Sashe 30
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shiru inno tayi kanta a ƙasa babu wanda ya fahimci halin da take ciki,Farida ce tace"amma Bintu kin shammace mu ko da ba shiri muke dake ba amma bantaɓa yi miki kallon ɓarauniya ba!'sai kuma gashi ta bamu mamaki!'cewar Nabil da yake ta watsa mata mugun kallo,cikin ƙanƙanin lokaci Bintu ta fahimci inda zancen nasu ya dosa,suna dai nufin suce A ɗakinta aka gano sarƙar, to tayaya kenan?katse mata tunani Taufiƙa tayi da cewa haba Bintu tayaya zaki ɓata rawarki da tsalle tunda inno tayi mana faɗa naji A raina ban kyauta miki ba abinda mukayi miki shiyasa ma har na nemi kusanci dake saboda kwaɗayin kyawawan halayen ki,ashe kuma duk zatone!' A hankali take takawa har ta ƙara sa gaban inno ta durƙusa, cikin tashin hankalin da ta daɗe bata fuskanta ba A rayuwarta tace" inno ki ɗago dan Allah ki dubeni, zama tayi daɓar A kasa yayin da wasu zafafan hawaye suka shiga yi mata ambaliya,cikin san fidda kanta daga zargi ta riƙe ƙafar inno cikin wata irin murya me sawa mutum kasala saboda tausayi tace" inno ki yadda dani bantaɓa sataba bantaɓa ji A raina zan iya ɗaukar A bin wani ba bare kuma naki, wallahi inno bani na ɗauka ba! yadda inno take bata motsaba shine abinda ya kuma tayar wa da Bintu hankali,komawa tayi ta riƙe ƙafar Rahima ka tamau cikin wani irin ƙaƙƙarfan kuka take cewa,Rahima dan Allah ki gayawa inno bani bace wallahi ban ɗaukaba!' Rahima tasa hannu ta ture Bintu gami da matsawa gefe,tana share ƙwallan da suka cika mata idanu,tanajin Bintu har cikin ranta sai dai kuma wannan abinda tayi ya matuƙar sosa zuciyarta,ba wani ne ya shiga ɗakin Bintu ba balle taƙi yadda ita da hannunta ta zaro sarƙar A ƙasan katifar Bintun,dan haka bata da bakin yin musu ita ganauce ba jiyau ba.
Ganin yadda Rahima tayi mata yasa taja gefe tana ci gaba da wani irin kuka mai tsuma zuciya,ta riga ta saddakar bata da fita bata da bakin cigaba da musan tawa tunda waɗan da take tsammanin zasu saurareta su goyi bayanta suma sun yadda da abinda ta aikata to meye amfanin maganar kawai ta miƙawa Allah ƙadiran wamaridan sarki buwayi gagara misali komai shi kawai take neman ɗaukinsa.
A hankali inno ta tashi ta bar falon,batare da tabari ta haɗa ido da Bintu ba,inno tana shigewa Bintu ta kuma fashewa da kuka harda bubbuga ƙafa,Farida ce ta kallesu tare da cewa guys wai me muke jira ne ai zaman ɓarauniya ba zai yiwu A cikin estate ɗin mu ba dan haka kawai musan nayi da ita!'tana rufe bakinta gaba ɗayansu sukayi kan Bintu Rahima ce kawai da Amna suka kasa taɓuka komai jikinsu A sanyaye yake,kafin Bintu tayi wani motsi sun rufar mata da duka yayin da suke janta kamar ta barma suna ƙoƙarin fitar da ita daga falon duk girman falon nan da tsayinsa haka suka dinga jan Bintu tana kuka tana musu magiya amma sam basu saurare ta ba har sai da suka dan gana da bakin ƙofar falon, ɗagata sukayi suka jefata waje,runtse idanunta tayi tana jiran ganin ƙudurar Allah A kanta.
Wurgatan da sukayi yayi daidai da tsayuwar shi a kofar falon dan haka tuni Bintu ta samu kariya daga faɗuwa A cikin faffaɗan ƙirjin sa,wanda jin ƙamshinsa yasa ta ɗago manyan idanunta da suka rikiɗe suka koma wata kala saboda tsabar kuka,tana ganin sa mai makon ta ji tsoro kamar yadda ta saba sai dai ma wata raruma da takuma kai masa yayin da ta kwantar da kanta kan kafaɗarsa ta zagayo da hannunta ta riƙe shi ƙam tana mai cigaba da sakin wani wahalallan kuka.
