Sashe 103
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 57 ```
Bazan iya misal ta muku irin farin cikin da waɗan nan mutane suka shiga awan nan rana mai matukar muhimmanci ba,A hankali sai da suka sanar da Dady duk wani labari da gwagwarmayar da suka sha,abu ɗaya ne bai sani ba Yadda aka saceshi sai kuma labarin rayuwar sa a hannun Abigirl wanda shima yace a bakinta zasu ji,kuka Dady yake da idanun sa kukan bakinciki da ta kaicin zamowar ɗan uwansa da step mom ɗin sa maha inta a cikin zuri'ar su,su waɗan can nasu mai sauƙine,tunda danganta kar bata kai wannan ba,da ƙyar suka rarrashe shi yayi shuru,daga nan suka yi sallama, Bintu tace"Dady sai gobe zan dawo!'Abdallah ya harareta tare da cewa bazaki kuma fitowa ba,saboda shima goben nake son mai dashi gaban tsohon sa!'bata san lokacin da ta ɗane shiba cikin farin ciki tace"yauwa ya Abdallah hakan ma yafi ko Dady tunda dai kasamu sauƙi!'dariya yayi cike da samun nutsuwa yace"hakane ɗiyata ina son ganin tsoffina nima naji daɗin da kikaji!'da wannan suka bar gidan zuciyoyin su fes,
Yaso ya kaita gidan da su Ummi Laila suke,sai dai kuma ya fasa saboda so yake yayiwa Bintu bazata dukan su ma,gashi dama Fafi ma ya samu sauƙi,dan haka kawai sai ya ƙyale Yahya ya maida su estate.
Abba umar ma dai yana can Itali,babu wanda yayi tunanin wani abu akan sa tunda babu wanda yasan abinda Anty Nafisa take kurdawa,kuma kowa yasan shiɗin ba mazauni bane,amma dai shima goben yake shirin dawowa dan san yiwa Nafisan tasa bazatar,(to Allah dai ya kaimu goben nan dan da alama ranar fallasace da fasa muggan ƙwayaye,ranar da zata yiwa wasu daɗi san nan ta zamo wa wasu ranar jin kunya da mozanta a idon ƴan uwa da abokan arziƙi,(nima dai zanso naga goben nan dan kuwa zata zo da abubawa masu yawa na kuka da na dariya mamaki da al'ajabi)
Suna fitowa daga mota suka ci karo da Dady Mansur wanda yake shirin shiga ɓangaren Alhaji Baba,har ƙasa suka durƙusa suka gaida shi, abinda Abdallah bai taɓa yiba,daga Bintun har Abdallah samun kansu su kayi da jin kunyar Dady Mansur ɗin,shima dai kunyar tasu yakeji saboda kasancewar ɗan uwan sa na jini da ya zama azzalumi agaresu,cikin tsananin ƙaunar yaran da tausayin su, ya dafa kawunan su,kana yace"Allah yayiwa rayuwar ku albarka, Allah kuma ya kawo mana ƙarshen duk wata musiba!'Amin suka amsa cikin jin daɗin yadda Dady Mansur ya koma mutum mai nutsuwa,da kama girman sa,yace"ku tashi mu shiga ko ba gurin Alhaji Baba zaku shiga ba? Abdallah yace"nan zamu shiga Dady!'daga nan suka rankaya suka shiga falon Alhaji Baba,shi kaɗai ne a falon yana kallon tashar aljazira hannun sa riƙe da tasbaha,yana ganin su fuskarsa ta kuma washewa da wani irin annuri,hannu ya miƙa wa Bintu da Abdallah yace"kuzo nan kwana biyu kunyi min ƙaura ban san dalilin da yasa hakan ta faru ba!'cikin girmamawa suka gaida shi,kana Abdallah yace"kayi haƙuri Alhaji Baba wasu aiyukane suka shamin kai kwana biyu shi yasa!'ya juya ga Bintu da take ta zuba murmushi saboda yau wani irin farin ciki takeji wan da tasan baya rasa nasaba da samun lafiyar Dady da kuma tabbacin da Abdallah ya bata na bayyanar ummin ta da fafinta akusan nan,yace"Batula ke kuma fa meye uzurinki?da sauri tace"ai tare muke yin komai!'ji tayi sun saka dariya shi da Dady Mansur,yace"wato kun zama ƴan biyu ke nan tare kuke yin komai?sunkuyar da kanta tayi saboda kunyar da ta ɗan kamata, Alhaji Baba yace"to masha Allah hakan yayi kyau!'cikin nutsuwa Abdallah yace"Alhaji Baba akwai alfarmar da nake nema awajen ka!'Alhaji Baba ya gyara zaman sa yana daɗa fuskantar Abdallah da bashi dukkan hankalin sa,kana yace"Abdallah ka faɗi buƙatar ka kai tsaye babu batun alfarma dan nasan ko me zaka zo dashi Alkhairi ne insha Allah!'ɗan kallon Dady Mansur yayi sai yaga ya gyada masa kai alamun ya faɗi abinda yake son faɗa babu matsala,dan haka sai Abdallah ya maida hankalinsa kan Alhaji Baba tare da cewa,dama ina sone gobe idan Allah ya kaimu katara duk mutanen gidan nan acikin falon ka,hatta da surukai ban ɗauke su ba,idan nace kowa ina nufin kowa da kowa sai dai wanda baya nan,ƙarfe huɗu bayan sallar la asar akwai abinda nake son GABATAR muku dashi mai matukar muhimmanci,amma dan Allah acikin waɗanda basa nan ina buƙatar Abba Umar a wan nan zaman saboda zuwan nasa yana da muhimmanci!'jinjina kai kawai Alhaji Baba yake sai da yaji Abdallah ya kawo karshe a maganar sa, kana yace"wannan ba abin damuwa bane Abdallah fatana kawai Allah yajiyar damu Alkhairi Allah yasa taron da zai amfanemu ne baki ɗaya,gaba dayan su suka amsa da Amin,daga nan suka bar falon shida Bintu suka bar Dady Mansur.
