← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 120

Sashe 50

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawowarsa cikin ɗakin yayi dai dai da wani irin juyi da Bintu tayi, lokaci ɗaya santala santalan fararen cinyoyin ta suka baiyana,wani irin hajijiya yaji tana ƙoƙarin kada shi da sauri ya samu gefan gadon ya zauna tare da dafe kansa,ɗan satar kallonta yayi cikin sauri ya runtse idanunsa shifa sam bai saba ganin irin wannan abun ba, haka kawai tazo ta wani baje min aɗaki!'(Abdallah kaji tsoran Allah kaifa kace ta zauna tajiraka ka gama) tsakin ya kumayi kana ya yunƙura ya tashi, inda take ya ƙarasa tare da duƙawa runtse idanunsa yayi ya shiga bubbuga ƙasan carpet ɗin,amma tamkar ma nauyin baccin yake ƙara mata sai ma ƙafa da ta kuma ɗora masa a jiki,(kai dai kace bata da magagi ehe)janye ta yayi yana mamakin nauyin bacci irin nata wanda shi sam bai zaci tana dashi ba,da ƙyar ya samu ta farka amma duk da haka cikin magagi take,kamata yayi ya miƙar da ita tare da saita mata hanya,yace" tafi kije ki kwanta Sarkin bacci!'kamata yayi dan taimaka mata amma sai yaji gaba ɗaya ta yi kansa kasancewar suna tsaye ne a bakin gadon hakan yasa basu sha wahalar fadawa saman gadon ba,gaba ɗaya ta sakar masa nauyin ta saboda baccin da take sosai dan bata san komai yana faruwa ba, Bintu da shegen san jiki tuni tasa hannu ta kuma kanainaye shi tare da cusa kanta cikin ƙirjin sa tana shaƙar dadda ɗan ƙamshin jikinsa, rumtse idanun sa ya kuma yi tare da cewa ya Allah!'buɗe idan yayi tare da zubawa kyakykyawar fuskarta ido yayin da ita kuma take kwance saman jikin sa duk tabi ta duƙunƙune shi kamar wanda take tsoron kar asace shi,kasayin kataɓus yayi saboda yadda gaba ɗaya ta saukar masa da wata irin kasala da mutuwar jiki ki yayi ko ɗan yatsan sa ya kasa motsawa, kawai sai ya rabu da ita tare da ci gaba da kallon fuskarta, ko A baccin ma bakinta a ture yake saboda da haushin sa ta yi baccin samun kansa yayi da ɗan jan ɗan ƙaramin leɓenta yana mamakin rigimar Bintu ita damuwarta ta lokacin da Abu ya faru ne amma sam bata barin damuwa aranta sai dai idan A lokacin damuwar tazo ko ta tuna amma sabgoginta take hankalin ta kwance, (Abdallah ba haka bane Allah ne yabawa Bintu baiwa da wani irin hali na rashin barin damuwa tayi mata tasirin da har zata hana ta walwala, duk da tarin ƙaddarorin ta sai Allah ya sakamata tawakkali da amsar ƙaddararta a duk lokacin da ta kutso rayuwar ta) hannunsa akan tattausan lip ɗin ta wani daddaɗan bacci yayi awan gaba dashi,Abdubint asuba ta gari ayi bacci lafiya amma kar amakara sallar asuba.

Labarin da Anty Nafisa taji na dawowar Bintu yayi mata daɗi sosai tana ganin matsalarta kamar tazo ƙarshe tanayiwa Bintu kallon maganin damuwar ta,ita Auren Bintun sam bai dameta ba dan aganinta bata ga abin damuwar ba wannan muskilin yaron da ba gane gabansa da bayan sa ake ba tsaf watarana zai iya sako Bintu,kuma da ɗin da ɗawa shi ba ahlin ALHAJI BALARABE bane balle abun ya dameta,kawai dai abinda ta sani ne dole a wannan lokaci Bintu tayi mata abinda take so dan haka ita kawai take jira ta gabatar da cikin ƙaryarta,daga tasamu abinda take nema babu wanda zai kuma jin ɗuriyarta sabuwar rayuwa zata buɗe ita da sabuwar soyayyar ta.

