← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 120

Sashe 80

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wan nan shine ɗan gajeren tatihina, ba zan jaki da nisa ba a takai ce dai dalilin aurena da Umar inno ce dan Hajiyata ce ta fara kawo mata maganar a matsayin ta na ƙawarta, to dake Allah ya ƙaddara nice matar Umar dole haka ya aureni ba dan yana sona ba!'Bintu ina da matukar kishi na hauka san nan ina son Umar da arziƙin gidansu,shi yasa nake matuƙar kishinsa,a haka muka ja shekaru ba haihuwa bare ɓari,Ni kuma alokacin sai na fara jin tsoro kar Umar ya fara tunanin ƙara aure ko Hajiya Babba ta saka shi yayi aure tunda dama kamar bata karɓeni amatsayin suruka ba,wan nan dalili ne yasa nayi matuƙar sawa Umar ido fiye da yadda kike zato,a kwai wani aminin sa Sulaiman tunda mukayi aure da Umar da shi kaɗai nasan shi kuma nasan yana zuwa Yola wajen sa dan haka sai da nasa aka yimin bincike ko yana da ƙanne dan ina tsoron kar shima yace zai bashi ƙanwar sa ya aura tunda yanzu kowa neman inda zaiji daɗi yake, A lokacin sai akabani tabbacin cewa yana da ƙanwa guda ɗaya amma anyi mata aure,hakan ne yasa hankali na ya ɗan kwanta kaɗan amma kullum ina cikin fargabar kar Umar yaje ya gano ƴar kyakykyawar bafulata na ya auro min,dan haka kawai sai na ɗauki wani salo na sakawa Umar tsoron yin aure da fargaba azuciyar sa sai na dinga yawan mugayen kalamai da alwashi kala-kala akan kishiya,har agaban Sulaiman nasha rantsuwa duk ranar da Umar yayi min kishiya sai na kasheta sai dai nima akasheni, Bintu duk wan nan abinda nakeyi ashe a banza nakeyi,dan katsaham na fahimci yanayin zuwan Umar Yola ya canja yana zuwa duk weak end a maimakon duk sati biyu ko wata, san nan Sulaiman shima zuwan sa ya ragu ba kamar da ba, anan ne nayi hanzarin tashi tsaye da bincike.

"Hawayen da suka zubo mata tasa hannu ta share saboda tuno abin sai take ji tamkar yanzu yake faruwa,ta cigaba da cewa, bincike na ya tabbatar min da cewa,Umar aure yayi kuma ya ajiye matar a Yola,abinda ya kuma tayar min da hankali shine wai har ma matar tasa na ɗauke da ciki wanda zata iya aifuwar sa yau ko gobe,hankalina yayi matuƙar tashi saboda nayi mamakin yadda Umar ya shammace Ni har yayi aure yana shirin samun ɗa ko ƴa amma ban sani ba,sawa nayi a binciko min matar tasa ƴar wace mutane ce dan nasan irin matakin da zan ɗauka,amma amsar da aka dawo min da ita,ita ta kuma saka Ni cikin ruɗani wai ƙanwar Sulaiman ce,Ni da A kace min Sulaiman bashi da wata ƙanwa sai mai aure, to ina yasamo wata ƙanwar?ko dai sakota akayi ne?ƙarshe dai har da kaina saida nayi tattaki naje har cikin gidan Laila batare da tasan koni wacece ba, na kuma ganowa kaina tashin hankalin da ya hana Ni bacci ya hana zuciya ta sukuni ya hanani walwala cin abinci ya zama wahala agurina,saboda ganin turtsetsen cikin ta,tana rayuwa cikin ɗaula da jin daɗi, tunanin da ya fara faɗomin shine kawai nasa akashe Laila da ɗan uwanta harma da shegen cikin dake jikinta,tunanin hakan da nayi sai nayi ƙoƙarin kawar da abinda ke fuskata na barshi acan ƙasan raina yana cina,ban nunawa Umar ko mai ba,kamar yadda ya ɓoye min ban nuna masa na sani ba,sai dai kuma can gefe na koma nayi hayar haya killer waɗan da dama tun can mun daɗe dasu mutanen Hajiyata ne,su natura domin su kashe Laila da Sulaiman domin na tabbatar zaman sa a duniya bazaiyi min amfani ba,cikin daren suka bugo min waya cewa ai sun same ta da jaririya banyi wani tunani ba na basu umarnin sukashe su duka su ukun har jaririyar kar su bar kowa a raye,Bintu a cikin daren suka kuma kirana suka sanar dani sun kashe su duka dan haka na kwantar da hankalina,duk abinda nake yi inayin sa cikin taku dan alokacin ma ko ɗakin Umar banje ba ina ɗakina dan nasan da abinda na shirya.

Bintu tun daga wannan rana na samu salama a zuciyata da kwanciyar hankali, amma sai dai kash mijina shi ya fansheni da ninkin baninkin damuwar da nashiga, wallahi Bintu halin da Umar ya shiga alokacin har saida na fara dana sanin abinda na aikata saboda idan nace miki bana son Umar tabbas nayi ƙarya,tun daga lokacin yake ciwo a tsaitsaye damuwa ta rafkar dashi ta wannan sanadin ya haɗu da ciwuka kusan kala uku,