Gaba ɗayan su sun kasa motsi daga inda suke bakamar Taufiƙa da Hauwa'u basu taɓa zaton zai iya dawowa A wannan lokacin ba,wani irin kallo yake musu mai wuyar fassarawa hatta da su Sayyid jikin su rawa yakeyi balle kuma su manya Farida da har yau bata mata da kaifin hannunsa A kan fuskarta ba,haƙiƙa dukkan su tsoro ya cika musu mara duk da suna da tabbacin shima idan yaji abinda Bintun ta aikata zai iya hukuntata,ganin ya motsa ne yasa suka shiga darewa suna bashi hanya,batare da ya janye Bintu daga jikinshi ba yashiga takawa,cikin nutsuwarshi da kamala har ya dan gana ga kujera,sai A lokacin Bintu ta farga da Abinda ta aikata cikin sauri ta sake shi kana kuma A hankali ta zame ta zauna A gabansa tana cigaba da sakin kukanta dayake yi mata matuƙar daɗi,haɗe hannunsa yayi waje guda ya shiga matsasu yayin da su kuma suka dinga bada wani sautin ƙara ƙasss ƙasss,cikin sanɗa suka shiga ƙoƙarin barin falon sai dai hakan bata samu ba saboda jin sautin muryar Abdallah cikin wani irin yanayi,yana cewa kar wanda ya sake ya bar falon nan!'kamar ansa inji an tsayar dasu haka duk suka koma suka ƙame A guri ɗaya,Nabil ne yayi ƙarfin halin yi masa bayanin abinda ya faru,jin yayi shiru tare da zubawa Bintu lulu eyes ɗinsa shiya basu ƙwarin gwiwar,cigaba da rattaba masa bayani,Bintu kallonsa itama ta shigayi da tsoratattun idanunta tana mai zubda hawaye ta rasa bakin magana komai ya ƙare daga bakinta bata da wani sauran kalami,
Ɗaga musu hannu yayi alamun su saurara masa, miƙewa yayi tsaye ya cusa hannunsa cikin aljihun wandonsa, A hankali ya shiga ta kawa cikin nutsatstsan takunsa mai kama da takun sarakai,har yazo tsakiyar falon kana cikin kakkausar murya yace"ina mai ja muku kunne da kuma babbar murya duk wanda na ƙara gani ya bugeta wallahi wallahi!' wata irin ƙwafa yayi kana ya juya yabar falon, daga su har Bintun binsa da idanu sukayi,summ summ kowannen su yabar falon jiki A sanyaye amma bawai dan sunyi na dama ba,
Bintu cikin tsamin jiki ta koma ɗakinta bayan tayi wanka tayi salla ta jawo wayar ta kira ta dannawa Hajiya ladidi,tana shiga kuwa ta ɗaga,ji tayi Bintu ta fashe mata da kuka,cikin tashin hankali tace" shikenan tamu ta ƙare Bintu me ya faru?da ƙyar ta saurara da kukan da takeyi kana ta zaiyanawa Hajiya ladidi abinda duk ya faru,cikin tsananin fusata Hajiya ladidi tace"kintabbatar dai bake bace ba ko? Bintu tace" wallahi Hajiya ban taɓa sata ba tunda nake A rayuwata!'to yi shiru ki kwantar da hankalinki,ki cigaba da walwalarki kamar da zanyi magana da inno ɗin wannan aini suke san yiwa,dan salam iskanci so suke kibar gidan kenan to dan ƙaniyarsu sai dai uwayensu da ubayensu su bar gidan amma bake ba sai mun kai ƙarshen manufar mu ina ai dasaura tukun bayanxu ba.
Cikin nutsuwa ta gama haɗa masa break , zama tayi har ya gama karyawa yana sane da ita amma yayi kamar bai sanda ruwanta A gurin ba, A hankali ya tashi bayan ya kammala karyawarsa, zuwa yayi zai wuce ta, da sauri ta tare sa cikin kukan dayake son kufce mata tace"Dan Allah kayi haƙuri!'cike da mamaki yake duban ta,ganin kamar bai fahimci abinda take nufi ba yasa ta kuma marai raice fuska cike da san ya fahimceta tace' nifa banice na ɗauka ba, wallahi bantaɓa sata ba Ni bani bace"ta ƙarasa faɗa cikin sanyin muryar ta da haryanzu bata dawo daidai ba saboda kukan da tasha,dafa kansa yayi yanajin shikam baƙaramin takura masa akayi da zaman gidan nan ba, abinda baya cikin halinsa an sashi yinsa yanzu,shida bai damu da kowa ba bai damu da shiga sabgar kowa ba, amma tunda tazo gidan take sashi waɗan nan ɗabi'un,kome yasa ma yake yawan tausaya mata oho, amma dai yana ganin fita zaiyi daga sabgarsu suje koma me zasuyi mata suyi mata,dan A gaskiya yana takura da wannan sabuwar ɗabi'ar ta yawan magana tunda shi bai saba ba,(Malam Abdallah kenan A hakan shine kana yawan magana)kaucewa yayi zai fita,cikin kukan ta tace kaima baka yadda dani ba,inno bata yadda dani ba Rahima bata yadda dani ba duk masu sona basu yadda dani ba to Ni ya zanyi?ɗan dakatawa yayi kana cikin gajiyawa yace" sai kiyi yadda kikeso,ba dole su miki haka ba me inno tarageki dashi da za ki ɗunguma mata gagarumar sata haka? yana gama maganarsa yayi saurin barin falon gaba ɗaya.
Wani irin yarfa hannu tayi gami da zubewa A gurin, hannunta tasa tashi ga mussike idanunta dasuka ƙi daina zubar ruwa,haka nan takejin wani mugun tashin hankali,to wai meyasa bata bi bayan inno ba sai shi? meyasa takeji A ranta yaddarsa kawai take buƙata A halin yanzu?kukan ta kuma fashewa dashi tana murza ƙafafuwan ta bisa tattausan carpet ɗin dake malale A tsakiyar falon,cikin dasashshiyar muryarta da babu sauti take cewa,kai kam meyasa ba A fahimtar zuciyarka bazakamin magana kafahimtar dani ba?Ni bazan iya gane abinda yake ranka ba,dan Allah-dan Allah meyasane? A nan bacci yayi awan gaba da ita batare data shiryawa hakan ba.