Cikin juyi da tsananin daɗin bacci takuma shigewa jikin sa tare da ɗora kanta saman ƙirjin sa tan shaƙar dadda ɗan ƙamshinsa alokacin tuni ya farka saboda kiran sallar da aka ƙwala,shi da yake tashi kafin kiran sallar dan gabatar da nafila, amma yau shine da wannan nauyin baccin gashi idan baiyi da gaske ba zata iya sawa ya makara,a hankali yake ƙoƙarin zare ta daga jikinsa amma da ta kuma yin wani juyi sai gata gaba ɗayanta a ruwan cikin sa tare da zagaye hannuwan ta a ƙugunsa,runtse idanunsa yayi tare kiran Ya Allah!'wannan yarinyar so take ta kashe shi, bai mutu da guba ba gashi nan zata kasheshi da wannan juyin data keyi a ruwan cikin sa,daya ga dai da gasken makara yake neman yi kawai sai ya saka hannu ya ture ta kana ya miƙe,ita kuma a daidai lokacin ta farka tare da ware manyan idanunta ganin a inda take yasa tayi wata wuntsilowa daga kan gadon tare da zaro manyan idanunta, tace"na shiga uku anan na kwana?shine bai tasheni na koma ɗakina ba!' harara tabi bayansa dashi lokacin da ya fito daga toilet ya nufi ƙofa dan fita,bata daina hararar saba har ya fita daga ɗakin,tashi tayi ta ta fita, cikin sanɗa ta shige ɗakinta dan kar wani ya ganta amma Taufiƙa wadda tun daren jiya da taga Bintu ta shiga part ɗin Abdallah ta kasa ta tsare ko da rintse bata rintsa ba shi kuma wan da takeyi domin sa ma baccin sa yayi tare da matar sa hankalin sa kwance,komawa ɗakinsu tayi tare da ƙarfafa mummunan alwashinta akan Bintu.

Alhaji Mansur ne zaune a falon Hajjah sai masifa yake zubawa kamar zai aro baki ya daɗa,Hajjah cikin takaici ta dubeshi tare da cewa kai kam Mansur ban san abinda yake damunka da yaran nan ba, duk kabi ka damu kanka kashiga cikin sabgar da ba taka ba kayi kane kane,shi Abdallah n da ya fito da ita bashi taiwa laifin ba? ina ruwanka da yaran da Ako da yaushe zai iya barin cikin ahlinka babu abinda ya tare maka wanda sai kaso zaka ganshi cikin gidan nan amma duk kabi ka damu kanka,Ni bana son wannan halin naka Mansur ka canja hali na gaya maka!'shuru tayi tana maida numfashi yayin da ran nan nata idan yayi dubu ya ɓaci da lamarin ɗan nata,ta rasa inda ya dosa cikin lamuran sa amma addu'a ita kaɗai ce zatayi maganin wannan matsala,cikin damuwa yace kiyi haƙuri Hajjah amma ina kan maganata bazaki gane abinda nake nufi ba yanzu sai nan gaba!'yana gama faɗa ya tashi ya barta,yayin da tabishi da wani irin kallo wanda yay kama da kallon tausayi, Ajiyar zuciya ta sauke tare da binsa da addu'o'in shiriya.

