← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 120

Sashe 2

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallama tayi can kasan makoshinta.
da wani irin hanzari ta karasa inda ta hangoshi ayashe tamkar wanda yay danbe, cikin tsananin razana da kuka take jijjigashi tare da cewa!" fafi fafi katashi me yasameka? me'akayi maka ? baka da lafiya ne? dan Allah fafi katashi
wayyo Allah na dan Allah fafi katashi karka tafi kabarni , Ina zanje? waye ze tallafi rayuwata ? kaddara karki biyo mun ta wannan hanyar karki rabani da bangona, rayuwata zata lalace.

Gaba daya ta rude bata cikin hayyacin ta sambatu kawai take zubawa kasancewar ta yarinya me kana Nan shekaru gaba daya takasayin wani tunani me kyau dan akiyasi baza ta wuce
sha shida zuwa Sha bakwai ba.

Ta sashi tayi agaba Tana wani irin kuka me taba zuciya manyan idanunta sun kumbura sunyi suntum muryarta ta dashe , ba'akojiyo sautin kukan nata.

Tana Nan zaune ahaka ta jiyo Kiran sallah ahankali ta zare hannuwanta Dake cikin nasa, so take taje tayi sallah ta roki Allah ya dawo mata da fafinta.

Bayan tayi alwala ta dawo, ta zauna, agabanshi Tana me cigaba da sheshshekar kukan ta, ruwan dake fuskarta da Kuma hawayen dasuke ta ambaliya ne suka sami nasarar d'uga akan kyakykyawar fuskar fafin nata.
Hakan kuwa yayi dede da Jan wata kakkarfar ajiyar zuciya da yayi kana alokaci daya yake bude idanunsa wanda suka sauka akan kyakykyawa Kuma kamilalliyar fuskar yartasa.
hannunta ya kama, wanda jin haka yasa ta farga da farkawar fafin nata.
cikin wani mabayyanin farinciki ta fada jikinsa tare da kankame shi tamkar za'akwace matashi.

cikin dariya dariya kuka kuka take cewa !"fafina katashi? dama nasan bazaka tafi kabarni ba nasan kanasona kana tausayina baza kabarni ni daya ba fafina.
yunkurawa yayi dan yana san tashi da sauri ta kamashi ta temaka masa yatashi tsaye, shafa kanta yayi yace jeki sallah bintu nima bari nayi alwala,
a'a fafi muje na temaka maka kayi alwalar jikinka babu karfi bintu ta fada cikin tausayawa mahaifinnata.
girgiza mata kai yayi yace!" kiyi naki lokaci Yana guduwa ni zan iya karki damu,
to haka dai ta hakura badan tasoba gani take Kamar idan ya fita baze dawo ba hijabinta tasaka
tare da daidaita nutsuwarta kana ta funkanci alkibla.

Bayan sun idar da sallah ne sukayi karatun alkur' ani kamar yanda suka saba sannan ta bude haddarta tayi bayan yaji ya kara mata a inda yanzu tana kokari cika izufinta na hamsin da uku.
ahankali ta mike ta mayar da kur anan inda suke ajiyewa ta dawo ta zauna agabansa tare da sunkwi da kanta saboda hawayen dasuke kokarin zubo mataasannu ya sa hannunsa ya dago fuskarta Yana me kada mata kai alamun kar tayi kuka haka nan ta daure ta hadiye shi.
acikin kimtsatstsiyar murya da kokarin nuna mata babu abinda yake damunsa. yace mata!" fadima me yasaki kuka ? ko kinyi zatan na mutune ? da sauri ta gyada Masa kai Tana kokarin danne kukan dakesan kwace mata.
murmushi yayi me cike da ma'anoni masu yawa, kana yace!" to kiyi hakuri ki dena kuka ko babuni akwai me temakon ki, cikin sauri ta kalleshi hawayen da takasa hana zubarsu suna tsiyayowa tace!" fafi waye yake da gwarin gwiwar temakona bayan kai? yace !"Fatima akwai shi Allah ne ze turoshi da sauri ta katseshi da cewa !" a'a fafi kana sani Ina cire tsammani, kana sani inaji araina na kusa rasaka fafi inajin tsoran faruwar wani abu ni banaso ka tafi kabarni a duniyar Nan me cike da azzalumai marasa tsoran Allah .

