← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 120

Sashe 36

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta tura ƙofar tare da sallama,cikin sauri ta ƙara sa gaban gadon,ta riƙo hannun Bintu,cikin tashin hankali tace" subhanallah Bintu baki da lafiya amma baki sanar dani ba? duba jikin ki kamar garwashi!'ɗago kan Bintu tayi ta ɗora kan cinyarta ta shiga shafa lallausan gashin kanta da ya baje har bayanta,cikin tausayi tace" sannu kinji Bintu tun ɗazu nake son dubaki amma ina tunanin ta ya zanyi hakan saboda yaran nan suna tare dani!'Bintu ta kama hannun inno cikin ƙarfafawa kanta gwiwa tace" inno karki damu ai naji sauƙi jiki nane kawai babu ƙarfi shi yasa kika ga ban fito ba!' inno tace" a'a Bintu ga jikin ki nan da zafin zazzaɓi amma kice min lafiya kike bari na duba ko Abdallah ya shigo nace yazo ya dubaki ya baki magani!'ai da jin haka Bintu tayi wata iriyar zabura sai gata zaune tana rarraba ido cikin rawar baki tace" Ni dai inno karki gaya masa naji sauƙi bari ma ki gani miƙewa tayi ta shiga dan tsalle,inno sakin baki tayi tana kallon Bintu cike da mamakin wannan tsoron da takewa Abdallah,kawar da tunanin tayi da cewa ke kam Bintu ban san wace irin matsoraciya bace!' ma rai raicewa tayi tare da cewa Wallahi inno zuwa zaiyi yamin allura gashi kullum fuskarsa A haɗe babu fara'a Ni kawai ki bani magani xan ji sauƙi!'numfashi inno taja kana tace" ai shikenan bari na kawo miki maganin kisha sai ki kwanta idan kika samu bacci zazzaɓin zai sake ki,shi kuma Abdullah bari naje nasamar masa wani abu da kaina ke ma sai ki ɗanci kafin kisha maganin! to inno na gode amma da baki wahalar da kanki ba zan yi masa da kaina!' inno ta miƙe tare da cewa a'a Bintu bana son gaddama ki kwanta ina dawowa!' daga haka tasa kai ta bar ɗakin.a hankali Bintu ta koma ta jingina da window tana mai jin ƙaunar inno har cikin ranta da kowa na gidan nan halinsu yayo ita da sauran kishiyoyin ta da kuma mai gaba ɗaya wato Alhaji Baba da tabbas sun zama abin koyi,wannan shi ake kira da ƘUDURAR ALLAH,

Duk abinda ya kamata inno tayi mata sai da tayi mata ta kuma kaiwa Abdallah haÉ—aÉ—en jalof É—in da tayi masa wanda yaji uban kifi sai gashin kaza da tayi masa mai shegen É—aÉ—i,dan haka yaci abincin duk da dai bakinsa yaji cewar ba Bintu ce tayi ba, dake ya riga yasan É—an É—anon girkin inno sai bai damu ba amma ya É—an yi tunanin abinda ya hanata yin girkin.

Dole washe gari ta sawa kanta ƙarfin jiki ko dan saboda damuwar inno,da kuma gudun allurar Oga Abdallah,sai da ta gama kimtsa masa ko mai kana ta bar falon batare da ta bari sun haɗu ba tun da tasan shi tamkar Aljani yake wajen gano mutum baida lafiya, Abdallah ganin tayi masa karin kumallo yasa ya dai na tunanin komai,cikin sauri ya kammala saboda shima kwana biyu yana cikin busy,

Aunty Samira tace"sir me yasa aka fasa miting ɗin jiya kamar yadda kace? cikin yanayin nutsuwarsa yace"Samira jiya an sanarwa dasu Alhaji Nasir zamuyi mitin hakan ya ƙara tabbatar min da akwai munafiki A cikin mu,dan haka yanzu inaso duk ki kira minsu a kwai binciken da zanyi akan ko wannen mu! ok sir Bari na sanar dasu!'