Cikin iya taku da ƙwarewa akan aikinta Samira tace"dear gaskiya idan muna so musamu abinda muke nema sai kayi tunani akan mutanen gidan nan sosai,dan ta hakane kawai zamu iya fuskantar inda za mu ɗora aikin mu idan kuma ba haka ba zamuyi ta bulayine,kuma ina ganin hakan kamar wata sabuwar hanya ce da zamu kuma samun bayanai akan kishiyoyin ku, tunda duk abu ɗaya kuke yaƙin nema!'Alhaji Sama'ila yace"gaskiya Samira kina da fikira da ace aikin jarida kikeyi ko aikin bincike baƙarmin alfahari ma aikatarku zatayi dake ba, wannan tunanin da kikayi tunanine me kyau dan duk cikin waɗan da suke neman duniyar nan babu wanda muka sani, saboda idan mu ya rufe batasu muke ba!'Samira ta ja wani dogon numfashi kana tace"amma kunyi sake ai sanin su shine zai baku damar mallakar abinda kuke nema,saboda dolene kudinga sanin shirin su idan ba haka ba ku kuna zaune sai dai kuji sunyi nasarar mallakar koma meyene kuke son mallakan sa!'tsaye ya tashi yana zaga gurin cike da tashin hankali yace" me yasa bamu taɓa yin wannan tunanin ba? gaskiya mun tafka babban kuskure!'Samira tace"ai gyara shi ba Abune da zaiyi wuya ba tun da har munyi nasarar gane hakan yanzu tunanin mu zai juya ne kan masu nema wato kishiyoyin ku!' tafa mata yayi tare da cewa gaskiya Samira kin burgeni dolene nayi miki babbar kyauta dan haka na baki motar can da nazo da ita!'ido ta zaro cike da mamaki tace"da gaske kake Alhaji!'murmushi yayi tare cewa kin fi ƙarfin haka duk abinda nayi miki ban faɗi ba saboda kin kawo babbar gudunmawa cikin tafiyar mu!'wani murmushi ta saki kana tace"tabbas bazaka manta dani ba wanda sai nan gaba zaka kuma tabbatar da haka!' batare da ya fuskanci inda maganar ta ya dosa ba ya miƙa mata mukulli motar tare da cewa ki tafi da ita yanzu zanyi waya za'a zo a ɗauke Ni!' karɓa tayi tana cewa kamar na san da wannan babbar kyauta shiyasa ban zo da motata ba!'koda kin zo da ita har gida zansa akai miki kyautarki,daga haka ya tashi ya rakata har bakin motar kana sukayi sallama tana tayi masa godiya.

Wata irin dariya ce ta ƙwace mata wato shi dai mutum duk girman sa da wayonsa bai isa ya kara da hukumar bincike ba,ga dai yadda tayiwa Alhaji Sama'ila wayo da ta shiga jikinsa,tabbas duk ranar da yagano ta zaiyi matukar mamaki saboda tanayin komai da lura bata zaƙewa yadda zai iya saka kokwanto akanta yanzu ta gama da wannan ɓangaren saura kuma jin sirrin abinda ya haɗa wannan rikitaccen al'amarin ita kanta tanason jin koda sunan abinda suke nemane, yanzun nan kuwa zata turawa Oga Abdallah recording ɗin da tayi saboda tana so yanzu yaji irin babbar nasarar da suka taka, lallai tana ji ajikinta baza su ɗauki dogon lokaci akan wannan case ɗin ba saboda duk wata hanya da ya kamata su kama dan samun nasara sun kama saura waccen tsohuwar Abigirl ɗin wadda tuni Oga Abdallah yasa ɗan leƙen asirin su yabi sahunta duk wani motsinta akan idonsa ne,gaskiya Oga Abdallah ɗan baiwa ne Allah ya hore masa basirar sanin makamar aikin sa shiyasa duk aikin da ya tunkara sai yaga bayan sa.

Tun daga ranar da ta kwana a ɗakinsa bata kuma bari sun haɗu ba yau kwana biyu kenan da faruwar al'amarin,ta ɓangaren sa kuwa yanzu so yake ya haɗu da ita saboda manyan tambayoyin da suke ƙunshe cikin zuciyarsa,wanda a yanzu ne yake ganin ya dace ya sakata cikin wannan al'amarin,amma taƙi bari su haɗu ko meye dalilin ta oho,

Yau rana ta uku kenan rabon da yasaka Bintu cikin ƙwayar idanunsa,haka nan yakejin son haɗuwa da ita saboda aikin ɓangaren ta da yake son fara gabatar da bincike akansa(hmmm su Abdallah manya daraktan wayo kayi sake dai fans ɗin ƙudurar Allah sun gano ka)
Chapter 50 · 0% Book details