Jawo ta jikinsa yayi yana bubuga bayanta alamun rarrashi shikaÉ—ai yasan taskun da yake ciki rayuwarsa tana cikin barazana baya san tashin hankalin fatima kokari yake yana 'boye mata, dan yasan ita din me rauni ce tabbas yasan shi bame tsawan rayuwa bane zuciyarsa Tana cike da tsananin fargaba akan rayuwar salihar yartasa yana addu ar Allah ya cigaba da rufe idanun makiyansu akan salihar yartasa.

**************

Abuja

Alhj Balarabe estate
zuri'ace guda babbar zuriya wadda tayi suna acikin fadin kasashen duniya.
zuri'ace wadda zamu iya kiranta da zuriyar ban kashi zuri'ace ta tushen larabawa, amma' yanzu saboda aurataiya, an cakudata da wasu yarirrikan da kuma mutane ma banbanta ahalaiya da dabia ...

Dan Kari har yanxu ba afara wasan ba. akwai, abubuwa masu tarin alajabi ,tausayi, bakin hali,
Jarumta SADAUKARWA da Kuma KUDURAR ALLAH se uwa uba soyayya me taba zuciya dasa mutum cikin shauki
Shin Wai waye fatash?
Wacece fatima ?
Meye asalinsu ita da fafinta?
Ina mahaifiyarta ?
Meye akunshe aziciyar fafi?
Wai suwaye makiyansu shida diyarsa?
Wacece abigel ?
Me danta fatash yayi da har ya jefa rayuwarta atashin hankali ?
Me pastor James yake nufi da kalamansa na cewa duk wanda yase rariya yasan zata zubda ruwa?
Sannu sannu bata Hana baya ns zuwa duk zaku samu amsoshinku daya bayan daya ku dai kuci gaba da bibiyata tare da sambado comments danshi ze bani kwarin gwiwar cigaba da rubuta wannan littafin me cike da abubuwa masu tarin yawa

Ina jiran comments kafun naci gaba da gashi......

Fatima yusha'u adam
*KUDURAR ALLAH*

*NA*

*Fatima y Adam*

Free book.

*page 2*

__________________________

Bismillahirrahmanirra

Dajin me tsananin, duhuwa da dogayen bishiyu, babu abinda zakaji se amon muryar !" nan,wanda hakan yasa dajin yake wani irin gigiza bishiyu na, kadawa, tamkar iskar damuna.
Sautin muryar nan ba daga ko Ina yake fita ba," illah cikin gidan Dake cikin tsakiyar dajin nan, shi daya kwallin kwal.

Abun mamaki, acikin gidan babu wasu kayan kawa, banda wasu muggan ababan tsoro.
duk 'ban garenda da ka kalla to akwai' abin da zakayi tozali dashi wanda ze kusa sa numfashin ka wuyar fita.

Mutanene wanda akalla zasukai kimanin su ashirin,kowan' nen su
Yana sanye da jan zani da kuma 'kwarya, ahannunsu, suna durkushe akan gwiwowinsu, babu me 'kwa'kw'kwaran motsi acikinsu dan sunyi amanna da abinda suke aikatawa shine ze basu nasara arayuwarsu.

Shugaba azikwi Wanda shine yakasance shugaba acikin, kungiyar,
Zaune yake Kan kujerarsa ta mulki, fuskar nan tasa, babu kyan gani
gaba daya ya juye ya koma wata irin mummunar halitta, shi ba mutum ba Kuma ba dodo ba , ita kanta kujerar mulkin da kafar mutum akayita haka ma hannayen ta na mutum ne.

Kai jama a idan daranka kasha kallo.

Cikin wannan katuwar muryar ya bude baki !" se ga wani irin hayaki na ciccidowa tamkar
hayakin turare.

A haka ya Fara magana !" cikin daga sauti Wanda hakan yake nuni da Yana cikin tsananin fushi.

'Yace " haka dama mukayi daku ? bance ku kashe shiba? lallai kuwa to kusani, tun wuri d'an zaki ya riga ya girma , kunyi sake kunyi sakeeee" ya 'karasa fada cikin wani irin mummunan sauti, wanda hakan yasa gidan, da dajin suka Fara wata kakkarfar girgiza.

Mutumin Dake fuskantar shugaba azikwi wanda yayi kokarin Fara goge!" zufar da take ta faman keto mashi tun Fara jawabin shugaba.

