Sashe 54
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Tun tana sauraran jin sakamakon abinda suka aikata wa Bintu har dai taji shurun yayi yawa, tashi tayi da niyar dubawa taga ko dai suma tayi saboda ƙayƙayin, zuciyar ta taji tayi wani irin fari tare da ƙara saurin shiga ɗakin tana fatan ganin Bintu cikin mummunan yanayi,turus tayi ganin babu kowa ɗakin toilet ta shiga ta duba nan ma babu Bintu babu alamar ta cikin sauri ta nufi kiching nan ma bata nan sai kawai tunanin ta ya bata Bintu ta gudu saboda azabar da taji tasan wannan ƙaiƙayin zai iya zautar da mutum na wani ɗan lokacin, da sauri ta koma ɗakin inno tana shiga taga inno tana nafilar dare ɗan zama tayi tana jiran ta ta idar da sallar,bayan inno ta idar ta dubi Taufiƙa tace"yaya dai cikin daren nan ince dai lafiya ko? Taufiƙa tace"Bintu nake nema bangan taba!' cikin wani tuhumammen kallo inno tace"mai zatayi miki Bintun ko kina tunanin muguntarku zatayi tasiri a gurin Bintu ne?idan ma wannan tunanin kike ki dai na dan Bintu kainuwace Allah ya riga ya kareta daga dukkan sharrin mai sharri,yanzu haka tana hannun mijinta yana can yana jinyar matar sa!'wani irin zufa ne ya shiga ke towa Taufiƙa tare da wani irin mummunan tashin hankali kallon inno tayi tare da cewa inno me yasa bakya ƙaunata me yasa kika fifita bare a kaina? inno ta katse ta da cewa mugun halinki shi na tsana bake ba da zaki gyara halinki da kinga soyayyata, Bintu kuma ba bare bace agurina kuma dalilin da yasa na fisonta halinta ne yaja mata dan haka dole naso Bintu fiye dake,kuma daga yau karki kuma yin tunanin zaki goge Bintu daga zuciyata saboda ta riga takafu na kuma yadda da ita ɗari bisa ɗari ki tashi ki bani ɗakuna zanyi bacci!'cikin wani irin kuka na tsantsan baƙin ciki da takaici tare da tsana me tsanani ta tashi ta fita daga ɗakin inno, tsayawa tayi saitin falon Abdallah kallon ƙofar takeyi tamkar wadda zata zuƙo Bintu ta ciki,wai me yasa rayuwa tazo mata da hakane me yasa duk lokacin da tayiwa Bintu wata mugunta take dawo wa kanta me yasa idan taso ganin Bintu cikin baƙin ciki da damuwa sai abin ya juya kanta? hannu ta ɗora a kanta tanajin kamar tayi ta zunduma ihu,to wai dama Abdallah yana son Bintu ne ko Yaya?me sukeyi idan suka shiga ɗakin?tunanin da tayi ne yasa ta zubewa a wajen tana mai ƙara sakin wani rikitaccen kuka mai sosa zuciya (wanda koni naji tausayin Taufiƙa wannan shi ake kira ƙaiƙayi koma kan masheƙiya haka nan kuma ramin ƙarya ƙurarrene kuma ƙarshen ta idan ka haƙa ramin mugunta kai zaka zurma)
A wajen gari ya wayewa Taufiƙa har lokacin da Abdallah ya fito dan shiga ƙofar part ɗin Alhaji Baba dan tafiya msallaci,cike da ɗunbin mamaki yake bin Taufiƙa da kallo wanda sai yace tunda yake da ita da kuma haukan da takeyi akan sa sai yaune zai iya tan-tance kamanninta,ɗauke kanshi yayi lokacin da yaga ta zubo mashi jajayen idanunta da suka kumbura suntum ga rashin bacci ga kuka,ji takeyi kamar ta cinyeshi kowa ya huta Allah ne ya jarrabe ta da wannan ƙaƙƙarfar ƙauna me zafi dasa ta fita daga hayyacinta,cikin sauri ya bar gurin tare da waɗawa ƙofar da zata kaishi part ɗin Alhaji Baba,yana maiyiwa Bintu addu'ar neman tsari da wannan azzalumar yariyar,Taufiƙa ji tayi kawai gara ta shiga ɗakin taje ta kashe Bintu koda kuwa ita ma za a kasheta ta gwammace hakan da ace dai tana gani Bintu tana rayuwar farinciki ita da Abdallah,yunƙurawa tayi ta tashi ta ƙarasa bakin ƙofar falon, tana saka hannunta taji alamun a rufe ƙofar take wanda bata sani ba shi kuma Abdallah ya rufe Bintu ne dan kar ta tashi ta gudu bai samu labarin dayake buƙatar samu daga wajen ta ba,wata irin ƙwafa tayi wato ma har wani kulle kofa takeyi saboda samun waje,juyawa tayi cikin fushi da ƙuncin zuciya.
Ita kuwa Bintu tunda ta tashi ta ta buɗe ƙofar falon yaƙi buɗuwa hakan ne ya tabbatar mata da cewa rufeta yayi,to ita yanzu da wane ido zata dubi Oga Abdallah me zata iya ce masa?gaskiya baza ta iya kula shi a halin da take ciki ba
babu yadda zatayi haka taje ta É—auro alwala tazo ta zurma doguwar jallabiyar sa wadda tayi mata tsayi sosai dubawa tayi ta É—auki wani sabon towel babba ta rufa ta tayar da sallar ta,
Tana idarwa ta cire rigar saboda yadda take taɗeta, towel ɗin ta mayar ta ɗaura kasancewar wannan babbane shi yasa ya rufe mata har ƙaurinta,zama tayi abakin gadon wanda tasan da aɗakin ta take da yanzu ta faɗa kiching,dole a yanzu tayi tagumi zaman jira, ko karatun da takeyi bata samu ba tunda babu suttura ajikinta sai dai tasbihi da sauran lazumukanta da tacigaba dayi cikin zuciyar ta,