Sashe 101
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zuba mata ido yayi yayin da yake zaune bisa kujerar dinning table,shigarta,da nutsatstsiyar kwalliyarta da babu hayaniya, ƙamshinta da yanayin takunta shi ya fi tafiya dashi,A hankali ya lumshe idanunsa tare da kwantar da kansa jikin kujerar,jinta dafdashi yasa shi ƙara buɗe idanun yana binta da wani irin kallo wanda ita kuma yake karya duk wata laka dake jikin ta,zama tayi tana bin jerin kwanayen abin karin dake kan table ɗin da kallo,zatayi magana ya rigata da cewa,inno da Hajiya Babba ne suka aiko dashi!'ya faɗa idanunsa na kanta bai ko rissuna su wajen kallon nata,ƙasa tayi da kanta tana jan yatsunta,ita kam ta rasa wannan kallon ko na magani da meyene?katse mata zancan zuci yayi da cewa,ki zuba mana ina saurine!'tashi tayi ta fara saven ɗin sa kana ta zuba itama,yunwa take ji dan haka ba ta tsaya nawa ba ta zage ta cika cikinta,shi dama Abdallah ba baya bane wajen bawa ciki haƙƙin sa,sai da suka gama kana suka fita falon inno,azaune suka sameta ita da taufiƙa wanda rabon da Bintu ta ganta har ta manta, Abdallah kuwa baima shaida ta ba,amma ita idanun ta tamkar zasu faɗo wajen kallon sa,har sai da Bintu ta samu kanta da zabga mata harara,gaishe da inno yayi,ya na gyara zaman agogon hannun sa, Bintu kuwa zuwa tayi jikin innon ta kwanta tana zuba mata shagwaɓa,inno tace"nikam zaki ƙarasani ne? jikina ba irin na mijinki bane mai ƙwari!'ta faɗa cikin dariyar farin cikin ganin su cikin walwala,tura baki Bintu tayi ba tare da tace" komai ba sai idanun ta dake kan Abdallah da take ganin kamar yana kallon Taufiƙa,kawai ji tayi idanunta sun kawo ruwa wanda kuma bata san dalilin hakan ba,Muryar Taufiƙa ta tsinkayo tana gaida Abdallah, ai ko da sauri ta kuma maida hankalinta kansa dan taga yadda zai karbi gaisuwar,amsawa yayi yana ƙoƙarin ɗora waya A kunnen sa,duk da taga yadda yayi amma hakan baisa taji nutsuwaba,juyowa yayi yace"da inno zamu fita amma bazamu jima ba!'inno ba ta tsaya tuhumar inda zasu ba,tayi musu fatan nasara,tashi Bintu tayi ta bi bayansa tana jin kamar ta tsinkawa Taufiƙa mari,Wanda ita kuma Taufiƙan fiye da haka take ji akan Bintun,duk sanda zata ga Abdallah to kuwa sai taji ana ƙara iza wutar san sa a zuciyarta,dan ma bata nan kwana biyu ita da Siddiqa da tasan abin sai yafi haka yawa azuciyar ta.
Yana kula da yadda Bintun ke ta faman cin magani,saboda duk wani motsinta akan idanun sa ne,shi dai bai ma gane Taufiƙa ba bare ya gane dalilin hararar da Bintu ke antaya mata,shiga mota sukayi duk da yaso yashiga ɓangaren Hajiya Babba da Alhaji Baba Amma hakan bai samu ba sakamakon saurin da yakeyi,Bintu na ƙoƙarin shiga suka haɗa idanu da Anty Nafisa,ɗauke kai tayi tare da rufe ƙofar,tana mai ci gaba da kallon Anty Nafisa ta cikin baƙin glace ɗin window motar,sosai ta hango tashin hankali kwance kan fuskarta da kuma asalin mamakin da ya rufeta wanda Bintu bata san na meye ba,ji tayi ya jiyo da kanta saitin sa,cikin al'adar sa ta dage gira yace"Ni zaki kalla ba itaba!' so tayi ta harareshi saboda haushin sa da tasamu kanta da ji,amma sai taji baza ta iyaba hakan ne yasa ta juya hararar zuwa wani irin kallo na musamman da bata san ta iyashi ba,kuma batasan halin da yasaka wanda aka yiwa kallon ba,kawai dai taga ya koma ya kwanta sosai yana ɗan lum-lumshe idanunsa tamkar wanda yake shirin komawa bacci,A hankali ta tsinkayi Muryar shi yana cewa,me haka Bint?me nayi Makine?ita zaton ta fushin da takeyi yake tambaya,dan haka sai ta kuma tura ƙaramin bakinta tana magana ƙasa ƙasa,ba waccen Taufiƙan ce take ta kallon ka ba!'sam Bint bata fahimci komai akan abinda tayiba hasalima bata san manufar yin hakan ba,buɗe ido yayi sosai yana kallon fuskarta dake a kwaɓe da alama dai har yanzu da haushin abun atare da ita,dogon hannun sa yasa ya jawota jikinsa gaba ɗaya,ya kuma haɗa fuskarshi da tata,ba tare da yace"da ita komaiba,sai numfashinsa da yake saukar mata kan fuskarta,kwantar da kanta tayi sosai tana jin abinda ya tsaya mata na sauka A hankali,sai kuma ta shiga fitar da numfashi mai ɗauke da manufar samun nutsuwa.
