesar yana mai cigaba da zame kayan dake jikin sa dan dawowar sake nan,ɗan ƙwanƙwasa ƙofar akayi batare da ɗaukar wani lokaci ba ya bada izinin shigowa, dan yasan babu mai shigowa ɗakin sa sai Bintu,sallama tayi cikin siririyar muryar ta tare da shigowa,kallon ta ya shigayi ƙasa ƙasa batare da yabari ta kula da hakan ba,tayi kyau cikin shigar riga da siket na atamfa wanda yayi ɗas ajikin ta, tamkar wata ɗawisu haka ya shiga kallon takun ta ga wani irin ƙayataccen ƙamshi da yagame ƙofofin hancin sa,samun kan sa yayi da ƙara buɗe hancin sa dan cigaba da shaƙar ƙamshin,yana wani lumshe idanun sa tamkar wanda yake jin bacci,Muryar tace ta dawo dashi hayyacin sa tare da saurin cigaba da abinda yakeyi,tace wai inno tace nazo kana kirana!'ko dai kike so kizo?ya faɗa batare da ya dubi inda take ba,cikin yanayin ta na sakalci tace"Ni kam Inno tace kana kirana!'yana ƙoƙarin shiga toilet ya ɗan dubeta kana yace"kawai kice kinzo gun mijinki ba sai kinyi wani kwana ba!'ya faɗa tare da shigewa toilet ɗin,kallo tabishi dashi kana tayi ƙwafa,wai miji Ni banga wani miji anan ba? Abdallah yana da matuƙar ƙarfin ji shiyasa bai sha wahalar jiyo abinda Bintu tace"ba,kaɗa kansa yayi tare da sakin wani murmushi yace"yarinya zakiga bakiga miji ba saikin gyara wannan kalamin naki.

Ita kuwa Bintu tafiyar ta tayi É—akin ta, tana cewa yau komai za ayi bazanyi kwanan wahalaba,mutum duk abi aka nainaye shi ya rasa ko hanyar yin numfashi mai kyau.

Lokacin da ya fito bai ganta ba yayi tunanin tana falon sa,dan haka shiryawa yayi cikin kayan bacci masu kyau kana ya fesa turarukan sa masu sanyin ƙamshi,tare da fita zuwa falon,da idanu ya dinga karaɗe falon amma bai ga ko ƙyallin Bintu ba,ƙara sawa yayi dining yacika cikin sa da girkunan gargajiya irin wanda Bintu tayi matuƙar ƙwarewa akan su,sai kuma akayi dace Abdallah yana matuƙar san girkin gargajiya shi yasa bai taɓa gajiyawa da nau'ikan girkin da take shirya masa ba, dan har abincin Fulani yi masa takeyi,haka kuma kullum ji yake kamar ana ƙara wa hannun ta zaƙi,sai da ya gama ya koma falon ya zauna yana ɗan taɓa aiki a computer,tun yana tsammanin dawowar Bintu har dai ya fidda rai,saboda lokaci yaja yasan bazata taɓa fitowa a wannan lokacin ba,tashi yayi ya koma ɗakinsa ya kuma yin brosh kana ya kwanta, sai dai haka nan yake ji ya kasa bacci kamar da abin da yake buƙata akusa dashi,sai diramar Bintu dake dawo mashi wani yayi murmushi wani yayi tsaki da haka dai bacci ɓarawo ya sace shi.

"Washe gari tunda ya dawo daga masallaci bai kuma fita ba yana zaune ta shigo tana ganin sa ta fara rarraba idanu kamar wata mara gaskiya,da ƙyar ta ƙara sa kusa dashi ta gaida shi amsawa yayi batare da ya kalli inda take ba,zata miƙe kenan wayar ta da sai yanzu ta kunna ta ta fara babureshon,juyowa yayi tare da zubawa Bintu ido, wadda ita kuma ta zubawa lambar da ake kiran da ita idanu,saboda wata irin nomba ce batafi guda uku ba kuma da wani irin yare ba da normal lambobi ba,ganin hannun ta yana rawa yasa Abdallah ruƙo hannun nata tare da karɓar wayar,shima zubawa nombobin ido yayi yana mai karanta addu'oi a bakin sa kana cikin yadda da Ubangiji da ka ɗaitakar zatin sa ya danna ok tare da saka amsa kuwa.

"Wata mummunan dariya aka saki tare da cewa yarinya mai tunani to ya kike keda gwarzan angon naki?ko da yake ba sai na tambayeki ba tun da Ni masani ne akan duk wani motsin ku,bawani Abune yasa na kiraku ba sai dan nayi muku gar gaɗi akan ku kiyaye da shiga sabgata domin ban kaɗai wani sirrina da sanin ko Ni waye, domin duk abinda kuke nema baza ku same shiba a halin yanzu daku da duk wani me san shiga hurumi na,baku isa ganin bayana ba ƙananan kifaye,sai dai Ni naga bayan ku da duk wani mai burin ƙwatar burina,ku tsaya iya matsayin ku na neman iyayen ku wanda kuma ina tabbatar muku da cewa bazaku taɓa samun su ba,domin ku ɗin ma baku tsira daga tarkona ba, kune cika makon burina da ku zan yi amfani na samu cikar burina,daga nan kuma sai nayi mai yuwu daku da iyayen naku!'

Wata mahaukaciyar dariyar ya kuma sheƙewa da ita, yana mai cigaba da cewa,yarinya mai hikima na yaba miki matuƙar yabawa da irin gudun mawar da kike bawa mijin ki dan ganin ya lalubo inda mahaifin sa yake,to ke mai yasa baki sanar dashi ya tayaki nemo taki mahaifiyar ba?kai ba daban zan ɓata shirina ba da na gaya miki inda mahaifiyarki take da kuma hannun wadda take riƙe dasu,ita da yayanta, FATIMAH UMAR BALARABE,DA ABDALLAH ABUBAKAR BALARABE,haɗin yayi kyau ina muku fatan shan wahala,daga haƙa ƙit wayar ta yamke,

Tofa kar ku manta Abdallah bai san wacece Bintu ba Bintu ma batasan wanene Abdallah ba,kamar yadda yake mata kallon wadda zata taimaka dan ceto rayuwar wasu mutanen,haka ita ma take masa kallon wanda zai ceci ahlin sa daga wata babbar matsala,ko ya zasuji? ko wane hali zasu shiga bayan jin wannan murya? to mu antaya gaba É—aya cikin fage na gaba dan jin yadda zata kaya........

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 38 ```

Wani irin kakkauran miyau Bintu ta haɗiya wanda yake tafe da wani gishirin tashin hankali,to waye wannan mutumin?waye kuma Abdallah A cikin ahlin ALHAJI BALARABE?dama shima ƙaddarar sa shigen tata ce?to shi waye ya sace masa mahaifin sa? kuma me yasa aka sace shi?wai wannan wane irin ahline masu baƙin hali? me yasa san zuciya yayi yawa cikin wannan ahlin?

Ɗagowa tayi a hankali tare da zubawa kyakykyawar fuskar sa idanun ta masu tsananin haske wanda suka suka fara sauyawa saboda halin ruɗani da take ciki, wani irin fargaba da tsorone ya kamata ganin yadda idanun sa suka sauya kala gawan nan maiƙon da yakuma tasowa wanda yake cike da zallar ɓacin rai,fuskar tayi wani irin ja,kana ganin sa kaga wanda aka tasowa da wani miki mai ɗaci,abin ya matuƙar bata tsoro,baran ma yadda yake mata wani irin kallo mai cike da tambayoyi marasa adadi.
Chapter 61 · 0% Book details