← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 120

Sashe 20

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi ta dubi Rahima tace" auta ina ƙawarki kuwa zahra?Rahima ta saki dariya tare da miƙewa zaune tana cewa" wai ta gidan inno? ni wallahi ma banje ba tun washegarin da Aka kai Amare, faɗa mukayi da inno! ta ƙarasa maganar tare da ɗan turo baki, Ammi tace"to ai ba da ƙawar taki kukai faɗa ba ya kamata dai ki dinga zuwa kina ɗebe mata kewa!'to Ammi amma sai na huta sosai zan koma zuwa!' Ammi tayi murmushi kawai A ranta tanajin haɗa kusanci tsakanin Rahima da Zahra shine kawai hanyar da zata 'iya bi dan fahimtar abinda take so ta sani A game da Zahra,tasan ko bata tambayi Rahima ba zata dinga bata labarin Zahra,ita kuma zata dinga hankalta da inda yarinyar ta sa gaba idan A kwai wani Abu maka mancin na rashin gaskiya zata sani.

Duk tsarin da Hajiya ladidi tayi shine ya kasan ce, sau biyu ne tasa Alhaji munir ya kira Alhaji Baba,ba tare da wani shan wahala ba tsarinta ya tafi yadda take so koma fiye da haka tunda A cikin kwana biyu Alhaji Baba yaji san sha'awar ya mallaka wa Bintu waya,ko dan sudinga gaisawa da bawan Allah Alhaji munir, tabbas yana jin daÉ—in yadda Alhaji munir É—in yake nuna kulawarsa A kan Æ´ar marainiyar Allah Bintu,shi yasa yaji A ransa gwara ya bata waya dan shi Alhaji munir É—in yasamu damar kiranta kai tsaye,

Alhaji Baba da kansa ya kira Alhajin Nafisa, yasanar dashi ya bawa Bintu waya kuma layin da yaƙi rasa dashi shine layin Bintun, dan haka zai'iya kiranta kai tsaye, godiya Alhajin Nafisa yayi masa kana sukayi sallama, A lokacin suna tare da Hajiya ladidi ya kuma sanar da ita yadda sukayi da Alhaji Baba,yadda Hajiya ladidi ta nuna farin cikinta,har saida ya tsaya yana dubanta cike da mamaki,ganin haka yasa ta waske tare da cewa, kai masha Allah gaskiya Alhaji Baba ya kyauta,tare da ɗaukar wayarta ta bar falon.

Ita dai Bintu kawai ganin inno tayi da ƙaramar waya ta bata,duban inno tayi tace"inno wannan wayar fa ta waye?inno tace nakine Alhaji ne ya baki saboda kurinƙa gaisawa da Alhajin Nafisa!'to inno kiyi masa godiya, yanzu zan ƙarasa aiki sai naje nayi masa godiya nima!'inno tace"aiko yace" karki sake kije da niyar yi masa godiya,yace kiyi masa addu'a kawai ita yake buƙata!'cikin sanyin jiki Bintu tace"inno ai addu'a tsakanina daku ba mai yanke wa bace, Allah Ubangiji yaja kwana me amfani!'inno ta amsa da Amin Batula,kana ta juya ta fita daga kiching ɗin.

Tunda inno ta fita ta kasa ci gaba da aiyukan ta, gaba ɗaya ji takeyi mutanen nan suna ɗaureta, wai yaya ita da take neman hanyar tserewa suke ƙara yi mata da baibayi da zaman gidan,anya kuwa zata iya ci gaba da zama A gidan tana cin karo da shaiɗanun mutane da kuma Aljanu?