"A haka ne muka kwashi shekaru rabon dana ce miki Umar yayi dariya har na manta sai dai ban sani ba ko idan ya fita cikin ƴan uwan sa da iyayen sa,damuwar da yake ciki ita ta sani yawan damuwa akan abinda na aikata har inno da wasu da yawa suke tunanin ko damuwar rashin haihuwa ce na saka a raina,sai kawai na bari a hakan amma Ni a raina na san ba haka bane,ganin halin da nake cikine yasa Hajiyata tadamu ta tasani a gaba da cewa lallai sai na faɗa mata damuwata,banyi niya ko sha'awar gayawa wani sirrina ba,shi yasa kawai na canja labarin da ce mata,likitoci sun tabbatar min da cewa bazan taɓa haihuwa ba, Ni kuma shine nasa akayi masa asirin da bazai taɓa yin aure ba ko da yayi ma bazai taɓa haihuwa ba,kuma gashi hakan ya tabbata shi yasa nake nadama A yanzu ina ganin kamar zanje nasa a warware sihirin da nasa akayi masa!'alokacin Hajiya sai ta nuna min abinda nayi nayi daidai dan haka kar na sake na aikata abinda nake son aikatawa,idan dai har ba so nake asirina ya tonu ba,tayi min faɗan dan me ban gaya mata tuntuni mun san madafa ba, wallahi Bintu alokacin babu wan nan tunanin da burin a raina amma lokaci ɗaya Hajiyata ta ɗorani a hanya idanuna suka rufe ya zamana babu abinda nake nema sai dukiyar Umar ita kaɗai nake buƙata,dan kuwa tabbas huɗu bar mahaifiyata tayi tasiri a zuciyata fiye da yadda ita take zato,har ma sai burina yake son fin nata yawa,sai kuma gashi katsaham Allah ya kawoki,dan haka sai nayi amfani da wannan damar nayi duk abinda nayi ko nake kanyi,har zuwa yau dana baki labarin abinda Umar ya faɗa min wanda ban taɓa tunani ko zaton cewa Umar zai kawoni cikin zargin sa ba,dan ina da tabbacin cewa ban bar masa wata alama da zai iya gano abinda na aikata masa ba.

Ba zan iya kwatan ta muku takaici da tsanar da Bintu ta ƙara ninkawa Nafisa ba,wai yanzu wannan matar dake gabanta ita ce tayi sanadin rabuwar ta da iyayenta,itace tayi sanadin da mahaifiyar ta take can cikin halin da bata sani ba,ke nan Nafisa bata san inda mahaifiyar ta take ba?to idan hakane waye ya kuma kawo musu farmaki na biyu?kuma shi meye nasa dalilin?kuma taya akayi suka san Lailan?da kanta ta shiga ta shiga hasaso komai dake faruwa, tabbatas tana zargin mutum ɗaya ne yake aikata duk wan nan,a yanzu ta gano me wayar nan shine ya ɗauke mahaifin Abdallah kuma shine ya ɗauke nata mahaifan,kuma shine masarrafin wan can ɗakin,to amma me yasa yace,bai san inda mahaifiyar ta take ba,domin ta tabbatar shine ya kira wayar ta wan can ranar,to meye yake ɓoyewa ko yake aikatawa a wan can ɗakin? tabbas dole lokaci yayi da zata farmaki wan can ɗakin ko ta wane hali kawai dai fatan nasara take gurin Ubangiji.

Anty Nafisa bata katse mata tunanin taba har sai da taga dai Bintun dai bata da niyar dawowa cikin hankalinta,kana tayi magana a hankali tace"Bintu ya dai bakice ko mai ba!'sai alokacin Bintu ta kalli Anty Nafisa tare da ƙirƙiro murmushi tace"to ai ke nake jira ban ji ƙarshen ba tunda har yanzu ban san manufar kiba,shin kinyi na dama ne ko zaki ɗora daga inda kika tsaya!'tayi shuru tana jiran amsar da Anty Nafisa zata bata,cikin jan dogon numfashi tace"gaskiya Bintu da naso na haƙura ki nema min fafitar da zan samu na cigaba da rayuwata a gidan nan,sai kuma naga hakan ba zai taɓa yiwuwa ba,saboda duk daren daɗewa wata rana asirina zai tonu balle yanzu da Umar ya tabbatar min da cewa, sai ya nemo farin cikin sa a duk inda suke,dan haka shawarar da nayan ke kawai zansa akashe shi bakuma na buƙatar hannun ki a wannan karon,Ni da kaina zan sa su babe su kashe shi idan kuma zasuyi min kamar yadda sukayi min a baya to sai na kashe shi da kaina,ta faɗa tana miƙewa tsaye,Binta da wani irin kallo Bintu tayi,kana tace"kina ganin hakan shine dai-dai?kai tsaye ta bata amsa tare da ficewa daga ɗakin bata ƙara koda waiwayenta ba,

"A wannan karon dai Bintu ta aro jarumtar mijinta,dan kuwa sam bata shiga tashin hankali akan furucin Nafisa na kashe mata mahaifi ba,zuciyar ta ta tsaida guri ɗaya da kuma naiman taimakon Allah,ta ɗaga wayar ta da tun shigowar ta ɗakin ta saka recording ta naɗe duk maganganun Anty Nafisa,wanda take fata su zame mata hujja ko anan gaba,yanzu babu abinda idanunta ke tun kara da hasasowa sai ɗakin nan zuciyar ta nan kawai take hanƙoro ta ƙagu da son ganin abinda ake aikatawa a cikin wannan ɗakin,da wan nan ƙwarin gwiwar ta tashi ta fara abinda ya kamata dan ida kyakykyawan nufin ta a yau.

Tofa yau ake yin ta,muje nest page muji shin ko Bintu zatayi nasara a wan nan karon,shin daniyal zai ganowa ogah Abdallah gidan da su Hajjon suke,shin zargin Bintu zai tabbata akan inno kuwa,ina labarin Abigirl? Duk ku biyo NI domin dai anzo gun....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 47 ```
Chapter 80 · 0% Book details