Tun bayan dawowar ta daga gidan ta rasa sukuni gaba ɗaya cikin fargaba take,duk motsin da zataji sai ta zabura,ta kasa zuwa ko ina,ta kuma rasa ta hayar da ya kamata ta binciki su Abdallah ko sun gano makircin ta,duk da ko tasamu hanyar baza ta iya aikatawa ba saboda kar taje allura ta tono garma,sallamar Taufiƙa ce"ta dawo da ita hayyacinta,zama tayi akusa da ita tana cewa Hajja me yake faruwa ne naga kamar ba anutse kike ba? murmushin yake tayi tare da cewa bana dan jin daɗi ne kwana biyu!'Taufiƙa tace"ayya sannu Hajja Allah ya sauwaƙe!'tace"Amin tana ƙoƙarin miƙewa ta bar falon dan tafi buƙatar kaɗaici a wannan lokacin,kafin ta kai ga mikewar ta kuma tsinkayar muryar BINTU tana rangaɗa sallama cikin sassanyar Muryar ta,wani irin tsinkewa zuciyar Hajja tayi tare da komawa ragwab ta zauna ba tare da ta shiryaba, duk wan nan tashin hankalin nata baya rasa nasaba da shigowar Abdallah cikin falon ba,yanayin takunsa na isasshen namiji da kuma kwarjinin sa, shine abin da yaso rikita ta da saurin fallasa rashin gaskiyar ta,zama yayi ba tare da ya ce komai ba sai hankalinsa dake kan wayarsa, Bintu ce ta tsuguna a gefan Hajja ta gaida ta,amsawa tayi cikin fara'ar da bata taba yiwa Bintu irinta ba,gaba ɗaya a ruɗe take saboda bata shirya komai akan tuhumar da Abdallah zaiyi mata ba,da ace ba tariga tayiwa Jafar waccen ƙaryar ba ne,to da zata iya samun abin cewa dan kare kanta,shuru falon ya ɗauka sai da Abdallah ya gama shan ƙamshin sa, kana ya juyo yana fuskan tar Hajja tare da gaishe ta,amsawa tayi cikin wani irin bugun zuciya,wanda har mamakin kanta take saboda bata taɓa tsammanin a kwai wani mahaluƙi da zataji tsoron fuskantar sa ba, sai kuma gashi har tana jin fiye da zaton ta akan jikan ta, cikin haɗe fuska da dauke kai yace"Hajja ta ɗan bamu guri!'duban Taufiƙa tayi wadda tasan cewa da ita yake,tace"Taufiƙa tashi ki bamu guri!'cikin sanyin gaddama ga umarnin da aka bata,tace"Hajja mu tashi dai ai naga bani ka ɗai bace a gurin!'wani irin rikitaccen kallo ya watsa mata wanda yasa ta tashi babu shiri har tuntuɓe take ci da ƙafar Bintu,
Tana shiga ɗakinta tayi sufa saman gadon ta,tare da saka wani irin kuka mai sosa zuciya,ko yaushe ne Bintu har ta samu irin wannan soyayya mai zafi daga gurin Abdallah?karfa bakin da inno tayi mata ya tabbata dan kuwa gashi nan ta fara ganin alamu, Taufiƙa sai dai hakuri fa dan daga dukkan alama dai Abdallah ya rufe ƙofa,