Lokacin da Anty Nafisa ta shigo falon inno bata tarar da kowa ba,dan haka kai tsaye kiching tanufa, dan anan takesa ran ganin Bintu, cikin Sa'a kuwa tana shiga ta sameta tana kan tunanin mafita wa matsalar datake ta tun karo rayuwar ta,

Tana ganin Anty Nafisa jikinta ya fara rawa, cikin sauri ta durƙusa ƙasa dan gaidata, batare da ta amsa ba ta ɗora mata da tambayar, ina inno? Bintu tace"ta tafi wajen Hajiya Babba,zata dubata da jiki!'saurin kamo Hannun Bintu tayi sukayi can cikin kiching ɗin,hannu ta mikawa Bintu tare da cewa ina wayar da inno ta baki?cikin sauri tace gata can, tanayi mata nuni da kan prezer,da sauri Anty Nafisa ta ɗauki wayar tare da buɗe ta tasaka mata wani layin A ciki, kana tasata A babiratin, sai da ta gama sannan ta dubi Bintu tace"ki kula da kyau, baki wayar nan yana daga cikin shirin mu dan haka ki kula da'ita tamkar yadda zaki kula da rayuwar ki,kuma duk wani shiri da kike na guduwa muna sane da hakan,zaro manyan idanunta tayi wanda idan tayi hakan baƙaramin kyau yake ƙara mata ba, Anty Nafisa tayi murmushin mugunta,kana tace" kina mamaki ko? to inaso kisani duk yadda kika zacemu mun wuce haka, mun zarta tunanin babban kaima barantana wannan ƙaramin kan naki, inaso kuma ki dinga sarrafa wannan shegen tsoron naki dan watarana zai iya hhhh gaiyato mana matsala cikin aikin mu, inaso kuma ki iya bakin ki A cikin gidan nan dan duk wanda kika gani ba Abin yadda bane ESTATE ƊIN ALHAJI BALARABE YA WUCE TUNANIN MAI TUNANI munanan munajira muga yadda ƘUDURAR ALLAH zata tarwatsa mugayen zukata da ɓara gurbin IYALEN ALHAJI BALARABE dan nasan namu ba komai bane shiyasa bana tunanin yin na dama akan abinda nake aikatawa ko kuma nace na aikata,A da har na fara karaya, na fara tunanin makomata sai Hajiyata ta nusar dani tare da ɗorani bisa hanya mai ɓullewa.

Babu abinda zuciyar Bintu take sai wani irin bugu mai tsanani, Anty Nafisa idon ta ya rufe ko lura da yadda yanayin Bintu ya koma batayi ba,dan tana gama zantukanta ta juya ta fita da sauri tabar kiching ɗin,yayin da ta bar Bintu tamkar butun butumi A daskare, tuni ƙwaƙwalwar ta tafi hutun wuccin gadi,ji tayi an jijjigata da ƙarfi,wata Irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tayi tare da fashewa da wani kiɗimam man kuka mai razanar da zuciyar mai imani, dije ta zuba mata ido cike da mamakin meye yasa ta kuka kuma? ko dai irin matsalar su ɗaya? tabbas ta daɗe A laɓe tanajin Anty Nafisa sai dai bataji komai ba, tunda bata daɗe da shigowa ba Nafisan tafita,tsoron irin kukan da Bintun takeyi shiya kama dije,tsoron biyune ya haɗe mata na farko kukan Bintu wanda har yi take kamar zata shiɗe, na biyu tsoron kar A zo akamata ace ita tayiwa Bintun wani abu, wannan tunani da tayine yasa tayi saurin juyawa zatabar kiching ɗin, Amma kuma sai taji ta kasa wani irin tausayin yarinyar ne ya dinga kewayawa har cikin ɓargonta wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata, cikin sauri ta durƙusa inda Bintu take ta kama hannun ta tare da miƙar da ita tsaye,A hankali ta jawota jikinta ta shiga bub buga bayanta tana shafa kanta tana bata baki cikin taushin murya,tace" haba ɗiyata ko mai yayi zafi fa maganin shi Allah kiyi haƙuri ki daina kukan nan kowa kika ganshi yana da matsalarsa, wannan kukan da kikeyi ai sai ya cutar dake ki dena ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah shine zai yaye miki kinji!'Bintu da yanzu ta riga tayi shiru sai ajiyar zuciyar da take fitarwa ajejjere,sai da dije ta tabbatar Bintu ta samu nutsuwa kana ta janye ta daga jikinta tace maza jeki ɗaki ki wanke fuskar ki kar inno tazo ta ganki A haka baza taji daɗi ba!'A hankali Bintu ta fara takawa sai da ta kusan barin kiching ɗin kana ta juyo cikin muryar ta da ta dashe tace" mama na gode Allah ya biya ki dukkanin buƙatunki na Alkhairi ya kareki daga sharrin maƙiya!' da sauri ta ƙarasa fita daga kiching ɗin saboda wani kukan dayake ƙoƙarin kufce mata,