Cikin tsananin rudewa da tashin hankali mabayyani
Yace !" shugaba atemaka asamo mana mafita ayi mana afuwa akasi, akasamu' amma' tabbas, mun kasheshi.

Wata irin tsawa shugaba 'azikwi yayi masa yace!" da da' akwai mafitar da' hankalina ze tashi ne? nayi iya'yina amma' nakasa ganin komai se tsananin duhu dodo jack, ma yayi fushi dan be taba,
haduwa, da irin wannan matsalar ba.

Yaci gaba da cewa!" tabbas nashiga rudani. wannan ba, karamar matsala bace dole se munyi wani abu akan wannan gagarumar matsalar."

Gurin yayi tsit bakajin motsin komai se na ka'dawar da bishiyun dajin,sukeyi saboda razanin da muryar shugaba azikwi ya jefasu
aciki.

na kusa da wanda yay magana! afarko shine cikin tsananin biyayya yace ! "shugaba ayi Mana afuwa agafarcemu asamo mana fafita kasan komenene zamu aikatashi indai akan samun masarar mune.

Yana rufe bakinsa wata kakkarfar guguwa ta taso
gaba daya ta shiga zagayasu se da akadauki
kusan mintuna biyu, sannan guguwar ta bace,

Shugaba azikwi, ne yashiga babbaka wata mahaukaciyar, dariya wadda ta Kuma hargitsa jejin gaba daya tsuntsaye
da namun jejin suka firgice kowa yashiga nemarwa rayuwar sa da dauki.

Saida ya gama mummunan dariyar tasa,
kana yace! " yayi dodon mu me share mana kukan mu bama taba shiga matsala baka, kawo mana mafita ba,
mukuma munyi maka alkawarin baka duk abinda kanema awajen
mu."

Juyawa yayi ya fuskanci ,
mutanensa sosai gami da dayin wani shu'umin murmushi,wanda ya Kara munana fuskartasa,kana yace!"muna mika godiyarmu ga dodo jack,
domin yakawo mana mafita bisa ga matsalar da Muke kokarin, antayawa' amma' Kuma akwai manyan sharadai,
yaci gaba da cewa zamu bawa dodo jack jinin jarirai da yanmata da samari , dan haka kowannen mu ze kawo way'annan mutanen guda biyar biyar ragowar sharadan kuwa bani ne zan fada muku ba dodo ze fadawa kowa aikin da ze masa.

A tare suka Mike suna wasu irin surutai !kowa da kwarya ahannunsa suna me É—aukar alkawarin zasuyi biyayya ga dukkanin abinda aka' umarcesu.

Acikin tsakiyar daren, ruhikansu suka koma zuwa gangunan jikinsu ,
Babu wanda zesan ba, mutum' amakwancinsu kasancewar kowannen,
su gangar jikinsa na shimfide amakwancinsa...

Bauchi

Firgigit tafarka Tana Mai nanata "innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un"
amatukar tsorace take da wannan' mummunan mafarkin da tayi aduk mafarkan da take Babu wanda yafi munana Kamar wannan,
fargaba tashin hankali tsoro sune suka taru suka mamaye zuciyarta.
dafe kahon zuciyar ta tayi saboda ji takeyi tamkar zasu Faso kirjinta su fito.

Da gudu ta fito daga dan matsakaicin dakin nata duk da cewar dare ya tsala 'amma' hakan be sa taji tsoran fitowa ba.

Dakin fafi ta nufa zuciyarta na wani irin bugawa da karfi cike da
tsananin fargaba ta tura dan langa langar da akayi makari dashi.

Sallama tayi can kasan makoshinta.
da wani irin hanzari ta karasa inda ta hangoshi ayashe tamkar wanda yay danbe, cikin tsananin razana da kuka take jijjigashi tare da cewa!" fafi fafi katashi me yasameka? me'akayi maka ? baka da lafiya ne? dan Allah fafi katashi
wayyo Allah na dan Allah fafi katashi karka tafi kabarni , Ina zanje? waye ze tallafi rayuwata ? kaddara karki biyo mun ta wannan hanyar karki rabani da bangona, rayuwata zata lalace.

Gaba daya ta rude bata cikin hayyacin ta sambatu kawai take zubawa kasancewar ta yarinya me kana Nan shekaru gaba daya takasayin wani tunani me kyau dan akiyasi baza ta wuce
sha shida zuwa Sha bakwai ba.
Chapter 2 · 0% Book details