Kallon su yakeyi ɗaya bayan ɗaya gaba ɗaya su goma ne suke ƴan team ɗin sa, sune Amin tattun da ya zaɓa dan yin aiki dasu sai dai bai san a cikin su wanda ya ke kware masa baya ba, amma dai yana da yaƙinin A cikin ƴan mintuna zai fito da ko ma wanene,ɗan gyaran murya yayi tare da gyara zamansa cikin haɗaɗɗiyar kujerar sa, kana ya fara magana cikin ƙasai tacciyar muryarsa wanda kana ji kasan babu wasa cikin dukan Al'Amuransa,yace"abinda yasa nace A yimin kiranku shine jiya nace zamuyi mitin amma hakan bata samu ba dalilin cin dunduniya da muka samu ɗaya daga cikin mu nayi mana!'shuru yayi tare da zuba musu ido ɗaya bayan ɗaya yana mai karan tar yanayin su,ci gaba yayi da cewa amma kusani na riga da na gama bin cikena A kan wanda yake fitar mana da sirrin mu na kuma gano kowanene!kallon kallone ya shiga giftawa tsakanin su kowa na tunanin waye? yayin da me aikata laifin ya fara fidda kansa wanda dama wannan duk shirin Abdallah ne yayi niyar kama kowaye A hannu shiyasa yay musu wannan hikimar,kuma Alhamdulillah yasamu abinda yakeso dan cikin hikimarsa da basirar da Allah Ubangiji ya fuwace masa ya gano mai laifin a cikin mutanen goma da ya amince dasu,ya ɗan daki table ɗin gabansa cikin wasu sakanni office ɗin yayi tsit,razanan nun idanunsa ya ɗora kan fuskar safyanu yana mai san ƙara tabbatar da zaton sa,mara gaski ance ko A ruwa gumi yake tuni safyanu ya shiga rawar jiki,cikin tashin hankali ya sauƙa ƙasa idanun sa na fitar da hawayen na dama yasan in dai a wannan harkar ne Oga Abdallah baida sassauci yana matuƙar girmama amana da gaskiya,cikin rawar baki ya buɗe baki zaiyi magana amma hakan bata samu ba saboda jin yadda wasu manyan ƙarti majiya ƙarfi suka da baibayeshi tare da sa masa sarƙa,ko su jabir baza suce ga lokacin da suka ga Abdallah yayi waya ba balle shigowar su Majid, kallon su Abdallah yayi fuskar nan babu alamar sassauci yace" ku tafi dashi karku saurara masa har sai na neme ku!'hankaɗa shi sukayi waje suka yi gaba dashi.

Dukkansu nutsuwa sukayi dan babu wanda jikin sa baiyi sanyi ba,sun riga da sun san hukun cin Oga Abdallah ba mai sauƙi bane,sai da yaga ma shaƙar ƙamshin sa kana cikin kakkausar murya yace" ina so duk wanda yasan zai ci amanata A wannan tafiyar salin alin ya fita daga office ɗin nan idan kuma ba haka ba duk wanda na kama da makaman cin abinda safyanu yayi hukuncin sa sai ya nunka nasa sau goma!'shiru yayi yayin da office ɗin ya ɗau shiru na wani ɗan lokaci kowannen su zuciyar sa cike take da tsoro sai dai kuma akwai sadaukar wa tsakanin su saboda suna san ogan nasu,shima safyanu dan badashi aka fara tafiyar bane bai san irin gwagwarmayar da ogan nasu yayi dasu bane,shi yasa har yaci amanarsa.

Dukkanin su sunyi alƙawari da kuma rantsuwa bazasu ci amanarsa ba, kuma zasu tsaya akan tabbatar da gaskiya ko mai runtsi komai wuya,daga nan ne kuma ya sallame su tare da sanar musu lokacin da zasuyi mitin ɗin ƙarfe shabiyu na daran yau in Allah ya kaimu da haka suka rufe tattatunawar.