Da ido dije ta bita tana ta nanata faɗin Amin akan harshen ta,haƙiƙa idan tace bata ji daɗin addu'ar da Bintu tayi mata ba tabbas tayi ƙarya, itama fita tayi jikinta A sanyaye, zuciyar ta kuma cike da tunanika iri-iri.

Tana shiga ɗakin ta waɗa kan gadon tare da kecewa da wani sabon kukan, zuciyar ta cike take da ƙunci wanda bata san ranar gushe war sa ba,yau tayi da tasanin zuwa garin Abuja,

Ashe dama wannan baƙin ahlin shine ahlina da fafi yake gayamin?tabbas iya abubuwan da na gani kawai sun isa tabbatar min da abinda fafina yake gayamin, yanzu wannan bawan Allah Alhaji Baba shine kakana? to wacece kakata kuma? wane ne mahaina?ya Allah hhhh kafitar dani duhu ka kawo min ɗauki, to ita Anty Nafisa wacece"?kuma matar waye?me yaya Abdallah yayi musu suke san cutar dashi?shi ɗan waye ne? wacece mamansa?ɗakin nan mallaki waye menene A cikinsa?shin me dame ake shiryawa da waye da waye masu shiryawar ?su waye suke neman halakani?suwaye suka ɗauke min mamana da fafina?ya Allah ka kawo min agaji, yanzu ta ina zan fara fuskantar wannan gagarumin yaƙin, fafi abin ya wuce zaton ka bazan iya ba bansan ta ina zan fara ba.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 16 ```

Hhhh sautin dariyar sa kawai kakeji amma baza kataɓa gane waye ba saboda yadda ya juya bayansa,waya ce kange A kunnen sa,ya kuma gyara zaman wayar yayi A kunnen sa,kana cikin wata murya me ƙarfi da wani irin sauti,yace"da kyau ɗan kaka aikin ka yanayin kyau,inaso kaci gaba da ɗora mun ladidi A kan hanya ita kuma tana ɗora mana yarinyar A saiti yadda zan samu biyan buƙatata batare da tasan mai nake shirya wa ba,kar kasake kayi abinda zata gane shirin mu A kanta!'

Daga ɗaya ɓangaren, na kaka yace"ranka ya daɗe Hajiya ladidi baza taba gane dawa take aiki ba, saboda duk wata hanya na tosheta A binda kawai nasan tasani shine tana aiki da ɗaya daga cikin ahlin ALHAJI BALARABE, amma baza ta taɓa gane da waye ba in dai ba gaya mata A kayi ba, kuma ina da tabbacin babu yadda za'ayi ta sani dan mun toshe hanyar, kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya saboda mun haɗa kifayen mu A guri ɗaya, ba ƙaramar nasara nake ganowa A tafiyar nan ba,

Ogan nasa ya sheƙe da wata muguwar dariya kana yace"naga fa kifayen nan suna da matuƙar wayo yaƙin suka fito da gaske, sai dai kuma ta yaro kyau take bata ƙarko basu san suna tun karar masifa da kansu bane, mutuwarsu suke kira, dan dazarar munci moriyar ganga zamu yada gauranta,ƙit ya yanke wayar tare da cire layin ya taune,cikin alfahari da kansa da yadda yake wasa da ƙwaƙwalwar mutane yace"shi yaƙi ɗan zanba ne idan baka iyashi ba zai kife da kai.
Chapter 20 · 0% Book details