Hajiya zulaiha dake tsaye itama ta lumshe idanun ta tare da cewa,insha Allah ka kusa dawowa gareni,inajin haka ajikina,tun sanda na fara ganin Abdallah nake jin wani abu game dashi wanda nake fata ya zama gaskiya!'Rahima dake bayanta tace"Ammi kamar me?kuma dama baki taɓa haɗuwa da Yah Abdallah ba tun tsawon zaman shi agidan?Hajiya zulaihat tace"ban taɓa haɗuwa dashiba ban taɓa ganin sa ba,sai a daren jiya da suka dawo akan idanuna!'Rahima tace"wallahi Ammi nima inajin kwatan kwacin abin da kike ji,to komeye dalilin hakan?kama hannun ta tayi suka shige falon tana cewa,Rahima Allah ne masani shi kaɗai yasan abinda ke ɓoye,sai dai muyi fatan duk abinda zai biyo baya ya zama Alkhairi!'..
Cikin wani irin tashin hankali da sauri mai haɗe da gudu ta koma ɓangaren ta, cikin karkarwar jiki ta zaro wayarta daga jaka har tana neman faduwa,wajen kira ta shiga ta nemo nomber da zata kira,wayar sai ƙoƙarin faɗuwa take saboda yadda jikin ta ke rawa,da ƙyar ta samu nasarar karata a kunnen ta,sai da ta daɗe tana ringin har ta kusa tsinkewa kana aka ɗaga,Ya dai Hajjaju aiki ya samu kenan?cikin wata irin muryar da take nuni da tsananin tausayin kanta tace"wai mai yasa bani da sa'a ne a rayuwata?me yasa duk abinda na saka agaba sai ina murna na kusa cimma shi sai ya kufce daga gareni?me yasa nake haɗuwa da mayaudara ma ha'inta acikin dukkan sabgata?dariya yayi kana ya shiga bata amsar tambayoyinta,da cewa abinda yasa baki da Sa'a saboda waɗan da kike neman sa ar halaka su basu da alhakin cutar da kowa ballan tana ke, sannan kuma abinda yasa duk abin da kika kama yake kufcewa daga gareki,saboda ba dan kyakykyawar manufa kika riƙeshiba,amsar ki ta ƙarshe itace" saboda kema mayaudariya ce kuma maha'inciya maci amana, dan haka babu ta yadda za'ayi kiyi abota da mai gaskiya da amana dole sai irinki!'ya ƙare da cewa, Hajjaju meye aikin ki? cikin wani irin baƙin ciki da ɓacin rai ga kuma damuwa tace"mai kake nufi da waɗan nan maganganun naka?yace"Hajjaju ke nan nifa tambayata kikayi kuma na baki amsa,kuma kema kinsan gaskiya na gaya miki,kawai dai dan mun kauce ne amma ko yau muna fatan shiriya!'babu yadda zatayi da wannan taƙadirin dolene idan tana so ya bata amsar abinda take nema agurinsa sai ta haɗiye fushin ta,dan haka cikin ƙoƙarin maida mugun fushi da haushin sa da takeji tace"aikin da na baku ba kunce kun gama dasu ba?kai Hajiya Nafisa yaza ayi ki dinga dawo mana da aiki baya,bayan har shaida sai da na turo miki,ki daina haufi akan aikina,ko kinga wani kuskurene?a jiyar zuciyar samun ƴar nutsuwa tayi kana tace"yarinyar da kuka turomin hotunan ta na gani yanzu acikin gidan nan,ita me yasa baku kashe ta ba?yace"sai dai idan lokacin da muka gabatar da aikin bata cikin gidan wannan itace amsar ki,kin gama ina da abinyi yanzu?shike nan dama abinda zan tambayeka ke nan!'kashe wayar sa tayi tare da cire layin ya taune shi kana ya haɗiye,yana cewa,bazaki ƙara ganina ba a rayuwarki har abada,ita kuwa Nafisa baƙaramin kwanciya hankalin ta yayi ba,tana ganin Bintu koda bata kasheta ba bazata bata wata matsalaba,tunda babu wanda yasan ko ita wacece,duk da ko ita har yanzu bata tabbar da abinda take zargiba..
Tun daren jiya baiyi bacci ba,duk inda ya juya tashin hankali yake fuskanta,yanzu abinda su shugaba zasuyi masa kenan? duk yadda aka daɗe ana gwagwarmaya tare,amma shine yanzu zasu juya masa baya har da ƙoƙarin razana rayuwarsa,juyawa yayi ya zubawa gurin da yake idanu duk da ba gani yake ba saboda tsananin duhun wajen,yanzu ɗan ɗan uwansa ne ya jefashi cikin wannan halin?abinda zuciyar shi ke ta tambayar shi ke nan,ji yake tamkar yasa hannu aka yayi ta zunduma ihu,abin duniya ya dameshi,zuciyar shi tamkar ana babbakata da wuta haka yakeji,sai dai kuma sam har yanzu babu alamun nadama atare dashi sai hanyar kuɓuta da samun cikar buri.
Zubawa kyakykyawar fuskar ta idanu yayi wanda sam baya gajiya da kalla,A hankali yayi magana cikin miskilar muryar sa,yace"sleeping beauty wake up!'ya faɗa yana ɗan taɓa tattausan kumatunta,buɗe idanun ta tayi wanda suke cike da baccin da Bai isheta ba,ɗage mata gira yayi tare da cewa,yarinyar nan na kula sam bazaki iya kwanan zaune ba!'a hankali ta zame daga jikin sa tana ɗan bin farfajiyar gidan da kallo,dawo da kallon tayi kansa tana shirin tambayar sa,nuni yayi mata da su fita kar tace komai,dole ta haƙora da abin da take son cewa suka fita daga motar,kai tsaye cikin falon suka nufa,bin ko ina takeyi da kallon baƙunta da kuma mutanen da bata san su ba,gaisuwa suke ta miƙa wa ogan su suna haɗawa da gaida Bintu yarinyar da yanzu suka gama gasgata cewar matarsa ce,ɗakin da Abigirl take suka nufa yana rike da hannun Bintu tamkar ance za a kwace masa ita.