Haka nan taji tana buƙatar ganin Dide ko da baza ta iya gaya mata halin da take ciki ba to tasan zata iya samun shawara cikin hikima,fita tayi can wajen, lokacin ƙarfe takwas na dare dan saida ta kammala wa Oga Abdallah girkinsa kana ta fito,

A hankali take takawa tana ɗan waige waige wanda har bata ankara ba sai jitayi an fincikota tare da toshe mata baki,A lokaci ɗaya kuma ana shiga da ita ta wani ɓangare wanda A halin da take ciki baza ta iya fahimtar inane aka nufa da ita ba....

Comments.....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 26 ```

Kiciniyar ƙwace kanta takeyi amma hakan ya gagara ƙarfin ba ɗaya bane,ji tayi an wulla ta saman gado bayan an shigo da ita ɗakin, ɗagowa tayi hankali A matuƙar tashe, Sayyid ta gani tsaye A kan ta riƙe da ƙugunsa yana binta da wani shu'umin kallo mai dauke da tarin manufofi,cikin ƙarfin hali ta miƙe A fusace tana nuna shi da yatsa cikin ɓacin rai da tsoron da ke cike taf A ranta, tace" wai me kake nufi dani? me zan maka da kakawoni nan?wani kallo ya bita da shi batare da ya bata amsaba yayi kanta gadan gadan,wani irin tsalle Bintu tayi ta yi hanyar ƙofa sai dai bata samu nasarar fita ba taji ya cafko gashinta, ƙara ta saka kafin kace meye sun fara dambe A cikin tsakiyar ɗakin,tun Bintu tana samun ƙarfin ƙwatar kanta har ya kai gacewa ta kasa kataɓus,har sai da ya samu nasarar kamata ya shinfiɗe ta asaman gadonsa, cikin dariyar mugunta yace" to yarinya me bakin fitsara ya kikaga wannan salon yau zan kwashe duk wani abu da kike ta ƙama dashi,babu mai ƙwatarki A hannun Sayyid Mansur Balarabe!'ya ƙarashe maganar da ɗage mata gira,yana mai ƙoƙarin zare rigar saman dake jikinsa wani irin ƙarfi ne yazo wa Bintu ta samu damar ture sa kana ta miƙe cikin hanzari har garin sauka a gadon tana bige ƙafar ta hakan yasa takasa tashi dan sosai ta bugu,shi kuma hakan ne ya bashi damar kusanto inda take tare da ɗauke fuskar ta da wani gigi taccen mari wanda har sai da bakinta ya fashe kuka tasa mai ƙarfi tare da fara masa magiya, Sayyid dan Allah kayi haƙuri kar ka ɓata min rayuwa Ni marainiya ce duk abinda kake so zan yi maka amma dan Allah kabarni da mutuncina!' jan yo ta yayi tare da hankaɗata saman gadon yana cewa dama kin san bada haƙuri?bakin rashin kunyar har ya mutu ne?to yau saina cimma burina ko mutuwa zakiyi!'kuka take tana yakushin sa da duka ta ko ina amma ina Sayyid yayi nisa baya jin kira ƙoƙarin sa kawai yaga ya cimma mummunan nufinsa A kan Bintu,duk yabi ya gajiyar da ita har yanzu ya kasa samun dama A kan ta amma hakan baisa ya saduda ba tun kukan ta na fita har ya zamana Muryar ta ta dashe baka iya jiyo sautin ta sosai,sun kai kusan awa ɗaya suna abu ɗaya.

Tun da ya dawo ya ci abinci ya shirya,yake jin zuciyarsa na wani irin bugawa,komai yanayin sane cikin sanyin jiki har sai da yasamu ya ɗan yi karatun ƙur'ani kana yaji sanyi a ransa, amma duk da haka ji yayi gaba ɗaya gidan yayi masa zafi,dan haka tun kafin lokacin miting ɗin su yayi ya gama shirinsa tsaf ya zari key ɗin mota ya fita.
Chapter 36 · 0% Book details